MAI KWAƊAYI

18

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 18```


_______Har jirgin su Uncle Ghali ya sauka bai daina jan tsakin takaicin auren ƴar shi da Faisal ba.Ghali mutum ne mai faran-faran a fuska kuma duk matakin daya taka na arziƙi baya sauya abokanai, sai dai idan kana so kaga ainihin halayyar shi ka tambaye shi kuɗi ko ka nuna kana son ɗaya daga cikin ƴaƴanshi, kana talaka ko ya kama ma su yin aiki a ƙarƙashin na ƙoƙarin ƙulla alaƙa da ƴaƴan shi, anan ne zaka gane fara'arshi ta iya fuskace sam bayason ƙulla alaƙar jini ko na mutunci tsakanin ƴaƴan shi da talaka, kan haka ya horar da Matar shi da ƴaƴanshi sai Mubeena da ta fita zakka duk da itama abaya kusan halayyarta kenan haɗuwarta da Salmanu ne ya sauya komai.

Saɓanin Uncle Suraj bashi da fara'a sam kuma duk matakin da zai taka to haka zai sauya Abokanan mu'amalarshi, amma ba shi da rowa sai dai ƙiyayyarshi ga talaka a bayyane yake kuma ya tsani Abdulnaseer ya yi kyauta batare da ya biyo ta hannunshi ba, shima duk kusan ɗabi'un daya ɗora Iyalanshi akai kenan sai Faisal da soyayya ya sauya.

Abdulnaseer kuma ba'a gane ina ya dosa saboda ba shi lokacin so balle ƙiyayya, ko sa ido akan abunda waninshi ya mallaka, shi dai kawai neman kuɗin shi ne agabanshi hakama Fahima da Maysarah suma kowanne da kalar halayyarshi.




Shigowar Mubeena Mota tana sauke numfashin gajiya ne ya dawo da Faisal hayyacin shi.

"Maiyake damunka haka"?

Ta faɗa ta shafa gefen fuskarshi.

"Babu kawai nagaji ne ina buƙatar hutu" ya faɗa yana sumbatar hannunta.

"Okay muɗan jira Salmanu ya ƙaraso Please"Bai ce mata komai ba sai ƙara gyara zamanshi da yayi.


Sai da Mubeena ta tabbatar Salmanu ya iso sannan suka tafi ranta fal zullumin abinda yake damun Mijinta saboda ta kasa yarda da gajiya ce zatasa ya yi yaushi haka.


Salmanu duk ya rame ya yi zuru-zuru kamar wanda ya zo daga gudun hijira,baƙaramin tashi hankalinshi ya yi ba lokacin da yaga condition ɗin Halime.


Ya hana a bari kowa ya shigo ganinta har Baba Isiyaku da baƙin ciki ya tilasta mishi komawa gida.


★washe gari da safe Innar Halime ta iso ita da Indo cikin tashin hankali.

Masifa takeyi kamar zata taune harshenta, kan yanda Halime ta koma saboda tabbacin da ta samu aikin Baba Isiyaku ne duk dan kada Halime taje Makaranta.


Ko da aka sallami Halime rantsewa Inna ta yi Birni zata tafi da ita har sai ta haihu tunda Mijinta ya yarje ma ta,Baba Isiyaku bakin shi har rawa yakeyi wajen tsawatar wa Salmanu kan karya kuskura ya bari Inna ta tafi da Halime,sunkuyar da kanshi Salmanu ya yi batare da ya tanka ba domin yasan hakan ne kaɗai mafita.


Baba Isiyaku ya na ji ya na gani su Halime suka hau Motar da Inna ta samo domin tasan bazai bar Salmanu ya kai su ba.


Kuka ya sa kamar ƙaramin yaro yana kife Salmanu da marin takaici,"anya ba abinda ya yi wa Salmanu ne ke neman mayar mi shi da ɗa soko ba"tuna hakan ya sa ya ƙara rushewa da kuka.

Ba zai haƙuraba ya zame mishi dole ya nemo addireshin inda Innar Halime ta ke aure saboda bibiyar abinda Halime zata haifa.


Bayan ya huce da kanshi ya sa Salmanu ya bi bayan su saboda yana so Salmanun ya ƙara yarda da shi.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Tun saukar su Halime matan gidan su ka fara gulma a tsakanin su da ganin wautar Baba Shehu, kan wani dalili Halime zata dawo gidan da zama ai tanada dangin Uba.

Su ma Mazajen su hawa kan zugar Matan su sukayi suka zauna tare da kafa hujjar bai dace Halime tana kwana ɗaki ɗaya da Babangida ba,cikin kunya da takaicin saɓa alƙawarin da ya yi wa Innar Halime Baba Shehu ya je mata da zancen...✍🏻