DUNIYA BIYU

Nineteen

by @jeddahlawals

*_Dutsinma-*


Cikin satin gabadaya ta kasa samun sukuni, idanuwan wannan bawan Allah data gani a shagon Bangis sun ki barinta har a cikin barcinta suna nan, haunting her. Duk nisan da makaranta take mata idan tabi ta wajen shagon Bangis hakan baya damunta, so take yi kawai ta sake ganinshi. Abin har mamaki yake bata. Abu sai kace wadda aka wa asiri? Daga ganin mutum rana daya kawai, tabi ta rikice a kanshi. Ga karatunsu da yayi tsauri saboda extra lessons da ake musu tunda jarabawar waec tana ta kara matsowa.


Ranar Litinin da yamma sun dawo daga makarantar islamiya, Hauwa'u da Basariyya sun sanyata a tsakiya. Su dukansu sanye suke da kayan makarantarsu na islamiya, ta rataye jakar makarantarta a kafadarta.

Sun zo bakin titi suna ta yan hirarrakinsu, suka tsaya suna jira su samu damar tsallakawa, wasu matasa su uku suka wucesu akan mashin. Kamar ance ta waiwaya, suka hada idanu da na karshen kan mashin din. Taji zuciyarta tana wasu irin abubuwa, wannan saurayin ne na shagon Bangis. Kallon-kallo suka dinga yi dashi har suka bace mata, sannan ta juya a sanyaye tana kallon kawayenta da suke hirarsu ba tare da sun kula da halin da take ciki ba. A sanyaye suka tsallaka su duka har zuwa inda suka saba rabuwa, Hauwa ta shige gidansu, ita da Basariyya kuma kowa tayi hanyar gidansu.


Tana zuwa gida ta hau taya Nana aikin sanwar dare, bayan sun gama girkin ta hada kan kayan ta wanke ganin dare bai riga yayi ba. Tana cikin yin aikin aka kira sallar magriba, don haka ta dauro alwala tayi sallah.

Suna gama cin abincin dare din ta dauki hijabinta ta tafi gidansu Hauwa'u kallon fim din Tarkon Kauna da ake yi a tashar arewa24.


Kwanakin da suka biyo baya Ameenatu tayi sune kawai ba don tana fahimtar yadda suke wucewa ba. Ta samu kanta a lokuta da dama tana tunanin wannan mutum, wasu lokutan har da mafarkin zaune akan sun fara magana ita dashi suna abokantaka dashi da zumunci.


Ranar juma'a bayan sun dawo daga makaranta, ta samu Nana ta tafi dubiya da gaishe-gaishe ita da abokanta. Ta dafa musu taliya 'yar hausa tare da share gidan. Da Baba Habu ya dawo daga masallaci, ta kai mishi abincin da ruwa ita kuma ta koma cikin daki tana kara gyara dakin. Daya gama ya tafi bakin kasuwa inda ya saba zama, ita kuma ta shimfida tabarma ta dan shingida anan.


A hankali taji mararta ta fara mata ciwo, dama tunda safe a makaranta ta fara jin alamun period dinta. Ta lumshe idanuwanta tana jiran tsammani.

Sai kuma tayi zumbur! Ta mike lokacin data tuna ashe fa bata da pad. Da sauri ta shiga dauki ta dauko hijabinta. Ta bude adakar Nana inda take mata tarin kudinta, a ranta tana ayyana yakamata tayi iloka da tuwon madara gobe da safe ta kai makarantar islamiya.

Kudi ta dauka ta fita. Tasan shagon Dantala da kyar idan ya fito tunda ranar juma'a bai cika bude shago da wuri idan ya tafi masallaci ba. Shagon Bangis ta nufa kai tsaye.


Tiredar tashi kamar kowane lokaci babu kowa a ciki, amma daga can gefe matasa ne a zazzaune suna ta faman bankar iska kamar tashin duniya. Kunya ce ta sanyata yin kasa da kanta ba tare data tsaya duba ko su waye da waye a wajen ba.


