Nine
_Katsina_*
A matukar gajiye ta zube a cikin daya daga cikin kujeru na alfarma dake mamaye da falon har kala biyu. Sababbi ne dal, saiti daya yazo daga kasar Saudi Arabia kai tsaye, dayan kuma daga kasar Turkiyya. Kwanansu biyu kacal kenan da zuwa. Duk cikin shirye-shiryen biki da ake ta yi ne.
Ta zame takalmin kafarta baki wanda ya matukar kayata farar kafarta tas, dogo mai tsayi wanda akalla zai iya kai inci hudu ko biyar.
"Wash!".
Ta furta hannu dafe da kanta tana murzawa.
Hajiya Uwani ta daga kai daga kan iPad dake hannunta tana duba wasu kayan kicin da wata kawarta ta aiko mata samfur daga kasar Malaysia.
"Autar Mamarta da Babanta, yaya ne, duk gajiyar ce haka? Daga ina kike?".
Ta yamutsa fuska, "hmm! Daga wajen wancan dan iskan Ali mai dinkin nake mana. Ya ki ya gama yi min dinki tun last week".
Mahaifiyar tata tayi dan murmushi, "to in banda abinki auta, bikin fa sai satin sama, mai kike ci na baka na zuba ne? Idan kika yi hakuri, zai hada ya baki ne. Kinsan mutumin naki na mutane ne".
Ta kara yamutsa fuska, "to ni ina ruwana da wasu mutanenshi? Ni kawai ya gama dinkina ya bani kayana shine bayani kawai. Kin fa san yadda na tsani jira musamman ta fannin dinki. Wai ina Badi ne?".
Tace "abokanta suka zo wai suka tafi duba halls da za ayi bridal shower, daga can su biya ta shagon daukar hoto suyi pre-wedding pics".
Kafin ta daga baki ta mayar mata da amsa, wadda take musu wanke-wanke ta fito daga kicin zata zagaya baya.
"Hanne!". Ta kirata gatsar, cike da gatsali kamar wata sa'ar wasanta. Alhali Hannen ta girme musu daga ita har Badi din.
Da sauri ta matsa kusa da ita ta duka, gabanta na dukan tara-tara. Yadda take tsoron mutuwarta, haka take tsoron taji Fauzah ta ambaci sunanta. Ba ita kadai ba har ma sauran ma'aikatan gidan haka take a garesu. Yarinya ce da bata da kirki ko na anini. Kadan take jira ta maka wankin ta-tas irin na babban bargo, Allah Yasa tsayinka ya kamo na falwaya kuwa, hakan bai dameta ba zata zage ka daga kai har danginka. Hakan ma fa wai idan tayi sa'a ce aka ci. Abu kankani kan iya sanyawa ta maka sanadin aikinka, ta kore ka ba tare da ta ko kifta ido ba.
Taja tsuka tana jefa mata harara, "to menene wai zaki zo ki min wani zekeke a ka? Warin hammata da daudar jiki ya cikawa mutane hanci. Miko min ruwa mai sanyi".
Da sauri ta tashi ta fada kicin, zuciyarta cike da takaici da bakincikin wannan kazafi wanda yafi zafin k'una ciwo da Fauza din ta mata. Cikin kankanin lokaci ta kai mata ruwan. Ta warta daga hannunta, ta bude ta daddaka. Tana gamawa tayi jifa da gorar, sai ita ta bi ta ta dauke taje ta watsar a cikin kwandon shara.
Ta dauki jakarta da wayarta a hannu ta kalli Hajiya Uwani, "Mommy, har sai yaushe ne Affan zai zo ne wai?".
Hajiya Uwani ta daga kai a hankali ta kalleta, "wai Fauziyyah, har sai yaushe ne zaki dau fadan da nake miki akan ambatar sunan Affan da kike yi haka gatsar? Sai kace wani sa'an wasanki?".
