DUNIYA BIYU

Fifteen

by @jeddahlawals

Ranar da aka ɗauki azumi na sha tara, su Ameerah suka dira a Katsinar kamar daga sama, don babu wanda yasan da zancen zuwan nasu.


Saukar safe suka yi, wajajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe.

Lokacin Ameenatu ta bararraje, tayi dai-daya a tsakar ɗaki da biredi da kofin shayi a gabanta don bata yin azumi. Tun da safiyar ranar ta waye sai lokacin ta zauna.

Suna tashi ta ɗauki geron da aka jiƙa jiya da dare, ta wanke ta kai niƙa. Tana dawowa kuma ta tace, ta kai store ta ajiye. Shine fa ta ɗora ruwa ta haɗa shayi, ta ɗauki guntun biredi da suka yi saura jiya da dare ita da Huwaila zata ci.


Tana fara ci, aka buɗe kofar ɗakin aka shigo.

Kwata-kwata bata kawo komi a ranta ba. Kafin ta tantance, sai jin sallamar namiji tayi a bakin ɗaki.

Sai data amsa, sannan ta tuna halin da take ciki a lokacin. Ta ɗaga kai da sauri ta kalli bakin ƙofa; Ameerah ce a tsaye tana kallonta tana murmushi. Daga bayanta kuma Yaya Baqeer ne. Suka haɗa ido.


Subhanallahi! Wata irin rikicewa da kunya suka kamata a lokaci guda! Tsabar kiɗimewa sai ta miƙe tsaye, tayi duru-duru, daga ƙarshe dai ta ɗaga ƙafa ta shige banɗaki a sukwane. Tana jiyo sautin dariyar da Ameerah ta dinga ƙyaƙyatawa.


Tana jiyo muryarshi da Hajja suna gaisawa, Hajja data rasa ina-taka-saka, ina-taka-tsare dashi, sai nan-nan take dashi tana jan shi da hira, tashin muryarsu kawai kake ji.

Nan da nan ta kirawo Huwaila, ta bata makullin ɗakin da suka saba sauka, ta umarceta da taje ta gyara, don ma dai lokaci zuwa lokaci ana gyara shi musamman ma saboda baƙin bazata.

Sai da suka jima suna hirar, har Huwaila ta dawo da makullin ɗakin ta ƙarɓi turaren ƙamshi taje ta kunna, sannan ya bar dakin.

Sai daya tafi sannan Ameerah taje tana buga mata ƙofar banɗakin, tace "ai sai ki fito tunda ya tafi".

Sai lokacin ta fita daga banɗakin tana sunne fuska, Ameerah kam na mata dariya.


Ta zauna a gefen gado, gabaɗaya sai taji shayin ma ta ƙoshi dashi. Ameerah ta yaye gyalenta ta jefa kan gado, ta kalleta tana ɗan murmushin tsokana, "har kin ƙoshi da abincin ne kuma?".


Ta kalleta ba tare data ce wani abu ba. Ameerah ta zauna ta ɗauki kofin ta kai baki ta kurɓa, ta ɗan yamutse fuska, Hajja da Ameentu suka bita da kallo baki a ɗage. Tace, "ya ma fara hucewa dai, haka nan zanyi maneji don dama yunwa nake ji, ban karya ba!".


Tayi saurin dira daga kan gadon ta warce biredin dake hannunta, tace "saboda kin fini zane a damtsen hannu ko? Wato ni yunwa ta kashe ni kenan?".


Ameerahr tayi dariya tace, "to ai naga kamar ba ci kike so kiyi bane. Kin wani koma gefe kina sunne kai wai ke nan kunya, a kanki farau?".


Harara ta watsa mata ƙasa-ƙasa cikin wasa, ta raba biredin gida biyu ta miƙa mata rabi, babu musu Ameerahr ta amsa suka fara ci.

Cikin dan kankanin lokaci suka tada shi, Ameerah taja jakar hannunta ta zuge ta ciro apple guda biyu ta mikawa Ameenah daya suka kara da ita. Kafin kuma suka hau hirar yaushe gamo.


Zuwa can da rana, suna shirye-shiryen haɗa abuwuwan kari, ta shiga ɗakin Hajja ta sameta a zaune tana gyaran shinkafar tuwo. A waje ta baro Huwaila da Ameerah suna gyaran waken da za ayi alale anjima da yamma.

Tace, "Hajja tun yanzu za'a kai niƙan waken ko a bari sai anjima?".


Hajja ta ɗaga kai ta kalleta, tace "ai zancen alale ya kau, tuwon shinkafa za'a tuƙa!".

Ta kalleta da mamaki. Hajjar tafi kwana uku tana musu ƙorafin alale take so ta ci, sai yanzu kuma da za ayi zata dawo tace ba zata ci ba?. Tace, "saboda me? Ba kya jin daɗi ne ko wani abu?".


Tace "lafiyata garau. Babban maigida yana gida ina ni ina cin wata alale yau? Tuwon shinkafa za'a tuƙa mishi da miyar alayyafo. Zo kije gidan Maman Imam ki sayo mana kayan miya da alayyafo. Ki dawo ki kira min Isiya yazo yaje bakin kasuwa ya sayo min naman miya da ɗanyen kifi".


Ameenatu ta kama bakinta cike da tu'ajjibi, yaushe rabon da su ci abin daɗi irin haka a gidan? Har ta manta. Lallai ba ƙaramin ji da Yaya Baqeer ɗinnan take yi ba.