Bangis din yana ganinta ya tashi da sauri ya tsallaka. Tace mishi, "don Allah kana da pad din virony babba?". Duk cikin tarin pads virony kadai tafi dadin jin amfani da ita.

Ya kalleta da kyau, "virony kuma? Sabon biskit ne ko alewa?".

Duk da tsabar ciwon marar dake ciwota, bata san lokacin data kwashe da dariya ba har tana dukawa kasa.


Bangis ya shaka, ya harareta, "Malama meye haka zaki zo har wajen sana'ata ki kuma sanyani a gaba kina min dariya kamar kinga wani sabon kamu?".

Tana shirin bashi amsa taji ance daga bayanta, "Baaba ka zuba mata kauyanci ba dole ta maka dariya ba? Banda kwalwarka ta cika da hayaki da dusa, waye bai san meye pad a wannan zamanin ba? Tana nufin kunzugun mata na bature to!".


Bangis ya juya yana harararshi, cikin irin muryar nan ta cikakkun yan daba yace, "Kai Gaula! Banson shiga sharo ba shanu fa! Ina ruwanka da wajen sana'ata ne? Ka bace min daga nan tun kafin in sassaba maka kamanni fa!!".

Matashin shima ya harareshi da wadannan idanuwan nashi da suke reeling Ameenah in, yace, "kai kauce daga nan Baaba!! Kasan ko fili aka bamu anan wajen tuni zan zubar da kai kasa kafin ka rufe idanuwanka ka bude!". Bangis ya dan ja da baya kamar cikin tsoro, kafin kuma daga baya ya kara tsayawa akan kafafunshi cikin dakewa.


Kafin yace wani abu matashin ya juya ga Ameenah, sai taga alamun fuskarshi ta dan sassauta, yace mata, "ba lallai ki samu irin wadannan abubuwan anan ba sai dai ko bakin kasuwa haka ko can sama", cikin lafazi mai taushi.

Ameenah ta gyada mishi kai kawai tana kokarin juyawa, yace, "akwai wani chemist a karyin kwanar can, nasan zaki iya samu acan. Muje in taka miki".


Ta daga baki da zata musa mishi, taga irin yadda yake kallonta without budging, daga gani duk abinda zata fada mishi ba zai canza mishi ra'ayi ba, don haka ta gyada mishi kai hesitantly kawai.

Suka jera suka fara tafiya babu mai cewa wani uffan a cikinsu. Sai da suka yi nisa sannan taji yaje, "menene sunanki?".

Maganar kamar daga sama haka taje mata, watakila shi yasa ta dan tsorata, sai data saisaita kanta, tace mishi "Ameenatu!".

Ya gyada kai yana dan murmushi hade da kara maimaita sunan, tasting, "Ameenatu... Suna mai dadi!".

Sai tayi kasa da kanta a kunyace.


Yace, "Sunana Amadu... Ahmad!".

A ranta tace, "sunan ya dace da kai!", amma bata fito fili ta fadi ba. Daga haka bata kara cewa komi ba har suka karasa kemis din. Can wajen bakin kasuwa yake, suka shiga tare shi da ita, ta fadawa mai shagon abinda take bukata. Ya fada mata kudin, taji ma tayi sauki akan yadda ta saba saya. Tana kokarin mika mishi kudi taga shima Ahmad ya yana mika mishi, ta kalleshi tana girgiza kai da sauri, "a'ah!! Gaskiya kayi hakuri, amma ba zan bari ka biya min ba!".

Yace, "saboda me?".

Tace, "haka kawai!". Kafin yayi yunkuri tayi saurin mikawa mai shagon kudin, ya kirga tare da bata canjinta. Ta amsa, suka juya suka fita ledar daya sanya mata pad din rike a hannunta.


