MAI KWAƊAYI

20

by @nafisatusasaal01

```Page 20```


________Baba Isiyaku na zaune a ƴar farfajiyar tsakar gidanshi, ya na girgiza ƙafa zuciyarshi cike fal da saƙe-saƙe kala-kala da wassafa yanda zai hana Salmanu kashe ko sisin shi wajen hidimar suna.

Bankowa ƙofar da akayi batare da sallama ba ne yasa shi zabura cikin kumfar baki da masifar wani mara tarbiyyar ne ya bankomishi ƙofa haka salon ya ƙarya m..,maganar shi ce ta maƙale ganin Isihu ɗan gidan ƙaramin ƙanin shi na kuka shaɓe-shaɓe haɗe da kiran sunan Salmanu.

"Kai Isihu banson shashanci maiyasamu Salmanun? yana ina?"

Ya faɗa cikin ɗimauta da gushewar hayyaci.

"Baba wallahi ga Salmanu can a motar gawa"

Iyakacin abinda Baba Isiyaku yaji kenan ya zube awajen.

Da gudu Isihu ya nufi iyayenshi dake ƙoƙarin shigo da gawar Salmanu cikin gida a lulluɓe.



INNA


Robar ɗibar ruwan hannunta ne ya suɓuce ya faɗi ƙasa, ƙirjinta ya buga da ƙarfi,idanuwanta bushewa sukayi saɓanin Indo dake kuku kamar zata haɗiyi zuciyarta,gefe Inna ta jata haɗe da ɗora hannunta akan bakin Indo.

"Ta ya ya zakicemin Salmanu ya mutu Indo? Nakasa yarda waye ya gayamiki wannan labarin Indo?" Inna ta faɗa a hankali muryarta na rawa.

"Wallahi Yaaya dagaske na ke wai hatsari ya yi"

Sai a lokacin wani irin kuka ya tahowa Inna,ɗago kan da zata yi sai taga a saitin window su ke kuma Halime zata iya jiyo su hannun Indo ta ƙara ja suka dawo tsakar gida.

Ko da ta shiga ɗaki sai taga Halimen a kwance alamun barci takeyi.toshe bakinta ta yi gudun kar Halime ta ji shesheƙar kukanta, hijjabinta ta ɗauka hankali cikin sanɗa ta bar ɗakin,abinda bata saniba Halime na kallonta kuma taji komai ta window ɗakin.

Ɗaya idon da ya rage mata ne ya kaɗa ya yi jajir abinda ke cikinta na motsi kamar zai fito,Salmanu ne ƙadai madogarar abinda zata haifa amma gashi ya tafi ya barta, ta san da Salmanu zai iya magana daya nemeta akan gawarshi. Sai a lokacin wani irin kuka mai sanyi da cire yaƙini akan komai na rayuwa ya ƙwace mata, zazzaɓi mai zafin gasken da ba'ason mai ciki da shine ya rufe ta.



Babu wanda rashin Salmanu bai taɓa ba mussaman Abokanan aikin shi da tare aka kawo gawar Salmanu da su, Baba Isiyaku kuwa har lokacin da aka gama shirya gawar Salmanu baya hayyacin shi.

Inna ta yi Kukan da sai da kowa ya tausaya ma ta,ba su fi awa ɗaya da zuwa ba ta nufo gida ta bar Indo acan saboda Halime bata iya yiwa kanta wa su abubuwa da dama.


Halin da tasamu Halime aciki ku san zautar da ita ya yi tarasa da wanne zataji haka suka dugunzuma zuwa Asibitin da ta ke zuwa awo.


Har washe gari Halime na cikin ɗimuwa babu kuma wanda aka bari yazo dubata gudun karta ga ɓakin fuska zarginta ya je wani wajen.


Cikin ɗan motsa laɓɓanta ta kira Sunan Inna.

Da hanzari na matso kusa da ita har tana tuntuɓe.

"Ya ya jikin Halime? mekike son ci?"girgiza kanta ta yi, ta ƙara yiwa Inna alamun ta matso kusa sosai saboda muryarta da baya fita dakyau. Cikin mutuwar jiki Inna ta hau gefen gadon ta zauna.

"Maiyasa bakya son na sani Inna? bayan shine ƙarfin yin rayuwata cikin walwala kamar kowa,burikana sun rushe,na abinda zan haifa ma na shirin rushewa,nasan ƴan uwan Baba Shehu baza su bari jinina ya rayu cikin aminci a tare da ke ba, Baba Isiyaku kuma bazai ƙaunaci abinda zan haifa ba indai ba Namiji ba ne,ga Aunty Mubeena ta gujeni, dama Yaya Salman ne ya rage madogarar abinda zan haifa shima ga shi ya tafi ya barni,Inna da kika je dagaske kinga gawar Yaya Salman dagaske ya mutu?"

Ta faɗa ɗaya idonta na ƙara soyewa da ɗimuwar rayuwa da ta tsinci kanta aciki.

"Allah Ne madogarar Bawa Halime,bana fatan ki ta tafi kibarni kin..."

Kasa ƙarasawa ta yi saboda kukan daya ƙwace mata harda shesheƙa haka suka kwana ita da Halime da takejin zuciyarta kamar ba nata ba.


MUBEENA


Tun tabbatar mi shi dagaske Halime ce su buge a mota komai ya sauya, soyayyar su ba kamar da ba lokuta da dama sai ta sameshi cikin tunani (dama shi haƙƙi haka yake bana kowa kake ci,ka ci banza ba) hakan ya hassada gagarumin rigima tsakanin su saboda bai ɓoyemata tunanin yanda ya ga Halime ne ya tsayamai a rai ba duk da ba wannan ne asalin damuwar shi ba, kishi da danasanin kai shi ƙauyen su Halime ya mamaye zuciyar Mubeena wannan dalilin ya sa ta toshe duk wani hanya da Salmanu zai ƙara samunta,mitar ta dayaƙi ƙarewa kan kawai ya fito fili ya ce ma ta son Halime yake yi ba tausayinta ba yasa ya tattara ya bar mata ƙasar.


Laulayin ciki da ƙananun ciwon da take fama da shi ne yasa Faisal ya dawo duk ya rame saboda ƙewarta da kuma kwanan neman mafitar yanda zai taimaki Rayuwar Halime kamar yanda ya yiwa Maysarah alƙawari kuma ya saɓa.


Satin shi biyu da dawowa Mubeena taga sanarwa mutuwar Salman Ishaq a page ɗin Abokanan karatun su ihu da salati ta sa wayar hannunta na suɓucewa ƙasa...