KI NA ZUCIYATA

Chapter THREE

by @nanameera08

*KINA ZUCIYATA 03*


MIKIYA Writer's asso.




*Queen of the Squad*

Nanameera ce#



Cikin sassarfa ya shigo cikin ajin yana tafiya a nutse sanye yake da wani yadi Kashmir maroon colour ya riƙo handout a hannunsa da idanu Nazeefa ta bishi harya zauna a wajen zamansa dukda bawai kwalliya ya yi ba kuma ba abu mai tsada ya sanya jikinsa ba amma ya yi kyau kasancewarsa asalin bafulatani, Hameed yana matuƙar burgeta coz mutum ne nagartacce wanda ya iya mu'amala da kowa babu yanda za'ayi kaji anyi faɗa dashi ga kuma ƙwaƙwalwa wacce Ubangiji ya bashi kyautarta yanada matuƙar ƙoƙari afannin karatu. Cike da ƙufula Suhaila ta furta




"Wai wannan wane irin abune haka Nazeefa?"



Kallonta Nazeefa tayi da dara-daran idanuwanta wanda suke ɗaukan hankali da alamar neman ƙarin bayani, tsaki tayi ta ce" gaskiya ki daina irin wannan abun babu daɗi akanme zaki wani dinga kallonsa haka sai kace wani babban mutum ai wlh kinfi ƙarfin haka"



Girgiza kai ta yi ta ce" Allah ya shiryeki Suhaila ina kallonsa ne kawai saboda yana burgeni inason naga namiji mai hazaƙa irin haka kuma sannan inason naji yana waƙa abun yana bani sha'awa"



Shuru Suhaila tayi dalilin lecturer daya shigo musu.





Zaune suke suna ɗan taɓa hira inda ya sunkuyar da kansa yana danna wayarsa ƙirar Huawei y6 bai damu da ƙanƙantarta ba, kallonsa Sadeeq ya yi ya ce




"Singer a rera mana waƙa mana"


Ɗago kansa ya yi ya kalleshi sai kuma ya lumshe ido cikeda gajiyawa ya ce



"Mefa?"


"Waƙa mana yau ayi mana sabuwa" numfasawa ya yi ya ce" sorry karka dameni I have alot to do so don't interrupt me ok?" harararsa Abdullah ya yi ya ce



"Tofa har ka fara wulaƙanci ne irinna masu ɗaukaka?" Shuru ya yi bai tankasa ba kuma daman yasan ba lallai bane ya yi magana hakan yasa ya kuma cewa




"Wai sai yaushe zaka fara shiga studio ne?"



"Inason na fara soon amma kuma banida hali ne coz kasan yanzu abubuwa suna min yawa matsalolin gidanmu wanda nine nake tafiyar dasu tunda Allah ya yiwa Abba rasuwa sannan kuma kaga ba wata sana'ar arziki nake ba toh shiyasa na haƙura zuwa sanda Allah zai hore mini"




Ajiyar zuciya Abdullah ya sauke ya ce" toh Allah Ubangiji ya hore mana baki ɗaya" Ameen ya amsa Sadeeq ya ce





"Karka damu Bro komai zai shige kamar bai faru ba don't worry" gyaɗa masa kai Hameed ya yi yana sakin murmushinsa mai kyau





Da sauri ta kalli Suhaila ta ce



"Please kizo muje wajensa ya yi mini waƙa " wani banzan kallo tayi mata ta ce "Allah Ubangiji ya tsareni ya kuma kiyayeni kedai kije sai kin dawo nikam badani ba" haɗe rai Nazeefa ta yi ta ce



"Harma nace miki dan Allah shine zaki ce min haka babu komai thank you" Bata tsaya jiran me zata faɗa ba tayi gaba abinta, da murmushi a fuskarta ta ce



"Assalamu alaikum"



"Wa'alaiki assalam"



Kallonsu tayi Sadeeq ya ce" Sannu Nazeefa" murmushi ta yi ta ce"yawwa ya gida?"

"Alhamdulillah"


Kallonta Hameed ya yi ta sakar masa murmushi bashi da zaɓi wanda ya shige mayar mata da murmushin, zama tayi daga gefen kujerar da suke kai ta ce



"Yawwa daman zuwa nayi ka yimin waƙa Please"





Da sauri ya kalleta sai kuma ya yi murmushi ya ce" ai ban iyaba" kwaɓe fuskarta ta yi ta ce" ayyah kai kuwa ka daure ka yimin kaji" yanda ta langwaɓar da kanta yasa baisan sanda ya yi murmushi ba ya ce "shikenan ki bari sai gobe" girgiza masa kai tayi ta ce




"Yanzu nakeso ka sani ko zamu kai goben?" Shafa kansa ya yi ya ce" oh sorry tom ki bari sai antashi kinga yanzu muna da lecture"




"Babu wani nan kawai kace bakayi niyyar yi mini ba shikenan nagode"



Dafe kansa ya yi ya ce" shikenan zanyi miki" murmushi tayi har saida beauty point ɗinta suka loma ta ce" yawwa thank you singer" girgiza kansa kawai ya yi yana murmushi sannan ya fara rera mata waƙar



_Karki barni yeee karki barni_


_Ki riƙe alƙawarin dake tsakaninmu karki barni masoyiya_


_Ki riƙe amana duk tsanani karki barni Aminiya_


_Ni dake na saba arayuwa karki barni duk wuya_


_Inaji dake azuciya banda kamar ki masoyiya_......




