MAI KWAĆŠAYI

10

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 10```


________Har gida Matar maƙocin su Halime ta kaiwa Alhaji Isiyaku gulmar abunda ya faru duk da batada tabbaci, saboda Halime ba gwanar surutu bace.


Zagayowar Sati ya biyawa Salmanu komai na Makaranta cikin farin ciki Salmanu ya nufi Zaria tunda dama tuntuni ya gama komai dama kuɗi ne Babanshi yaƙi biya.


Bayan tafiyar Salmanu ya tara dukka ƴan uwanshi kan Halime ta ce acikin gadonta abiyawa Salmanu kuɗin Makaranta saboda goben su da yaran su baki ɗaya. Babu wanda lamarin baiyiwa zafi ba har Inna lokacin da labari yaje ma ta har kuka tayi,sai dai duk cikinsu babu wanda yayi tunanin tuntunɓar Halime.


Har Salmanu ya dawo, komai na Makarantar shi ya kammala batasani ba, saboda sosai take gujewa mu'amalantar mutane gudun ɓacin rai.


Sai bayan tafiyar Salmanu da kwana biyu takejin labari abakin munafukar maƙwafciyarta,a fuska bata nuna komai ba amma zuciyarta kamar zai tarwatse. Bayan ta shige ɗaki tayi kuka sosai dama tana sa rai da cin mutuncin ma dayafi wannan.


Salmanu saboda buƙatarsa sai ya fara dawowa gida akai-akai idan ya kalli ƴan Mata ya more sai yazo ya sauke buƙatarshi kan Halime acewarshi "ga sadaka can ba ɓukatar ya ɓata kuɗinshi wajen bin wa su"

Sai ya zamana ta ɓangare biyu yake morar Halime dukiyarta da kuma jikinta da take lallaɓawa ga hantara kamar baiwarshi.


Dalilin fara ƙeƙashewar zuciyar Halime kenan. Number Bala da ya taɓa zuwa dubata yabata ta nemo duk da tsabar takaici ta yi alƙawarin da bazata nemeshi ba har abada.


A wayar maƙotanta ta kira Bala cikin Kuka ta nemi taimakon kuɗi tanason shiga Makaranta. Kuma ya taimaka mata da sandar dogarawa tana ganin zaifi ma ta daɗi.


Sati biyu bayan nan sai ga Bala har ƙauyen su Halime da duk abunda ta buƙata har Makarantar yaje ya biya mata komai kuma suka bata gurbi a aji ɗayan sakandare da kuma Malamin da zai dinga yi mata darasi bayan antashi saboda ko aji ɗayan sakandaren ta yi girma dayawa amma hakan zai sa ta ƙara hazaƙa.bayan ta shigo gida idanuwanta suka ƙarawa kaɗawa batason ta ƙarayin kuka a rayuwarta,inama da tasan Bala tuntuni da yanzu bata nakasa ba saurin ambaton Allah tayi gudun kartayi saɓo.


Wa su kwanakin bayannan akaga Halime da sabon É—inki kayan Makaranta da sandar dogarawarta.


Tuni magulmata sun kaiwa Baba Isiyaku labari. A haukace ya nufi Makarantar sai dai fafur shugaban Makarantar ya hana shi shiga.


Kamar haɗin baki yana zuwa gida ya samu Salmanu agidan duk da ba ranar dawowarshi bace, bai san kasuwar baƙatarshi ce ta dawo dashiba.


Hamdala yayi yanajin matsalar shi kamar yazo Ć™arshe domin barin Halime ta yi Boko tamkar ya barta da takobin yaĆ™arshi ne.


Tsaf Salmanu ya gama saurarar bayanin Mahaifinshi, atake kuma ranshi ya fara suya wato ta rama kenan yanda ya tafi Makaranta bai sanar da ita ba itama ta shiga Boko bada izinin shi ba kenan to wallahi bata isa ba....✍🏻