Ta turo baki gaba, har tana hadawa da buga kafa a kasan kafet, tace "to wai don Allah meye amfanin ma wani kara Yaya don kawai za'a ambaci sunanshi? Mommy ke ce fa kawai baki san abinda zamani yake ciki bane, wannan ai duk 'old fashioned' abubuwa ne, wadanda aka gama yayinsu. Shi kanshi nasan ba zai so wannan kari akan sunanshi ba".
Hajiya Uwani ta girgiza kai kawai, "to Allah Ya kyauta muku ku duka". Ta mayar da kanta cikin wayarta. Ita kuma ta juya ta wuce dakinta. Tana shiga tayi watsi da duka kayan dake hannunta a tsakiyar dakin, ta fada kan gadonta a ruf-da-ciki.
Tana jin lokacin da Hanne ta shigar mata da takalmin da ta bari a falo, ta kuma sanar mata da cewa abincin rana ya kammala, idan tana da bukatar ci.
Bata ce mata komi ba, sai tsaki data ja.
●
Tunda mai Napep ya ajiyeta a kofar gidan, ta sallame shi, ta fitar da jakar da ta shirya duk kayan da zata bukata a ciki. Yana juya kan mashin din, itama ta juya tana kallon katoton gate din gidan.
Abinda ya kasance ja mai cizawa, ya koma ya zama baki, wanda tsatsa da dukan ruwa ya dafar.
Tun bayan rasuwar Alhaji, gabadaya gidan ya bi ya lalace.
Ta tura kofar ta shiga cikin gidan, tsakar gidan a karan kanta ba zaka taba hada shi da gida mai tsafta, mai cike da rayuwa da zirga-zirga ta mutane wanda ya wanzu shekaru tsiraru da suka wuce ba. Yanzu gidan baka jin motsin komi, sai karan busassun ganyayen bishiyoyi da suka zuba idan ana takawa. Ta ratsa ta tsakaninsu, ta bude kofar falo ta shiga.
Tunanika na rayuwarta ta baya a gidan suka bugota full force, kamar a lokacin suke faruwa. Sai dai wannan karon, dodannin nata basa nan, Alhaji da kullum zaka sameshi zaune akan kujerar daya saba zama akai, Hajja a gefenshi tana yanka mishi kayan marmari ko kuma suna hira kawai, basa nan. Babu ko karan talbijin balle motsin mutane. Isiya da yake zama dasu, baya gidan da alama. Babu mamaki ko ya tafi wajen aikinshi ne ko kuma wajen abokanshi.
Ta ratsa ta cikin falon har zuwa dakin Hajja. Tayi sallama ta shiga.
Hajja ta rasa ina taka saka ina taka raka da ita, sai nan-nan take da ita kamar ta dauki wasu shekaru bata ganta ba, fuskarnan tata cike da murna.
Ta zauna a gefen gado ta cire hijabin jikinta, nadeta tayi ta ajiye a gefenta. Kafin ta juya, Hajja ta ajiye mata farantin soyayyar ayaba (plaintain) -abinda Ameenatun tafi so- da ruwan gora mai sanyi.
Ayabar ta riga tayi sanyi da alama tun da safe ta soyata, amma bata sanyayar mata da jiki ba, ta dauka ta fara ci tana isar mata da sakon gaisuwar su Nana a gareta.
Hirar yaushe gamo suka sha, har aka fara kiran sallar magriba. Hajja ta shiga bayi domin dauro alwala, ita kuma Ameenatu da bata yin sallah, ta mike ta hau tattara dakin da yayi kaca-kaca kamar ba dakin da mutane ke rayuwa a ciki ba.
Hajja data fito daga bandaki ta ja tunga a bakin kofar, "ai fa, dakin zai san Aminatuwa sarkin tsafta ta zo. Allah dai shi miki albarka. Me ake da Huwaila? Yarinya sai dan banzan son jiki da kyale-kyalin kwalliya kamar wata diyar tsohuwar karuwa?!".
