Chapter FIVE-TEN
by @nanameera08
*KI NA ZUCIYATA 05-10*
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION.
*Queen of the Squad ce*
*Nanameera*
Kusan two months kenan zuwa lokacin sunyi mugun sabo da Hameed dan babu wnada bai sansu tare ba cikin makarantar wasu suce soyayya suke wasu kuma suce jininsu ne kawai ya haɗu, yauma kamar kullum suna zaune gefen cafeteria ɗin yana rera mata waƙa kamar yanda suka saba kullum haɗe rai tayi jin abinda ya ce bai lura ba ya ci-gaba da waƙarsa yana murmushi tsaki yaji tayi kawai ta miƙe batareda ta ce masa komai ba tayi gaba miƙewa shima ya yi yabi bayanta yana kiran "Nazeefa!! Nazeefa!! Nazeefa" ko juyowa bata yiba bare ya yi tunanin amsa masa ta ci-gaba da tafiyarta, shafa kansa ya yi yana murmushi dan daman yana sane ya yi mata hakan idan ba haka ba bazata rabu dashi ba. Ita kuwa bata zarce ko'ina ba sai bakin gate tana zuwa ta tsari napep ta sanar dashi inda zai kaita...
Da sallama ta shiga cikin gidan tana ƙare masa kallo, da sauri ta ƙaras tana murmushi ta karbi tsintsiyar hannunta tana cewa" A'a Mama ki bari nayi miki kinji" girgiza kai Mama ta yi ta ce" A'a Nazeefa kinsan fa baki yin shara kada wani ciwon yazo ya kama ki anan bansan ya ya zanyi ba dan Allah ki barni nayi" kwaɓe fuska ta yi tana kallonta ta ce" please Mama ai inada face mask babu abinda zai sameni in Sha Allah" duk yanda Mama taso hanata sharar kin yarda tayi saida tayi mata bayan ta saka face mask ɗinta dukda yanda takejin numfashinta na ƙoƙarin janyewa haka ta daure dan batason Mama ta fahimci hakan harta kammala sannan ta ajiye tsintsiyar. Saida ta wanke hannayenta sannan ta zaune gafen tabarmar Mama ta ce" sannu Nazeefa sannu kinji" murmushi kawai ta yi tana sunkuyar da kanta tashi Mama tayi ta shiga ɗakinta not too long ta dawo hannunta riƙe da wani bowl ɗan ƙarami zama tayi tana kallon Nazeefa ta ce" daman ke na ajiyewa zan aiki Zainab ta kai miki gida sai gashi Allah ya kawo ki" karba Nazeefa ta yi tana murmushi ta ce" aikuwa na gode sosai Mama daman na daɗe banci alkaki ba" murmushi Mama ta yi ta ce" karki damu Allah ya yi miki albarka" "Ameen Mamana" gyara zamanta tayi ta sanya bowl ɗin agaba ta faracin alkakin tana lumshe ido saboda wani daɗi da yake mata ita a rayuwarta tana matuƙar ƙaunar irin waɗannan abubuwan wanda bata samesu a gidansu ba, tana cikin ci ta kalli Mama wacce itama ita take kallo ta ce" Mama daman ƙara na kawo miki" da mamaki Mama ta ce" ƙara kuma Nazeefa ƙarar wa?" "Hameed mana" murmushi Mama ta yi ya ce"kice ke da abokin naki ne" kwafa ta yi ta ce"wlh Mama ki ce masa ya daina ce min wata Slimzy wai siririya bayan da girmana idan ba haka ba wlh ransa sai ya ɓaci" murmushi irinna manya Mama ta yi ta ce" shikenan kiyi haƙuri Nazeefa in Sha Allah zan sanar masa kuma bazai sake ba kinji" murmushin itama tayi ta ce" yawwa Mama na gode", miƙewa tayi tana ɗaukan handbag ɗin ta Mama ta ce" ina kuma zaki je?" buɗe jakar tayi tana cewa " wlh Mama makaranta zan koma ba tashi akayi ba kawai fitowata nayi" "Ayyah to shikenan Allah ya bada sa'a" Ameen Nazeefa ta ce sannan ta ajiye mata rafar ƴan dari biyar ta ce" babu yawa Mama" kasa magana Mama ta yi sai kuma ta rungumeta kamar tayi kuka ta ce" Allah ya yi miki albarka ya kula da rayuwarki ya baki miji nagari wanda zai ji ƙanki Nazeefa na gode sosai kinji" murmushin jindaɗi tayi ta ce" Ameen Ameen Mama na gode nima" sallama tayi mata sannan ta juya ta fita.........
