Twelve
Bayan sun gama cin abincin dare, shinkafa dafa duka, Hajja ta umarci Ameena data je dakin dasu Fauza suke amfani dashi ta gyarawa Ameerah. Ameer yana tare dasu Affan a cewarta, su suna tsohon dakin Alhaji.
Tana yunkurin tashi Ameerah din ta tare ta, "wannan gadon ba zai daukemu mu duka bane?".
Ameena ta kalleta, Hajja tace, "zai isa mana! Wai don kada a takura miki ne".
Ta dan tabe baki, "ni ai ko a gida na fi son kwana a kusa da Ammi, bana son kwana ni daya".
Hajja tayi murmushi, "kice dai kawai tsoron kwana ke kadai kike yi. Kinga yanzu na samo mabuyarki daya, idan kika batawa mijinmu rai, sai in zuga shi ya kulleki a daki ke daya da dare".
Ameerahr ta kalleta baki a dage, "mijinku ke da wa?".
Tace, "ke din fa! Baki san cewa yayi sai ya fara kaini gidanshi a matsayin ta farko kafin ya kaiki a ta biyu ba?".
Da alama Ameerahr bata fahimci inda suka nufa da zancen ba, idan ma ta fahimta, to ba karamin aiki take yi wajen pretending din nuna bata fahimta ba. Ta sake cewa "wai wa?".
Hajja tace "mai gidan naki mana!".
Ameerah ta kwashe da dariya, "lallai ma! Ai wallahi in fada miki ni daya ce cal a gidana. In rasa ma da wadda zan yi kishi sai tsohuwa?".
Ameenatu kam kai kawai ta girgiza tana murmushin hirarsu.
Ta tashi ta kunna musu kallo a jikin karamar tv dake dakin, ta koma ta zauna aka cigaba da yin hirar da ita har kaset din ya kare, ta kashe. Suka kwanta barci.
******
Washegari aka yi kamu anan cikin gidan Anty Mommy kasancewar suna da fili babba mai kuma fadi. Tun safe suna gida ita da Ameerah, cikin dan kankanin lokacin nan sun saba sosai, in ka gansu kamar sun dade da sanin juna.
Ameerah irin outgoing mutanen nan ce, bata duba da yanayin shekaru ko rashin sabo, zata fada maka magana babu wani gargada. Sai dai abinda Ameena ta kula dashi shine, akwai girmamawa a cikin maganganunta, akwai kuma kula da taka-tsantsan. Idan tasan ta fadi abinda bai dace ba, ko kuma wanda tasan zai bata maka rai, a take zata baka hakuri. Wani lokaci kuma sai ta fara kwashewa da dariya sannan za ta baka hakuri.
Shi yasa ta saba da ita nan take, babu wani awkwardness da zaka fuskanta daga Ameerah idan har kana tare da ita. Idan ma abin jin kunya tayi ko kai kayi, a take zata dara a wuce wajen. Ba'a kara tada zancen kuma.
Karfe hudu suka gama shirin tafiya gidan kamu. Ameerah ce mai shiryawa din ma, tafi awa daya a gaban mirror tana ta kakale-kakalen fuska da kaloli na hoda da janbaki. Ameenah na zaune a gefenta, baki a dage tana kallon yadda ake wa fuska wannan hidima. A ranta ta raya ina zata iya wannan aiki?.
Tana cikin wannan aikin ne aka kirata a waya, ta daga hadaddiyar wayarta kirar Samsung. Bata san kan wayoyi ba balle tasan ko wace irin model ce.
Ameerah ta kara wayar a kunnenta tare da furta, "hello?".
Bata san ko me aka fada daga daya bangaren ba, ta dai ji tace, "yanzu zamu fito fa, mun gama shiryawa".
Ta sake saurarawa tana jin abinda mai wayar yake fada, baki ta turo gaba, "to gamu nan!".
Bata jira an kara cewa wani abu ba ta kashe wayar.
Haka ta koma ta cigaba da daurin dankwali. Kafin ta gama an kirata yafi sau biyar. Daga karshe dai ta mike da sauri ta warci jaka, cikin rawar jiki take jefa tarkace ciki, ta dauko takalmi cover shoe ruwan madara mai kwalliyar duwatsu masu sheki, ta saka a kafarta. Gyalenta ma sai daukarshi tayi a hannu, ta kalli Ameena "Anty Ameenah me kike jira ne? Su Yaya Lamido ke jiranmu, don Allah taso mu tafi kafin su tafi su barmu mu rasa wanda zai kaimu!".
Dama ita kadai take jira, tunda ita ta riga ta gama shirinta tsaf. Suka yiwa Hajja sallama, ta bisu da addu'ar su dawo lafiya.
