Seventeen
Bayan sallah da kwana biyu su Ameerah suka yi niyar komawa. Shi Daddyn Abuja da Ameer tun a washegarin sallah din suka juya.
Ana washegarin zasu tafi sai ga Fauzah da yamma, Affan ya kaita wanda shima yake haramar komawa wajen karatunshi.
Huwaila da Ameerah sun je gidan Indo lokacin Ameerah zata mata sallama, ita kam da take jin alamun ciwon kai a jikinta tace musu sai sun dawo.
Ta mike daga kishingidar da tayi lokacin da suka yi sallama suka shiga dakin. Ta musu sannu da zuwa. Ba tare data jira taji ko sun amsa ko basu amsa ba, ta tashi ta fita daga dakin kamar yadda ta saba yi. Bata bari ta zauna musu a daki balle a zargeta da jin hirar da kunnuwanta basu kamata su ji ba. Yaya Baqeer da Daddyn Abuja ne ma basu damuwa da wanzuwarta a dakin idan suna nan. Don sau tari ko tayi niyar tashi zata fita sai su ce tayi zamanta.
Falo taje ta zauna tana kallon tashar mbc 3. Bata yi mintuna biyar da zama ba sai ga Affan ya shiga falon shima ya zauna a can gefenta. Ta kalleshi a kaikaice, tana tunanin ko nan dinma ba'a so ta zauna ne?.
Tana kokarin tashi ta fita can waje inda ba za'a bita a koreta ba, taji ya mata magana.
Ta kalleshi da mamaki a cikin ranta, tun yaushe ne Affan ya fara yi mata magana a cikin radin kanshi?.
Yace, "kallo kike yi ne ke kadai?".
Ta gyada kai tana binshi da kallo intently. Bata san ta yaya zata iya mu'amala da Affan dinnan ba. Affan mara kirki mai son ya muzantata a duk wata wucewar dakika? Wannan kam ta san ta yadda zata bi dashi. Amma Affan mai nuna mata tsololon kirki kamar duk duniya babu mai mutunci kamar sa? Bata san ta yaya zata iya dashi ba.
Yace, "Hajja tace kema karshen satinnan zaki koma ko?".
Ta sake gyada mishi kai.
Hannu ya sanya a aljihu ya ciro wayarshi ya mika mata, ta kalleshi da mamaki.
Yace, "sanya min lambarki a ciki, kinga sai mu dinga gaisawa. Don nasan idan muka bar nan ba lallai mu sake haduwa ba kuma, tunda ni dai ban cika zuwa Nigeria sosai ba".
Ta bi wayar tashi da kallo kamar wata abar tsoro, wata rantsattsiyar waya da case dinta ma kanshi sheki yake yi, bata san ko wace iri bace ba, amma tasan ko kasheta za ayi ba zata iya sanin ta ina zata kunna ta ba.
Cikin sanyin murya tace, "bani da waya ai!".
Ya dubeta da mamaki zane akan fuskarshi, kamar wata wadda ta tsiro da sabon kai daga wuyanta. Kafin taji ya fashe da dariya, har yana hadawa da dukawa yana kama ciki.
Ta bishi da kallo tana jin ranta yana suya, dama me take tsammanin gani daga Affan wanda ya wuce rainin wayo? Wato rashin wayarta a wajenshi ma abin ban dariya ne, saboda yana mata kallon yar kauye wadda bata san ta yaya zata iya rike waya ba?.
Yace, "da girmanki ace baki da waya? Saboda me? An hana ki rikewa ne ko kuma dai baki da niyar rike waya ne?".
Ta daga mishi kafada kawai. Kafin ya sake jefa mata wata tambayar, taji Hajja tana kwala mata kira. Ta kalleshi na dan lokaci kafin ta tashi da sauri tayi daki.
Fauza na kwance akan gadon Hajja ta dora daya-kan-daya da waya a hannu tana dannawa.
