KI NA ZUCIYATA

Chapter ELEVEN-FIFTHEEN

by @nanameera08

*KI NA ZUCIYATA 10-15*

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION.



*I Dedicated this book to yhu friend Riamcool Star of the Squad Ina matuƙar ƙaunarta Allah ya barmu tare dear, together with SQUAD Members*



*Gajeran labari ne*



*Queen of the Squad*

*Nanameera ce*



*END*


Shuru ward ɗin ya ɗauka kowa yana sauraren Hameed wanda yake bada labarin yanda akayi ya samu aiki har ya yi kuɗi haka ajiye gorar ruwan hannunsa ya yi ya ci-gaba da faɗin



"Bayan anyi arba'in ɗin Mama na rasa makama da abinyi banida wata sana'a wacce zanyi a lokacin sannan kuma makaranta ta gagareni zuwa kullum gani nake kamar zanga Nazeefa ta dawo wajena hakan yake sakawa naji banida sukuni cikin wannan yanayi da nake ciki wani daga cikin abokaina yazo gidanmu, cikin wannan hali Najeeb ya jani cikin abokansa tun ban fahimci abinda suke aikatawa ba har nazo na fahimta sana'ar su ita ce sace-sace da kuma kwace idan sun samu kuɗi kuma sai su siyo kayan maye tun ina gudun shiga cikinsu har nazo na saba dasu harma na fisu kwarewa a harkar, haka muka cigaba da rayuwa kusan 5months ina cikin wannan sana'ar watarana kawai muka shiga gidan wani Alhaji mu kayi fashi, mutumin babban mutum ne kuma mai faɗa aji alokacin da suke ƙoƙarin kwashe masa kuɗaɗe ni kuma sai Allah ya haɗani da wata yarinya cikin gidan ganin yanda take ta kuka yasa naje wajenta ina kallon kyakkyawar fuskanta sosai take kuka tana jan numfashi banyi aune ba naji ta riƙo hannuna cikin nata gam rasa abinda zan yimata nayi domin bangane abinda take nufi ba ganin yanda take ta kokawa da numfashinta yasa kawai na ɗaukota da sauri na fito parlon dan har cikin raina na mance abinda ya kawo mu gidan miƙewa mahaifinta ya yi ganin yanda na rikota cikin rikicewa ya ce"dan Allah karka cutarda ita yarinya ce kuma batada cikakkiyar lafiya" kallonsa kawai nayi na ce" a kaita asibiti" kowa na wajen mamaki ya shiga barinma ƴan tawagata wanda suke ganin abun kamar rainin hankali, ban sake bi takan kowa ba nayi waje da'ita hakan yasa suka biyo ni abaya na shiga mota har sannan tana jikina kuma numfashin nata bai daidaita ba, bayan likitoci sun dubata suka yimata allura sai a sannan naji ashe asthmarta ce ta tashi.





Saida komai ya saisaita sannan Alhajin ya ce" dan Allah yaro kayi haƙuri kaji karka cutarmin da'ita ita kaɗai nake magani banida wata ƴar a duniya sai ita kuma muna matuƙar ƙaunarta" sanda naji ya yi wannan furucin sai duk jikina ya yi sanyi domin nasan zafin rabuwa da masoyi dan har sannan Nazeefa tana Zuciyata ban manta da'ita ba, numfasawa nayi na kalli Najeeb wanda yake ta kallona na ce" Najeeb mu rabu dasu please abar wannan harkar haka" da wani irin expression suka kalleni duka sai kuma ya ce" kaga malam karka raina mana hankali idan bazaka iya tafiyar nan ba to kana iya warewa ka kama gabanka amma mu babu gudu babu ja da baya okay" kallon Alhajin ya yi ya ce" dan Allah ku daina kodan gobenku ku zama mutanen kirki ni kuma nayi muku alƙawarin baku jari wanda zai isheku kuyi sana'a" murmushi kawai Najeeb yayi sannan ya ce" Allah ya sawwaka Alhaji mu munfi ƙarfin abunka kuma ko yanzu muma mun tara dayawa".




