JUYIN KWAƊO 3
🪄...JUYIN KWAƊO...🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad
Page-3
*Moorfields Eye Hospital, 20 street Al Razi Building 64, Block E, floor 3, Dubai.*
ARMAN POV.
“Buɗe idon a hankali”
Dr Ƙuraishi ya bawa Arman umarnin yayin da ya gama duba masa idonsa. Arman ya buɗe idonsa a cikin hasken da Dr Ƙuraishi yake haska idonsa. Amma babu abin da yake gani face duhun da ya saba gani, saboda shi bai san banbancin da yake tsakanin idonsa na a rufe ko a buɗe ba, tun da duka biyun abu ɗaya yake gani.
“Kana iya ganin wannan hasken?”
Dr Ƙuraishi ya tambaya.
“Ba na ganin komai Dr babu komai sai duhu”
Dr Ƙuraishi ya kashe fitilar da ya haska idon nasa, sannan ya ɗauki glasses ɗinsa dake aje a gefe, ya mayar masa shi idonsa yana faɗin.
“Za ka iya sauƙowa”
Arman ya gyara zaman glashin, sannan ya sauƙe ƙafafunsa ƙasa, ya ɗauki canvas ɗinsa dake aje a ƙasa, ya saka a ƙafarsa, sannan ya dawo cikin main office ɗin Dr Ƙuraishi, inda Gulazar ke zaune tana jiransu.
“Babu wani ci gaba!”
Dr Ƙuraishi ya faɗa yana miƙawa Gulzar takardun lafiyar idon Arman ɗin. Gulzar ta karɓa, sannan ta kalli ɗan uwanta da shi ma yake kallonta.
“Za mu iya tafiya?”
Ya tambaya yana murmushi, shi sam bai ga wani abin shiga damuwa ba, dan ya san sam babu ci gaba a lafiyar idon nasa, ba dan Gulzar ɗin ta takura masa ba ma da ba zai zo ba, dan tun daren jiya ta yi booking appointment. Gulzar da gaba ɗaya take a dame ta miƙe, sannan ta ɗauki bag ɗinta ta rataya a kafaɗarta, ta bi bayansa suka bar office ɗin.
Suna tafiya a hanya ya dafa kafaɗarta yana bata haƙuri, kamar ita ce marar lafiyar ba shi ba. Har suka shiga mota suka nufi hanyar gida Gulzar ba ta sauƙo ba. Sai da suka kusa kaiwa unguwarsu kiran PAn Abby ya shigo wayar Gulzar.
“Alo Falak ya kike?”
Ta faɗa bayan ta ɗaga kiran, daga ɗayan ɓangaren Falak ta amsa, sannan ta faɗi dalilin kiran nata.
“Agha (Honorable person) Iƙlab ne yake son ganinki yanzu a kamfani”
Ta tattare girarta tana ɗagawa Arman hannu alamun ya dakata, ya dakatar da motar yana kallonta.
“Lafiya yake naimana?”
“Eh yace yana son ganinki ne”
“Ɗayib jaye! (Okay gani nan zuwa)”
Ta sauƙe wayar tana kallon Arman.
“Abby yana son ganina a kamfani, dan Allah ka kaini can”
Ba tare da yace komai ba ya jinjina kansa yana gyara zaman glashin dake idonsa, sannan ya ja mota ya juya akalar tuƙin nasa zuwa Alhadi Group of Companies. Duk kuwa da ya jima rabon da ya je kamfanin, amma tun da ta buƙata ba zai ƙi kaita ba.
*Majmu'at Shirkat Alhadi, Al Saaha street, Lobby C, Downtown Burj Khalifa, Abu Dhabi, Dubai.*
“Jininka ya hau da yawa Sayid Iƙbal (Mr Iƙbal). Ya kamata ka riƙa sauƙaƙawa kanka”
Faɗin likitan Sayid Iƙbal, yayin da yake tattare blood pressure monitor ɗin da ta yi amfani da shi wurin duba hawan jinin nasa, saboda haka kawai ɗazu ya yanke jiki ya faɗi ba gaira ba dalili. Zaune yake a kan wata boudoir chair, yayin da suit ɗin da ya cire daga jikinsa ke rataye a jikin chair ɗin. Ya lumshe idonsa yana shafa damtsen hannunsa da aka cire abin blood pressure monitor ɗin a jiki. PAnsa na tsaye a gefe, haka ma babban abokinsa Sayid Nusayr (Mr Nusayr), duka sauna cikin karafaren office ɗinsa dake ma'aikatar ne.