Sosai ake traffic akan hanyar ga zafin napep wanda bata saba dashi ba duk sai taji hankalinta ya tashi kuma batada nutsuwa, cikin wannan halin wata Black ɗin motar ta tsaya daga jikin napep ɗinsu kamar wanda aka ce ya juyo haka ya juya lokaci ɗaya kuma idanunsa ya sauka akan Nazeefa wacce take ta faman fiffita da mayafinta with mouth agape Daddy yake kallon ɗiyar tasa shin me takeyi a wannan lokaci awaje kuma cikin Napep shi dai yasan tunda suka zo duniya basu taɓa hawa wannan abun ba duk inda zasu je amota ake kai su kuma a ɗaukosu da suka girma kuma wani lokacin suke driving ɗin da kansu amma yau Nazeefa ce cikin Napep kuma alokacin da ake gudanar da lecture acan school ji ya yi kamar ya fita ya kamota ya yi mata dukan tsiya awajen amma sai kawai ya share bayan sun samu hanya ya ɗauki hanyar makarantar tasu. Tafiyar napep dana mota ba ɗaya ba hakan yasa Daddy ya riga su zuwa makarantar kai tsaye kuma office ɗin H.O.D ɗin nasu ya nufa yana shiga bayan sun gaisa dashi ya faɗa masa yana son cire ƴarsa Nazeefa ne daga cikin makarantar sosai ya yi mamaki amma rashin sanin abinda yake faruwa yasa ya bashi takardar suka yi sallama sannan ya fito bai tsaya sai ya tafi dasu ba ya yi shigewarsa mota ya bar makarantar..
Turo ƙofar akayi ya saka ta kalli wacce ke shigowa sai kuma ta ɗauke kanta, kallo ɗaya Munnubiya ta yi mata sai kuma ta ce" Daddy na kiranki" okay Nazeefa ta ce sannan ta miƙe tana dafe kanta wanda take jin yana mata ciwo ta yi waje.
Zaune ta tarar dashi sai Mommy dakuma Munnubiya sai Auntynsu wato babar Munnubiya, tsugunawa tayi ta ce" Daddy gani" ajiye jaridar hannunsa ya yi ya ce" ɗazu ina kika je daga makaranta?" ji tayi gabanta ya yi wani irin faɗuwa lokaci ɗaya ta fara rawar kerma sanin halin Daddyn nasu ko ya akayi ya ganta ohoooo, tsawar daya daka mata yasa ta kalleshi afirgice sai kuma ta fashe da kuka ta haɗe hannayenta biyu ta ce" Daddy dan Allah kayi haƙuri wlh babu inda naje gidansu Hameed naje wajen Mamansu dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba wlh.." shuru tayi sanda tagama recalling abinda ta faɗa miƙewa ya yi yana kallonsu duka su biyun ya ce" Hameed wane kuma Hameed kuma mene ne haɗinki dashi da har zaki tafi gidansu???" ɗora hannunta ta yi amma akanta dan tasan batada wata mafita da zata kare kanta babu abinda zai hana Daddy ya hukuntata, shurun da tayi shine abinda ya ƙara ƙona masa rai cikeda masifa yake kallon Munnubiya wacce itama duk tasha jinin jikinta ya ce"keeeee faɗa min wane Hameed?" bakinta na rawa ta ce"Daddy wllh... Wlh..Wlh saurayinta ne"
"Saurayinta??????"
A firgice Nazeefa ta ɗago tana kallon ƴar uwartata amma ta kasa magana dan batasan ma abinda zata ce ba wasu zafafan hawayene suka shiga gangarowa kan kuncinta duk ta haɗa gumi kana ganinta kasan hankalinta atashe yake.