Babu yanda bai yi dasu ba amma kwata-kwata suka ƙi yarda musamman daya kasance duk basu yi karatu ba nikuwa nan take nace na daina kuma na fita daga cikinsu hakan yasa Alhaji Sulaiman ya ɗaukeni matsayin ɗansa wanda ya haifa, sanda yarinyar ta farka shine yake sanar dani cewa ita kaɗai ce ƴarsa wacce ya haifa mahaifiyarta ƴar ƙasar UK ce hakan yasa kana ganinsu zaka gane ba ƴan Nijeriya bane. Cikin ƙankanin lokaci muka saba da Raihana ta ɗaukeni tamkar yayanta kullum muna tare da'ita cikin wannan halin ne nake sanar da'ita abinda nakeson na zama na mawaƙi sosai Raihana ta yi murna dan kullum sai ta zaunar dani nayi mata waƙa aduk sanda na zauna zanyi mata waƙa sai na tuna da Nazeefa hakan yasa nake yawan rera waƙar


"_KI NA ZUCIYATA ban manta dake ba masoyiya_


Wani lokacin tana tambayata wace nake yiwa waƙar sai nake ce mata ƙawatace. Sanda ta sanar da Daddynta sai ya yi murna Mommy kuma ta ce akwai wani friend ɗinta mawaƙine zata haɗani dashi, cikin ƙanƙanin lokaci aka gama yimin komai na tafi UK inda naje na fara koyar waƙa Allah kuma ya taimakeni lokaci kaɗan na iya alokacin mun yi kamar shekara biyar da rabuwa da Nazeefa ina dawowa 9ja sai Daddy yazo mini da maganar auren Raihana tabbas bazance banason Raihana ba amma ba kamar Nazeefa fa ba kuma bazan iya cewa Daddy A'a ba hakan yasa na amince cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗaura mana aure da'ita zuwa lokacin kuma abubuwa sun fara sauyawa nafara samun Alkhairi da waƙar sai muka koma UK tare wanda anan ne nayi suna sosai har na kawo wannan matakin...............






Ajiyar zuciya Daddy ya sauke yana sake jinjina ikon Allah wato idan Ubangiji ya yi hukuncinsa babu wanda ya isa ya sauya masa Allah ya ƙaddara Hameed mai arziki ne kawai ɓoyewa ya yi wanda kuma shine abinda yasa ba'ason wulaƙanta mutum dan kana ganin kanada wani matsayi domin shima bakasan abinda Allah zai masa gobe ba, tasowa Daddy ya yi yazo har gabansa cikin sanyi murya ya ce" dan Allah Hameed ka yafemin kaji" murmushi Hameed ya yi ya ce" karka damu Daddy ya shige Allah ya yafe mana baki ɗaya" kasa tashi Daddy ya yi saida doctors ɗin suka fito hakan yasa duka suka tashi a tsorace suna kallonsa Fateeha ce tayi ƙarfin halin cewa "doctor ya jikin nata?" numfasawa ya yi ya ce"ku na iya shiga ku ganta" hawayene ya wankewa Fateeha fuska domin tunda taji ance haka tofa tabbas akwai abinda yake ba daidai ba Daddy kuwa kamar wanda aka angizashi haka ya shige ward ɗin yana haɗa hanya.





Kwance take tana sauke numfashi a hankali ɗakin ya yi shiru sai ƙarar computer wacce ke auna bugun zuciyarta ke aiki, dakyar Daddy ya ƙarasa gaban gadon yana zuwa ya kalleta samun kansa ya yi da kasa magana bakinsa sai rawa yake hannayenta ya kama ya sanya cikin nasa amma har sannan ya gagara furta komai, hannunta ɗaya ta ɗago tana murmushi ta shafa fuskarsa cikin sanyin murya wanda badaban babu hayaniya a ɗakinba bazai jiba ta ce" Daddyna ka daina kuka kaji ka yafemin ka yimin addu'a kaji" sake fashewa ya yi da kuka ba shi kaɗai ba harsu Mommy da Mama, Munnubiya, Fateeha, Uncle, da kuma Hameed wanda shi yama kasa kallonta, kwaɓe fuskarta ta yi ta ce" Daddy kace su daina kuka wai mene ne ya faru?" cikin gunjin kuka Munnubiya da Fateeha suka zo suka rungumeta suna kuka kamar ransu zai fita, tana jan numfashinta ta ce" nikam banason kukan nan ku tayani da addu'a please" sosai duka suke kuka wanda hakan itama ya sanyata kuka ta juya idanunta ya sauka cikin na Mommy wacce ta kasa ƙarasowa wajenta sai kuka take da hannu Nazeefa tayi mata alama da tazo, ta kowa Mommy tayi tana jan ƙafa tazo gabanta ta riƙe hannunta, tana jan numfashi ta ce"Mo..Mommy...Mommyna ki daina kuka kinji" shafa fuskarta ta yi ta ce"sannu Nazeefa Allah ya baki lafiya ya yi miki albarka ya ƙara miki imani da son mutane" murmushi Nazeefa ta yi ta ce" Ameen Mommyna dan Allah ki yafemin" girgiza mata kai tayi ta ce" na yafe miki har abada Nazeefa" lumshe idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka sakko mata. Dakyar ya ƙaraso wajenta ya tsaya yana kalllonta dan batasan ya zoba cikin dashasshiyar murya ya ce"Slimzy" da sauri Nazeefa ta juyo jin Muryar da ko a mafarki bazata taɓa mance taba, kallon-kallo suka shiga yiwa juna kowanne da abinda yake ji cikin ransa, wata nannauyar ajiyar zuciya suka sauke atare sai kuma ya kalleta murmushi yaga tayi masa wanda ya sake narkar masa da zuciya aduk lokacin da yaga Nazeefa tayi masa irin wannan murmushin tofah tabbas akwai abinda yake nufi cikin sanyin murya ya ce" sannu ya jikin naki?" lumshe idanunta tayi ta ce"I'm sorry singer please forgive me" girgiza mata kai ya yi ya ce" karki sake faɗar haka Nazeefa dan Allah" numfasawa ta yi ta ce" ka mata dani ko??" goge hawayen fuskarsa ya yi ya ce" *KI NA ZUCIYATA* ban manta dake ba Nazeefa kuma bazan taɓa mantawa dake ba" murmushi yaga tayi tana runtse idanunta ta ce" ka rera min waƙa Singer" murmushi ya yi ya ce" shikenan my Slimzy" harararsa ta yi ta ce" bana hanaka ba?" yanda tayi maganar ne ya sanya kowa na wajen yin murmushi ya riƙe kunnensa ya ce" I'm so sorry hajiyata" shafa kansa ta yi ta ce" good boy may god bless you" "Ameen Nazeefa"........





