KI NA ZUCIYATA

Chapter TWO

by @nanameera08

*KI NA ZUCIYATA 02*


*Mikiya writer's asso.*



*Nanameera ce#*



Tunda suka shiga da ita suke tsaye babu nutsuwa mussamman Mom wacce duk ta rikice dan ba ƙaramim so takewa Nazeefa ba tana matuƙar jin yarinyar aranta, har akayi sallar asuba babu wani likita ko ɗaya daya fito dukda daman arna ne likitocin musulman cikinsu kaɗan ne, ana idar da sallar asuba Fateeha ta kira Mommy da Daddy ta sanar dasu iyaka tashin hankali sun shigeshi dan daman kowa a tsorace yake da ciwon Nazeefa ɗin. Wajejen ƙarfe 7am likitocin suka fito daga cikin ɗakin, da sauri Mom tayi wajensu tana tambayar lafiya kallonta ya yi ya ce


"Asamu namiji ya biyoni office"


Jikinta na rawa ta ce"okay ba matsala" komawa wajen Fateeha ta yi wacce ta zuba uban tagumi ta ce" sunce namiji suke so ba mace ba" shuru tayi da farko sai ta ce" ok sai anjira su Daddy sunzo kenan?" girgiza kai Mom ta yi ta ce "bazai yiwuba bazan iya jira ba gashi kuma Abishak baya nan dole a nemo wani saboda ba yanzu zasu zo ba dole" kallonta kawai ta yi dan ita iya tunaninta babu wani wanda zasu kirawo tunda dai yaya Abi baya nan



"Mom ko na kira Hameed?"


Kallonta tayi ta ce" wane Hameed kuma?"

"Hameed dai tunda shi kaɗai ne yake kusa yanzu nasan bazai ƙi zuwa ba" numfasawa ta yi ta ce" kina ganin babu matsala?" "in sha Allah Mom". Fita tayi daga harabar asibitin ta danna numbernsa wanda ya bata jiya, ringing biyu aka ɗauka cikin sanyin murya ta ce


"Ina kwana?"


Bai ɗauki muryar ba ya ce"lafiya kalau wacece?" rasa me zata ce masa ta yi da farko kusan 2mins ya ce


"are you on the line?" numfasawa ta yi ta ce


"Daman Nazeefa ce batada lafiya shine nace.." bai bari ta ƙarasa maganar ba ya ce


"Wace Nazeefa?, Slimzy?"


Gyaɗa masa kai ta yi kamar yana gabanta da sauri ya miƙe jin tayi shuru ya ce"i'm talking to you"


"E, ita"


Bai sake cewa komai ba ya kashe wayar kallon screen ɗin tayi sai kuma ta koma ciki, kallonsa Raihana tayi ganin yanda yake shiri babu nutsuwa atare dashi saida ya gama shiryawa tsaf ya ɗauki car key ɗinsa sannan ta ce



"Wai ina zaka ne?"


Yana yin gaba ya furta


"I'm coming"



Saida ya yi nisa sannan ya sake kiran Fateeha, bayan ta ɗaga ya tambayeta address ɗin asibitin ta faɗa masa sannan ya nufi asibitin. Wajejen 9am ya isa asibitin bayan ya shiga ward ɗin ya tarar dasu zaune kan kujera duk sunyi tagumi da sauri ya ƙarasa wajensu yana zuwa ya ce


"ina take?"


"Basu fito da'ita ba sunce wai namiji yaje ya yi magana da doctor" Ok ya ce sannan ya yi hanyar office ɗin.Zare farin glasses ɗin idanunsa ya yi ya ce



"Rayuwarta tana cikin hatsari domin gabaɗaya zuciyarta ta rigada ta gama lalacewa gab take da daina aiki i don't think zata ƙara koda 3months a duniya saboda yanda zuciyarta tayi kwata-kwata ba'a tari al'amari sanda ya fara ba saida abu ya yi nisa sannan" kallonsa kawai Hameed yake amma ba sosai yake fahimtarsa ba tunda ya furta Slimzy zata iya rasa ranta yaji jikinsa ya fara sauyawa tabbas idan Nazeefa ta mutu tofa babu wani sauran abu wanda zai sakashi farin ciki idan bai mutu baa tofa zai kasance bashida maraba da mataccen, ganin ya tafi duniyar tunani yasa likitan ya ce


"Hyyyy "


Da sauri Hameed ya kalleshi sai kuma ya sauke numfashi "yanzu mene ne abunyi doctor?"


