Eleven
Tun a ranar talata din aka fara gudanar da shagulgulan biki.
Bayan sun gama hada kayan, an zuba su a mota an tafi wajen walima, suka wuce can bangaren masu aiki ita da Indo suka kimtsa jikinsu. Gidan shiru, duk an tafi wajen walima sai yan daidaikun mutane wanda yawanci duk yara ne.
Can kurya dakin Anty Mommy inda ita da abokanta suke ta yiwa tsinke. Daga Anty Mommyn har abokanta su hudu dake cikin dakin, sun sha ankon wata bugaggiyar shaddar getzner, kai daga ganin yadda take ta zuba sheki babu tambaya kasan cewa ba karama bace ba.
Duk suka katse hirar da suke yi lokacin data shiga dakin suna kallonta. Ta durkusa ta gaida su, duk suka amsa mata, Anty Mommy tace "ashe fa kun zo, Jenny take fada min zuwanku, hidimar baki yasa na manta in leko ku".
Ameenah ta kada kai tace "ai babu komi. Ya hidima da taro? Allah Ya tabbatar da alkhairi".
Tace "ameen. Ya har yanzu baku tafi wajen walimar ba?".
Tace "ai mun baro kayan da zamu sanya a gida saboda bamu yi zaton zamu jima ba, gashi kuma yamma ta fara yi".
Wata daga cikin kawayen Anty Mommy din tace "zancen banza kenan! Yo me zaki canza a haka? Ku kama hanya kawai ku tafi don a haka ma kinyi kyau abinki, ki dan samu kwalli da janbaki kawai ki zizara, nan zaki ga kin fito fes abinki!".
Wata ma tace "ehh, ku shirya kawai. Dama yanzu Eeshey zata dawo ta dauki jakarta data manta, kin ga sai ku tafi kawai!".
Tana shirin ta daga baki ta musa, don ita har ga Allah bata yi niyar zuwa wajen walimar ba, Anty Mommy ta kada baki tace "to kinji, sai ki kama hanya. Ku jirata a nan bakin kofa don kada tazo tayi ta nemanku".
Koda zata sake yin korafi, bata ga fuskar yi ba, dole ta tashi ta fita daga dakin.
Kofar dakin na rufewa bayan fitarta, Anty Mommy ta juya tana jefawa kawarta Hajiya Salamatu harara, "yanzu don Allah aminiya wannan wane irin zubar da aji ne kika min a gaban yarinyar nan? Don ki jawo mana raini, har ki wani dinga cewa tayi kyau a haka? Gaskiya ni fa bana son haka!".
Sauran abokan nata suka sanya dariya har da sakin ihu. Hajiya Salamatu tace "ke fa matsalata dake kenan, shegen kyashin tsiya. Yabon wani ma ba za ayi a gabanki a zauna lafiya ba? Naga ai ita din kamar ta gida ce, tunda ga kamanninta nan da na Badi har ma da Affan sun fita sosai".
Tace "to daga ganin kamanni sai ki dauketa a matsayin diyata ko me? Sanin kanki ne ba kowa ya kan zama dan gida ba sai wanda ya isa!".
Nan ma suka kara sakin wata shewar har da masu shan hannu.
Sai da suka lafa sannan Hajiya Salamatu tace, "amma fa ni maganar gaskiya yarinyar nan ta burge ni da kuma yanayin tarbiyarta, a yanzu da yarintarta da komi ma tayi halin manya ina ga ta girma? Kinga Abdul yana makaranta yanzu amma ya kusan gamawa, da ba don ba ai da nace ina mishi kamu!".