Ameenatu bata ce mata komi ba sai murmushi da tayi tana girgiza kai, sam Hajj da Huwaila basa ganin ido da ido. Kullum kaje gidan cikin cece-kuce suke kamar wasu kishiyoyin juna. Ta fitar da duk wasu kaya masu datti, tun daga na sanyawa da kwanuka, zuwa su zanin gado dake kan gadon ta canza da wani.
Tana cikin yin aikin aka dauke wuta. Ta kunna fitila babba, ganin bata kawo haske ba yasa ta kalli gefen da Hajja take zaune.
Tace, "wannan fitilar ta lalace ne Hajja?".
Tace "ko kadan, babu batiri ne dai kuma wajen cajin ya lalace. Yaushe rabon ma da a sanya sabon batiri? Tun wani zuwa da Uwani tayi ta kawo mana".
Ta girgiza kai cike da wani gululun bakin ciki da ya taso mata. Da ace lokacin da Alhaji yana raye ne, da tuni an jima da kunna musu inji. Manyan fitilu masu aiki da caji suke amfani dasu. Gida ne wanda a da, yake cike da yan aiki iri-iri, amma yanzu babu kowa.
Ta hadiye abinda ya tare mata a makogoro, tace "to da me kuke amfani idan an dauke wuta?".
Tace "ai ga tocila din wayata. Kwana biyu ma babu caji a ciki, tunda Huwaila ta lalata waccan, a wajen Isiya nake ara kafin zuwan Uwani sai in fada mata".
Bata kara cewa komi ba, ta warci hijabinta, ta zuge zip din jakarta ta fito da kudi.
"Bari in leka nan waje...", kawai ta iya furtawa ta fita daga dakin.
A kofar gida ta ci karo da Isiya, zaune akan benci yana shan rake. Da yake wajen tar da haske, sakamakon inji da sauran gidaje suka kunna.
Ya tashi da saurinshi yana murmushi, "a'ah, manya-manya maganin yara! Yaushe a garin?".
Tayi murmushi a sanyaye, yana daya daga cikin dalilan da yasa ta tsani zuwa Katsinar kenan. Rayuwar kaskanci da Hajja din take yi a gidan. The very sad reality, that, irin kulawar da suka dinga nuna mata a da, saboda mahaifinsu ne kawai, abin yana matukar taba ranta. Ashe basu dauketa a matsayin mahaifiya ba?.
Tace "dazu-dazunnan nazo Isiya, lokacin da nazo baka nan ai shiyasa".
Yace "kwarai kuwa, na je wajen aiki ne shi yasa. Ina zaki je ne haka?".
Tace "wai da batiri ne zan siyo da kuma cazar karamar waya".
Yace, "to bari in tsallaka nan wajen Jannati sai in samo miki!".
Da sauri ta girgiza kai, "a'ah! Ba za ayi haka ba gaskiya. Ka bari in leka da kaina. Ai babu wani nisa".
Yace "kece dai baki ganin nisan, ki kawo kawai in sayo miki, babu komi wallahi!".
Tasan tunda ya kafe, ba zai kyaleta ba. Don haka ta mika mishi kudin a kunyace, ba karamar kunyarshi take ji a duk lokacin da yace zai je mata aike ba, saboda babban mutum ne. Matarshi daya da diyarsu Fatima.
Ya karbi kudin, ita kuma ta koma cikin gida.
Cikin ikon Allah, tana shiga cikin dakin aka dawo da wuta. Hajja tace, "ya aka yi kika dawo yanzu? Ko kin fasa zuwa ne?".
Ta girgiza kai, "Isiya ya hutar da ni. Shi ya tafi ya siyo".
Hajja tace "Allah sarki, yaron arziki! Babu ruwanshi shi kam. Kullum nan yake zuwa ya wuni idan ya dawo daga wajen aiki, matarshi ma na zuwa nan lokaci zuwa lokaci, watarana ma ki ganta har da abin arziki".
Tace "hmm, sun kyauta kuwa".