“Ni zan wuce”
Cewar Dr, yayin da ya gama haɗa kayan gwajinsa, sai a lokacin Sayid Iƙbal ya buɗe idonsa, sannan da ido ya yi wa Falak alama da ta raka Dr, ta jinjina kanta tana nunawa Dr hanya.
“Mu je na rakaka Dr”
Daga haka suka fice daga office ɗin. Suna fita Sayid Nusayr ya zauna kusa da Abby yana masa sannu.
“Bai kamata ka riƙa saka damuwa a ranka ba Iƙbal”
Abby ya kalle shi yana sakin hannun dress shirt ɗin dake ƙasan suit ɗin da ya cire, dan bayan suit ɗin akwai waist coat a ƙasa. Zamansa ya gyara yana shafa sumar kansa da ta fara sirkawa da fari, alamun tsufa ya fara masa sallama.
“Dole na shiga damuwa Nusayr! Sam Arman ya kasa fahimtar abin da nake son nusar da shi, ba na so na faɗi na mutu na bar shugabancin kasuwancin da na sha wahala kafin na kafa shi a hannun da ba na gari ba. Da ace Akhi Anwar da kansa ne yake son shugabantar kamfanin na bayan raina ba zan ji komai ba, amma Faisal yake so ya danƙawa shugabancin nan, ya nuna shi ba shi da sha'awar ci gaba da kasuwanci. Arman ba ya son karɓan abin da yake nasa, Gulzar mace ce, kuma har yanzu tana da ƙarancin shekaru, sam ba za ta iya shugabantar babban kafani kamar wannan ba... Na rasa abin da zan yi!”
Nusayr ya girgiza kai cike da tausayin abokinsa.
“Ka yi haƙuri Iƙbal, ka ci gaba da addu'a, da yardar Allah ba za ka mutu ba har sai ka ga Armaan a kan waccan kujerar!...”
Ya ɗan yi fasali yana nuna hamshaƙiyar kujerar dake office ɗin, sannan ya ci gaba da faɗin.
“A matsayin shugaban kamfanunuwan Alhadi..”
Abby ya yi murmushi me sauti.
“Wannan shi ne mafarkin da na daɗe ina yi, kuma da dukkan fatan duniya nake roƙon Allah ya sa ya zama gaskiya kafin na bar duniya”
Kafin Nusayr ya kai ga faɗin wani abu Gul ta buɗe ƙofar office ɗin ta shigo a dugunzume. Tana ganin Abby zaune ta fara hawaye, ta nufe shi da gudu ta faɗa kansa ta rungume shi tana kuka.
“Abby!?”
Abby ya shafa dogon gashin kanta dake cikin style ɗin long wavy. Yana murmushi, a da Arman ne yake masa haka, saboda a baya Arman ya fi kusanci da shi fiye da kowa. Amma a yanzu Arman ya fi gudunsa fiye da kowa, kuma ba komai ya ja hakan ba face maganar gadon kamfani da yake yawan yi masa.
“Abby me ya sameka?”
Abby ya sake yin murmushi yana shafa gashin kanta.
“Lafiyata ƙalau, kawai na ɗan ji jiri ne, sai na yi kamar zan faɗi, amma babu abin da yake damuna”
Ta kwanta a jikinsa tana kallon Sayyid Nusayar dake murmushi.
“Ammu Nusayr wai haka ne?”
Sayid Nusayr ya jinjina mata kai.
“Abby ka dinga kula dan Allah.”
Ta ƙarashe tana kallon Abby, Abby ya share ƙwallar da ta zubo mata yana gyaɗa kai, sannan ya sumbaci kanta yana kwantar da kanta a kafaɗarsa.
“Ina ɗan uwanki? Imminku ta faɗa min cewa tare kuka fita da shi”
Nan da nan ta ɓata fuska.
“Yana reception, wai zai jirani a can”
Abby ya girgiza kansa, dan ya sam dalili, wato shi ba ma zai shigo ba, ballantana ya ga office ɗin da bathroom ɗinsa ma ya fi shi muhimmanci a wurinsa.
“Ki yi haƙuri, Akuki (Ɗan uwanki) zai daina duk wannan abin da yake”
Ran Gulzar a ɓace tace.
“Ai sai dai idan zamanin baya yaje ya dawo, sannan ne zai sauya ra'ayinsa, taurin kai ne da shi kamar mutumin wancan zamanin!”
Abby ya dungure mata kai.
“Kin taɓa ganin wanda yaje zamanin baya ya dawo?...”
Ta turo baki tana tura gashinta baya, sannan ta kwanta a jikinsa tana zuba masa shagwaɓarsu ta autanni.