Anty Mommy ta yamutsa fuska, "don Allah ki jiki da wata irin magana marar dadin ji! Yanzu don Allah don annabi me kika gani a jikin yarinyar wannan? Fari da hancin ne suka rude ki hala? Idan ma su dinne ina ce ga Fauza nan? Me zata gwadawa Fauza bayan shi? A hakan ma bani da shakka ko hau fi akan na kanti ne wallahi. Don haka ki ma ajiye maganar nan a gefe, idan an gama wannan bikin amarya ta tare, zan zo in same ki kawata. Yo gida bai koshi ba an kaiwa na waje?! Ga auta ta nan, son kowa kin wanda ya rasa?".
Hajiya Laila ta gyada kai a hakimce, mace ce mai shegen dagawa da fankama, tace "wallahi zancenki dutse Hajiyata. Gwanda ma dai ayi-ayi, mu zo mu kara shan wani bikin!".
Aikuwa me zasu yi idan ba kara daukar wata shewa da guda ba??.
*
Suna tsaye a bakin kofa ita da Indo da wata yar aiki Juma, wata matashiyar budurwa ta fito daga gidan cikin ankon da za'a sanya na wajen walima. Atamfa ce English, fara wadda aka yi zanen circles ruwan kasa mai cizawa, tayi dinkin riga da zani wadanda suka bi shape din jikinta sosai. Tayi nadin dankwalinta mai burgewa, ta dora gyale ruwan zuma akan kafadarta wanda ta danne da jakarta vincci mai tsayin hannu ita kuma fara. Yanayinta yafi kama da sa'ar Fauza amma ba Badi ba duk da cewa daga gani ta girmi su Ameenatu din.
Tace "ku ne wadanda zasu je wajen walima?".
Suka ce mata "ehh!".
Tace "to muje, Allah ya taimakeku na manta jakata na dawo dauka".
Basu ce mata komi ba suka bi bayanta har zuwa wajen motarta vibe, ruwan gwaiduwar kwai.
Ta mata key ta bude, Indo ta shiga gidan gaba, Ameena kuma da Juma suka shiga gidan baya. Babu bata lokaci ta kunna motar ta ja.
Sautin kidan wakar 'let me down slowly' ta Alec Benjamin ce take tashi a cikin motar har suka karasa inda zasu je.
Tuni wajen ya cika. Motoci ne birjik a wajen anyi parking, itama Eeshey ta samu waje ta faka tata motar suka fita.
Su kam sai can gefe suka samu suka raba a tsaye. Suna hango inda aka ajiye amarya a tsakiyar wajen, an zaunar da ita akan kafet da su tuntu, ita da jerin abokanta. Yayin da malamai masu Wa'azi suke zaune akan teburi da kujeru. Su kuma masu sauraro sai aka shirya fararen kujerun roba.
Basu jima da zuwa ba aka yi addu'ar tashi. Daga nan aka raba souvenirs, samosa din da suka yi ce aka zuba a cikin leda da lemu, sai abubuwan amfani, wasu tandun zuba humra, wasu kuma kaskon turaren wuta, har da kananun burners. Abubuwa dai iri-iri.
Bayan mutane sun ragu, ita da Indo suka fita da niyar tarar acaba ko adai-daita sahu su tafi. A bakin gate suka sake cin karo da Eeshey da wata a gaban motar.
Ta tsaya a gabansu tare da lekawa ta jikin gilashin motar tace musu, "ina kuka nufa ne?".
Ameenatu ta fada mata, tace "to kuzo in sauke ku mana!".
Tayi saurin cewa "da kinyi tafiyarki wallahi, babu komi ai, zamu samu abin hawa".
Tace "haba, babu komi, ai ba wani nisa ne damu daku ba".
Don haka suka bude gidan baya suka shiga.
Suna tafe a cikin motar, Eeshey, -da sai a lokacin suka san sunanta na ainihi A'isha- suna ta hirarsu da kawarta, jifa-jifa su kan sako su Ameenatun a ciki, sai dai su dan dara kawai. Sai da suka ajiye Indo da gidanta yake anan bakin titi kafin suka karasa gidan Hajja.