Zagaye parlon ya fara yi kamar wani wanda ya yiwa Sarki ƙarya sai kuma ya juyo afusace ya ce" wato abinda na aikeki kiyi a makarantar kenan ko??, daman shine dalilin daya sanya kika ci-gaba da karatun saboda ki shiga duniya ko??, idan aure kike so meyasa bazaki sanar dani ba ai daman akwai wnada ya taɓa cemin yana sonki zai aurawa ɗansa nace masa A'a saboda naga karatu kike ashe ke kina can harda yawo gidansu saurayi saboda ke bakida hankali" ya ƙarashe maganar yana rufe ta da dukaa, da sauri sukayi kansa suna bashi haƙuri banda kuka babu abinda Mommy take yi cikin magiya take cewa" dan girman Allah Alhaji kada ka kasheta dan Allah dan Annabi kayi haƙuri duk hukuncin daya kamata kayi mata amma dan Allah karka kasheta ko ka illatata na roƙeka" sosai suke kuka ganin yanda yake dukan nata Kamar babu imani atare dashi Munnubiya ce ta riƙe shi ta ce"Daddy kayi haƙui bazata sake ba dan Allah kaga batada lafiya" yi yayi kamar baisan suna wajen ba hakan yasa ta tafi ɗakin Nazeefa da gudu wayarta ta ɗauka cikin sauri ta yi dialing number Hameed kira ɗaya ya ɗaga cikin tashin hankali take faɗa masa ya zo gidansu bai tsaya ƙarasa saurarenta ba ya kashe wayar suka tawo shida Abdullah.....
Cikin hanzari suka zo wajen Daddy Saida suka sanya ƙarfi sannan suka ɓanɓareshi daga jikinta, kallonsu Daddy ya tsaya yana yi dan baisan sanda suka shigo masa gida ba kuma bai ma san su waye ba yana huci ya juya ya fice daga parlon inda sukuma suka yi kanta dan ganin halinda take ciki. Munnubiya ce ta tafi kitchen ta ɗauko ruwa agora da cup tana fitowa Mommy ta karɓa ta bata, saida tasha sannan ta jingina da jikin Mommy lokaci ɗaya ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya rungumeta Mommy ta yi tana bata haƙuri cikin haka basu san sanda Daddy ya shigo ba sai ji sukai ana cewa" Arrest them" da sauri suka ɗago idanu dukkansu suna kallonsa ashe yan sanda yaje ya ɗebo kafin suyi yunƙurin yin wani abu har an sun sakawa Hameed da Abdullah handcuff, miƙewa Nazeefa ta yi dukda yanda take jin kanta na barazanar tsagewa ta riƙe ƙafafuwanshi cikin sigar magiya ta ce" Daddy dan Allah dan Annabi kayi mini duk abinda kake so amma dan Allah karka saka a kamashi Wlh shi kaɗai mahaifiyarsa take da dan Allah Daddy kayi haƙuri" murmushi Daddy ya yi yana kallonta ya ce" ohooo da yasan bashi da wani gata har ya nemi haɗa hanya dake?, to bari kiji Wlh sai na saka an ɗaureshi kuma kema bazan barki haka ba ki jirayi hukuncin da Zanyi miki" yana kallon ƴan sandan ya ce" officer ku tafi dasu" okay suka ce sannan suka yi waje da Hameed tsaki Daddy ya yi sannan ya shige apartment ɗinsa durƙushewa tayi anan ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya wannan wace irin rayuwa ce?, ta rigada tasan halin Daddynta babu abinda bazai iya aikatawa ba tunanin hakan yasa ta sake fashewa da wani kukan wanda batada mai rarrashinta tashin hankalinta ɗaya ya Mama zataji idan taji ankama Hameed wane zai tallafi rayuwarsu inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun abinda ta dinga maimaitawa kenan cikin ranta ko Allah zai kawo mata mafita......
Cikin kwanakin da basu shige uku ba Nazeefa ta fice a hayyacinta kwata-kwata batada nutsuwa kullum cikin tunani take gashi har sannan ba'a sallamo su Hameed ba har gidan Mama tazo tana kuka amma ko ajikin Daddy sai sakawa da ya yi aka fita da'ita, batada wani aikin yi sai kuka haka take kwana take yini gashi ya ƙi ya saurareta bare ma ta samu tabashi haƙuri,
"Nazeefa!! Nazeefa!! Nazeefa!!"