Suka sake daukar hanyar komawa ta inda suka fito, tana lura da yadda yake ta satar kallonta alamun yana so yayi mata magana ko wani abu amma bai ce komi ba. Zuwa can kuma sai taji yayi gyaran murya, yace, "ina yawan ganinki anan wajajen, ke yar nan unguwar ce?".

Ta dan gyada mishi kai tana murmushi, "ehh, nan bayan gidan Alhaji Kallah Naira".

Ya dan bude idanu, "ai muma can wajajen muke, bamu da nisa dasu".

Tace, "amma kaima dan nan wajajen ne? Ban taba ganinka ba sai a yan kwanakinnan da suka wuce".


Yace, "eh mana! Kawai dai ban cika zama anan din bane shi yasa!".

Suna yan hirarrakinsu har suka karasa kofar gidansu Ameenah din, yace, "to sai anjima Malama Ameenatu!".

Kunya ta kamata, ta juya da sauri zata shige gida, sai taji yana kiran sunanta. Ta juya tana kallonshi cikin alamun tambaya, ya dan shafa bayan wuyanshi alamun nervousness, yace, "uhm... cewa nayi dama... tunda muna unguwa daya, zan dinga lekowa muna gaisawa lokaci zuwa lokaci. Ina fata babu damuwa?". Murmushi ta saki a hankali, "ehh, babu damuwa!".

Shima yayi murmushin, "yayi kyau. Nagode Malama Ameenah". Ta fada gidan da dan sauri don kada yaga yadda fuskarta tayi flushing.


Ta maida kyauren gidan ta rufe, ta koma ta jingina a jiki tana murmushi mai kama da dariya. Sai data gama hucewa sannan ta karasa ciki ta kimtsa kanta.


Daga wannan rana suka zama abokai ita dashi, idan sun hadu a cikin unguwa zasu gaisa, haka lokaci zuwa lokaci ya kan leka gidansu su gaisa ita dashi. Wani lokaci da Baba Bala ya dan samu karamin hatsari a hanya, wani mai mashin ya bugeshi har ya dan kurje, da Ahmad din yaje dubashi ya shiga har cikin gida suka gaisa. Yayi shiga ta kamala, wadda bata taba gani a jikinshi ba. Rigar shadda da wandonta har da hula, ya kai musu kankana, lemu da balangu. Suka yi ta sanya mishi albarka.


Tunda suke dashi bai taba furta mata kalmar so ba, and she's fine with it. Bata taba zaton mace da namiji zasu jima suna tare, zama na mutunci da girmamawa ba tare da kalmar so ta shiga tsakaninsu ba sai a lokacin.

Haka bai taba daga baki ya nufeta da wata magana ko wani abu na banza wanda ba daidai ba, haka halayen daya nuna mata so far, masu kyau ne. Ba irin halayen yan daba ba, bana banga ba, bana yan iskan kan titi ba. Halin mutum mai ilimi da sanin ciwon kai ne, shi yasa take girmama shi saboda haka.


Yawan ganinsu tare da abokanta suke yi yasa suka fara mata magana akan hakan, akan ta rabu dashi, shi ba mutumin arziki bane, blah-blah dai, duk tayi biris dasu.


Watarana sun taso daga makaranta da yamma, suka hadu dashi da wasu abokanshi biyu da take yawan ganinsu tare, Huzayfa da Isah suna tafiya, sai ya dan dakata suka gaisa kafin suka wuce inda zasu. Suna bada baya, ta juya tana kallon abokan nata cikin harara, dama sun taba magana akan yadda suke treating dinshi. Wannan shine kusan karo na hudu da suka hadu da Amadu din, amma basu sakar mishi jiki da fuska. Ta kula kuma hakan ba karamin sanyayar mishi da gwiwa yake yi ba, duk da bai taba fita ya fada mata ba.


Ta harari Hauwa'u, "wai meye haka kuke yi saboda Allah da Annabi?? Amadu ba mutum bane kamar ku? Amma haka kawai ba tare da kunsan ainihin waye shi ba ku hau gaba dashi kuna hade mishi fuska, akan me?".

