MAI KWAÆŠAYI

13

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 13```


________Har Mubeena taje gida takasa daina kuka da hasashen ya Halime takeji, idan itace ya ya zataji aranta.

Zancen soyayya sai ya kau tsakanin Salmanu da Mubeena sai zumunci mai ƙarfi da ya maye gurbin shi,kullum idan zai tafi gida sai ta bashi sutura ko kayan daɗi ya kawowa Halime harda kayan kwalliya.


Lokacin da Halime ta kammala secondry school Mubeena ta yi aure da hamshaƙin mai kuɗi irin su. Babu yanda batayi da Halime ba amma sam taƙi amincewa da zuwa bikin da ta matsa sai ta sanya mata kuka dole ta haƙura sai Salmanu ne kaɗai yaje.


Duk da Mubeena ta yi aure hakan bai rage komai daga zumuncin su ba takan zuwa jefi-jefi da kuma yi musu aike.


Har lokacin Halime bata ƙara samun wani cikin ba tun Baba Isiyaku na mita har ya gaji ya haƙura.


Da taimakon Salmanu da Mubeena Halime ta shiga babban kwalejin dake ƙauyen su.


Baba Isiyaku kamar zai ari hauka da kukanshi da magiya ya ke roƙon Salmanu ya cire Halime a Makaranta.

Zame kanshi Salmanu yayi yace Mubeena ce ta nemawa Halime kuma a Human Right take aiki,idan suka hana Halime karatu zatayi ƙarar su.

Yanaji yana gani Halime ta cigaba da karatunta wannan daliline ya dasawa Baba Isiyaku mugun tsanar Mubeena a zuciyarshi.


Da taimakon Mijin Mubeena Salmanu ya samu aiki a Asibitin Ahmadu Bello dake Zariya.


Halime ta kammala kwalejinta cikin dumbin nasara.

Bayannan tafara shirye-shiryen shiga babbar Jami'a.kafin nan Halime ta buƙaci ɗaya daga cikin filayenta domin buɗe Makaranta.

Nan ma da goyon bayan Mijinta Salmanu da Mubeena komai ya kammala duk da ajujuwan na langa-langa ne,wannan karon Baba Isiyaku kasa riƙe damuwarshi yayi har sai da ya kwantar da shi ciwo.


Akan kuɗi mai sauƙi take koyar da dalibai yanda mutanen ƙauyen su zasu iya biya,da kuɗin sana'ar ta na zoɓo da take samun ciniki sosai take biyan malaman da suke taimaka mata duk da ba wani albashine mai tsokaba, amma basa rainawa saboda suma ma su burin cigaban yankin su ne kamar Halime...