Afirgice ta ɗago tana kallon Mommyn tata sai kuma ta fashe da kuka numfasawa Mommy ta yi ta ce" ki daina wannan kukan kizo babanki yana kiranki" da sauri ta kalli Mommy sai kuma ta ce" Mommy ya haƙura?" "nima bansani ba Nazeefa idan kinje sai ki tambayeshi" ji tayi jikinta ya yi sanyi amma haka ta miƙe Mommy ta taimaka mata ta sanya hijab ɗinta sannan suka fito. Zaune yake kan royal cusion ɗin dake parlon ya dora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon tashar BBC, a hankali ta zauna daga can gefen kujera two seater kanta a ƙasa, zama Mommy ta yi tana kallonsa ta ce" gata nan" bai kalleta ya ce" okay" kusan 2mins sannan wasu mutane suka yi sallama suka shigo parlon manyan mutane ne dan zasuyi sa'anni da Daddy sai kuma wani matashin saurayi wanda baifi 30yrs ba zama ya yi yana ƴan kalle-kalle kamar me son gano wani abu kallo ɗaya Nazeefa tayi musu ta sunkuyar da kanta daidai lokacin Munnubiya suka fito itada Mommynta bayan sun zauna Daddy ya kalli mutanen cikeda girmamawa ya ce" Alhaji sannunku da zuwa" fuska a sake suka ce" yawwa ya gida ya yaran?" "Alhamdulillah".
Kallon Nazeefa Daddy ya yi ya ce"baki iya gaisuwa bane?" cikeda girmamawa ta ce" ina yini?" "Lpyklao ykk?" "Ina lpy" "Masha Allah, Ubangiji ya yi albarka" Ameen ta ce sannan ta sake maida kanta ƙasa saida suka gaisa da matan gidan sannan Daddy ya ce
"Nazeefa!!"
"Na'am Daddy"
"Ina son sanar dake wani abu wanda na yanke game da rayuwarki domin ina ganin kamar shine mafita, na ɗaura miki aure da ɗan mai gidana Fahat jiya da daddare saboda haka in Sha Allah zuwa anjima ki shirya duk abinda kike buƙata domin zasu tafi dake ne banason wani bidi'a okay?"
Ba Nazeefa ba hatta su Mommy tsayawa sukai suna kallonsa, sun kasa gane wane ma'aunin zasu ɗora maganganunsa, babu wanda ya fahimci gundarin abinda yake son ya faɗa musu, ita kuwa Nazeefa wacce ta gama naɗe duk maganganun da ya faɗa kasa motsi ta yi haka kuma ta kasa yin kukan zuciyarta duk ta bushe batada zarafin yin magana a wannan lokacin domin tabbas idan ta buɗi bakinta to fah zuciyarta zata iya bugawa ta kasa gane mene ne abinda yake shirin faruwa da rayuwarta acikin wannan ɗan taƙin gabaɗaya rayuwar ta juya mata takoma upside down ji take inama ta mutu tun tana ciki da ace tazo ta riski irin wannan ranar, ina ma Daddy kasheta ya yi sanda ya fara dukanta da zuwan wannan lokacin, inama ta haɗiyi zuciya ta mutu tabar duniyar gudun ganin irin wannan ranar wace irin masifa ce haka?, wace irin ƙaddarace haka?, meyasa sai ita??, meyasa Daddy zai yi haka??, waɗannan tunanin sune abinda suka mayar da ita tamkar wata zautacciya, Munnubiya ce ta jijjigata dalilin maganar da Daddy yake ta yimata wanda Bama tasan yana yi ba domin kwata-kwata hankalinta yabar jikinta.
Afusace ya ce"ko baki ji abinda nace miki ba?"