Hajja ta cewa Ameenah, "dauki makullin dakin su Fauza ki gyara, ashe anan zata kwana".
Wani abu ya tukota a cikin ranta kamar zata fasa ihu. Bata ce komi ba ta dauki makullin a gaban Hajja ta fita daga dakin ta bude wanda su Fauza din ke kwana a ciki. Babu abinda yake bakanta mata rai sai yadda suke zuwa kai tsaye, gaba-gadi, su ce a gyara musu wajen kwana. Kamar yan aiki kawai suka daukesu. Kamar basu da wata daraja wadda ta wuce ta bayi a wajensu.
Allah Yasa ma dakin bai wani yi kura da yawa ba, da alama basu jima da zuwa gidan ba.
Ta karkade ko'ina ta goge. Ta tattara wasu kwalaye da babu komi a ciki sai dan burbushen abinci da kasusuwan kaza, babu mamaki zuwansu na karshe suka kasa cin abincin gidan Hajja suka sayo nasu, amma kuma shine fitar dashi ya gagara.
Ta bude wardrobe da take cike da kayan sawarsu kala-kala, nan ma ta kade, ta ware wankakkun kaya dana datti, a ranta tana mitar yadda gardama-gardaman yan mata kamarsu suka kasa iya gyara wajen sanya kayansu.
Tana gamawa ta koma ta maidawa Hajja makullin. Fauza bata tsaya jiran komi ba ta tashi ta bar dakin. Tana shirin zama a gefen gadon, Hajja ta katseta da cewa, "an kunna mata abin kamshi a dakin?".
Ta girgiza mata kai.
Nan da nan ta hau fada, "wannan wane irin sakarci ne haka? Tashi maza ki dauki turaren wuta tunda suna da kaskon turarawa kije ki sanya mata a dakin".
Bata ce komi ba ta sake tashi, ta dauki turaren wutar, ta koma dakin. Fauza ta cigaba da kwanciyarta akan gado tana chatting abinta. Har ta jawo burner ta jona a jikin socket ta kunna, bata daga kai ta kalleta ba.
Sai data juya zata fita, har ta kai bakin kofa, sannan ta jiyo muryarta daga bayanta, wai, "me za'a dafa yau da dare?".
Ta juya a hankali tana kallonta, tana so ta gaya mata magana dai-dai da ita, amma wani bangare na zuciyarta yana hanata. Har kullum tana tunanin alaka da kuma mutuntakar da basu nuna mata kafin tayi wani abu. Sai ta daure ta hadiyeta, tace, "ban sani ba nima, ki tambayi Hajja mana".
Ta bude kofar ta fita abinta.
⋆⋆
Spaghetti suka dafa ranar da dare. Aka zuba a kuloli aka kaiwa su Baqeer nasu, itama Fauza da tunda ta shiga daki bata fita ba, aka ba Huwaila nata ta kai mata. Sai gata ta dawo tana yatsina fuska da kular a hannu. Hajja tace, "lafiya kika dawo da kula a hannu?".
Ta tabe baki tana zama yaraf kusa da Ameenatu, "cewa tayi ita bata cin taliya dafa-duka!".
Nan da nan Hajja ta fara dube-dube, "me tace tana so a dafa mata ne? Ke Ameenah, tashi kije ki nemo indomie a dafa mata taci, ba dadi mutum ya kwana da yunwa!".
Huwaila tace, "ai cewa tayi za'a kawo mata abinci, tayi waya".
Sai sannan hankalin Hajja ya kwanta, tace "to! to madallah. Hakan yafi ai!".
Ameerah ta dan gyada kai, tace "lallai Anty Fauza na hutawa. Mu a gida mun isa a dafa abinci muce ba zamu ci ba har mu samu wanda zai kawo mana? Ai sai dai mu kwana da yunwa kuwa!".
A ran Ameenatu tace "hakan ai shine dai-dai!".