Haka suka ci-gaba da hirarsu suna dariya tamkar ma ba ita bace batada lafiyar ahaka har akayi magrib kasancewar ba'a kwana da mara lafiya a asibitin yasa duka suka tattara zasu tafi kwaɓe fuskarta ta yi ta ce" kuma duka tafiya zaku yi??" dariya Daddy ya yi ya ce"karki damu in sha Allah da asuba zan tawo" haɗe rai ta yi tana kallon Munnubiya ta ce" please ki kwana kinji" harararta Munnu ta yi ta ce" ke kam kin fiye shagwaɓa to sai gobe in Sha Allah zan tawo miki da chocolate" dariya ta yi ta ce" tom" kallon Mommy tai ta ɗaga musu hannu itama ta mayar mata tana murmushi. Saida suka fita sannan ta kalli Hameed wanda yake kallonta shima ya ce" kin girma Slimzy" harararsa ta yi ta ce" babu kyau gulma kai da Allah" dariya ya yi ya ce" toh sai gobe zan zo Allah ya ƙara lafiya" okay ta ce sannan ya juya Saida yaje bakin ƙofa sannan ta ce" singer" juyowa ya yi yana zuba hannayensa cikin wandonsa ya ce"yadai Slimzy?" sauke idanunta ƙasa ta yi sai kuma ta ce" ka manta dani ko??" girgiza mata kai ya yi ya ce



"*KI NA ZUCIYATA* ban manta dake ba"



Murmushi ta yi ta ce"shikenan sai da safe" murmushin shima ya mayar mata sannan ya fita......







Cikeda annashuwa suka shigo asibitin Munnubiya ta ce" nasan Nazeefa na cen tana jiran chocolate" murmushi Fateeha ta yi ta ce"aikam kinsan halinta" dariya Mama ta yi ta ce" ku cigaba da gulmarta kuna shiga zata ce babu kyau kuda Allah" tuntsirewa suka yi da dariya banda Mommy wacce haka kawai taji ta Moody, suna shiga suka tadda Hameed shima ya shigo sannan, gaisawa suka yi sannan suka shiga cikin ward ɗin, tsayawa suka yi ganin Doctors a tsaye suna tattaunawa Hameed ne ya ƙarasa wajensu suka gaisa sannan ya ce" Nazeefa fa?" numfasawa Doctor ya yi ya ce" sir I'm so sorry to say....." Bai barshi ya ƙarasa maganar ba ya ture shi ya shige ɗakin cikin zafin nama ganin haka yasa suma suka biyo bayansa.




Turussss suka tsaya ganin Hameed tsaye kanta yama kasa komai, Daddy ne ya ƙaraso yana kallon fuskarta wacce suka rufe da duvet, wata ƙara Daddy ya fasa sai gashi ƙasa timmmm sumamme.





