MAI KWAÆŠAYI

17

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 17```


________Mutuwar Zainab ya taÉ“a zuÆ™atan rabi da kwatan ahalin Abdulnaseer, saboda suna da yaÆ™inin Zainabu ce zata kawo sauyin da za su samu damar morar arziÆ™in É—an uwan su yanda suke so amma mutuwar Zainabu ya rusa waccan yaÆ™inin na su.


Goggo A'isha ita take kula da Maysarah da amintacciyar hadimar da Abdulnaseer ya samo.tun Maysarah na shekara ɗaya dangin Zainabu ma su adalci suka damƙa kuɗin dukka gonakin Zainabu da suka siyar na kuɗi ma su nauyi a hannun Kaka.

Batun soyayyar da Maysarah yake samu a kowani ɓangare na gidan ɓata baki ne.

Yana shekara biyar Fahima tasa Abdulnaseer ya kawo ma ta shi, da farko ya nuna ƙin amincewar shi amma ganin yanda take kuka dayiwa kanta gori ya sa shi ɗauko Maysarah.


Ta raine shi cikin azaba da tsananin son zuciya, batare da kowa ya lura ba, saboda tsananin makircinta. Anan Maysarah ya yi primary school batare da tabari anƙara komawa da shi ba koda lokacin hutune.

Ranar da KAKA ya birkice mu su kan sam bai yarda da rayuwar Maysarah tare da Fahima ba kan wani dalilinta zata hanashi zuwa ko da hutune.

Duk son ya faranta ran Fahima abayan na Mahaifanshi ya ke don haka dole ya tattara su suka dawo gida.


Maysarah ya da banbanci kalar fata da mutanen gidan domin baÆ™aÆ™e cikin su tsirari ne saÉ“anin shi dayake da sirkin kalar fata biyu, Abdulnaseer fari ne tas kyakkyawa,Zainabu kuma baÆ™ace itama mai kyau sai kyawunshi da kalar fatar Maysarah yafi nasu kyau da birgewa, hakama kyawun Halittar shi daban da na ragowar yaran gidan saboda É“angarori biyun daya kwaso, rayuwar kaÉ—aici da azabar dayake sha awajen Fahima ya sa zuciyarshi take a Æ™eÆ™ashe duk da yaro ne Æ™arami amma yasan shi bashi da Uwa duk da babu wanda ya taÉ“a gayamai.


Cikin fushi da faÉ—a sosai Kaka yake yiwa Abdulnaseer magana, duk da Fahima na wajen a zaune. Saboda rashin walwalar dake tare da Maysarah ga shi atakure alamun bayajin daÉ—in Rayuwar da yakeyi sa'o'in shi duk sun fi shi girma a waccan lokacin.


Ko da zasu koma mirje idanuwanshi Kaka ya yi kan dole su tafi tare da shi.


Wannan dalilin ne ya farfaÉ—o da rayuwar Maysarah kasantuwar Kakannin shi na rayuwa a kusa da shi cikin tsananin so da kulawa.


A hankali a hankali yayyan Abdulnaseer Uncle Suraj da Uncle Ghali suma suka tattara da Iyalansu suka dawo Æ™asa É—aya da Abdulnaseer,Fahima kamar ta haÉ—iyi zuciya da Mutu saboda Æ™ara kafuwar familyn awaje É—aya.sai waccan gidan ya zamana na dangin Abdulnaseer ta É“angaren Uwa da Uba ne kawai suke rayuwar aciki, dayawan Maza da Matan da ke rayuwa agidan masu alfahari ne da jin sunfi kowa, kwaÉ—ayi da kyawun gidan ya sa sukayi bake-bake aciki ba don Unguwar yayi mu su ba, duk kusancin ka da Kaka sai kanama da hanya zaka samu muhalli agidan,ga wanda bai san asalin tarihin gidan ba bazai taÉ“a sanin ina mutanen gidan suka dosa ba, saboda asalin masu gidan sukan share shekara biyar ba su waiwayi gidan ba.babu kuma abinda Abdulnaseer baya ajjiye mu su na buÆ™atar rayuwa da É—aukar nauyin karatun su da motar hawa kuma da zarar sun kammala karatu da aikin su a hannu.