Kallonsa kawai Nazeefa take har ya kai ƙarshen baitin aikuwa suka shiga yi masa tafi ita da su Sadeeq dan sai ka ɗauka shekara ya yi yana tsara waƙar, cikin farin ciki ta ce




"Masha Allah Hameed inada yaƙinin watarana zaka zama shahararren mawaƙi wanda duniya zatayi alfahari Allah ya ƙara maka basira"




Lumshe idanunsa ya yi dan sosai yaji daɗin addu'ar Nazeefa, miƙewa tayi ta ce



"Zan tafi amma kullum zamu dinga haɗuwa kana yi mini waƙa indai mu tashi daga lecture da wuri" murmushi ya yi ya ce



"Tom slimzy"


Wara idanunta tayi ta ce"slimzy kuma?"


Gyaɗa mata kai ya yi ta ce


"Me kenan?"


"Sunanki kenan daga yau coz yanda kike siririya"



Haɗe rai tayi ta ce" nice nayi maka kama da siririya duk ƙiba ta?"


Tuntsirewa sukai da dariya harda riƙe ciki aikuwa ta cika tayi fam kwafa kawai tayi sannan ta juya. Da sauri ya biyo bayanta yana yi mata magana amma taƙi juyowa har suka ƙaraso gaban motarsu inda Munnubiya ke jiranta, da mamaki take kallonsa saidai batace komai ba dan batasan abinda ya haɗashi da Nazeefa ɗinba






"Please I'm so sorry kinji"


"Babu ruwana dakai ni kawai ka kyaleni sai gobe" girgiza kansa ya yi ya ce



"No bazan iyaba dan Allah kiyi haƙuri"



Ganin yanda ya shiga damuwa yasa ta ce" shikenan na haƙura amma da sharaɗin zaka yimin waƙa mai daɗi gobe" gyaɗa mata kai ya yi sannan ta shige mota shikuma ya juya ya koma inda ya baro. Kallonta Munnu tayi ta ce



"Wai mene haɗinki da wannan na ganku tare?"


Tana kallon waje ta ce



"Abokina ne"



"Aboki kuma?"



"E."


Tsaki ta yi ta ce"ke kam wlh Allah Ubangiji ya yaye miki wannan abun naki daman da kowane kare da doki ake abotar?"



Da matukar fusata Nazeefa ta ce



"Wai mene ne matsalar ku ne?, daman bawa shine wanda yake wa kansa arziƙi?, what kind of nonsense is this har zaki buɗi baki ki cewa mutum kare kinsan kuwa mene kare?, are you mad?"




Haɗe rai itama tayi ta ce" na faɗa ɗin daman nasan ai ba bawa kewa kansa arziƙi ba amma ki sani wannan abinda kike zubar da mutuncine bawai burgewa ba kowane irin mutum sauki yarda dashi kice arziƙi na Allah ne wlh bari kiji kina nan sai mutanen da kike taimakawa sun wulaƙanta ki arayuwa nasake nanata miki saboda haka behave your self my dear banason wani nuna kai na Allah ne kuma ai kema kinsan babu wata abota tsakanin namiji da mace face soyayya dole aciki ɗaya na muradin ɗaya kuma kinsan ko zaki mutu babu yanda za'ayi Daddy ya bari ki auri wannan ƙazamin mutumin"



Tsabar takaici kasa cewa komai tayi sai bin yar uwartata da kallo da tayi ita arayuwarta tana mamakin dalilin daya sanya mutane suke ɗaukan talaka matsayin wani abun kyamata ba musanman ma masu kuɗi kullum basu burin talaka ya raɓesu wannan abu yana matuƙar ƙona mata rai, har suka ƙarasa gida uffan bata ceba dan batajin zata iya kula Munnubiya a ƙarashen wannan ranar.





Da sallama ya shiga cikin soron gidan wanda yakasance ƙarami ba kuma mai kyau ba, zaune ya tarar da mahaifiyarsa wacce aƙalla zata kai shekaru 60yrs ɗin nan. Da sauri ya ƙarasa ya karɓi albasar hannunta yana kallonta ya ce



"Haba Mama nace ki dinga tsayawa ina yi miki ki daina yi kinji kinga albasar akwai yaji" murmushi ta yi ta ce



"Karka damu Abdulhameed zan iya shiyasa nayi" girgiza kai ya yi ya ce



"A'a Mama nufaci dan Allah ki daina saboda bakida cikakkiyar lafiya bai kamata kina aikin wahala ba kuma naga gidan daga ni sai ke" Tom tace masa ya cigaba da yanka albasar





*Queen of the Squad ce*


*Nanameera#*



*SQUAD BOOKS*



*KI Na ZUCIYATA*

*Nanameera*



*AN YA UBA NE?*

*Riamcool*



*SAUDEH*

(Laifin Abbana ne)

*Sherntee ghayu*




*BA MUTUM BACE*

*M.lumu*




*GUDAN JININA*

*Princess Bahilot*