KI NA ZUCIYATA

Chapter FOUR

by @nanameera08

*KINA ZUCIYATA 04*

MIKIYA Writer's asso.



*Queen of the Squad*



*Nanameera ce*


Da sallama ta shigo cikin gidan tana tafiya cikin nutsuwa kallonta Mama ta yi ta ce "Zainab sai yanzu?" zama tayi kan tabarmar tana kallon Mama ta ce"wlh Mama na ɗan tsaya ne a gida shiyasa ban dawo da wuri ba, yaya bani na ƙarasa" murmushi ya yi ya ce" A'a tunda nafara barni na ƙarasa kinji" tasowa tayi ta karɓe wuƙar hannunsa ta ce" ai ba aikinka bane kuma naga daga makaranta kake baka huta ba kaje ka huta kawai" toh ya ce sannan ya tashi ya shige ɗakinsa wanda ya kasance ɗan ƙarami amma kuma ko ina a tsaftace Saboda kasantuwarsa ma'abocin tsafta.




Tana fitowa daga toilet ta zauna gefen gadonta tana danna wayarta, ringing wayar ta fara yi ta kalli number da aka kirata da ita lokaci ɗaya ta saki wani kyakkyawan murmushi wanda yake nuna farin cikin da take ciki, ɗaga wayar tayi ta saka kunnenta daga ɗaya ɓangaren ya ce



"Barka dai princess fatan kina lafiya ya school ɗin naso nazo na ɗauke ki amma nayi busy sosai" murmushinta mai kyau ta yi ta ce



"Ayyah babu komai kasan ma nida Munnubiya muke tawowa idan na biyo ka zata faɗawa Daddy ne"




"Ok tom in Sha Allah ranar Friday zan shigo kinji love"



"Tom sai kazo amma kazo da wuri coz nasan halinka" ok ya ce mata sannan sukai sallama, kwanciya tayi akan royal bed ɗinta ta ɗora wayarta bisa ƙirjinta idanunta a lumshe tana jin wata nutsuwa ta musamman na saukar mata a rayuwarta tana matuƙar so da ƙaunar Fu'ad kamar yanda shima yake sonta tamkar yanda shima yake sonta aƙalla sun kai kusan 1yr da haɗuwa lokacin da suka gama secondary school. Banda ƙarar cokula babu abinda ke tashi a parlon kowanne ya yi busy yana cin abinci banda Nazeefa wacce tayi shiru ita kaɗai tasan abinda take tunani alokaci lura da haka yasa Mami ta ce



"Nazeefa me kike tunani haka?"



Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce" nothing Mami" kallonta kawai ta yi amma bata ce komai ba ta cigaba da cin abincinta, Munnubiya ce ta ce



"Daddy Please gobe inason zani gidansu friend ɗita"


Kamar bazai magana ba sai kuma ya ce"when?"


"Da yamma in Sha Allah"


Miƙewa ya yi ya ce "ki tafi tare da ƴar uwarki" da sauri Nazeefa ta kalleshi dan Allah ya sani bata ƙaunar fita ko nan da can sai dai makaranta wacce ta zame mata dole, ganin yanayinta yasa ya ce"akwai wani abu ne?" Sunkuyar da kanta ta yi ta ce



"Daman gobe inada lecture har yamma ne ita kuma iya safe take da shiyasa" gyaɗa kansa ya yi alamar ya fahimta sai kuma ya ce"ok Aishatu ki bari sai weekend kwaje" tom kawai ta ce saboda basa musu da Dad ɗinsu ya shige ciki sukuma suka cigaba da cin abincinsu. Washegari da wuri tagama shirin makaranta saboda tanada lecture da safe fitowa tayi parlon cikin wani hijab ɗinkin julbab sister colour ya yi matuƙar yi mata kyau da sauri suka gaisa da Mami sannan suka shiga mota suna ƙoƙarin fita daga gidan ta ce


"Oops na yi mantuwa Please"


Kallonta Munnu ta yi bata ce komai ba ta sauka daga motar, kitchen ta shiga ta ɗauki wani ƙaramin food flask ta zuba soyenyen dankalin da kwai aciki sannan ta rufe ta fito da mamaki Munnu ta kalleta har ta shiga motar sannan ta ce



"Wannan fa?"


"Yaron da nayiwa alƙawari jiya shi zan kaiwa abinci" sakar baki tayi tana kallonta dan ta rasa abinda zata ce mata kawai ta girgiza kanta Ita kuwa Nazeefa hankalinta yana kan titi dan kada su shige wajen da yaron yake tsaiwa, suna isa kuwa ta hango shi hakan yasa ta tsayar da drivern ta sauka, saida ta tabbatar ya tafi domin cin abincin sannan ta koma mota suka cigaba da tafiya.





Suna fitowa daga lecture ta kalli Ayrah da Suhaila ta ce"Please kuzo muje wajen singer" harararta Suhaila ta yi ita kuwa Ayrah ta ce



"Haba baiwar Allah wlh baki isaba kedai can kije kiyi ta zubar da mutuncinki amma wlh babu mu acikin wannan abin kunyar" kallonsu kawai tai dan sosai maganar ta ɓata mata rai amma kawai ta danne ta girgiza kanta ta yi gaba, tana tafiya suhaila ta ce"kinsan Allah ji nake kamar na shaƙe Nazeefa idan tana irin wannan abun kwata-kwata batada class ita ganin abinda take kamar wani abun arziƙi take wai ita mai tsoron Allah" taɓe baki Ayrah ta yi ta ce" nifa shiyasa nake mata shiru wani tym ɗin Saboda fusata ni take" tsaki Suhaila ta yi sannan ta ce"please zoki rakani wajen Taj" ok ta ce sannan suka tafi.






