DUNIYA BIYU

Sixteen

by @jeddahlawals

Sai washegari da safe Baqeer ya shigar musu da kayansu na sallah wanda Daddyn Abuja ya bada ya kai musu.

Hajja aka bata wata hadaddiyar English, har da gyale, takalmi da turare mai kyau. Ita kuma Ameenatu atamfar Holland da wani ɗanɗasheshen paper lace ruwan kore mai haske kamar bulu. Sai takalmi mai tsini da gyalenta har da wata ƴar karamar jaka da taga Eeshey na yawan rataya irinta, har da su agogon hannu da yan kunne. Huwaila kuma aka bata atamfar cote d'evoure da kuma lace da jaka irin ta zamani. Ga kuma kudin dinki an hada musu dashi. 


Ameenatu kam har bata san da wani baki zata yiwa mutumin nan godiya ba, ƙarshen mutunci da halacci yana gwada musu kamar shi ya haifeta, ko kuma Hajja ce ta haifeshi.

Hatta da su Nana da Baba Habu da Indo ba'a barsu a baya ba, suma sai da aka basu atamfa, Baba Habu kuma aka bashi shadda mai kyau. Shima Isiya an kai musu shi da matar shi.


Da yamma suka tafi gidan Indo da kayan, ta rakasu gidan wadda take yi mata ɗinki. Da yake mai ɗinkin babbar aminiyarta ce, ta tabbatar musu babu matsala zasu samu ɗinkin kafin sallah.

Daga can ma suka yi sallama da ita suka juya saboda ayyuka da suke jiransu.


Suna tafe a hanya ita da Ameerah, a gida suka baro Huwaila tana shara. Ameerah tace mata, "Ni fa humra ɗinnan da kika bani gaskiya ta burgeni sosai wallahi. Kinga har ta ma ƙare. Gaskiya kafin mu koma sai kin sake yi min wata!".


Tace, "idan wannan ne ai baki da matsala, zan miki mai yawa har da na turaren kaya ma duk zan haɗa miki in Allah Ya yarda".

Ta ɗan yi tsalle cike da murna ta riƙeta, tace "nagode sosai Anty Ameenah! Ina son ƙamshi wallahi fiye da tunaninki! Tare ma zamu yi dake wannan karon, in ga yadda ake yi don in koya. Nima in dinga haɗawa da kaina".

Ta ɗaga kafaɗa, "to ai shikenan!".


Suka ɗan yi shiru suna tafiya, Ameerah ta sake katse shirun ta hanyar cewa, "kinsan fa wannan paper lace ɗin Yaya Baqeer ne ya sayo mana mu uku, ni da ke da Yaya Fauza. Sai da muka tsaya ma ya bata nata jiya sannan muka ƙaraso nan!".


Steps ɗinta suka ɗanyi faltering, bata taɓa tsammanin haka ba. Sai kawai ta share, tayi ɗan murmushi tace, "ko? Amma nagode ƙwarai. Idan mun haɗu cikin gida zan mishi godiya".

Duk da ko a ɗazu da safe ta mishi godiya kamar bakinta zai tsinke, yanzun sai taji kamar tana buƙatar ta sake yi mishi wata, kamar wadda tayi ɗin bata isa ba.


Ameerah ta girgiza kai, "da kin ƙyaleshi wallahi, baya son yawan godiya da kike ganinshi nan, shi yasa fa ya haɗa kayan waje ɗaya bai banbance ba. Wannan turaren na cikin kayan Hajja ma shi ya sai mata da lace din da aka ba Huwaila".

Sai ta gyaɗa kai kawai, ba wai don ta gamsu ba. An taɓa haka dama? Mutum yayi maka kyauta amma godiya ta gagara?!.


Ameerah taci gaba da bata labarin abubuwa, da alama yau cikin ƴan hira take. Tana bata labarin bayan sallah za ayi posting Yaya Baqeer din zuwa wajen aikinshi, ashe akan sojan ruwa yayi training. Kwanaki can da ɗadewa taji Hajja ɗin na ƙorafin yaro ya rasa abinda zai yi ɗuk tarin ayyukan dake faɗin duniya, sai karatun soja? Har Ameenatun na mata dariya, tana cewa, "to ina ruwanki ke kam? Tunda ba ke zaki mishi aikin ba, ba kuma kuɗin makaranta zaki biya masa ba?!".

Ashe Yaya Baqeer ne. Don a lokacin bata ma tsaya tambayar ko da wa take ba.


Ameerah ta gyara mata, lokacin da tace sojan ruwa, tace, "sojan ruwa na musamman. Ana kiransu da Navy-SEAL. Sojawan da suka taɓa ɓangaren ruwa, sama da kuma ƙasa. Zasu iya sajewa da kowane sauran forces, shi yasa horarwarsu take intense (mai tsauri). Sai da suka ƙara wata shekara ɗaya fa suna ƙara horo akan wanda aka saba yiwa sauran sojoji. Yaya Baqeer ya fita da shaidar most hardwork a cikinsu. Shi yasa ma aka kaishi ɓangaren dake ji da special cases saboda ƙwazonshi".


Ta jinjina kai a hankali, "masha Allah! Allah Ya taimaka Ya kuma tsare".