Ameerah na zaune tana hada kayanta a cikin trolley dinta, Affan ya shigo dakin da wata leda a hannunshi. Ya zauna a gefen Hajja yana tsokanarta, Ameenatu kuma na kusa da Ameerah tana tayata hada kayan, yayin da Huwaila ke wasa da kan wayar Ameerah.
Affan ya mikawa Ameenatu ledar, da mamaki ta karba ta bude. Kwalin wayar infinix sabuwa dal ce a ciki, Ameerah tayi tsalle tana wartar wayar daga hannun Ameenatu ta cirota daga cikin kwalin.
Babbar wayace mai kyau. Hajja tace, "kai Affan, har da dawainiya haka? Kai kam baka gajiya sam. Allah Yayi albarka, an gode!".
Yace, "naga ai kamar yanmata kamar ta duk suna da wayoyi ne, ita kuma bata da ita!".
Hajja ta tabe baki, "babu yadda ban yi da ita akan ta bari in fadawa AbdulKareem ya sayo mata ba, tace ita bata so. To ya zan mata?".
Ameerah uwar yan rawar kai har ta ciro sim card da aka hada a cikin ledarshi ta hada da wayar ta kunna.
Ameenatu da ta rasa bakin magana. Na farko dai ita ba ma'abociyar son rike waya bace balle ma babbar waya kamar wannan. Na biyu kuma taraddadin karbar waya daga hannun Affan. Har yanzu bata san ta yadda zata iya sabawa da wannan sabon hali nashi ba. To amma kuma dai tasan cewa babu mai maida hannun kyauta sai shaidani. Don haka ta daga baki ta mishi godiya sosai.
Huwaila kuma ta kalleshi tana turo baki tace, "Yaya Affan shine ni baka sai min ba ko?".
Yace, "to banda rigima irin taki Huwaila, waya biyu kike son rikewa ne ko me? In ban manta ba dai nasan cewa na sayi waya na baki".
Tace, "tun yaushe aka sace ta?".
Yace, "to ai ban sani ba, bari dai mu gani to kafin in tafi".
Ta gyada kai tana murmushi cike da murna. Nan dai ya musu sai da safe ya tafi.
Yana bada baya sai ga Yaya Baqeer shima ya shiga. Suka gaisa da Hajja, tace, "ina ka shiga ne haka? Ko fita kayi?".
Ya gyada kai a hankali, idanunshi akan su Ameerah da take ta kokarin nunawa Ameenatu yadda zata sarrafa sabuwar wayarta.
Hajja ta kalli su Ameerah din tayi murmushi, tace "ina ruwan Ameerah manya, wai waya ce Affan ya kawowa kanwarshi Ameenatu, shine take ta kaudin ta koya mata".
Ya jinjina kai a hankali yana kawar da kallonshi daga kansu, yace, "ya kyauta kwarai. Allah Ya amfana".
Hajja tace "ameen".
Bai dade ba shima ya musu sai da safe ya fita. A hankali ya taka zuwa dakinshi, aljihunshi dauke da nauyin kwalin waya.
Sai da suka gama hada kayan Ameerah sannan ta ciro jarkar data hadawa Ameerah humra a ciki, wannan karon mai yawa ta hada mata yadda zata dauketa lokaci mai tsayi kafin ta kare. Tace mata, "sai dai ki barta ta kara jika sosai yadda kamshin zai fita".
Ta amsa da murna sosai, "babu komi ai, zan jira. Nagode Anty Ameenah!". Ta gyada kai.
Sai wajen karfe tara na safe su Ameerah suka dauki hanyar tafiya. Shayi da biredi aka dafa musu da soyayyen kwai, suka ci suka yi nak, kafin suka tafi.
Bayan tafiyarsu Ameenatu da Huwaila suka koma daki. Suna shiga Huwaila ta rarumi wayarta ta hau latse-latse. Ita Ameenatu da yake wayar ba damunta tayi bama, yadda Ameerah ta ajiyeta jiya da dare bayan ta gama loda mata lambobin wayarta dana Daddynsu har da ta Yaya Baqeer, haka Huwaila din ta sake daukarta.
