MAI KWAÆŠAYI

12

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 12```


________Halime nayin sati bataje Makaranta ba wani sa'in bai fi taje sau biyu ba a wata.

Kulawar Salmanu da dangin Mahaifiyarta ne yafi komai faranta ranta.


Cikin Halime na Wata Bakwai ta haifeshi ba rai bayan baƙar azabar datasha.


Tabbacin Namiji ta haifa kuma ya zo ba rai ne yasa Baba Isiyaku maƙalewa a ɗaki yasha kuka saboda rasa damar shi akaron farko, Addu'a ya shiga yi ba dare ba rana Allah Yasa Halime ta ƙara samun cikin wani ɗa Namijin.



Bayan taji sauƙi ta ɗora da gwagwarmayar neman Iliminta na Boko dana Arabia.Babu wanda baya kwatancen Halime da kuma bada misali da ita.


Har shuɗewar shekara Halime bata samu wani cikin ba, tun Baba Isiyaku na lissafi har lissafin ya fara ƙwacemai.


Bashida yarda shiyasa baya tattauna sirrinshi da kowa amma awannan gaɓar kasa jurewa yayi ya tuntubi Abokanan shi na Majalisa.


"Haba Alhaji Isiyaku kai sai kace ba kai ka haifi Salmanu ba,bazai wuce tsarin Iyalinsu na ƴan Boko ya ɗorata akai ba,banda abinka wayake barin ɗanshi haka sakaka yana bautawa Mace tun wuri kanemawa ɗanka tsari" Mallam Barau ya faɗa ragowar na ƙara yimishi fanfo.

Sune suka jagoranci Baba Isiyaku in da yakai Sunan Salmanu.


Salmanu ba mutum ne mai yaÉ—a sirrin iyalinshiba ko da ga Mahaifanshi ne, amma wannan karon tsaf ya gayawa Babanshi babu abinda yake bawa Halime da yanda suke rayuwa da tausayinta dayakeji yasa bayason yawan matsa mata.


Hure mishi kunne Baba Isiyaku ya yi kan yadaina wani ɗaga mata ƙafa har ta ƙara samun wani cikin,kuma yadaina wannan yawan dowawar dayakeyi Halime zata raina shi.


Babu abinda Salmanu ya rage a huÉ—ubar Mahaifinshi.


Sauyin Salmanu bai wani ɗaga hankalinta ba saboda samun gulmar komai daga bakin munafukar makwafciyarta, don haka ta dage da addu'a domin idan ya fi ƙarfinta baifi ƙarfin Allah ba.



Rashin dawowar Salmanu gida akai-akai ne ya haifar da shaƙuwa tsakanin shi MUBEENA GHALI BARI ƙanin Mahaifinta Attajirine ita da iyayenta duk suna rayuwane a ƙarƙashin arziƙin shi sosai takeson Salmanu da kashe mai kuɗi ma su nauyi,sai dai bata samu ya kulata sai a wannan lokacin.



Tana yawan matsamai kan yazo gidan su. Ranar data kaishi Æ™arshe sai yace mata bashi da ra'ayin Æ™ara aure a rayuwarshi har abada.

Ko da ta nemi ba'asi,Sai ya ce mata idan bata gani da idonta ba bazata taɓa fuskarta abinda zai gayamata ba.


Ranar data matsa sai ta ga abinda yasa yace har abada bazai ƙara aure ba.sai yace ta shirya ya kaita taga Matarshi.

Banda tanason gani babu abinda zai kaita ƙauye ganin wata Matarshi ya ma raina ma ta hankali.


Tafiyar Safe sukayi don haka kafin rana tayi sosai suka isa,abakin ƙofar gidan drivern Mubeena ya yi parking.

Lokacin Halime na Makaranta.

Tuni gulmar ga Salmanu can yazo da Balarabiya daga Birni ya fara yawo. Ƙofar gidan ta fito suka tsaya bayan ta gaji da zaman Motar dai-dai lokacin da Halime ke dosowa gidan tana dogara sandarta fuskarta a sake kamar kullum duk da ta hango Mijinta da baÆ™uwar fuska.


Lokacin da Mubeeta taga nakasun Halime kuka tasanya tana rungumeta haÉ—e da shafa bayanta, son Salmanu ne ya fa ra bin iska acikin zuciyarta tsananin tausayin Halime na maye gurbin shi.

Shima Salmanu ƙwallane ya cika idanuwanshi,duk lokacin da ya kalli Halime sai ya ƙara sanin darajar ni'imomin da Ubangijinshi ya yi mishi da kuma ƙara gode Mai ....