"Zuwa yanzu babu abinda zan faɗa muku domin banajin akwai wani magani wanda idan kuka bata zai saka ta samu sauƙi kamar yanda na faɗa saidai kuyi haƙuri ku mayar da ita gida ko kuma ku zauna da'ita anan duka babu matsala" miƙewa Hameed ya yi yay waje dan baiga alamun hankali atareda likitanba dan babu wanda yasan ranar mutuwar wani, yana fitowa Mom ta ce


"Ya ake ciki?"


Numfasawa ya yi yana zuba hannayensa cikin trouser ɗin jikinsa ya ce" zan canza mata asibiti, amma yaushe Slimzy ta gamu da ciwon zuciya?"



Goge hawayen fuskarta ta yi ta ce" labarine mai tsayi mayi maganar wani lokacin" bai sake cewa komai ba ya yi waje. Ƙarfe 1:35pm aka canza mata asibiti, sosai asibitin yafi wancan wanda suka baro komai da komai dan kwarewar likitocin ma ba ɗaya ba, bayan sun karɓeta ya kalli Mom wacce duk ta fita hankalinta ya ce



"Ko zakuje gida ki shirya Mama?"


Girgiza masa kai ta yi ta ce" A'a bazan iya tafiya nabar Nazeefa ba zan tsaya har sanda zata farfaɗo" ok ya ce sannan ya cigaba da kallon ƙofar ward ɗin duk ya ƙagu su fito da'ita. Kai tsaye asibitin suka nufa bayan Fateeha ta tura musu address ɗin, a firgice suka shigo kowanensu hankalinsa atashe Daddy ne ya kalli Mom ya ce



"Ina Nazeefa?, Asma'u ina Nazeefa?"


Kallonsa Mom tayi amma ta gagara furta komai ya kalli Fateeha ya ce" ina take?" da hannu ta nuna masa ward ɗin ya tafi gadan-gadan da niyyar shiga Abbane yayi saurin riƙeshi yana kallonsa ya ce



"Haba Ibrahim mene haka?, ka nutsu mana sun fa shiga da ita" kallon Abba ya yi ya ce"inason na ganta ne inason nasan halinda Nazeefa take ciki inason na sake nemar yafiyarta kan abubuwan dana aikata mata abaya dan Allah ka barni na shiga" sake riƙeshi Abba ya yi dan ya tabbata yana sakinsa tofa babu makawa sai ya shiga juyo dashi ya yi ya ce



"Ka nutsu ka zauna waje ɗaya in sha Allah yanzu zasu fito da ita" tom ya ce sannan ya juyo da niyyar zama sukayi ido huɗu da Hameed wanda yake kallonsa tunda ya shigo bakinsa na rawa ya nuna Hameed da yatsa ya ce



"Dam...Dama..Daman kana nan?, ina ka samu labarin Nazeefa?"



Ajiyar zuciya Hameed ya sauke ya ce" kayi haƙuri ka zauna Daddy zan yi muku bayani dalla-dalla yanda zaku fahimta" shuru Daddy ya yi amma har sannan ya kasa ɗauke idanunsa daga kan Hameed shi kaɗai yasan irin abubuwan da yake tunowa, tabbas ya cuci rayuwar Nazeefa haka zalika ya cuci rayuwarsa domin duk abunda ya samu Nazeefa tofa shi ya sama, kallonsa Munnubiya ta yi tana mamakin yanda akai yazo London ko ina ya samu kudin? ita kuwa Mommy zata kawai tayi kan kujera ta zuba uban tagumi tana tuna irin abubuwan da suka faru ada tabbas duk wanda ya tuna bara to baiji daɗin bana ba kuma alhaki kuikuyo duk inda kaje sai ya bika tabbas daman tasan watarana sai Hameed ya zama wani arayurwasa saboda yanda suka nuna masa zallar ƙiyayya da auren ɗiyarsu saboda bai kasance mai arziƙi ba, shuru kowa na cikin ward ɗin yana tuna rayuwar baya shi kaɗai ya tafi tunanin abunda ya faru shekaru takwas da suka shige.