Sai wajen karfe sha daya sannan Fauzah da Affan suka tashi daga barci. Dama can su din ba wasu masu tashin wuri bane.
Da aka musu tayin shayin da aka ajiye musu, Affan yace shi dai ba zai sha shayi ba, Fauza ma tace itama haka.
Hajja tace "to bari a tashi a dafa muku ko yar shinkafa ce!".
Sai suka kalli juna shi da kanwar tashi suka kwashe da dariya, abinda Ameenatu ta kira zallan rainin wayo.
Fauza tace "haba Hajja, shinkafa dai da wannan safiyar? Ina laifin indomie?!".
Hajja tace, "to bari a bada sai a sayo".
Affan yace yana zuwa, ya tashi ya fita.
Can sai gashi ya dawo da indomie kwali har da kifin gwangwani. Ya ajiye a gaban Hajja, nan kuwa ta hau sanya mishi albarka kamar bakinta zai fado kasa.
Ta cewa Huwaila ta tashi taje ta dafa musu.
Affan yayi saurin tareta, yace, "Rufa mana asiri Hajja! Salon taje ta kara zuba mana daddawa a ciki irin yadda ta mana ranar nan? Ameenatu daure ki dafa mana don nasan ke taki dahuwar tafi kama data yan birni".
Huwaila ta fara buga kafa a kasa tana cewa itama ai yar birnin ce, yayi dariya kawai. Ameenatu tace mishi, "me za'a yiwa kwan ne? A dafa ko kuma a soya?".
Yace, "dafawa zaki yi".
Fauza tayi caraf tace, "ni kuma a soya min!".
Ameenatu tasan cewa a yadda ko wasu kwanakin Allah Fauza take kara kure hakurinta, lalle watarana tura zata kai bango.
Ta dauki indomie guda uku da yake manya ce, da sardine din, ta tafi kicin ta hau dahuwa. Tana saukewa ta zuba a farantai, ta kaiwa Affan nashi, sannan ta dauki ta Fauza data koma dakinta ta kai mata.
A tsakiyar dakin, kwalin pizza ne da aka ci rabi, aka bar rabin a yashe a tsakiyar dakin, ta riga ta gama lalacewa ta yadda babu yadda zata amfanu sai dai a kaita shara. Da yake ba a wannan lokacin Ameenatu ta fara ganin hakan ba, sai kawai ta kawar da kanta ta bar dakin.
Sai washegari su Affan suka wuce gidansu, shi dai da alkawarin kafin ya koma zai sake zuwa ya yiwa Hajja sallama. Dama Allah-Allah take akan su tafi, don kuwa ta riga ta gama sikewa da tsirfar Fauza. Gani take yi kamar iskancinta karuwa yake yi a ko wane kwana da yini. Kome aka yi mata bai mata ba, sai an sake mata wani. Ga wani kyararsu da hantararsu data dinga yi ita da Huwaila, har sai da Affan da kanshi ya tsawatar mata sannan.
Tunda suka tafi ake neman wayar Ameenatu da aka jona a jikin caji aka rasata. Sai can da magriba Huwaila ta tsintota a kicin, a bayan firjin, cikin bokiti cike da ruwa tsundum... Yadda aka yi taje can? Allah kadai ya sani.
Hajja tace a barta, zata kira Affan sai ya kaita wajen gyara.
Ameenatu tace a'ah ta barshi kawai don babu ma ta yadda za ayi wayar nan ta tashi, Allah kadai yasan lokacin data dauka. cikin ruwan kafin a cireta. Ta kuma san da kyar idan bai ce zai sake sayo mata wata wayar ba.