*
“Asirul laimun wu bass (Juice ɗin orange ma ya isa)”
Ya bawa ma'aikacin kamfanin da ya tambaye shi abin da yake son sha amsa. Ma'aikacin ya amsa da to, sannan ya bar wurin, Arman ya ɗaga idonsa yana kallon katafaren reception ɗin kamfanin dake ƙasan ma'aikatar. Gaba ɗaya jinsa yake kamar zaune a kan ƙaya, dan ko kaɗan ba ya son abin da zai haɗa hanyarsa da ta kamfanin nan, kamar yanda Faisal ya saba yi wa rayuwarsa karan tsaye, haka ma yau ya masa.
“Makaho!?”
Idonsa ya rintse yana gyara zaman glasses ɗinsa, kafin ya buɗe idon nasa ya ɗaga kai ya kalle shi, sai dai yau ba shi kaɗai ba ne, akwai Sakina tare da Anwar mahaifinsu. Kansa ya kawar daga barin kallonsu, dan haka kawai ya ji zuciyarsa na hassala da dariyar da suke masa.
“Kaya ka kawo kamfanin ne?. Dan na san ko cikin ma'aikatan dake wurin nan babu makaho irinka” Cewar Sayyid Anwar yana dariya.
Arman ya dunƙule hannunsa yana haɗiyar yawu da ƙyar, dan yau ji yake kamar ba zai iya ɗaukan cin zarafin da suke masa ba.
“Ai ko a cikin masu shara babu makaho Abbu, ballantana a cikin masu kawowa kaya”
Sakina ta faɗa tana tata dariyar. Arman bai tanka musu ba, kansa kawai ya sake sunkuyarwa, saboda yanda mutanen dake kusa da su suka fara kallonsa.
“Allah sarki makaho! Su fa da ma makafi ba su da wani aiki da ya wuce bara a gefen hanya... A taimaka min da sadaka! A taimaka”
Faɗin Faisal yana kwatanta yanda mabarata ke bara. Arman ya miƙe da sauri zai mayar musu da martani muryar Abby ta kaste shi.
“Arman!”
Ya tsaya cak da shirin dukan da yake son kaiwa Faisal yana huci, ya dunƙule hannunsa da mugun ƙarfi yana jin kamar ya daki bango ko zai huce. Abby da Gulzar da suka sauƙo ƙasa tare suka tsaya a wurin suna kallonsu.
“Me yake faruwa?”
Abby ya tambaya yana dafa kafaɗar Arman. Amma sai Arman ɗin ya kauce, ya kalli Gulzar.
“Idan kin gama ina mota”
Yana gama faɗin hakan ya juya zai bar Building ɗin kamfanin. Har ma'aikacin da ya tafi kawo masa ruwan laimo na binsa da shi yana faɗin ga ruwan laimon nan ya kawo masa, amma bai tsaya ba ballantana ya karɓa. Tun da Gulzar ta ga haka ta san cewa wata baƙar maganar Faisak (FAISAL AND SAKINA) suka faɗawa ɗan uwanta da har ta sa ya shiga wannan halin.
“Me kuka gayawa ɗan uwana?”
Ta tambaya tana raba idonta a kan su ukun. Amma babu wanda ya amsa mata, sai murmushin da suke suna duban juna.
“Wai ko kunya ba ku ji?... Sakarkaru kawai!”
Ta faɗa rai a ɓace, sannan ita ma ta juya ta bi inda ɗan uwanta ya bi ba tare da ta yi wa Abby sallama ba. Daga Anwar har FAISAK ba su ji haushin abin da Gulzar ta yi ba, dan sun san su ne a gaba.
“Na ji an ce ka faɗi da fatan ba wata matsalar ba ce?”
Sayyid Anwar ya tambaya yana duban Abby da murmushi, Abby dake cikin jin rashin daɗin halin da yaransa ke ciki ya girgiza kansa.
“Na ji sauƙi”
“To sai a kula nan gaba, dan wata ƙila idan an faɗi ba lalle a tashi ba!”
Faɗin Sayyid Anwar yana murmushi, tare da taɓa kafaɗar Abby, sannan ya ja yaransa suka bar Abby cike da zullumi.
*FACT MAGAZINE, Building 8, Dubai Media City, Abu Dhabi, United Arab Emirates.*
ADAM POV.
Sanye yake cikin baƙin dress trouser, da farar sweat shirt, kafaɗarsa rataye da briefcase ɗinsa, ƙafafunsa cikin moccasin dockside. Sumar kansa me ƙarfi irin ta Africans na cikin askin crew cut. A ɗarare ya ƙarasa seat ɗinsa dake cikin na tarin ma'aikatan kamfaninsu ya zauna yana raba ido. A hankali ya aje briefcase ɗinsa a kan table, sannan ya buɗe system ɗinsa dake kan table ɗin, ya ciki gaba da aikin da bai ƙarasa ba.