Dafe kansa ya yi ya ce"ayyah Slimzy dan Allah ki taimaka ki barni da wannan waƙar yau ina busy Please" turo baki ta yi ta ce" A'a nikam ka yimin ko kaɗan ce" rasa abinda zai ce mata ya yi Sadeeq ya ce" yanzu abinda za'ayi ki bari zuwa anjima sai ya yi miki" kallonsa ta yi sai kuma ta ce"nikam babu ruwanka dani" murmushi sukai duka Abdullah ya ce" yanzu kai Singer ka yiwa wannan rigimammiyar ƙawartaka waƙa tun kafin ta fashe da kuka dan naga ta gama cika fam sauran kiris ta fashe" tuntsirewa sukai da dariya ta haɗe rai kamar zatayi kuka ta ce" ai duk ba daku nake ba ku bari shi ya faɗa da kansa saina haƙura" ajiyar zuciya ya sauke ya ce




"Shikenan zan yi miki waƙa amma not now yanzu inada uzuri babba kinji" ya ƙarashe maganar yana langwaɓar da kansa, sauke numfashi ta yi ta ce"shikenan zan tafi amma ka bani number ka idan ka koma gida da yamma sai kayi min waƙar" babu yanda ya iya haka ya bata number sa sannan ya ce



"Now kinji daɗi?"



Da murmushi a fuskarta ta ɗaga masa kai ya ce"Tom shikenan?" gyaɗa masa kai ta yi ta miƙe ta ce



"Thank you my friend"



Murmushi ya mayar mata ya ce" You Are always welcome dear" bye bye tayi musu sannan ta juya ta tafi, taɓoshi Sadeeq ya yi ya ce" yadai singer wannan kallonfa?" Harararsa Hameed ya yi ya cigaba da duba handout ɗinsa.






Da mamaki take kallon wanda ke tsaye jikin motar yana kallonta da murmushi a fuskarsa jiki asanyaye ta ƙarasa wajensa



"Surprised"



Murmushi ta yi ta ce"shine baka faɗamin ba ko?" Cikin fara'a ya ce" I'm so sorry dear daman inason na ɗan baki mata⁰⁰maki ne" turo baki tayi cikeda shagwaɓa ta ce" aikam babu ruwana dakai" dafe kirjinsa ya yi ya ce" Allah na tuba dear ban ƙarawa" murmushi ta yi ta ce"shikenan na haƙura amma dai zaka siyamin ice-cream?" Kallonta ya yi sai kuma ya buɗe murfin motarsa ya ce" muje" tsayawa tayi tana kallonsa ya ce



"Ice-cream ɗinfa"


Murmushi tayi sai kuma ta girgiza kai, shiga motar tayi shima ya shiga sannan ya kalleta ya ce



"Sai kace zan kama ki ko?"



Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi ya girgiza kai sannan ya juya back ɗin motar ya ɗauko wata leda ya miƙa mata karɓa tayi ta buɗe ta waro idanunta cikeda farin ciki ta ce



"Thank you so much prince I love it" sosai ya murna ganin yanda ta nuna farin cikinta daman kuma yasan indai kanason burge Nazeefa to ka bata ice-cream or chocolate tana matuƙar ƙaunar waɗannan abubuwan, kallonta kawai ya tsaya yi ganin Yanda take shan ice-cream tana lumshe ido saboda tsananin garɗin madarar da yake zuwa har cikin kwakwalwarta cikin yan mintuna kaɗan ta shanye roba ɗaya daga cikin ice-cream ɗin. Buɗe ledar tayi da niyyar ɗauko chocolate suka haɗa ido dashi saurin zare hannunta tayi tana rufe fuskarta, murmushi ya yi ya ce"nifa ba hana ki zanyi ba Princess idan kina so zan ƙaro miki" dariyarta mai kyau tayi ta ce"thank you alot my prince".






Saida yaga tagama ci sannan ya ce"yanzu mu tafi na kaiki gida" saurin kallonsa ta yi sai kuma ta ce cikin kwantar da murya




"Kasan ba ni kaɗai nake tafiya ba da Munnubiya muke komawa gida kuma driver ne yake tafiya damu idan Daddy yaji na dawo gida ni kaɗai faɗa zai yimin kasan halinsa kuma" gyaɗa mata kai ya yi alamar fahimta ya ce




"Ok tom shikenan in sha Allah nima Friday ɗin zan shigo"



"Karka manta fa"



"I will not"



Ok ta ce sannan sukai sallama ta sauka yana ɗaga mata hannu taje ta shige motarsu. Kallonta Munnu ta yi ta ce"meyasa biki bishi ba?" Tana ajiye ledar hannunta ta ce" saboda ba daidai bane hakan shiyasa kawai" taɓe baki ta yi ta ce" amma ai Fu'ad bashi da matsala kuma kema kin tabbatar da haka" gyaɗa kanta tayi ta ce" that's why ma ban yarda na bishi ba" numfasawa ta yi ta ce" Allah ya kyauta"



"Ameen".




*Queen of the Squad*

*Nanameera ce*