Hauwa'u ta dan hade fuska, "wai kamar ya? Baki ga irin mutanen da yake mu'amala dasu bane? Ko kuwa shi a karan kanshi baki ga yadda yake bane?? Ko kuwa don saboda idanunki sun riga sun rufe da 'so' har ba kya iya bambance mai kyau da mara kyau?".


Taja tunga ta tsaya tana dafe kugu, "ba soyayya muke yi dashi ba! Idan ma kuma soyayyar muke yi wannan ai ba abinda ya dameki bane tunda rayuwata ce ba taki ba! Bansan me yasa kuke yi mishi haka ba amma ina so ku san cewa ina jin dadin mu'amala dashi, ba kuma zan taba rabuwa dashi kawai saboda baku karbeshi ba, don haka sai ku san yadda zaku yi!".


Ta daga kafa da sauri ta fara tafiya, Hauwa'u da Basariyya suka daga kafa har suka kamota. Sai a lokacin Basariyya tayi magana, tace, "amma kinsan mu'amala da mutane irin wadannan ba irin halayenki bane ba ko? Me ma zaki yi dashi? Ke da mutum kamar Malam Hadi yake bibiyarki?".

Ta harareta, "oho! Wato akan maganar Malam Hadi ne kuke yi min haka kenan? To ni bana son Malam Hadi, ba kuma zan taba bashi dama ba. Rayuwata, zabina. Wai shin, mutumin banza ba zai taba dawowa mutum na gari bane ko me kuke nufi? Shi Amadun kun taba zama kunji yadda yake a da da kuma dalilin daya mayar dashi yadda yake a halin yanzu? Baku taba ba! Kun kuma fini sanin cewa it's not good to judge book by its cover!!".


Jikinsu sai yayi sanyi da jin haka, Hauwa'u tayi saurin bata hakuri, "kiyi hakuri Ameenah, mu fa duk cikin damuwa akan abinda zai je ya dawo ne yasa muke yin haka, amma zamu gyara da yardar Allah!".

Bata ce musu komi ba sai kafa data kara dagawa tana sauri, don kuwa ranta ya gama baci kwarai da gaske.

Daga lokacin dai abubuwa suka fara canzawa.


*****


Ahmad, ko kuwa Amadu Goje kamar yadda mutane suka fi saninshi dashi, matashine da yake cikin shekarunshi na ashirin da shida zuwa da bakwai. Mahaifiyarshi haifaffiyar Allo ce dake can Zango a Jihar Katsina. Ta hadu da mahaifinshi Malam Habibu a lokacin da yaje bautar kasa kauyen, suka fara soyayya ita dashi. Yace mata shi haifaffen Dutsinma ne kuma yana so ya aureta, amma sai iyayenta suka kekashe kasa akan basu yarda data aureshi ba. Aka fitar mata da miji a cikin dangi, ita kuma ta badawa idanunta toka akan ba zata aureshi ba tunda tana da wanda take so. Aka yi ta kaiwa da kawowa, daga karshe dai sai wan mahaifinta ne ya daura mata auren ita da Habibu, iyayenta kuwa suka ce su da ita haihata-haihata.

Haka aka yi auren wannan babu wani abin azo a gani sai na wanda dangi suka taimaka dashi kawai, aka kaita gidanta dake Dutsinma. Yawancin kayan daki dana amfani sai shi Habibun ne ya saya.

Suka tare suna ta kwasar amarcinsu ba tare da wata matsala ba. Sai dai tana samun ciki al'amura suka sauya, Habibu ya fara canza mata. Da cewa ma yayi sai dai ta zubar da cikin, ita kuma ta kafe akan cewa tana son cikinta ba zata zubar ba.