Hajja ɗin ta zaro kuɗin da Ameenatu bata san daga inda suka fito ba, don kuwa kullum cikin faɗin bata dasu take, ta miƙawa Ameenatun ta karɓa.


Ta samu su Huwaila da Ameerah suna gyaransu da ƴan hirarraki, suka bita da kallo. Huwaila tace, "ina zuwa haka ke kuma?".

Tace, "kayan miya zan sayowa Hajja. Ku ma baza waken a rana kawai, tuwo za ayi".


Yadda Ameerah ta dafe ƙirji tana zare idanu ne ya bata dariya, tace "na shiga uku! Tuwo kuma? Gaskiya gidan su Anty Mommy zan je shan ruwa yau".

Huwaila kuwa da yake ta riga ta saba da halin na Hajja, ko a jikinta. Sau nawa zasu tayar da sanwar abinci a gidannan Baqeer yana dira gidan ta tada sanwar nan? Komin dare sai anyi tuwon nan saboda shine abinda yafi son ci.

Ta kalli Ameerah tace, "to ke da ba ma wani azumi kika yi ba?".


Nan Ameenatu ta wuce su dai, tana ji Ameerah na, "tsaya in ɗauko hijabina sai mu tafi". Tayi murmushi kawai.


*


Ameenatun da kanta ta tuƙa tuwon ta kuma yi miya, don in ta kai ga Huwaila da Ameerah duk ragwage ne, musamman idan ta kai ga harkar tuka tuwo da hura murhu.

Tana cikin kicin din tana kara duba miyar data bari akan garwashi ta karasa, Hajj ta leka. Tace mata, "idan kin sauke, ki dora shayi kadan a zubawa Baqeer a flask, kullum sai ya sha shayin wannan sai kace wani bakin balarabe".

Ta danyi yar dariya, "to Hajja".

Hajja ta juya ta kalli Huwaila dake yanka fruits din da Baqeer ya kai, su kankana, abarba, lemu har da ayaba da inabi. Tace mata, "ajiye wannan aikin ki ba Ameerah ta karasa ko kuma Ameenah, kizo kije nan gidan Maman Ameer ki samo mana citta da kanumfari da lemun tsami".

Huwaila ta mikawa Ameerah wukar hannunta ta amshi hamsin din ta Hajja take mika mata, sai ta koma ta daki don ta dauki hijabinta kafin ta wuce. Ameenah kuma ta fito ta kamawa Ameerah aikin da take yi.


Data gama shayin, aka zuba mishi a flask aka dora akan tray da kofi, cokali da sugar da kuma dabino. Suka dauki kayan, da fruits din da aka yanka da kuma tuwon, suka kai mishi falon farko inda aka saba jera mishi kayan abinci idan yana gidan suka ajiye.


Ba ƙaramin daɗi tuwon yayi ba kuwa. Hatta da Ameerah mai ihun ita ba zata ci tuwo da dare ba, sai data tayar da malmala ɗaya da rabi. Suka yi ta mata dariya.


Tana cikin wanke bayi bayan an sha ruwa. Babu yadda Hajja bata yi da ita akan ta bari sai da safe ba, amma ta ƙi. Tafi son idan zata yi wankan tsarki ya kasance muhalli da kayan da zata yi amfani dasu a tsarkake suke.

Tana cikin wankin ne taji Baqeer ya shigo ɗakin, tana jin lokacin da yake cewa Hajja, "lallai yau ba ƙaramin tarba mai kyau aka min ba Hajiyata. Yaushe rabon da kiyi min girki irin haka?".


Taji lokacin da Hajja ɗin ta ke tsokanarshi da cewa lallai yau abin har da santi? Yayi dariya. Tace, "ai da yake yau ƙanwarka Ameenatu ce ta ciyar damu. Tunda tazo gidannan ita take komi, ba girki ba gyaran gida ko na ɗaki ba. Haka take kamar wata inji, bata gajiya sam!".


Sai ya ɗanyi shiru yana ɗan sosa kai, daga baya dai ya miƙe tsaye. Yace "ni kam da so samu ne a ajiye wanda za'a ɗunɗuma min da asubahi inyi sahur, bana son cin wannan taliyar taku ta indomie ko shayi, basa riƙe min ciki sam!".


Hajja ta nuna mishi flask ɗin abinci da aka ajiye a kusa da gado, tace "ai sai da aka ɗaukar maka na sahur ma kafin aka zubawa ƴan gida!".

Yayi murmushi yace "yauwa Hajiyata, godiya nake ƙwarai. Shayin ma don Allah a dinga min irin na yau, yayi dadi sosai, kuma kayan kamshin sun fito yadda yakamata".


Hajja tace, "ai in dai kanwarka Ameenah tana gidannan to ka sanya ranka a inuwa, za'a dinga maka".

Yace, "yauwa!. Bari muje muyi sallah an kira. Mata masu yin sallah su fito da abin sallarsu!".

Ya ƙarasa faɗar hakan cike da alamun tsokana kafin ya fita daga ɗakin. Bata san ko kanwarshi Ameerah yake tsokana ba ko kuwa har ita? Duk da bata sani ba, hakan bai hana ta yin murmushi ba.


Huwaila ta ɗauki sallayarta ta fita. Hajja kam ta tayar da tata sallar a ɗaki don cewa tayi ba zata iya bin jam'in sallar Baqeer mai tsayi ba.