Adam baƙi ne a kalar fata, kuma dogo ne, sannan yana da kyau dai-dai gwargwado, dan a fuskarsa ba ka ce ga abin kushe ba. Yana tsaka da aikin da yake wani cikin abokansa na wurin ya lallaɓo ta bayansa, ya shammace shi yace.
“Booom!”
Da ƙarfi, hakan yasa Adam ya zabura har yana ɗaukewa ƙafafunsa daga ƙasa, zuciyarsa kuwa kamar ta fasa ƙirjinsa ta fito tsabar tsoro. Sai jujjuya ido yake yana haki, abokin nasa da ya tsorata shi ya kwashe da dariya yana tafa hannu. Haka sauran abokan aikinsa da teburan aikinsu ke kusa da nasa suka taya shi dariyar.
“Matsoraci!... Ka gama aikin da shugaba ya baka?”
Abokin nasa ya tambaya yana duba system ɗinsa, Adam ya masa banza yana sauƙe ƙafafunsa da ya ɗora a kan kujera zuwa ƙasa, tare da dafe ƙirjinsa dake barazanar ɓallewa.
“Haisam bana son irin wannan, kuma ka sani”
Ya faɗa cikin son nuna ɓacin ransa a kan abin da Haisam ɗin ya masa, Haisam na dariya ya dafa kafaɗarsa yana faɗin.
“Ka yi haƙuri abokina, a duk sanda na ganka cikin tsoro nishaɗi kake bani”
Adam ya galla masa harara yana ɗauke kai. Har Haisam ya ƙaraci surutansa bai ce da shi uffan ba. Har ya ƙyale shi dan dole, ya ci gaba da aikin dake gabansa, kafin landline phone ɗin dake kan teburinsa ta shiga ruri. Shi ma ringing ɗin wayar sai da ya kusa tsorata shi, da ƙyar ya saita kansa ya ɗaga wayar.
“Sabahul Khair Ustaz (Barka da safiya shugaba)”
Ya faɗa bayan ya ɗaga wayar, dan kira ne daga wayar ogansu.
“Barka da safiya, da fatan ka gama aikin da na baka?”
Ya jinjina kai yana faɗin.
“Eh Ustaz na kammala shi”
“Ina son ganinka yanzu a office ɗina”
“Hadir Ustaz (To Shugaba)”
Daga haka ya aje wayar, ya ɗauki system ɗinsa ya miƙe ya nufi office ɗin ogan dake can wata kusurwa ta ma'aikatar. Sai da ya ƙwanƙwasa ƙofar gilashin dake ofishin, dan ko daga nan inda yake yana iya ganin ogan nasu zaune a kan kujerarsa yana cin shawarama, sai da Ustaz ya ba shi izinin sannan ya shiga da sallama.
Shugaban ya amsa sallamar da ya yi yayin da yake zama a kan kujerar ofishin nasa. A ladabce ya buɗe system ɗinsa, sannan ya miƙawa Ustaz. Ustaz ya karɓa, ya shiga duba ayyukan yana jinjina kai, alamun sun burge shi.
“Hotuna sun yi kyau Adam. Kuma na ji daɗin ganinsu a haka... Lalle na jinjinawa ƙoƙarinka”
Adam ya yi murmushi me sauti yana faɗin.
“Haza wajibi Ustaz (My pleasure shugaba)”
Ustaz ya jinjina kai shi ma yana murmushi, sannan ya aje guntun shawarman da bai ƙarasa cinyewa ba, ya kalli Adam, kana ya furta masa dalilin ƙaddarar da za ta zama silar juyin rayuwarsa.
“Nan da wattani biyu masu zuwa gwamnatin Dubai na shirin bamu kyautar karramawa, a wannan bikin da za'ayi ina so mu gabatar da hotuna masu kyau da jan hakali. Hotuna irin wanda ba'a saba ganinsu ba, kuma ina so ya zama kai ne wanda zai zo da hotunan... Da fatan za ka zo min da abin da zan yaba”
*Dubai Miracle Garden, Street 3, Al Barsha South, Dubai.*
IVANA POV.
“Na gode”
Ta yi wa mutumin da ta sai juice a wurinsa godiya, sannan ta juya da nufin barin wurin, domin zuwa wurin ɗan 'yar uwarta Imran da suka zo Miracle Garden ɗin tare, dan shi ne ma ta zo wurin. Hannayenta duka biyu na riƙe da cups ɗin juice ta nufi wurin da wani jirgin wasa yake, wanda aka haɗa shi da ganyayyaki, a jikinsa kuma akwai rubutun 'Emirates'. Kasancewar a kusa da wurin ta bar Imran na wasa da wasu yara.
