MAI KWAƊAYI

19

by @nafisatusasaal01

19


________Har Baba Shehu ya gama bayanin shi bata tofa kalma ko ɗaya ba sai kaɗawar da idanuwanta sukayi, takaicin Baba Shehun na kamata a karon farko domin bata taɓajin haushin sauƙin halinshi ba sai ranar.

★Kamar yanda ta tsara da Asubahi ta tattara dukka kayan su amma banda na Babangida suka nufi tasha ko Baba Shehu bata yiwa sallama ba saboda tsabar takaici Babangida ta bawa sallahun ya sanar da shi ta wuce ƙauye.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Duk yanda ta so Faisal ya faɗa ma ta ainihin damuwarshi ƙi yayi sai tambayar ya daya jefo mata na ya ya akayi Halime ta samu wannan nakasun? Ajiyar Zuciya ta sauke saboda gano bakin zaren abunda yake damunshi sai dai bata daina mamakin maiyasa ya damu da lamarin haka ba.tun daga farko ta bashi labari har zuwa accident ɗin da ya faru da ita.

Shiru ya yi gumi na tsatsafo mishi ta goshi ihun da ya yi wa driver da izgilanci da ya yi wa Halime da uban maƙudan kuɗin daya ƙarbe a hannun Maysarah da sunan magani na dawo mai cikin kai.

Hannun shi Mubeena ta riƙo cikin shagwaɓe fuskarta ta kira sunanshi haɗe da ɗan matsa hannunshi"Faisal" shiru bai amsa ba "menene matsalan bantaɓa ganin ka damu haka ba".

"Mubeena driver na ne ya buge Halime bisa Umarnin ƙara gudu da na ba shi,shi ne kawai abinda ya ke damuna"ya faɗa yana haɗiye ainihin abinda ya ke damunshi,ba a irin wannan ya saba cin miliyoyin kuɗin Maysarah ba amma wannan karon Allah ya jarabbeshi da maƙalewar abun daya aikatawa Halime a zuciyarshi tun bayan da ya yi ido biyu da ita saboda tsabar kuɗin da ya damfari Maysarah akanta ne yasa fuskarta ke maƙale a zuciyarshi tun bayan faruwar lamarin.

"How comes? Halime? anya Beb bakayi kuskuren tunani ba?amma bari na taɓa Salman a waya"

Ta faɗa tana miƙewa domin samun damar yin waya da shi.


Suman kanshi ya hargitsa ya na taune leɓanshi, da ya yi amfani da kuɗin da ya ƙarɓa a hannun Maysarah da yanzu Halime ba irin wannan rayuwar takeyi ba,amma tayaya zai gyara kuskurenshi?

Dai-dai lokacin Mubeena ta fito fuskarta itama ɗauke da damuwa.

"Faisal dagaske ne Halime ce amma Please kar ka wani damu a hakan ma ai munyi ƙoƙari ko?"ta faɗa tana ɗage girarta. Kai kawai ya gyaɗa ma ta ya miƙewa zuwa sashen shi


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Tsakanin Halime da Salmanu sai suka koma abin tausayi saboda har lokacin Baba Isiyaku bai daina ƴan biye-biyen shi akan Salmanu ya daina ɓarnar kuɗinshi kan Halime ba, domin kullum ya tambayi Salmanun kuɗi kamar yanda ya saba sai Salmanun ya sakomai uzurin bashi da kuɗi saboda cimar Halime da yawan kashe kuɗin Asibiti. Damuwar hakan ya sa Salmanu fara fita hayyacinshi ga zaryar hanya dayake yawan yi,Baba Isiyaku bai yarda Salmanu ya je ƙauyen su Innar Halime dubata ba bai zo na su ƙauyen ba. Itama Halime ta zama shiru-shiru sai yawa kuka wa su lokutan sai tacewa Innarta ta na yawan mafarki ƙasa ya lulluɓe idanuwanta wasu lokutan kuma tace mutane na yin gini asaman jikinta, duk lokacin da ta yi irin wannan surutan haka Inna zata yini tana kuka.


Safe rana dare Halime bata da aiki sai rubuta a ƙaton littafin da ta sa Salmanu ya siyo mata tun Inna na mita har ta haƙura saboda duk ranar da ta fara yi mata mita sai tace mata saƙon ƴarta ne Halime haka shima Salmanu duk ranar dayazo ya sameta tanayi idan ya karɓe sai ta sanya mishi kukan ta na cewa yabari ta rubutawa Halimenta komai da komai, cikin ƙwallar da ya ke tafiya da shi kullum yake ce mata"ohh kice zan haɗa Halime biyu kenan"maimakon ta bashi amsa sai ta sa kuka haɗe da girgiza kanta,haka shi da Inna zasuyita lallashinta,bayan kowannen su ya keɓe sai ya sha kukan tausayinta.



Ranar da Salmanu ya yi zuwan ƙarshe tanajin jiki matuƙa, ƙura ma ta ido ya yi kanshi na ƙara ɗaukar zafi kamar daga sama ya ji muryarta"nasan kullum idan ka kalle ni bakajin daɗi da farin ciki kamar ko wani magidanci saboda ni mai ido ɗaya ce kuma bani da ƙafafuwa"ta faɗa tana ƙoƙarin zama.

"Wa ya ce miki haka Halime ko ya ya kike inasonki a haka karka ƙara faɗar haka kinji" da ire-iren waɗannan hirarrakin mai daɗi tsakanin su sukayi sallama.


Har shuɗewar wata huɗu Mubeena bata ƙara waiwayar su ba kuma ko Salmanu bata ƙara kira a waya ba, da farko idan Salmanu ya kira shiga ne bayayi daga ƙarshe sai ya gane Blocking ɗin shi Mubeena ta yi.


Damuwa da rashin nutsuwar zuci da Salmanu ya samu kanshi aciki ne ya sa ya yi gagarumin kwaɓa a aikin shi hakan ya sa nan take aka sallame shi daga aiki, da wannan damuwar ya tuƙo motarsa zuwa ƙauyen su Halime sai dai kafin ya shiga ya samu mummunan hatsari....✍🏻