Kallonsa kawai Nazeefa take domin idan tace ta ji abinda ya ce tofah ƙarya take Mommy ce ta kama hannunta ta ce"muje ki haɗa kayanki" ɗaya ga cikin mutanen nan ne ya ce"A'a basai ta haɗa wani kaya ba akwai komai acan na buƙata karku damu"
Kasa magana Mommy ta yi kawai ta saki hannun Nazeefa domin tasan ko zata mutu Daddy bazai bari ta shiga cikin ba, banda kuka babu abinda Munnubiya take yi domin bata taɓa tunanin Daddy zai iya aikata hakan ba ta ɗauka abin zai shige kamar ba ayiba ashe ba haka bane, ƙarasowa Nazeefa ta yi gabansa tana kallonsa cikin rawar murya wacce take adashe ta ce" Daddy dan Allah ka yafemin abubuwan dana aikata maka ka yimin afuwa dan darajar Annabi Muhammadu (S.A.W) banason na tafi batareda ka yafemin ba domin nadan cewa babu tabbacin dawowata araye, Sannan dan Allah ina neman alfarma awajenka Daddy ka taimaka ka saki Hameed koda shine alfarma ta ƙarshe tsakanina dakai dan Allah Dadd......" kasa ƙarasa maganar tayi dalilin sarƙafewa da numfashinta ya yi hakan ya sanyata yin shuru tana maida numfashi, ajiyar zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce" zan sake shi amma sai ya yi watanni uku wanda sune abinda na ɗaukar masa zai yi agidan yari daga sannan bazai sake tunanin haɗa hanya da ƴar wanda ba sa'ar shi ba" kallonsa kawai Nazeefa ta yi sai kuma ta girgiza kai a hankali ta ƙarasa wajen Mommy samun kanta ta yi da kasa furta kalma agaban Mommynta sai kuka wanda ya ci ƙarfinta rungumeta Mommy tayi itama tana kuka kamar ranta zai fita haka Munnubiya tazo ta rungumeta itama suna kuka wanda tunda su kazo duniya basu taɓa yin irinsa ba, ganin abun nasu bamai ƙarewa bane yasa Daddy yazo ya janye ta daga jikinsu tana kallonsu haka suka shiga da'ita motar sannan suka bar gidan.........
Allah Sarki rayuwa haka Nazeefa ta kasance cikin ahalin da ba nataba kuma waƴanda bata sansu ba, kwata-kwata ta kasa sabawa dasu kuma har sannan basu miƙata ɗakin mijinta ba.
Ranar da ta cika sati biyu dazuwa aranar suka kaita ɗakin mijinta kuma aranar ta buɗe wata sabuwar rayuwa wacce babu jindaɗi a cikinta domin itadai tundaga angonci bata taɓa ganin miji irin Fahat ba kwata-kwata bashi da ɗabi'a kuma babu wanda yake jin magana bare wani ya tsawarta masa babban abinda yafi damunta shine yanda bai ɗauki addini matsayin komai ba sannan kuma ya kasance mai biye-biyen mata, ko bacci Nazeefa bata iya yi kullum cikin fargaba da tashin hankali take gashi ko sau ɗaya Daddy bai taɓa kiranta yaji wane hali take ba, a haka har tayi watanni biyar matsayin matar Fahat.
Zaune take kan kujera banda zufa babu abinda yake ketowa daga fuskarta ilahirin jikinta rawa yake ita kaɗai tasan halin da take ciki, shigowa ya yi yana dariya kallonsa ta yi taga ashe waya yake da budurwarsa wanda ba sabon abu bane awajensa, kallo ɗaya ya yi mata sannan ya shige ciki abinsa, da kallo itama ta bisa ta runtse idanunta wasu zafafan hawayene suka shiga gangarowa kan kuncinta wannan wane Irin aurene???, Allah Sarki babu wanda ya faɗo aranta sai Hameed ko ya yake??, murna ɗaya take daya kasance an fito dashi daga gidan yari wanda kuma kafin wannan lokaci Allah ya yiwa Mama rasuwa kuma ta mutune da baƙin cikin rashin ganin ɗanta sanda Munnubiya ta sanar da'ita babu yanda batayi da Fahat ba akan ya barta taje amma ya ce babu inda zata haka tasha kukanta ta haƙura idan har zakaga Nazeefa awannan lokacin tofah zaka iya ƙin ganeta duba da yanda ta zama kamar wata tsohuwa duk ta fice a hayyacinta babu cima mai kyau dan sai yaga dama yake bata abinci ga kuma ciki wanda yake da buƙatar kulawa amma bai samu ba duk fatarta ta yamushe ta yi baƙi, fitowa taga ya yi cikin wata farar shadda ƙal ya ɗora hula sai baza ƙamshi yake, ganin kamar ƙoƙarin fita yake yasa ta ce
"Dan Allah ka bani abinci Wlh yunwa nakeji kamar na mutu kuma cikina ciwo yake". Wani shegen kallo ya yi mata sannan ya ce" auhhhh toh ki mutu kiga idan wani kika yiwa karki fasa mutuwa kuma abinci sai sanda na dawo cikin gidan nan sannan zaki ci saboda haka karki dameni" yana gama faɗin hakan ya yi ficewarsa.
Fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita yunwa take ji ba kaɗan ba amma ko a jikinsa, haka ta zauna akan kujerar tana kukanta har bacci ɓarawo yazo ya saceta..........