Sauri-sauri, gudu-gudu, a haka suka fita.
A farfajiyar gidan wata bakar mota ce ta albarka, BMW, sai sheki take yi a cikin hasken rana. Matasa uku ke tsaye jingine da motar, sun yi anko na farar dakakkiyar shadda wadda ta dau wani lafiyayyen surfani na hannu.
Gabadayansu sun fito kamar wasu taurari a cikin bakin sararin samaniya, wadanda zasu haska waje komi duhunshi.
Duk cikin wadannan taurari, guda daya yafi haske mata idanu.
Ya kere su a tsayi gabadayansu, ya kere su a suffa. A tsaye yake kyam, babu alamar rankwafawa.
Ma'abocin doguwar fuska, wadda ta kunshi wasu kauraran cikakkun lebba, siririn hanci, wasu dara-daran manyan idanu da suke lullube da dogayen gassu na gira bakake. Idan ka kura mishi idanu, sai kaga kamar a lumshe suke, wannan da ace a dage suke suna kallon tsakiyar idanun mutane, da hakika ba karamar barna za'a aikata ba.
Bata gaskata tunaninta ba, sai daya daga kai a kaikaice, ya sauke idanunshi a kansu, sai data ji kamar zata kifa kasa saboda yadda gwiwoyinta suka yi sanyi a take!.
Gefen fuskarshi lullube yake da gassu, bakake sidik kamar yadda sumar kanshi, gira da gassun idanunshi suke. Irin wannan sajen da bature kan kira -quarter million-. Kalar fatar jikinshi baka ce mai haske, irin wanda hausawa kan cewa wankan tarwada. Sauran samarin da yake tare dasu sun fishi hasken fata mai cizawa. Ba kowa bane face Baqeer-Lamido Turawa!. Namiji daya tamkar da dubu! Kamar yadda Alhaji Allah jikan rai yake yawan yi mishi kirari.
Bata bari tunaninta yayi nisa ba saboda tasan ba huruminta bane, tayi gaggawar sauke kallonta zuwa ga sauran samari biyu dake tare dashi. Daya wanda ta gane a matsayin Affan, dayan kuma duk da cewa bata san shi ba, ta ganeshi a matsayin Ameer saboda kamanninsu data gani da Ameerah, kamar an tsaga kara an karya.
Tun kafin su karasa Ameer yake jefawa Ameerah harara, suna karasawa kuwa ya tareta da fada, "wallahi daga yau 'tweenie' na daina jiranki idan zamu yi tafiya. Ke kullum kece ta karshen fitowa idan za ayi abu? Gaki nan kullum da katuwar agogo makale a wadannan siraran hannuwan naki kamar sanda, amma baki san amfaninsu ba!".
Gwalo ta mishi, ta bude gidan baya tana murmushin tura haushi, "to suda sarkin magana, zuga-zugi uban yan shayi! Duk don Yaya Lamido yayi min fada ne kake wani daga murya kana babatu, to in Allah ya yarda ba zaka samu wannan galabar ba. Anty Ameenah shigo mu tafi!".
Ta shige cikin motar tana dan yin murmushi, Ameerah ma tabi bayanta. Ta kalli Ameer daya tsaya daga waje yana kallonta, har lokacin cikin harara. Daidai lokacin da Baqeer da Affan suka bude gidan gaba na motar suka shiga, Affan ne ya zauna a gefen mai tuki, Baqeer kuma a gefen mai zaman banza.
Ta kalli Ameer, "Malam idan ba zaka shigo ba ka kauce ka bamu waje don akan hanya muke!".
Sai lokacin ya shiga motar ya maida ya rufe. Yayanshi ya kalla, "wallahi Tallahi Yaya ka daurewa yarinyar nan da yawa shi yasa ta raina mutane. Ko Hasina bata rashin kunyar da take yiwa mutane".
Mintsininshi tayi a hannunshi, yayi kara yana shafa wajen. Tace "Kai fa ka cika shegen son girma kamar gyambo. Tsakanin ni da kai wai waye ya girmi wani? Kai kullum sai rainin wayo da raina mutane?!".
Kafin ya maida mata amsa, Affan daya tashi motar yake kokarin barin cikin farfajiyar gidan, yace "don Allah stop with that bickering of yours da kullum baya karewa. Amma dai nima ina goyon bayan Ameer, saboda Allah tun yaushe muke tsaye muna zaman jiranku?".
Ameer yace "gaya mata dai!".
Ameerah kuwa baki ta turo tana dira kafarta a kasa, "dama can Yaya Affan ai kai kullum cikin goya mishi baya kake".
Baqeer kuwa murmushi ya saki hade da girgiza kai ba tare daya furta musu ko 'a' ba.
