9
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 9```
________Duk wannan Bayanan na Mahaifinshi bai fuskanci ina ya dosa ba amma har cikin ranshi bayajin son Halime ko É—iso amma zai yi yanda Mahaifinshi ya ce ko dan tafiya ya barta ya huta da auren.
Daga kan uban kayan É—akin da Baba Isiyaku ya yiwa Halime musamman É—akin Salmanu kasan da mugunta aciki balle idan kaji da kuÉ—in gadonta akayi komai.
Tsabar baƙin ciki kafin akai Halime gidanta Inna ta tattara kayanta ta bar gidan.
Lungu da saƙon ƙauyen gulmar Salmanu da Mahaifinshi suke yi tareda tausayin Halime saboda sun san ba don Allah Baba Isiyakun ya haɗa auren ba.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Ba kasafai damuwar wani ke samun gurbi a zuciyarshi ba amma tausayin yarinyar ya tsayamai arai duk da bai ƙara bi takan komai na kai ba saboda kwananshi ɗaya ya bar garin. Tafiyar MAYSARAH United States military Academy ne ya shafe tunanin Halime daga kanshi da ma zuciyarshi gabaɗaya.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Kamar yanda Baba Isiyaku ya yi wa Salmanu alƙawari sai yaƙi cikawa,sai ya ɓullo da bazai biyamishi ba har sai Halime ta samu juna biyu.
Komai na zaman aurenta baya zuwar mata da sauƙi musamman Salmanu da baya iya boye ƙiyayyar da yake ma ta bata ƙazanta tana ƙoƙarin gyara duk wani waje na gidan duk da batajin daɗin tafiya da ƙafafuwa robar da Bala yasa akayimata amma haka take ɗaurewa.
Ganin bashida wani hanya na kaucewa umarnin Mahaifinshi yasa dole ya je ga Halime cikin izgilanci da baƙaƙen maganganu masu zafi.
Bai kula da ita ba duk da yasan tana buƙatar hakan,ficewa ya yi yabar gidan saboda ya tsani kallon mannannen idonta.
Ta yi kuka mara iyaka,cikin dauriya da taurin zuciyar daya fara shigarta ta fara ƙoƙarin gyara kanta. Gudun kowani irin ƙorafi daga bakinta yasa ko kwana agidan Salmanu bai yi ba.
Update anjima In sha Allah
Nafisat
***