LUBE (BODARA)

5

by @zinariya0102


 ______Cefanan da ya aiko Mata da shi ta gyara hakama kajin da zata yi amfani da su,stew ta shirya masa mai kyau wacce zai kwana biyu da ita, tayi masa cake,samota da donut, sosai Humaira take gatanta mijin nata.Da son faranta masa.

Tun safe bai shigo gidan ba sai da rana ta take domin zaga gari ya yi shida Ɗanliti, fitowarta kenan daga wanka ta kammala aikinta, ɗaure take da short towel wanda da kaɗan ya rufe mata duwaiwai, hakama saman breast ɗinta a waje yake santala-santalan cinyoyinta ya bi da kallo, ta ce" ni nasan dole ka dawo irin wannan rana da ake yi, kana can cikin dan cage kamar ba mutum ba" Zayyad da idanunsa sukafara sauyawa har wani ruwa suke tarawa na jaraba, ya ce" Dan Allah Humaira ki fasa tafiyar nan,wallahi zan shiga wani hali idan baki kusa dani" kutumar tabdijan ai kuwa Abban Insaaf sai dai kayi haƙuri ka koyi juriya, na tabbata Allah zai sa maka dangana idan ba ka gani na" Zayyad ya ce "kinfi kowa sanin sha'awa halitta ta ce Humaira,ko mahaifiyata ba ta sanni kamar yanda kika sanni ba" ƙunƙuni ta hau yi idan na tafi ka haƙura, ta faɗa a ranta tana kammala alwalar da ta ke ɗaurawa ta nufi ɗaki,duk tsaurin Zayyad da jarumtarsa akan mace ba sa tasiri, ɗakin ya bita.

Zaune take tana murzawa skin ɗinta lotion mai sanyin ƙamshi ta haɗe rai.


Kallonta kawai yake tamkar ya haɗiyeta sonta da shaawarta na ƙara samun muhalli a zuciyarsa. Affan na kan bed yana ta wasa shi kaɗai yana gwarancinsa.

Ɗakin ya bari ya shiga toilet ɗan watsa ruwa, wanka ya yi ya shigo ɗakin ya buɗe trolly bag ɗinsa ya ɗauko jallabiyya brown ya zura, babu wanda ya ke kula wani cikinsu, kwanciya ya yi dan ya ɗan matse ya ji ta ce" ba dai bacci zakayi a zafin nan ba?" banza ya yi da ita ya rufe idonsa.


Baki ta taɓe ta ci gaba da shirya kayanta da na ɗanta, so yake ya sami sauƙi yasa ya kwanta,amma tamkar tsumi shaawa ce ke ƙara bujiro masa, "ke never never for how long zan ɗauka ina lallaɓaki okay ni kenan bansan ciwon kaina ba da nake miki duk abinda kike da buƙata ko, ke kin kasa ɗaukar lalurata impact ma guje min za ki yi, to ki sani muddin kika tafi ki ka barni ki kuka da kanki"


"Na rantse da Allah Babu abinda zai hanani tafiya gobe" ta Faɗa tana takaicin irin sakayyar da Zayyad yake mata na hidimar da take ta faman yi da shi, ya ce" okay mu zuba mu ga ni" ya fice ransa a ɓace. "mtsww jarababbe ba shi da aikinyi sai abu ɗaya" ta ƙarasa da hararar hanyar da ya yi.

Ko lunch bai dawo ci ba, ya yi zamansa a shago, maƙota Humaira ta shishiga tana yi musu sallama, gidan Baba Delu ta yada zango. 

"Baba ni fa gobe zan koma garinmu?" Baba Delu da take kaɗin lagwani sai ta tsaya ta na sakin zaren ta ce" ta shi za ku yi haba ƴar nan wani abu akayi muku?" dariya Humaira ta yi ta ce"a'a wallahi ko kaɗan ai shi ya na nan, ni ce dai zan koma gida" Baba Delu ta ce" toh wata sabuwa me ya sa ke kuwa zaki tafi bayan an saba" ta ce " zaman nan ɗin ne dai ya ƙare amma ai baa rabu ba zan dinga zuwa" Baba Delu ta ce" Allah sarki za mu yi kewa ba kaɗan ba.


"Baba,Babaa, ga shi can ana faɗa da Lube an....Da sauri Delu ta miƙe tsaye ta na faɗin" kai ni ƴasu bari in zo mu je" Humaira ta ce" Allah ya shiryi Lube, a ina ne mu je ni in tawo da ita, Baba bari ni inje" a'a a'a ke ƴar nan baki san yaran garin nan ba, ba su da kunya kai mu je" ta yi gaba Humaira ta ce "Allah ya sauwaƙe yarinya kamar Karya, daga faɗa sai hauka" da haka ta koma gidanta.