Ita kuwa Ameenatu kallonsu take yi cikin murmushi. Burgeta suke yi. Tunanin wani lokaci can daya wuce da suka kasance kamar haka ita da Yayarta Murjanatu take yi.
Muryar Affan taji yana jefo mata tambayar data bata mamaki, yace "wai wannan Ameenatu ce?".
A hankali ta daga kai ta kalleshi. Bata da riko, kuma bata taba rike su a cikin ranta ba, amma ta rasa dalilin da yasa ta kasa sakin jiki dashi.
Sai kawai ta samu kanta da gyada kai a sanyaye, tace "Ni ce Yaya Affan, ina yini? Yaya Baqeer ina yini??".
Sai lokacin ya juya ta kalleta, yace "lafiya lau Ameenatu. Ya hidimar biki?".
Tace, "Alhamdulillah!".
Affan yace "kwana biyu? Kusan kullum nazo sai dai ace kina can Dutsin-ma kina hutawarki".
Ta kalleshi kawai, saboda bata data cewa. Bata yi wannan sabon dasu ba su duka.
Ameerah tace, "kamar kuwa ka sani Yaya Affan. Ai wallahi Anty Ameenah yar hutu ce ta gaske. Babu abinda take yi sai hutu da jin dadi".
Ameer yace "shut up! Ke akwai wanda ya kaiki hutu ma wanda yafi karfin misali a duk duniya ma?".
Jakarta ta dauka ta buga mishi a baya.
Affan yayi yar dariya yana girgiza kai, "ku dai kam Allah ya shirye ku wallahi. Zan so in ga wannan rana".
Ameenatu ta maida kanta baya ta kwantar a jikin kujerar motar data kasance zallar leda, tana kallon cikin birnin Katsina ta cikin gilashin motar.
Bata kara furta komi ba har suka isa gidan Anty Mommy. Sai a bakin gate suka ajiyesu saboda babu ma wajen yin parking din mota. Suka wuce wajen walimarsu.
Cikin gidan an shirya shi sosai, decoration aka yi na a fada a ji. An shirya kujeru da tebura a tsakiyarsu. Tun daga masu biyu, hudu, shida, har zuwa takwas da goma. Kowacce zaka gani a wajen, tayi shiga ta burgewa cikin ankon da suka sanya a ranar. Atamfa ce ruwan bula mai cizawa, yawancinsu free gown aka dinka musu. Ita Ameenatu A-shaped doguwar riga aka mata, sai ta hada da gyale ruwan madara mai cizawa, ta hada da takalminshi. Gata ba ma'abociyar sanya gyale ba, sai zame mata yake yi a jiki. Allah Yasa gyaleluwa biyu da takalman da Indo ta sai mata, wadanda zaka iya hadawa da kowane kaya ne.
Suna shiga wajen Ameerah ta hadu da wata da babu mamaki kawarta ce, ko kuma ta santa, nan ta janyeta suka wuce.
Ta wuce wajen a dosane, tana laluben wajen da zata samu ta zauna ita kadai don bata ga kowa wanda ta sani ba.
Hannu taga ana dago mata, ta hangi Indo can cikin jerin yan aikin gidan. Sai lokacin taji ta dan saki ranta, da har ta fara tunanin zamewa ba tare da kowa ya kula ba ta koma gida abinta.
Da saurinta ta karasa wajensu, suka gaisa dasu. Waje suka samu ita da Indo wanda yake cin mutane biyu suka zauna.
Tuni an fara sha'ani. Sautin kida ke tashi kawai daga can inda masu kidan suka ware. Gefe kadan daga wajen da aka shirya inda amarya zata zauna. Su kuma suna can daya gefen inda suke fuskantarsu.
Tana hango Fauza da abokanta suna ta kaiwa da kawowa abinsu cikin kokarin entertaining abokan Anty Mommy da 'ya'yansu da kuma kawayensu. Ba'a jima ba aka fara fitowa da abinci ana rabawa. Su Fauza sune kan gaba, su suke ba wadanda aka dauko musamman saboda haka, waje da inda zasu kai abincin.
A gabansu za'a wuce da plate a kaiwa teburin bayansu, ko na gefensu, ko na gabansu. Da yake ma ba wata yunwa take ji ba, don haka bata kai a kanta ba.
Suna nan a zaune, har lokacin ba'a fito da amarya ba, ga yamma tana yi. Suna cikin yin hirarsu, sai ganin Eeshey suka yi ta ja kujerar da wata ta tashi daga kai, ta zauna tana fuskantar Ameenatu cikin murmushi.
Ta ajiye plate din dake hannunta a kan teburin, fried rice ce da masa, sai soyayyen naman sa da cinyar kaza da hadin coleslaw a gefe.