“Marhaba (Hello)”
Ta ji muryar a bayanta, hakan yasa ta juya domin ganin me maganar, duk da ta ji kamar ta san muryar. Wannan matashin ɗan kasuwar da suka haɗu a Cavo Espresso Bar ne tsaye a bayanta yana murmushi, sanye yake da farin plain jogger sets. Hannayensa zube cikin aljihun hoodie ɗin kayan, yana kallonta yana murmushi a lokaci guda.
“Ahalin (Hi)”
Ta amsa da ɗan guntun murmushi, sai ta ga ya faɗaɗa murmushinsa yana nufota, sannan ya tsaya a gefenta.
“Mu je”
Ta jinjina kanta, sanna suka jera suka fara tafiya, kanta a ƙasa tana kallon interlocks ɗin dake ƙasan hanyar da suke bi.
“Ke kaɗai kika zo nan?”
Ta ji ya tambaya bayan wani lokaci, sai ta ɗaga kai ta kalle shi, amma shi ba ita yake kallo ba, ita ma kuma sai ta ɗauke kai tana faɗin.
“A'a tare da yaron 'yar uwata na zo”
Tana jin sautin murmushinsa, kafin yace.
“Shi ne wancan?”
Ya nuna mata Imran dake wasa tare da wasu yara. Ta kalli yaron da ya nuna, sanna ta jinjina masa kai.
“Eh shi ne, ka san shi ne,?
Ya girgiza kansa.
“Ban sa shi ba, amma na ga sanda kuka shigo nan tare”
Ta ɗan yi murmushi kaɗan, a lokacin da suka isa jikin wani bench, suka zauna ta kiran Imran. Imran ɗin da ta kira ya zo da gudu ya karɓi juice ɗin da ta siyo masa, sai da suka gaisa da Uwais, sannan ya juya ya koma suka ci gaba da wasa.
“Asir?” (Lemo?)
Ta faɗa tana miƙa masa cup ɗin da ya rage a hannunta, ya girgiza mata kai yana shafa sumarsa me kyau da ƙyalli a ido. Ita kuma sai ta jinjina kanta, sannan ta ɗan sha lemon kaɗan, kana ta aje shi a gefenta tana saƙala ganshinta a bayan kunnenta, sakamakon iskar da ake ta sa yana tashi a iska, dan yana cikin style ɗin flat iron waves ne
“Wani aiki kike?”
Ya sake tambayarta, wannan karon ma kafin ta amsa masa sai da ta kalle shi.
“Ina aikin koyar da kiɗan guitar ne a Repton school Dubai...”
Ya jinjina kansa.
“Aiki me kyau... Ni ma na iya kaɗa guitar, ta kan bani nutsuwa a lokuta da dama, shi yasa ban cika kaɗawa ba sai ina cikin nishaɗi, domin ta ƙara daɗaɗa yanayin da nake ciki”
Ivana ta yi murmushi.
“Kai fa, menene aikinka?”
Wannan karon ma kafin ya bata amsa sai da ya shafa sumar kansa.
“Kasuwanci, mahaifina shi ne shugaban rukunin kamfanunuwan Al Aida, ni kuma ni ne magajinsa”
Ta dube shi, dan ta san Al Aida babban kamfani ne, da suke sarrafa abubuwa da dama. Shiru ya ratsa wurin na wasu mintuna, kafin ya miƙe tsaye yana faɗin.
“Ni zan tafi”
Ita ma sai ta miƙe tana kallonsa.
“Sai mun sake haɗuwa”
Ya miƙa mata hannunsa alamun su gaisa, tare da faɗin.
“Sunana Uwais Faizal”
Ta kalli hannun nasa, sannan ta miƙa nata hannun suka gaisa.
“Ivana Sagar”
A lokacin da ya jinjina hannunsa tare wani abu kamar wucewar iska ya gifta a cikin kanta. Haka kawai take jin kamar ta taɓa haɗuwa da wani kamar haka a can baya, kamar akwai wani me kammani irin nasa da suka taɓa gaisawa irin haka, amma ba'a Dubai Miracle Garden ba, a wani unknown wuri da ba ta isa tace ga shi ba.
“Na ji daɗin haɗuwa da ke Ivana”
Faɗin Uwais yana murmushi, ita ma sai ta jinjina kanta.
“Ni ma haka”
*Salma Ahmad Isah ✍️*