A haka har ta haifi danta namiji aka sanya mishi suna Ahmad. Ta haifi Ahmad da watanni uku, rana daya sai tashi tayi ta nemi Habibu a garin Dutsinma ta rasa, neman sama da kasa aka nemeshi amma ya bace bat!.

Ashe iyayen daya nuna mata a matsayin nashi ba iyayenshi bane, na bogi ne. Iyayen abokanshi ne saboda ce musu yayi shi maraya ne, baya da kowa sai Allah. Su kuma suka ji tausayinshi suka mara mishi baya har ya aureta.


Larai tayi kukan wannan cin amana da Habibu ya mata ba kadan ba. Daga baya ta tattara yan kayanta da danta ta koma kauyensu. Taje ta tarar ashe mahaifinta ya jima da rasuwa. Tun bayan yin aurenta ya kamu da rashin lafiya, bai kara tashi ba. Tayi kuka, tayi jimami marar adadi. Mahaifiyarta kuwa tace ita dai ba zata iya riketa a haka ba, duk da cewa kafin mahaifinta ya rasu ya fadi cewa ya yafe mata, hakan ba wai yana nufin zasu karbeta ta koma wajensu bane bayan ta yace musu baya. Haka ta koma Dutsinma cikin dacin zuciya.

Allah Ya taimaketa gidan da suke ciki mallakin Habibun ne kuma bai dauki takardun ba, taci gaba da kula da dan jaririnta cikin dadi da rashinshi. Abokan Habibu na da tun suna dan taimaka mata, har ya zamanto bata ko ganinsu sai lokaci zuwa lokaci, daga baya ma kuma ta daina ganinsu kwata-kwata.


Haka Ahmad ya taso daga shi sai Innarshi. Babu wani mai taimaka musu, su suke komi da kansu, ranar da suka samu kudin abinci da yar sana'ar da Inna Larai take yi suci abinci mai kyau, ranar da bata yi ba kuwa hakanan zasu ci da gamje-gamje.


Yawan zama cikin yara da abokai zauna gari banza ya sanyashi sajewa dasu. Duk da halin da suke ciki, Inna Larai tayi kokari sosai wajen ganin cewa ta sanyashi a makaranta. To matsalar wannan zamani da muke ciki idan ba hanya gareka ba, karatun kanshi sai ya zame maka babbar matsala. A haka ya samu ya gama karatun NCE da kyar, aiki bai samu ba, dama kuma ba dogara dashi yayi ba. Ya biyewa abokai suna bin yan siyasa zuwa wajen kamfen da sauransu. Idan suka yi bangarsu, nairarsu dubu goma sha biyar a hannu cas ake basu duk karshen wata, a ganinshi me yafi wannan? Aikinsu kawai idan wani shugaba zai shigo suje su gyara mishi hanya, idan kuma wani ya mishi ba daidai ba suje su musu ruwan sanda. Idan aka biyasu kuma yayi yan abubuwa a gida tunda yanzu Alhamdulillahi, Innarshi ta samu tsayayyiyar sana'a. Sauran kudin kuma da aka samu, sai a hadu da abokai ayi ta bankar iska. Wai ma don Allah bai dora mishi shaye-shaye da zazzafar akidar yin dabar ba.


Haka rayuwarshi take na wasu lokuta masu tsayi, bai taba jin ta isheshi ba ko wani abu sai daya hadu da Ameenatu. Kai tsaye yaji yarinyar ta shiga cikin ranshi kwarai. Karbarshi da tayi hannu bibbiyu, ba tare da duba da halayyarshi da yanayinshi ba yasa yake kara jinta a cikin ranshi a kullum kwana. Ya kuma fara jin cewa wannan harka da yake yi bata dace data mutanen dake mu'amala da ita ba a cikin ranshi, don haka ya fara ja baya da ita. Gashi nan yanzu yana bin wasu abokanshi zuwa wajen harkar gine-gine da suke yi.

Aikin akwai wahala, amma bai dameshi ba. Saboda ita kadai ranta, zai ma iya yin fiye da haka!.