Ke!ke!!ke cika ta na ce" ce war Inna Maimuna ta na isowa filin kaci uwaka wanda babu wani babba sai yara ana ta zuga Lube akan ta caskala Wattini, duk da kuka yarinyar take amma ta ƙi rabuwa, Lube na faɗin" ku barta alkur'an sai na sauya miki halitta" 


Cakumo Lube Inna ta yi ta ɗauke ta da Mari tasss ka ke ji, wani irin ihu Lube ta ƙwala. "Wayyo idona, na shiga uku idona" tsalle take tana juyi a wajen, Inna sai sababi take" hegiya irin masifa da jaraba ke kaɗai kin buwayi yara a gari ba ƴar mayya ba ko ke ce maitar yau sai naga waye ya tsaya miki a garin nan ni nan da kike gani na ci dubu sai ceto alkur'an".


Baba Delu ce ta ƙaraso ganin su Mara riƙe da Lube wacce ta kasa tsayuwa tana ta uban ihun idonta ya tsiyaye.

Inna na hango Delu ta ja hannun ƴarta suka bar wajen, "wa ye ya dake ta?" ce war Delu.

Take kowa ya hau faɗin Innar Wattini ce ta fasa mata ido, "Ido!!? ce war Delu tana dafe ƙirji!!! lalube Lube ta hau yi tana faɗin" Baba ta kashe min ido na makance" cikin kuka na tashin hankali, hankalin Baba Delu ya yi mugun tashi, ta ce " ya subuhanallahi kwarankwatsa bazan yarda ba, watan tara makafi a Gulu ya kama ko zanyi yawo tsirara sai naga bayan ahalinki Maimuna" ta ce" Ku je gidan Gandu ku kira min Sa'idu da Rabe" cikin tashin hankali ta ke magana.


Lube da ko zafin marin ya baje, ba ta ji amma ta ɗaga kai sama tana ware hannu ta na lalube ta riƙe Baba Delu gam. 


Zayyad da Ɗanliti ne suka biyo hanyar ganin yanda aka cika a wajen suka ƙarasa.


Hango Lube ya yi a baje a ƙasa kai a sama tana ta faɗin " bana gani Baba sun makantar da ni" da hanzari ya kutsa ciki yana faɗin "lafiya Baba me ke farawa?" Baba Delu da take ta matse kwallah ta ce" mahassada sun kassara min Lube, an kashe mata idanu" ta kunce gefen zani ta hau share kwallah. 

Lanliti ya ce" innalillahi......Su waye, ba ri na je na kira ƴan doka" ya juya cikin zafin nama Zayyad ya riƙo hannunsa ya ce" waye ya ce ta makance?" Baba Delu ta ce" ga shi nan kana gani bata gani" Zayyad ya kalli Lube idanunta a rufe suke, ya ce" me ya faru?" take yara suka hau faɗar abinda ya faru.

Jin marinta akayi ya sa ya saki murmushi yana faɗin " Baba ki daina wannan kukan, ai likita ne kawai zai ce muku haka ku yarda" Lube ta kuma ƙara sauti " wayyo Allah na shiga uku, bana gani Baba, Inna ta makantar min da idanu na" Baba Delu ta ce" alkur'an shari'a daga nan har yaumu ta nannaɗe sai an makantar da Maimuna da wannan soyayyiyar ƴarta ta, shegiya me ƙirjin Babe" ta kuma sa kuka.


Zayyad ya ce" ki yi haƙuri Baba kafin yaumu tanannaɗe ɗin ta zo, ke malama ki rufe mana baki, ke ko kunya bakya ji kin tarawa kanki mutane, a ina kika makance, za ki tashi ko sai na tashe ki da kaina!

Lube ta saki ta hau lalube tana faɗin" wayyo Babana kazo za a kashe ni!!!" Abin ne ya ba shi dariya ganin yanda ƙaramar yarinya ta iya pretending.

"Kai Zayyanu banason rashin Imani, wani ya ce ka zo ko kuwa angayamaka muna zuwa asibiti, ungo nan kai da likitan,alkur'an koto zan kai" Ƴan gidan Gandu ne zuga guda suka tawo har su Manu,jin an tsiyayarwa da Lube ido yasa matasan fitowa a fusace.


Zayyad ya dafe kai ya ce "wannan yarinyar shaiɗaniya ce shikenan ta tada fitina" jin muryar su Baba Rabe,hankali tashe yasa Lube shiga laluben inda suke "Babaaaaa..........





_Yawan comments yawan typing