Shekarun Maysarah 18 Allah yayiwa Kaka rasuwa,babu wanda ya kai Maysarah jin Mutuwar saboda ya fi kowa son shi da ƙaunar shi.

Gaba ɗaya suka tattauro suka yada zango a asalin garin Mahaifin su Bari cikin tafkaken gidan da Abdulnaseer ya jima da ginawa nan ma dangin Mahaifinshi ne shaƙe agidan har da wasu dangin Mahaifiyarshi.

A lokacin da rigimar rabon gado ya tashi tsakanin su Maysarah dake da shekaru 18 ne ya siye gidan Unguwar su Halime da kuÉ—in gadon Mahaifiyarshi da Kaka yasa ake juyamai,kuma yace kowa ya cigaba da rayuwa aciki gidan kamar yanda burin Kakan shi yake lokacin da yana raye,Fahima ce kawai lamarin bai yiwa daÉ—i ba.


Zalama da hangowa kai cigaban zamanshi a ƙasar shi yasa Uncle Suraj tattarawa suka dawo gidan da zama shida iyalanshi duk da a baya yafi kowa zaƙewa kan asiyar da gidan,a can yabar Faisal dakuma umartar shi da ya riƙi Maysarah amatsayin Aboki kar ya yi tunanin ratar shekarun dake tsakanin su saboda Maysarah shine gundarin linzamin samun arziƙin su.


Uncle Suraj da Uncle Ghali sun samu cigaba da tara dukiya amma ba irin wanda suke muradi ba na kamo Abdulnaseer ko wuce shi a arziƙi ba.


Har Mayrasah yakai shekaru 19 ko ɓari Fahima bata ɓatayin ba wannan dalilin yasa ta yin adopting ɗin yarinya agidan Marayu saboda ta haɗata aurenta da Maysarah ta samu damar juya dukiyar shi yanda ta tsara, dama Kaka ne mai taka ma ta birki kuma Allah Ya karɓi Abunshi Goggo A'isha kuma bata da son haniya tun bayan rasuwar Mijinta tana zaune abinta a ƙauye cikin kwanciyar hankali.


Tunanin Fahima da na Uncle Suraj da Uncle Ghali duk É—ayane su ma burin su Maysarah ya gama Karatun Makarantar Sojin da zai shiga su haÉ—ashi aure da Æ´aÆ´an su ma su tasowa.


Zuwan Maysarah na farko tun bayan barinshi gidan yanada shekara biyar motocin gidan su ka buge Halime a lokacin bai fi ya girmeta da shekaru uku ba.


Ba don ran kowannen su yasoba suka bari akayi auren Mubeena da Faisal saboda Uncle Suraj na burin Faisal ya auri ƴar shararren mai kuɗin da zai kawowa arziƙin su cigaba shima Uncle Ghali na burin Mubeena ta auri wanda zai kawowa arziƙin su cigaba, wannan dalilin ya sa bayan gama biki Uncle Ghali ya tattara ragowar ƴaƴanshi Mata daya turo su zauna wajen Uncle Suraj saboda tarbiyyar su har Mubeena ta samu damar soyayya da Faisal suka bar ƙasar.don da Mubeena tana gabanshi ne wallahi bazai barta tayi soyayya da Faisal ba "dudu har wani arziki Faisal ya tara Abuja fa ya dawo da aiki sai girman kai da ƙafafa da arziƙin da bana na shi ba",Uncle Ghali ya faɗa azuciyarshi yana jan ƙaramin tsaki.



Da MAI KWAƊAYI paid book ne amma In Sha Allah zan yi ƙoƙari na yi shi free.dafatan mun wayi gari lafiya