8
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 8```
________Fargabar yanda idan Halime ta farka da wani idon zata kalleta ne ya mamaye zuciyar Inna.
Duk zafin ƙiyayyarka da Halime sai ka tausayamata. Lokacin data farka taga babu ƙafafuwanta kuka mai haɗe da ihu tasa tana ƙoƙarin miƙewa tsaye taga ko mafarki takeyi,fizge-fizgen da takeyi ne yasa dole aka yimata allurar barci.
Bala ne yake ta hidimar komai da duk kuɗin da aka kashe.
Har aka sallami Halime daga Asibiti kullum cikin kuka take ba dare ba rana.
Lokacin da'aka sallame su ƙauye suka wuce domin takaici bazai bar Inna komawa gidan Mallam Shehu ba saboda habaicin Inna Huwaila da zai ninka na da, wanda batajin zata iya jurewa.
Tururuwar zuwa duba Halime ƴan uwan da abokanan arziƙi har da maƙota sukayi ta yi,sai dai dayawan su ganin ƙwaƙwaf ne yake shigo da su.
Alhaji Isiyaku shine yayan Mahaifin Halime Uwa ɗaya Uba ɗaya ragowar kuma duk Uba ne ya haɗasu a hannushi dukiyar Halime yake, shiyasa ƙwaɗayinshi ya fi na ragowar tasiri akan dukiyar. ɗan shi ɗaya a duniya Salmanu daya ɗauki burin duniya ya ɗora akanshi.
Salmanu kyakkyawane sosai mai farin jinin ƴammata burinshi ya fi na Halime zurfi,baya kula Matan ƙauyen saboda har cikin ranshi kallon gidadawa yake mu su.
Burinshi ya yi Ilimi mai zurfi ya zama likitan ƙwaƙwalwa( Neurologist) ya auro mace kyakkyawar gaske suyi zaman su a birni.
Ɓullowar zancen auren da Baba Isiyaku ya haɗa na Halime da Salmanu ne ya tashi hankalin Inna da ita kanta Halimen. "tayaya matashi kamar Salmanu zai karɓi aurenta lamarin da cutarwa aciki".
Shima Kuka ya zauna yi gaban Mahaifinshi kan bai yarda da auren ba.burika kala-kala daya tsara Salmanun zai mora cikin ruwan sanyi yasa yayi biris da shi batare da ya tanka mai ba.
Da sassafe ta fara haɗa kayan su ranta na suya,Halime dake kallonta cikin mamaki tace"Inna ina zamuje".
"Gida zamu koma Halime"Inna ta faɗa tana cigaba da haɗa mu su kayan su.
"Mezanje yi Inna?burikana sun ruguje koda na koma sabon Suna zasu ƙara samun da zuciyata bazai ɗauka ba,duk azabar da yaya Salmanu zaiyimin saboda ƙiyayayata dake cikin zuciyarshi bai isa ya kashe ni ba, zan rayu ne dai-dai adadin kwanakin da Ubangiji ya ƙayyade min" bayanan Halime baƙaramin sanyayya jikin Inna sukayi ba,cikin tsananin kuka ta tashi ta rungumeta suka cigaba da kukan tare.
Gidan mai kyau Baba Isiyaku ya siya da kuɗin gadon Halime, acewarshi Salmanu ba shi da muhallin da zaisa Halime, isu-isu suka hau rigimar gano manufarshi na liƙawa Halime ɗanshi.
Babu wanda ya san da ɗaurin auren sai iya mutanen cikin gida domin daga shi har Salmanu kunya sukeji ace ga kalar matar da Salmanun zai aura.
Zaunar da Salmanu ya yi kamar mace yana mishi huɗubar ya tabbatar ya kasance da Halime a wannan daren,shi kuma ya mishi alƙawarin biya mishi kuɗin zuwa Makarantar share fagen shiga jami'a.
Please follow my account