DUNIYA BIYU

Thirteen

by @jeddahlawals

Haka aka cigaba da gudanar da shagulgulan biki har zuwa ranar assabar ranar da ake yin daurin aure. Gida ya cika ya tumbatsa babu masaka tsinke, mutane na ta shigI da fice.

A kuryar dakin Hajiya Uwani, zaune take a gefen gado cikin wani rantsattsen leshi pink wanda suka yi ankon shi su uku kacal, ita da amarya da autarta. Affan kuma sai ya dinka shadda ruwan makuba. Kayan arziki ne libge a gefen gadon wadanda yan'uwa da abokan arziki suke kai mata.


Dakin daga ita sai manyan shakikanta biyar lokacin da Hajiya Maimunah mahaifiyarsu Lamido da babbar diyarta Muneerah suka shiga cikin dakin.

Cikin yan sakannin da suka yi kafin su karasa inda suke, ta gama karade jikin Hajiya Maimunah tun daga saman kanta har zuwa tafin kafarta da kallo. Wani hadadden takalmin Channels wanda aka yiwa samanshi kwalliya da wasu irin duwatsu saye a kafarta, ga jakar takalmin a hade, da kuma rantsattsen material din dake jikinta. Taji wani abu ya daki cikin ranta, kishin matar take kwarai kamar wata kishiyarta. Ta tsani taga ta sanya wani abu wanda ya fi nata.


Sai da suka karasa kusa dasu sannan ta janye idanunta daga kallonsu.

Suka samu waje suka zauna a gefen gadon, nan aka gaggaisa da juna cike da fara'a. Sun jima a zaune anan, dama can ba wani hira da shiri ne na azo a gani ba a tsakaninsu, Hajiya Maimunah ta dauki wata jaka da take hannun Muneerah ta mikawa Hajiya Uwani din, "ga wannan ba yawa, a ba amarya".

Ta sanya hannu ta amsa shelakai, kamar wadda ta ba ajiya, "har da wata hidimar kuma Hajiya kamar ba ayi ba dama? To angode!".


Ta girgiza kai, "Haba dai, Badi ai kamar 'ya ce a gareni. Bari mu tashi mu leka wani gidan bikin sai mu tsaya a gidan Hajja. Jirgin karfe bakwai zamu bi mu koma gida".

Tace, "to mun gode kwarai. Ba lallai ku ga gidan amaryar ba kenan?".

Tace "idan har ba da yamma za'a kaita ba kam, sai dai daga baya mu zo Allah sanya alkhairi".


Tace "ai da yamma za'a kaita, idan an daura aure karfe biyu, akwai dinner da za ayi a gidan nata karfe takwas na dare, shi yasa za'a kaita da wuri don a kimtsa komi".

Ta gyada kai, "haka ne. In Allah ya yarda zamu leka".

Da haka suka musu sallama, suka fita daga dakin.


Suna fita, yar guntuwar fara'ar dake kan fuskarta ta kau. Tayi watsi da jakar data kai mata can gefe tana jan tsaki.

Hajiya Salamatu ta janyo ledar ta daga, ta fara fito da wasu hadaddun turaruka na wuta dana jiki da na wanka zuwa air fresheners na daki. Tace "turkashi! Wannan fa shine aiki sai mai shi din. Wannan hidima haka ai ba karama bace. Kin kuwa san inda ake samun kayan kamfanin nan? Saboda tsadarsu ko a cikin Saudiya ba kowane shago bane yake saida su ba fa!".


Wani takaicin ya kara kamata. Ta tsani taji an yabi wani kan wata bajinta da suka yi, ba ita ba. Dama farko-fakon bikin dubu hamsin ta tura mata akan ayi hidima. Yanzu kuma ga wannan.


Ta yamutse fuska, "to sai me? Aikin banza, sai yau ne ma taga damar zuwa min? Tun yaushe aka fara bikin? Har da wani 'jirgin karfe bakwai zamu bi!' sai kace wata babba din nan". Ta fada tana makale murya irin yadda tayi.

Abokan nata sai kallonta kawai suka yi saboda sun san hali sarai. Babu wanda ya furta uffan.


*


Har sun kusa kaiwa wajen motar da suka zo da ita inda direban daya kawo su yake jiransu, suka jiyo sautin karar murya ana kwala kira, "Ammy!! Ammy!!". Basu yi tunanin dasu ake ba sai da Fauza ta tari gabansu tana haki alamun ta ci gudu.

Ta duka tana gaida su gabadayansu, tace "ai ban san kun zo ba, na shiga dakin Mommy naji suna maganar. Shine nace bari in zo mu gaisa".


Ammy ta gyada kai, "wallahi kuwa, sauri muke yi ai shi yasa. Wajen wani bikin zamu je yanzu haka, sannan mu wuce gidan Hajja. Don a yau dinnan zamu koma Abuja".

Ta wani yamutsa fuska cikin alamun shagwaba, tace "Haba Ammy, maimakon ku bari sai gobe?".

Tace "ai a goben su Muneerah zasu koma shi yasa".


Ta gyada kai, "ok. To ku gaida gida".


Da kanta ta budewa Ammy kofar mota, ta shiga ta rufe. Ta ja da baya tana kada musu hannu har suka tafi. Sannan ta juya.


Can gefen gidan tayi, inda study din Daddynsu na musamman yake.

Ta kwankwasa kofar dakin, aka bata izinin shiga ta tura ta shiga.


Zaune yake akan kujera a bayan wani wawakeken tebur da takardu suka lullubeshi ta ko'ina. Wasu bakaken suits ne a jikinshi da farin gilashin taimakawa wajen yin karatu a fuskarshi. Ta taka zuwa gaban desk din, yana ta rubuce-rubucenshi bai daga kai ya kalleta ba.


