MAI KWAÆŠAYI

11

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 11```


________Babu kunya Baba Isiyaku ya bi Salmanu gida saboda tayashi tsawatarwa Halime.


Ba su jima da zuwa ba,ta shigo gidan. Yayi tunanin ganin tsoronshi a idanuwan Halime musamman dawowar bazata dayayi ya kuma kamata ta dawo daga bokon da bai san tafara zuwa ba. Amma sai yaga tana ƙoƙarin shigewarta ɗaki bayan ta gaishe su fuskarta asake saɓanin na su dake ɗaure.

"Ke Halime da izinin wa kika fara zuwa Makaranta?,tukunna ma dawani kuÉ—in kika biya komai? ina magana kinyi shiru ko bakya jinane!" Salmanu ya faÉ—a cikin hargagi yana miÆ™ewa tsaye.daÉ—in maganganun Salmanu ya sa Baba Isiyaku sakin Murmushi yana gyara Babbar Rigar shi.

" Wallahi sai dai ki zaɓi ɗaya ko bokon da kike zuwa ko zaman aure da ni,banda ƙaddara maiya haɗa kamar Ni Salmanu da auren mace takasasshiya irinki"


"Burina mai zurfi ne akan cigaban Rayuwata kuma wannan burin bazai cikaba har sai nayi gwagwarmayar Rayuwa na nemi ilimi,ban tambayi Baba kuɗi ba saboda nasan bazai bani ba duk da haƙƙin ne. Da babu kai acikin Rayuwata hakan kuma bai sa nafasa Rayuwa ba, yanzu ma idan ka rabu dani babu abinda zai canza,kuma kuɗi na da kake karatu da shi ko bayan raina ina binka bashi" ta na gama faɗar haka ta ɗogara sandarta ta shige ɗaki.


Kalaman Halime sunyiwa kwanyar Salmanu girma kenan dagaske gori da habaicin da ake mishi ashe Mahaifinshi yaudarar shi ya yi yace mai ƙaryane da kuɗin shi ya ke biya mai komai.


Cikin sanɗa Baba Isiyaku ya tattare Babban Rigar shi yabar gidan saboda kunyar ƙaryar dayayiwa Salmanu,tuntuni ya kwana da sanin waye Salmanu sam baiyi halinshi na ƙwaɗayi ba,sai dai ya hanga ya hango Salmanu ne kaɗai mafitar shi na samun kaso mai yawa a dukiyar Halime da baisan wahalar yanda aka tarashi ba.



Tun daga Ranar sai zaman Halime da Salmanu ya canza salo domin idan yana gari da kanshi yake rakata Makaranta hantara da kyararta duk sai ya daina saboda tsananin tausayinta dayake ji bayan ya bincika facakar da Mahaifinshi yake yi da kuÉ—in gadonta da sunan kuÉ—in Makarantar shi yake biya.


Bata iya zuwa Birni duba Innarta sai dai ita tazo ta yinar ma ta,sai dai duk ranar da tazo da Kuka suke rabuwa,saboda tsananin tausayinta da Inna takeji.


Shaƙuwarsu da Salmanu ya sa ta yafe mishi dukka kuɗin Makarantar da ake amfani dashi wajen Karatun shi da wanda zasu kashe har yagama.

Aciki suke ci kuma suke sha duk da itama Halime tana ƴan ƙulle-ƙullenta balaifi kuma tana samun ciniki.


Halime ta yi gwagwarmayar Rayuwa wajen ganin ta samu ilimi amma lokacin da take shiga aji huɗun sakandare sai ga cikin da bata taɓa sa rai dashi ba wannan dalilin ya dakatar da duk wani karatu na Halime saboda Wahalar da take sha