☆
Bata taba jin dadin ganin karshen sati ba sai wannan karon. Ranar Lahdi tun da safe ta hade kan kayanta tsaf a cikin jaka. Tun jiya ta gama yin sallama da duk wadanda ya kamata. Da yake ta sake yiwa wata mata kwangilar humra data kai mata, aka sallameta, da kudin ta shiga kasuwa ta musu sayayyar tsaraba.
Tana gama sallar Azuhur tayi sallama dasu Hajja ta nufi Dutsin-ma.
Ta koma ta samu su Nana da abokanta sun sha kewarta har sun gaji.
Washegari suka koma makaranta, aji shida.
*****
Har ta dora sanwar dare, ta tuna babu magin girki. Gidan ita kadai ce, Nana ta fita wajen gaishe-gaishe. Ba'a jima ba da Hauwa ta tafi gida bayan taje sunyi wani aikin makaranta da aka basu. Kimanim sati uku kenan tun bayan data dawo daga Katsina. Komi na rayuwarta ya koma daidai kamar yadda ta saba yi da.
Ta duba cikin kwanon da take ajiye kudin tuwon madara da iloka, ta dauki naira hamsin ta fita. Da yake yamma ce, rana ta fara alamun faduwa.
Shagon Bangis cike yake da samarin unguwarsu har ma da yan ba-ni na-iya dake wajen unguwar.
Samarin sunyi kashi-kashi, wasu a cikin tiredar, wasu kuma suna daga can gefe a waje saboda kasancewar tiredar karama ce, ba zata iya daukar su duka ba.
Tun kafin ka karasa shiga shagon ma zaka ji warin taba yana shiga hancinka. Shi yasa ta tsani zuwa shagon, ko ba don hayakin tabar da zaka shaka ko baka so ba, sai don saboda yanayin mutanen dake yawan ziyartar shagon. Sun fi yawan kiran mutanen yan daba ko yan bangar siyasa, wasu da kananun makamai ma zaka gansu a hannu, wasu sun sarkafe adda ko hauya a kugu da wuya. Da ba don inda ta saba siyayya yayi nisa ba, kuma ta riga tayi daren girki, da babu ta yadda za ayi ta je wannan shagon.
Ta rakube gefen wasu samari su uku da suke ta faman tada hayaki kamar tashin duniya, ta mikawa Bangis -mai shagon-, kudin hannunta. Tace, "magi mai tauraro zaka bani na talatin da aji-no-moto na ashirin".
Ya zuba mata a leda fara ya mika mata. Ta juya kenan, wani daga cikin matasan uku ya fesar da hayakin daya busa, ya sauka akan fuskarta. Ta sanya hannu tana koreshi tana tarin daya sarketa sakamakon shakar tabar da tayi har cikin makoshinta.
Ta bude idanunta dake mata zafi, babu mamaki ma sunyi ja, ta saukesu akan wanda ya aikata mata wannan ta'addanci.
Babu abinda ya dauki hankalinta a tattare dashi sai idanunshi, irin idanun dake nuna wuya da tsananin duhun rayuwa da suka gani, suka kuma jure. Duk rashin kunyar mutum, karya yake yace zai tsaga tsakiyar idanun mutumin nan yace zai mishi rashin kunya. Don haka ne yasa ta kame bakinta, yar Allah Ya isa din data dauko daga cikinta zata yi, ta tsaya a makoshinta. Ta sadda kai ta kara rabawa ta gefensu.
Bata sani ba, wani abu game da wannan bakon mutumi da bata taba gani ba, seems nagging. Ta kasa fitar dashi daga cikin ranta. Dai-dai zata karya kwana, ta juya tana kara kallon tiredar.
Yanzu ya fito daga cikin tiredar, yana tsaye daga waje. Sai dai kaifafan idanuwan nan nashi suna kanta kyam. Wata irin kunya da faduwar gaba suka rufeta, musamman dan guntun murmushin da taga yana yi mata. Tayi saurin yin kasa da kanta, wani dan karamin murmushi itama yana ziyartar fatar bakinta, kafin ta juya da sauri karya kwanar.