15
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 15```
________Tun tana sa rai da dawowar Salmanu har ta fara cire rai saboda shuɗewar sati uku babu shi babu labarin shi, ko ta kira da ƴar ƙaramar wayar daya siyamata bata samunshi.
Komai na Halime tsayawa ya yi cak kamar shekarun baya, duk yunƙurin ta na nuna ƙarfin halinta kasawa tayi,da taimakon maƙwafciyarta mai son ganin diddigin komai aka kai Halime Asibiti.
Gwajin farko likita ya tabbatar da cikin Halime É—an wata biyu.
Da rawar jiki Baba isiyaku ya nemo mai taimakawa Halime acikin ƴaƴan ƙannenshi, danasanin abinda ya aikata na kamashi sai yake ganin kamar idan da Salmanu na kusa Halime zatafi samun kulawa amma wani sashe na zuciyarshi na bashi ƙwarin gwiwar ban da ya yi haka da yanzu cikin ya zube garin yawon zuwa Makaranta.
Tun daga ranar Baba Isiyaku ya fara addu'ar Allah yasa Halime ta haifi É—a Namiji.
Maimakon laulayin Halime ya yi sauƙi saboda cikinta da ke ƙara girma sai laulayin ya daɗa yin gaba komai taci sai yadawo.
Indo ƙanwar Mahaifiyarta ce taje roƙon alfarma wajen Baba Isiyaku kan ya bari ta tafi da Halime sai tafi samun kulawa tunda Salmanu baya gari kuma mai taimaka mata bakomai take iyawaba yarinyace ƙarama ga ƙiwuyar aiki wa su a abubuwan da jan jiki Halimen take yiwa kanta.
Murje idanuwanshi ya yi kan bai san zancen ba saboda gani yakeyi tafiya da Halime zaisa su sauya abinda ke cikinta saboda tsanarshi da yake tunani sunayi na babakere akan dukiyar da banashi ba.
Haka Indo ta haƙura sai dai tana ƙoƙarin zuwa duba Halime lokaci zuwa lokaci.
Cikin Halime na wata huɗu ta rame tayi baƙi saboda rashin maikula da ita dakyau gashi ba'a bari Innarta tasan komai ba.
Wata ranar Laraba sai ga Mubeena da Mijinta da bai taɓa zuwa ƙauyenba a lafiyayyar Motar su.
Yanda taga Halime ta koma ne yasata yin ƙarar daya janyo hankalin Mijinta ya shigo gidan duk da ba'abashi izini ba.
A yashe suka sameta a ƙofar ɗaki, Rahila mai zama da ita tayi tafiyarta gantalin yawon maƙota.
Numfashinta daƙyar yake fita,ƙarfin da Mubeena batasan tana da shi bane ya zo mata ta kinkimi Halime da hanzari FAISAL Mijinta ya juya yana buɗe mata gidan baya ƙirjinshi na bugawa wasu abubuwan da suka faru shekarun baya na dawo mai cikin kanshi,a hanzarce driver yaja mota suka ɗauki hanyar babban Asibitin dake ƙauyen.
Akan idon Rahila dake ɓoye komai yafaru cikin kuka ta nufi gidan Baba Isiyaku dayake rayuwa shi kaɗai aciki kamar tsohon maye.
Kwataccen sumar kanshi na fulanin usul dayake a tsaftace ya ke shafawa tattaunawar su da Mubeena safiyar ranar na dawo mai.
" Na kasa yarda da ƙauyen nan dakike zuwa har wani irin nakasune da ita da bazakina taimakon su da iya kuɗi ba, kuma Mijinta yanzu yana aiki,bansan yaushe tausayin talaka yayi tasiri aranki haka ba"
"Bazaka gane ba, Labarin Halime abin tausayi ne ga kowa bawai iya talaka kaÉ—ai ba zan so kazo muje ka ganta" ta faÉ—a da kyakkyawan murmushi a fuskarta.
Faisal na tsananin son Mubeena a dalilinta ya rage wasu tsauraran halayyarsa da bata so duk da wasu suna nan amma kaso saba'in cikin É—ari duk babu.
Kanshi ne ya fara ɗaukar chaji zuciyarshi na ƙosawa yasamu damar keɓewa da Mubeena don jin dalilin dayasa Halime ta koma haka Allah yasa zargin shi kar yazama gaskiya.
A haukace Baba Isiyaku ya iso Asibitin don yasan baza su wuce nan ba,tsanar Mubeena na ƙara shigar shi.
Bai samu koda gaisuwarta ba saboda wayan da take yi da Salmanu cikin fushi.haƙuri Salmanu ya ke ta bata da kuma yi ma ta alƙawarin tabashi nan da awa ɗaya zai taho.
A take ta tura Rahila ƙauyen su Indo kan taje
garin su Innar Halime ta sanar da ita halin da Halime take ciki, da rawar jiki Rahila ta tafi saboda kuÉ—in da Mubeena ta bata.
Baba Isiyaku kamar zai yi bindiga sai muzurai yake yi yanajin kamar ya tashi ya maƙure Mubeena har sai ta daina numfashi.
Su waye FAISAL DA MUBEENA...🤔