Har Ameenatu zata fita, taji Eeshey tana tambayarta, "Ameena kamar baki samu abin rabon ba ke?".
An bata, shima sai da Jenny tayi fafatuka sannan ta samo biyu da kyar ta basu ita da Indo, ganin Juma bata samu ba ta dauki nata ta bata.
Kai kawai ta gyada mata.
Ta bude murfin motar ta fita, ta zagaya ta bude booth din motar, Ameenatu na tsaye har ta maida ta rufe. Ta mika mata ledoji guda biyu, "kinsan mu abokai har na iyaye da kanne aka bamu. Ki dau daya sai ki kaiwa Hajja daya".
Bata san ta ina tasan Hajja ba, sai dai bata tsaya tambayarta ba. Tasan tunda kawar su Badi ce, babu mamaki idan tasan su Hajja din. Tunda yawancin al'amuransu acan suke, kamar idan zasu yi wasu manyan baki, sau tari acan suke ajiye su, ko dan get-together na abokansu ko party, duk acan suke yi.
Sai ta mata godiya ta karba ta shige gida.
Tana tura kofar dakin Hajja da sallamarta, Hajja ta tare ta da sannu, "yanzun nan na kira Indo inji ko kwana zaku yi a can, take ce min ai kina ma kan hanya ke da wata wacece? Ko Ishalle ne tace?".
Ameenatu tayi murmushi, "Eeshey sunanta Hajja, yanzu ta ajiye ni ta wuce gida". Ta mika mata ledar, "gashi ma tace a kawo miki".
Sai a lokacin ta lura da wasu jakunkunan irin na hannunta har guda uku a gefenta, tace "to ai an kawo miki ma".
Ta kallesu, "wannan? Ameerah ce ta shigo dasu yanzu. Sai dazu suka zo ita da yan uwan nata. Su kuma mahaifan ina ga sai ranar daurin aure".
Ta gyada kai a hankali, rabon da taga su Ameerah din tun rasuwar Alhaji, lokacin tun suna yan yaransu. Baqeer ta ganshi a lokacin da aka yi zaman makokin Murjanatu, bayan nan ta kan ganshi a gidan ko taji labarin yazo idan taje Katsina.
Ta maida hankalinta kan kofar bandaki da taji alamun budewa, Ameerah ta fito itama sanye da ankon da aka yi ta walimar, fuskarta da lema da alamun alwala tayi. Suka yi kallon-kallo ita da Ameerah din, kafin ta maida kallonta ga Hajja, kamar wadda take neman wani taimako daga gareta.
Bata taba iyawa da baki ba, bata san ta yadda zata taresu ba. Ko sabon da tayi da rayuwa a inda babu bakin ne, ko kuwa halinta ne? Bata sani ba.
Hajja ta cewa Ameerah, "ga yar uwarki Ameenatu, nasan ai baki mantata ba ko?".
Tayi murmushi wanda ya fitar mata da wasu dimples masu zurfi a gefen bakinta, tace "laaa! Anty Ameenah ce ashe?!".
Ameenah taji wani irin dummm! A jikinta. Bata yi tunanin tarbar da zata samu daga gareta ba kenan.
Ameerah ta cigaba da cewa, "kinsan fa shekarun da yawa, kuma duk lokacin da zamu zo nan sai dai ace taje ko kuma ta jima bata zo ba...", Hajja ta gyada kai, ita kuma ta kalli Ameena din, "ina wuni?".
Sai Ameenatun taji kamar kasa ta tsage ta fada ciki saboda kunya, duk da cewa tasan ta girmi yarinyar, amma a halin yanzu da tsayin Ameerah, duk da cewa itama tana da nata tsayin, amma Ameerah din ta kusa kamota. Ta daure ta amsa mata. Bayan gaishe-gaishe da tambayar kwana biyu, Ameerah ta tayar da sallah, ita ma sai ta shiga bandaki ta dauro alwala din.