Tace "tun dazu naga shigowarku ke da su Affan da cousin dinsu dinnan Ameerah. Ya Hajja?".
Ameena tace "lafiya lau. Ya hidima?".
Zata amsa mata, idanunta suka sauka akan empty space din dake gabansu, girar idanunta ta daga sama cikin alamun tambaya, tace, "ya ba'a kawo muku abinci har yanzu bane?".
Ameenatu ta daga kafadunta sama, "kila basu kula damu bane. Ni bana jin yunwa ma, amma ban sani ko Indo tana ji ba?".
Indo da abin da aka musu ya matukar yi mata zafi, tace "kema dai kinsan bana taba yin fushi da nama don haka idan dai na samu ci zanyi".
Eeshey da Ameenatu suka yi dariya.
Hannu Eeshey ta dagawa daya daga cikin masu raba abincin dake can gefe a tsaye suna kallon yanmatan amarya dake ta tikar rawa a filin rawa.
Da sauri ya taho ya tsaya a gefenta, ta kalleshi tace "ya aka yi baku kawo abinci nan bane har yanzu?".
Yace "ai Hajiya Fauza ce tace kada mu kuskura mu kai inda bata ce mu kai ba".
Tace "bullshit! Su kuma sauran mutanen fa suyi me? Kuje ku zubo a kawo nan da wadancan teburan biyu...", ta nuna wajen da yan aikin gidan suke su biyu, ".... ku kuma hado da lemuka. Idan ta tambayeka kace ni Eeshey ni nace ku kai".
Babu musu ya juya da sauri don gudanar da abinda aka umarce shi.
Wata budurwa tazo wucewa ta gefensu, Eeshey ta ambaci sunanta, "wai sai yaushe ne zaku fito mana da amaryar ne Salbi? Tun dazu ita kadai muke jira. Kun hallara mutane amma kun ki kawo musu amarya".
Wadda aka kira Salbi tayi dariya, tace "dangin ango muke jira su karaso. Yanzu zata fito don suna kan hanya".
Eeshey ta tabe baki, "sai ku bada himma ai. Ni na taba ganin inda aka yi haka? Kenan idan basu zo ba, ba zamu ga amarya bane kenan nufinku?".
Salbi tayi dariya, "ke dai kika sani sarkin korafi". Ta wuce.
Koda aka kawo musu abincin, Ameenatu kasa ci tayi, sai lemun Teem ta dauka mai sanyi tana kurba. Sauran mutanen, musamman abokansu da wasu daga cikin dangin ango da suka je, lemukan exotic da five alive zuwa hollandia ne a gabansu. She's not complaining, a ganinta a hakan ma ba wani karamin mataki suka taka ba.
Eeshey taci gaba da jan su da hira suna yi, jifa jifa idan wasu sun zo wucewa, zasu tsaya su gaisa da Eeshey din kafin su wuce.
Wata farar budurwa yar duma-duma da ita, ta sanya atamfar an mata dinkin riga da zani single, tayi shigar kamar yadda yarbawa suke yi, ta isa wajen idanunta akan Eeshey din kawai.
Tace, "Aysha kizo muje mu taka mana, tun dazu Fauza take nemanki".
Tace mata, "kuje kawai kuyi abinku. Kinsan fa ni ba gwanar rawa bace".
Bata ce komi ba, ta juya abinta. Bata wa su Ameenatu ko sannu ba. Yawancin wadanda suke wucewa dama haka suke tsayawa su wuce.
Su Fauza da abokanta suna shiga filin rawar, aka sakar musu sautin kidan 'Taki-taki' ta DJ Snake. Nan suka sha casunsu kamar ba diyan musulmai ba.
Sai can wajen yamma aka fito da amarya. Cikin shigar wani farin material, komi nata fari ne. Ta tsaya aka yi hotuna, kafin suka shiga filin rawa ita da abokanta da wasu daga cikin danginsu dana ango. Aka yi barin kudin like kamar babu gobe. Bata jima ba aka maida ta cikin gida.
Daga nan taron ya watse, kowa ya tashi.
Sashen yan aiki suka je suka yi sallah. Suna shirin wucewa ita da Indo, sai ga Ameerah ta shigo nemanta. Nan suka dunguma suka koma gida, wannan karon Affan ne da Ameer kawai suka koma dasu.
*
Washegari aka kai kayan lefe. Akwatuna goma sha biyu, kowanne makare da kaya na gani na fada kamar shagon saida kaya ne dungurungum suka dauka suka zuba a ciki. A ranar da yamma aka yi sisters eve, Ameenatu data tashi da dan ciwon kai saboda rashin samun cikakken barci a dan tsakanin lokacin, sai ta samu damar lafewa akan gado taki zuwa.