Cikeda tashin hankali take kallonsu duka bakinta sai rawa yake tama kasa furta komai shi kuwa ko ajikinsa haka yake kallonta banda budurwar wacce take ta faman zare idanu, juyawa Nazeefa ta yi zata fita ya yi saurin fizgota wanda hakan yasa ta waɗi ƙasa ji kake taassssss, cikin ƙanƙanin lokacin ta fara bleading jini amma hakan bai hanasa shaƙeta ba cikeda rashin imani yake cewa" Wlh idan har kika kuskura kika sanar da wani abinda yake faruwa toh ki sani Wlh ni Fahat ni ne ajalinki, Wlh saina kasheki"
Wata ƙara Munnubiya ta saki tana shigowa da gudu tana zuwa ta sunkuya tana kallon ƴar uwartata cikin rashin hankali ta ke cewa" Nazeefa!! Nazeefa!!" kasa magana Nazeefa ta yi sai hannunta taga kamo ta riƙe shi gam amma ta kasa magana, fashewa tayi da kuka cikin tsananin baƙin ciki take kallon Fahat ta ce" Wlh ka sani bazamu taɓa yafe maka ba kuma Wlh sai na faɗa wa duniya abinda ka aikatawa ƴar uwata idan kuma har ta mutu toh wlh kaima ni ce ajalinka"
Ko kallonta Fahat bai yiba ya kama hannun yarintar suka bar ɗakin ya yi hakane kuma gudun karta tara masa jama'a bai fitarda yarinyar ba. Hankalin kowa atashe yake lokacin da akace Nazeefa na asibiti kuma kusan 2hrs kenan likitocin basu fito daga emergency ɗinba, iyaka tashin hankali tofah Daddy ya shige shi domin bai taɓa tsammatar hakan zata iya kasancewa ba bai ɗauka Fahat zai iya cutar da Nazeefa fa ba, Mommy kuwa banda kuka babu abinda take dukda yanda Daddy ya yita bata baki haka taƙi haƙura, Mom ɗin Faheeta lokacin tazo ƙasar ita ta dinga kwantar musu da hankali akan zata samu sauƙi.
Banda zufa babu abinda Daddy keyi cikin rawar murya ya ce" doc..doct.doctor kana nufin Nazeefa nada ciwon zuciya?, yaushe doctor??" zare farin glass ɗin idanunsa ya yi ya ce"I'm sorry sir amma tanada ciwon zuciya kuma ya yi ƙarfi sosai kowane lokaci daga yanzu za'a iya rasa rayuwarta domin ta rigada taje matakin ƙarshe na cutar ga kuma mahaifarta wacce ta rigada ta lalace dalilin takata da aka yi bayan kuma akwai ciki ajikinta a halin yanzu abinda ke cikinta ya mutu kuma mun cire mata shi ita kuma akwai buƙatar fita da'ita ƙasar waje domin duba lafiyarta acan"
Daddy baisan sanda ya fashe da kuka ba tabbas ya cuci kansa ya cuci Nazeefa ya kuma cuci mahaifiyarta bashida bakinda zai nemi yafiyar yarinyar yasan ya aikata kuskure amma duk tsawon lokacin nan baya iya bacci kullum sai ya ɗauko hotonta ya sanya agaba yana kalla lokaci zuwa lokaci yake cewa " KI NA ZUCIYATA" Nazeefa ina matuƙar ƙaunar ki kuma ina ganin nayi abinda ya dace da rayuwarki" ashe ba haka bane, ashe shine silar lalacewar farin cikin ƴarsa wannan wace irin ƙaddarace???????
Babu wanda bai yi kuka ba bayan sanar dasu abinda ya faru duk da bai ce musu mahaifarta ta lalace ba haka aka shirya komai na tafiya India cikin ƴan awannin suka bar ƙasar da'ita. Aƙalla ta ɗauki kusan shekaru 7 tana jinya a asibiti cikin ƙasar India kafin daga bisani su sallameta ta koma wajen Mom ɗin Fateeha da zama wai dan ta manta da abubuwan da suka faru abaya wanda bana jin Nazeefa ta manta dasu, har zuwa sanda yanzu take kwance a asibiti dalilin ganin Hameed da tayi....
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU SHEKARU TAKWAS BAYA YANZU KUMA ZAN DORA DA CIGABAN LABARI.
*Queen of the Squad ce*
*Nanameera*