14
đđ```MAI KWAĆAYI```đđ
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 14```
________Manya da yaran dake Rayuwa a Ćauyen yabon Halime ne abakunan su.
Inna ma taji daÉin ganin yanda Halime ta saki ranta take Rayuwa kamar kowa.
Tsabar baĆin ciki daina kulata Baba Isiyaku ya yi kota gaisheshi baya amsawa hakan kuma bai sa ta fasa ba,lokuta da dama dariya yake bata,ta rasa wani irin kwaÉayi ne da Baba Isiyakun duk ni'imar da Ubangijin ya yi wa Éanshi da duk dukiyarta da aka kashe wajen kammaluwar karatun Salmanu baya gani.shi dai burinshi ta haifi Éa Namiji su samu Magaji.
Mutuwar Yayan Mubeena Uwa Éaya Uba Éayane ya tilastawa Halime zuwa Birni gaisuwa.
Abun mamaki da al'ajabin daya samata zazzaÉi nan take gidan da bazata taÉa mantawa arayuwarta ba ne har abada ake zaman makoki Éan uwan Mubeena, Unguwar su Innarta,a wannan lokacin ma Motoci ne lafiyayyu da sojoji birjik.
DaĆyar ta mu su gaisuwa duk da bata wani samun tarbar arziĆi daga fuskokin dangin Mubeena da suke da tsananin kyau da burgewa ba,duk da itama Halime ba baya ba amma kyawun mazaunin birni mai kuÉi da kyawun mazaunin Ćauye talaka da banbanci.duk Salmanu bai san wainar da'ake toyawa ba yana zaune awajen ma su karÉar gaisuwa.
Shi ya kaita har gidan Innarta cikin matsakaicin Motar da bai jima da siya ba.
BaĆin ciki kamar ya kashe Inna Huwaila,batayi tunanin ganin Halime tsaf haka ba.
A tsakar gida ta yada zango Inna na tambayarta cikin farin cikin zuwan bazatan da tayi mu su. Ciki sanyi jiki da damuwar dake bijiromata batare da lura da yanda Inna Huwaila ta bazo kunnuwanta ba take bawa Innarta labari.
Shewa Inna Huwaila tasa harda guda.
"Na rasa kwaÉayi irin wannan, kina Ćauyen ma baki haĆura ba kin Ćara biyo su,nan gaba motocin gidan takan hannayenki za su bi" Inna Huwaila tafaÉa cikin hassadar dake danĆare acikin zuciyarta don batajin yau zata iya barci mai daÉi.
Kalaman Inna Huwaila sun daki zuciyar Halime, duk dauriyarta sai da Ćwalla ya cika idanuwanta.
Maimakon zuwan Halime ya yi wa kowa na gidan daÉi yanda ta Ćara kyau da samun kwanciyar hankali sai yazama abun baĆin ciki ga mutanen gidan duk inda taje gaishe su baĆaĆen maganganun ne su ke biyowa baya.
Tun kafin ta bar gidan zazzaÉin jikinta ya fara Ćarfi, Inna tayi kuka bayan tafiyar su Halime, Tanajin kamar ta dawo da nakasun Halime kanta.
Hankalin Salmanu a tashe suka Ćarasa gida,chemist yakaita wajen Abokinshi,batare da wani gwaje-gwaje ba yayi mata Allura da bata magani.
â washe gari jikin Halime ya Éanyi sauĆi. Kwana biyu bayan nan Salmanu ya yi mata albishir Éin komai na Makarantar ta kammala zata fara zuwa Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria don haka tare za su tafi idan ya Ćara dawowa ta Ćarasa shirye-shiryenta acan.
Dalilin Ćara samun Ćarfin jikin Halime kenan.
A daren da labari yajewa Baba Isiyaku ya shiga ya fita kan idan Salmanu ya tafi kar ya Ćara waiwayar gida har sai zancen tafiyar Halime Makaranta ya rushe.
Ranar da Halime ta yi sallama da Salmanu cikin soyayya da Ćewar junan da zasuyi tare kuma da yimata alĆawarin dawowa bayan kwana biyu ciwo mai zafin gaske ya kwantar da Halime....âđť