A shagwabe tace, "Daddy!".


Sai lokacin ya daga kai ya kalleta, fuska babu yabo babu fallasa yace, "meye? Wai ba na hana ki shigo min ofis idan ina aiki ba?".

Ta turo baki gaba, "Daddy, bani da kudin yin kari ne idan muka je wajen dinner anjima".

Ya ajiye biron da yake amfani da ita akan takardun, fuskar nan tashi a turbune, kamar wadda tace mishi ya dauki ranshi ya bata. Yace, "sai kuma aka yi yaya? Na riga na fada miki dama babu kudin da zan kara miki, kije wajen babarku ki amsa. Ki rufe min kofa idan kin fita".


Ya fada cikin alamun sallamarta. Ya dauki bironshi yaci gaba da rubutunshi.

Bata dauki abinda yace da muhimmanci ba, ta kara takawa zuwa gaban desk din sosai, "dadd...!".

A matukar harzuke ya daga kai ya kalleta, "ba cewa nayi ki fita daga wajen nan bane? Come on, get out!!".

Ya karasa fada cikin fushi da daga murya, yana mai nuna mata kofar fita.


Bakinta ya fara rawa alamun zata fashe da kuka. Da gudunta ta juya ta fita daga dakin karatun, kofar dakin data bude da karfi ta bi ta rufe, ji kake garammm!! kamar wadda zata balle daga marikinta.

Ya koma ya jingina da jikin kujerar yana shafa gefen goshinshi da hannuwanshi.


A bayan gidan suka hadu da Badia rike da waya kare a kunnenta. Ta kalleta cike da mamakin yadda ta ganta, fuska dauke da alamun tambaya.

Ita kuma tana ganinta ta rage saurin da take zubawa.

Badi tace mata, "ke kuwa lafiyarki haka? Ke da waye?".


Ta harari inda ta fito, "waye kuwa da ya wuce Dad? Wai daga ya bani kudin liki, kinji wata uwar tsawa daya daka min kamar wata karamar yarinya?".


Badi ta kada idanu sama, "ni wallahi kina bani mamaki idan kika wani tsaya jin haushin abubuwan da wannan _man_ din yake yi, sai kace baki san halinshi ba?".


Ta tabe baki, "mantawa nake yi kam. Shi ya sani ai! Kina da kudi a hannunki ne? Dazu Mommy ta turo min kudi na kuma riga nayi amfani dasu, gashi bani da wadanda zanyi amfani dasu anjima".

Badi ta girgiza kai, "bari in tura miki ta banki, sai ki aiki wani ya ciro miki".

Tayi murmushi cikin murna, "yauwa Babbar Yaya! Ina yin ki wallahi. Ki tura da wuri fa!".

Daga haka ta juya da azamarta ta koma gida tana kwalawa Danladi mai musu ban ruwa kira.


Badi kuma taci gaba da kiran da take yi a waya, amma ba'a daga ba. Karo na kusan biyar kenan. Tana shirin saddakarwa ta koma cikin gida, taji an daga kiran. Da murnarta tayi sallama. Sai dai a maimakon taji muryar angonta, sai muryar wani daban taji yana zabga mata kirari...

Nan da nan ta hade fuska, tace "ina Fahad din?".

Sahabi, babban abokin Fahad din ya saki wata iriyar dariya irin ta cikakkun sakarkarun nan, yace "angon naki wanka yake yi amarya. Ko kina bukatar in mika mishi wayar ne?".


Tana shirin bashi amsa, taji alamun ana bude kofa daga can daya bangaren, sai kuma taji maganganu kasa-kasa.

Sahabi dinne yake sanar da Fahad wadda take kiranshi a waya, tana jin lokacin da yace mishi, "me zan mata kuma? Tun dazu take kirana a waya haba! Wajen dinner ne, na kuma ce zan je, ba sai a kyaleni ba in huta haka nan ba?".


Wani irin abu ya daki kahon zuciyarta, bata san me yasa yake yi mata haka ba. Kamar ba shi ya daga baki yace yana sonta ba. Hawayen suka ciko mata idanu, amma ta cije bakinta don hana su sauka. Su bata mata kwalliyar da ta kai darajar naira dubu hamsin, idan ma bata fi ba.


Sahabi ya sake sakin wata dariyar wadda ta matukar kular da ita, yace, "to ke kinji, angon naki bashi da lokacin daukar wayarki a halin yanzu. Zaki iya barin sako idan da hali, sai in sanar mishi!".

A yawancin lokuta abinda yake faruwa kenan, har ta riga ta saba da hakan. Don haka ta gaya mishi cewa Yayyen Babanta maza su biyu da suka zo daga kasar Turkiyya inda suke zaune, suke so su gaisa dashi kafin a daura aure saboda hidimar mutane. Tunda suma ana daura auren zasu koma.

Tana gaya mishi ta kashe wayar ba tare data jira sunyi sallama ba.


Duk dauriyarta sai da digon kwalla ya sauka daga cikin idanunta. Ta kai yatsarta ta dauketa da sauri lokacin da taji an ambaci sunanta, ta juya. Aysha ce diyar Anty Luba, yar autar dakinsu daddynsu. Ta sakar mata murmushi a sanyaye, "ya aka yi ne Ayshe?".

Tace, "Su Mommy suka ce wai kije ki canza kayan jikinki".


Aikin kenan! Har ta gaji da canza kayan sawa. Da ta saka wannan, ba'a jimawa za'a nemota ta canza wasu. Kai kawai ta gyada mata, don bata da wani zabi daya wuce wannan. Bata isa tace musu ba haka ba, yanzu sai azo a hau kanta da fada, kowa yana fadar albarkacin bakinshi.