Ameerah tace "ameen!".


Daidai lokacin suka isa ƙofar gida, don haka suka ƙarasa ciki suka hau aiki. Ranar ƙosai suka yi da kunun gyaɗa, ta karawa Yaya Baqeer da shayinshi. Sai Hajja ta bada aka ƙaro biredi ga wanda yake da niyar ƙarawa. Ameerah kam data ƙeƙashe ƙasa tace ba zata ci ƙosai ba, sai ƙwai aka sayo aka soya mata.


Bayan an sha ruwa, Yaya Baqeer ya leƙa ɗakin kamar yadda yake yi, ya yiwa Hajja barka da shan ruwa, suma suka mishi. Daya tashi fita yace masu yin sallah su fita, ita da Huwaila suka tashi, Ameerah ta sake naɗewa akan gado saboda bata samu tsarki ba har yanzu.


Suna fita suka sameshi shi da Isiya da wasu samarin unguwar su uku. Shi ya ja su sallar.

Wata irin ƙira'ah yake mai matukar taushi da burgewa, yadda ma yake tankwasa harshe wajen yin karatun bi-da-bi, kowane harafi yana bashi haƙƙinshi, abin birgewa ne ƙwarai da gaske. Wa zai yi tunanin matashi kamar Baqeer zai iya yin wannan ƙira'ah haka?.

Ta samu kanta da jindaɗin ƙira'ar shi fiye da sauran duk wata ƙira'ah data taɓa ji. Sai tayi ta fatan dama kada ya daina karatun.


Ko da suka gama sallar, ya jima yana janyo addu'o'i masu tsayi, kafin suka shafa. Ya tsaya suna musabiha da mazan, ita da Huwaila kuma suka ɗauke abin sallarsu suka nade. 

Ameerah ta fitar musu da shayin daya umarci a dafa musu shi da samarin. Huwaila har ta bada baya, Ameenatu ta duƙa a gefenshi, tace, "Yaya Baqeer nagode, Allah Ya amfana Ya ƙara buɗi!".

Daga kallon da Ameerah ta mishi, ya gano ko akan me take yin godiyar. Sai kawai ya ɗaga mata hannu, cikin rashin sanin abin cewa. Haka Allah Ya halicce shi, bai cika son yayi abin arziƙi a dinga binshi da godiya ba. Sai ya dinga jin wani iri.

Ganin haka ita kuma sai ta tashi ta koma ɗaki.


*


A daren ranar suka fara Tahajjud, wadda shi ya sake jansu kamar ɗazu, a tsakiyar falo.

Bayan sunyi sahur, sunyi sallah, Ameenatu ta kwanta akan gado. Sanyin iskan asuba yana hurata, ta lumshe idanu, wani ɗan faint murmushi akan leɓɓanta. 'She could get used to this!', ta tunana hakan a cikin ranta, kafin wani barci mai nauyi ya ɗauketa.


*


Kwanakin da suka biyo baya haka suka dinga wucewa in a sequence. Kullum ita take dafa mishi shayi a hada da abin buda baki akai mishi. Ranar nan ma da tayi dare a gidan Indo lokacin da tayi rashin lafiya taje tayata aiki, sai Huwaila ce ta dafa mishi shayin. Ranar bai sha ba, duk da bai fita ya nuna bacin ranshi ba. Ya dai tambayi Hajja yadda aka yi shayin ranar yayi 'so bland' babu taste din kayan kamshi sai uban lemun tsami kamar me! Tace, "kyale Huwaila da shiririta, wai kayan shayin ne suka kare kuma ba taga wadanda aka shanya na jiya ba shine ta dafa shayin a haka!".

Bai ce komi ba. Washegari da hantsi sai ga Isiya niki-niki da kaya, wai Baqeer din ya bashi kudi yaje kasuwa ya hado kayan shayi. 


Ana sallah saura kwana biyu shima Affan ya sauka. Anan gidan shima yayi masauki saboda ganin Baqeer yana nan. Da yamma kuma sai ga Ameer da Daddyn Abuja. Ita Mami a Yobe zata yi tata sallar. 

Ranar sallah duk tare suka tafi wajen sallar idi, sai da suka dawo ne suka tsaya suka ajiye mazan a gidan Anty Momy. Ita kam da yake ma akwai aiki da yake jiranta a gida, don da kyar ma Hajja ta barta taje masallacin. Sai Daddyn Abuja ya maidata gida, sannan shima ya kara komawa gidan Anty Momy wajen karamar walimar da suka hada ta sallah. 


Tana zuwa gida ta cire leshin da suka sanya anko ita da Ameerah na wajen Yaya Baqeer, ta dauki riga da zani na atamfa ta sanya ta fada kicin. Aiki aka kaiwa Hajja na masa daga nan makotansu, abincin sallah da na rabo kusan kwano hudu. 

Suna gamawa suka zuba a cikin manyan kuloli da aka kai, suka dauka suka kai ita da yaran gidan. 

Sai bayan data gama kimtsa ko'ina sannan ta zauna ta karya. 

Daga nan ta kira su Nana da mahaifiyarta ta musu barka da sallah.