*Eight years ago (8)*


*Sultan road/Kano State*



Da sauri ta ce"please baba ɗan tsaya" kallonta Munnubiya ta yi ta yi tsaki, batare da tabi ta kanta ba ta sauka daga cikin motar tana kallon ɗan ƙaramin yaron wanda aƙaalla bazai shige 7-8yrs ba, dafashi ta yi cikin sanyin murya ta ce


"Kai ina mamanka?" kallonta ya yi ya ce" tana can ƙauye ni almajiri ne" girgiza kanta tayi lokaci ɗaya hawaye ya kawo idanunta wace irin rayuwa ce haka ace yaron da bai shige yana gaban iyayen yana karatu ba shine za'a turo almajiranta?, tabbas duniya ta lalace kuma su kan su iyayen basuda hankali, tsaki tayi ta ce


"Have you eaten?"


Kallonta kawai ya yi dan bai gane abinda take nufi ba lura da hakan yasa ta dafe goshinta ta ce


"sorry kaci abinci?"



Girgiza mata kai ya yi ta zaro dubu ɗaya a jakarta tana kallonsa ta miƙa masa ta ce "karɓi kaje ka siya abinci kaci ka dunga tsayawa anan kullum zan dinga tawo maka da abinci da safe kaji" cikeda murna ya karɓi kuɗin ya ce


"Angode Allah ya saka miki da alkhairi Allah ya biya miki buƙatunki na alkhairi"shafa kansa ta yi tana murmushi ta ce



"Ameen ya rabb"


Juyawa ya yi ya tafi ta tsaya tana bin bayansa da kallo, saida ya ƙurewa ganinta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta koma cikin motarsu, Nazeefa kenan kullum burinta ta taimaki wanda bashida shi indai kana ƙasanta tofa burinta ta kyautata maka. Tsaki Munnubiya tayi ta ce



"Kin san Allah zan faɗawa Daddy kowa abashi drivernsa daban wlh bazaki dinga makarar dani a banza ba" ta ƙarashe maganar cikeda tsiwa, murmushi Nazeefa ta yi ta ce




"I'm sorry kinji dear"


Tura baki tayi ta ce" nidai babu ruwana kije ki ƙarata da halin ki wlh irin haka watarana sai kin taimaki wanda zai nemi yaga bayanki" murmushinta mai kyau ta yi ta ce



"Nagode Allah da zai kasance ba nice zan ga bayansa ba" sakar baki Munnubiya ta yi tana kallon ƴar uwartata ita halinta har tsoro yake bata kamar ba mutum ba.




Suna shiga makarantar tasu bayero university of kano State (BUK) Kasancewar ba department ɗinsu ɗaya ba yasa kowacce ta kama gabanta dan ita Munnubiya Fashion and desire take karanta ita kuma Nazeefa medicine take karanta. Tana shiga class ɗinsu ta tafi gefen ƙawarta wato Suhaila dan ita kaɗai ce suke mu'alama sosai kasancewarta ba mai son hayaniya ba murmushi tayi ta ce



"Wai wa kike hange ne?"


"Wannan mutumin na jiya wanda yake waƙa shi nakeson nagani wlh" taɓe baki ta yi ta ce


"to dai ki iya riƙe kan ki dan nasan halinki Hameed ba tsararki bane babu ta inda kuka haɗa hanya" da mamaki Nazeefa ta ce



"wai meyasa kukeda irin wannan dabi'arne kenan indai mutum bashida kuɗi ya zama banza kenan bai isa akula shi ba?, kenan sai wanda yakeda arziƙi shine ya cika mutum?, karfa ki manta duka ubangiji ne ya halicce mu kuma da kansa ya ce ni na girmama ɗan adam to akanme ku kuke raina shi? gaskiya banji daɗi ba kuma ban zaton haka daga gareki ba" girgiza kai Suhaila ta yi ta ce




"Shikenan malama Nazeefa Allah ya huci zuciyarki ban ƙarawa" numfasawa tayi batace komai ba.




*Nanameera ce#*



*SQUAD BOOKS*



*KI Na ZUCIYATA*

*Nanameera*



*AN YA UBA NE?*

*Riamcool*




*SAUDEH*

(Laifin Abbana ne)

*Sherntee ghayu*




*BA MUTUM BACE*

*M.lumu*



*GUDAN JININA*

*Princess Bahilot*





*Together we Stand 🤝*