Allah Sarki rayuwa haka kowa yasha kuka na mutuwar Nazeefa sunyi matuƙar girgiza musamman Daddy wnada ya zama kamar zararre haka ma Hameed ko abinci ya kasa ci musamman idan ya tuna hirarshi da'ita ta ƙarshe sai yaji inama shima ya mutu ya huta Allah sarki Nazeefa ta samu shaida gurin mutane masu tarin yawa wasu ma saida ta rasu sannan Family ɗinta suka san dasu ta rayu cikin biyayyar Allah da iyayenta ga kyauta abun hannunta bai rufe mata idanu ba kowa nata ne bata banbancewa tsakanin mai arziki da talaka tana cewa arziki da talauci duk na Allah ne kuma bawa bai isa ya yiwa kansa arxiƙi ba, har akayi bakwai ɗinta Hameed bai dawo dai-dai ba dan ko magana baya iya yi shi kaɗai yasan halinda yake ciki, haka ma Daddy wanda yake ganin kamar ma shine wanda ya kasheta bai taɓa zaton Nazeefa zata rasu ba ya ɗauka abinda ya faru ya rigada ya shige bai san yana matuƙar son yarinyarsa ba saida ta rasu haka ƴar uwarta Munnubiya kaɗan ya rage ta zubarda cikin jikinta wanda sannan ya kai watanni tara, hatta Raihana Saida taji mutuwar Nazeefa domin iya labarinta da take ji taji tana ƙaunarta Mommy ma haka ta shiga cikin halin damuwa har tsawon wani lokaci....





Ranar da akayi 40days ɗinta ranar Munnubiya ta haihu kuma cikin Sa'a ta haifi ƴa mace wacce ta ci sunan ƴar uwarta Nazeefa kuma haka suke kiranta, a duk lokacin da Daddy yaga little Nazeefa sai ya tuna da ƴarsa Nazeefa wani lokacin yana ɗaukan pic ɗin ta wanda su kayi tare lokacin data gama secondary school ya dinga kalla baya sanin sanda yake kuka da kuma sanda yake cewa



" *KI NA ZUCIYATA* ban manta dake ba Nazeefa"




*Four years later*



"Nazeefa!! Nazeefa"


Tsayawa ya yi yana riƙe ƙugu yana kallon ƴar ƙaramar yarinyar da bazata shige 4yrs ba ya ce" baki ji ko kina son wahalar da Daddy ko?" dariya yarinyar tayi tana kallonsa ta ce" Daddy inason muyi wasa sosai dakai" ɗaukanta ya yi ya ɗora kafaɗarsa ya ce" shikenan Babyn Daddy"



Sakkowa tayi daga kan royal bed ɗin tana buɗe drawer ɗinsa, wani hoto tagani ta ɗauko tana kallon hoton ta ce" Daddy wannan wace?" da sauri ya juyo yana kallonta sai kuma ya karɓi hoton yana kallo lokaci ɗaya yaji mood ɗinsa ya sauya cikin ƙaramar muryarta ta ce"Daddy ka faɗa min wacece?" kasa magana ya yi yana sake kallon hoton ya ce" *KI NA ZUCIYATA* Nazeefa"



Da sauri Nazeefa ta kalleshi ta ce" nima kana Zuciyata Daddyna" murmushi ya yi ya ɗauke ta ya ce"let's go karmu makara" okay ta ce tana jan beard ɗinsa.






Babban gidane wanda kana gani kasan da kuɗi aka ginasa anyi masa ginin part-part kana gani kasan ba mutu ɗaya bane yake rayuwa aciki, murmushi Daddy ya yi yana sake karanta sunan dake saman ginin inda aka saka


*Nazeefa orphange*


Kallon Hameed ya yi amma ya kasa magana kawai ya rungumeshi yana kuka ya ce" Allah ya biya ka Hameed" murmushi ya yi ya ce" haba Daddy karka manta nayi ne saboda Nazeefa kome nayiwa Nazeefa ban faɗi ba Daddy" murmushi Daddy ya yi yana kallon little Nazeefa ya ce"kin girma sosai" dariya ta yi ta ce" kaima haka granny" tuntsirewa suka yi da dariya dukansu, ɗaya Nazeefar ta kalli Mommynta Munnubiya ta ce" Mami na daina kula granny tunda shima baya kula ni" dariya Daddy ya yi yazo ya ɗauketa saida ya juyata sama sannan ya ce" I'm sorry my Nazeefa ni Ina kulaki" dariya ta yi ta ce" nima ina sonka granny" sauketa ya yi ta tafi wajen Nazeefar Hameed tana murmushi ta ce


"Namesake ya kike?"


"Ina lafiya"


Yanda sukayi maganar yasa duka Family ɗin suka kallesu Mommy ta ce" Masha Allah"


Haɗa baki sukai duka wajen faɗin


"Alhamdulillah".



*Alhamdulillah!! Alhamdulillah Tammat bi hamdul lah, Allah nagode maka anan zan ɗiga aya cikin littafina mai sunan KI NA ZUCIYATA Allah ka sanya ya zama silar shiryuwar wani/wata Allah ka yaye mana masifun da suke damun mu*



*Ameena I Ibrahim*


*Nanameera ce*



*I dedicated this book to yhu my partner Riamcool Star of the Squad Ina matuƙar ƙaunarta ƙawata Allah ya barmu tare Ameen*