16
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 16```
________Surajo, Ghali,da Abdulnaseer,ƴaƴan Mallam Abdullahi ne ɗan asalin ƙauyen Bari dake ƙarƙashin jahar Kaduna Mahaifiyarsu Goggo A'isha baffulatana ce ƴar asalin rugar Fulani dake ƙaramar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.
Yawon neman kuÉ—i Abdullahi da iyayenshi sukeyi gari-gari, har Allah ya haÉ—a Abotar su da Mahaifan A'isha wanda suma yawon neman kuÉ—i ne ya kawo su garin Kano.Aminta da yardar dake tsakaninsu da kuma fatan É—orewar zumunci tsakanin su ne yasa suka haÉ—a Abdullahi da A'isha.
Abdullahi shi kaɗai iyayenshi su ka haifa saɓanin A'isha dake da ƙanne Mata biyu da Namiji ɗaya.
Abdullahi ya yi gwagwarmayar Rayuwa wajen ganin ya tara dukiya amma Ubangiji bai nufa ba.Wahala Rayuwa da ƙaruwar gwagwarmaya yasa Mahaifan su komawa tushen su amma Abdullahi na maƙale a Birni shi da Matarshi A'isha da dukka ƴaƴan su.
Har tsufa ya fara cimma Abdullahi burinshi bai cika ba sai akan ƙaramin ɗan shi Abdulnaseer.
Duk da ciki É—aya Ghali, da Surajo da Abdulnaseer suka fito akwai banbanci mai tazara a halayyar su,da tsananin son kai.
Hassadar kuɗin da Abdulnaseer yake samu ta ko ina ne ya fi damun zuƙatan su tun lokacin ƙuruciya har girman su sai dai hakan baiyi tasirin raba zumutar su ko su yi ƙoƙarin cutar da shi ba.
Ghali ne ya farayin Aure kafin Surajo duk da shine Babban su.
Sai da Matar Ghali ta haifi yara biyu dukka Maza sannan Matar Sirajo ta haifi FAISAL bayannan Faisal na da ƙanne Mata biyu Matar Ghali ma bayannan ta ƙara haifan Mata biyu a lokacin MUBEENA ce ƙarama.
Har lokacin Abdulnaseer baya zancen aure sai neman kuɗin dayasa agaba, daƙyar Mahaifinshi ya tilasta mai ya bayyana Fahima amatsayin wacce zai aura, ƴar babban wani Attajiri ne ɗan kasuwa mazaunin ƙasar Birtaniya da iyalanshi.
Har bayan shekara biyu Fahima bata samu haihu ba. Batare da yin shawara da kowa ba saboda son farantawa Fahima rai,ya auri kyakkyawar matashiyar da take mata hidima kan idan ta haihu zai saketa ta riƙe abinda ta haifa. batare da sanin shirin su ba Zainabu ta amince.
Ranar da labari yaje kunnen Mahaifinshi kamar zai rufesu da duka shida Fahima,ya kuma kafa mishi sharaÉ—in ko bayan ranshi bai yarda ya Saki Zainabu ba.
Zaman Abdulnaseer jefi-jefi ne aƙasarshi ta haihuwa kuma duk inda zai je Fahima na biye da shi,makirci da mugun ƙudirinta kan Zainabu yasa ta bashi shawarar mai zai hana suna tafiya tare saboda tabbatar da adalci atsakanin su.baya musawa zancenta don haka atake ya amince.
Zainabu ta sha baƙar azaba a hannun Fahima wanda ya haddasa babban rigima tsakaninta da Abdulnaseer domin duk yanda yaso kaucewa kar ya kamu da son Zainabu hakan bai samu ba.
Ganin bazata canza ƙudurinta da kuma son cikar burinta na ganin bayan Zainabu ba yasa ya tattara komai na Zainabu ya dawo da ita wajen Iyayenshi.lokacin Zainab na da shigar cikin wata ukun da babu wanda ya san da shi.
Duk da sauyin Rayuwar da Mallam Abdullahi ya samu bai bar tsohuwar Unguwar su ba( Unguwar su Innar Halime).
Saboda son faranta ran Mahaifanshi ya siye ragowar filayen dake layin hakama gidajen ya yi musu farashi mai darajar da zai siya musu wani gidan har da ƙari.Dalilin komawar dukka ƴan uwanshi gidan kenan da ragowar makusantar shi ma su girman kan tsiya.da rashin son mu'amalantar mutane har sunfi Abdulnaseer ɗagawa da tinƙaho da gudun talaka.
Ranar da Abdulnaseer da Fahima suka dira gidan daya ƙuntata ran fahima saboda dukiyar da Mijinta ya kashe da ƴan uwanshi da suka cika gidan da ƙaton cikin da taga Zainabu da shi,Washe gari Zainabu ta haifi santalelen ɗanta kyakkyawan gaske.
Babu wanda bai yi farin cikin samun ƙaruwar da Abdulnaseer ya samu ba sai tsirarun mutane ciki har da Fahima, adaren ranar Allah Ya karɓi ran Zainabu.Cikin kuka da tsananin tausayi da ya lulluɓe zuciyar KAKA kamar yanda suke kiran Mallam Abdullahi ya yi wa jaririn huɗuba da MAYSARAH.