21
```Page 21```
________Da gudu Faisal da ke kwance a Bedroom ɗinta ya fito, ganin yanda take zare ido hawaye na fitowa daga cikin su yace" what again Mubee?" Saboda tun safe ta dameshi da ƙorafe-ƙorafen ta gaji da rashin kulawar dayake nuna mata kamar da.
"Salman ya mutu wai"
"Wai? ba guarantee kenan amma kike wannan kukan?"
"Beb is true dagaske ne, wanda ya yi posting ba zai yi ƙarya ba"
ta faɗa tana nufar ɗakinta dasauri domin kimtsawa.
Ƙirjinshi ne ya yi mishi nauyi,tausayin Halime na ƙara bijiromai,kai tsaye gida ya kira kan anemo mishi Number Bala driver,sannan ya wuce na shi sashen domin kimtsawa.
Sai Rana sosai suka isa ƙofar family house ɗin su Salmanu, mutane ne ta ko ina, hakan ya ƙara tabbatarwa da Mubeena dagaske Salmanu ya rasu.
Bayan sunyiwa ƴan uwan Salmanu gaisuwa da Mahaifinshi, suka buƙaci ganin Halime,duk da Mubeena bataso haɗuwa da Halime ba saboda tanason ta cire Halime a lissafinta gaba ɗaya, kuma mutuwar Salman na nufin Mijinta zai iya auren Halime kenan? tuna hakan ya sa ta tsaya abakin mota taƙi shiga,har Faisal ya zauna dakyau Mubeena na tsaye fuskarta a ɗaure,ya gane nufinta ya kuma jinjinawa rashin hankalinta,banda haka yasan tasan waye Iyayenshi da su bari alaƙa kona taimako ne ya shiga tsakaninshi da Halime gara su ɓatar da ita,balle aje ga maganar aure,ita kanta da Mahaifinta yasan tana zuwa ƙauye wajensu da tuni yayiwa tufkar hanci.
Wani irin kallon bakida hankali ya ke watsa ma ta, sai dai bai ce ma ta komaiba yana jira yaga iya gudun ruwanta, a haka Bala ya cimmu su,da mamaki take kallon maiya kawo Bala kuma nan,ba dai ta yi magana ba tana dai tsaye ko gaisuwar Bala bata amsa ba.Fitowar Isihu da zai rakasu ƙauyen Innar su Halime ne ya sa Faisal rufe ƙofar da ƙarfi zuciyarshi na zafi,maimakon ta shigo sai ta gwammace ta shiga motar da Bala yazo da shi,shi da Isihu na zaune a gaba Ita kuma tana baya fuska a ɗaure kamar ba Mubeena ba.
Ko da suka kai Asitin ƙin fitowa ta yi,sai Isihu da Bala ne suka fita, saboda tasan ganin Halime zai rusa duk wani ƙudirinta.
Kuɗi motar komawa Faisal ya miƙawa Bala ya bawa Isihu,har lokacin fuskarshi a ɗaure yake wanda Bala baiga wani banbancin da yanda ya sani a baya ba, dama can haka Fuskarshi ta ke ga ma su yi mu su hidima.
A zafafe Faisal ya nufi cikin Asibitin ranshi na ƙara ɓaci ganin ruɓewar Asibitin da Halime ta ke ciki.
Ɗakin da suke ba laifi a tsaftace ya ke kuma su kaɗaine ba majinyata.
Cikin girmawawa Inna ta gaishe shi,ya amsa yana ƙara yimusu gaisuwar Salmanu. Halime dake zaune jingine da pillow rabin fuskarta lulluɓe da mayafin ɓakin Abayar da Mubeena ta taɓa bawa Salmanu ya kawo mata,sosai ya haskata ya ƙara fidda haske fatarta da tsinin dogon hancinta.
Cikin wasa da zara-zara fararen yatsun hannunta take gaishe da Faisal haɗe da tambayarshi ina Aunty Mubeena.
Bai amsa ba sai gefen fuskarta daya zubawa idanuwanshi tausayinta na ƙara kamashi.
Gyaran murya ya yi yanajin nauyi maganar da zai faɗa akaron farko a rayuwarshi.
A gaban Inna Faisal ya tambayi Halime ta faɗi duk abinda takeso,shi kuma ya yi alƙawarin zai yi mata.
Hannun Inna dake zaune agefenta ta ɗamko zuciyarta na bata ƙarfin gwiwar ta tambaye shi zai amince,iyakar abinda ta sani Faisal Mijin Mubeena na ne, banda haka batasan yanada alaƙa da accident ɗin da ta samu ba.
A hankali ta yi baya da mayafin kanta rufaffen idonta ɗaya ya bayyana.dasauri Faisal ya yi ƙasa da kanshi ƙwalla na taruwa a idanuwanshi.
"Inaso kai da Aunty Mubeena ku riƙemin abinda zan haifa"
Kamar saukar Manyan duwatsu haka Faisal da Mubeena dake laɓe a bakin ƙofa suka ji zancen.
Ajiyar zuciya ya sauke,batare da kokwanto ko dogon tunani ba ya ce,
"Na yi miki alƙawari Halima".ya faɗa idanuwanshi na ƙara kaɗawa.
Inna kuka ta sa "Halime na hanaki irin wannan shirmen sabbatun, waya ce miki mutuwa zakiyi eh? Ki gayamin"
A hankali Faisal ya tashi ya nufi ƙofa,jin motsin takunshi ya sa Mubeena nufar hanyar fita da sauri har tana haɗawa da gudu, gilmawarta Faisal ya gani ranshi yaƙara ɓaci, wato har laɓe ta koma yi, bai san Mubeena bata da hankali ba sai yanzu, har wani irin makahon kishi ne wannan?.
Number shi ya rubutawa Bala a takadda ya ce ya kaiwa Innar Halime.
"Kai Bala karka kuskura ka kai takaddar nan ba ni shi" Mubeena ta faɗa muryarta na rawa zazzaɓin jikinta na ƙara ƙarfi.
"Idan har kabata abakin aikin ka" Bala na jin Faisal ya ce haka ya nufi cikin Asibitin dasauri.
Fuska a ɗaure ya shiga Mota batare da ya ce ta shigo ba, ganin driver ya shiga kuma tasan zai iya tafiya ya barta yasa ta faɗa motar haɗe da sakin kuka mai ƙarfi,bai lallasheta kuma bai tanka mata ba.
"Halime kinada hankali kuwa? tayaya zakice a basu abinda zaki haifa,kin san su waye su,ko da iya rashin nemanku da Mubeena ta yi ya isa yasa ki gano akwai dalili, ko kina raye ko bakya raye bazan taɓa ba su abinda kika Haifa ba".Inna ta faɗa cikin kuka.
A dai-dai lokacin Bala ya nemi iso.
Da mamaki Inna da Halime su ke kallonshi.
Number Ubangidanshi ya fara bawa Halime, sannan ya ƙara yi musu gaisuwa, kafin ya sanar da su alaƙar shi da su Faisal.
Daga haka Bala bai ƙara tofa komai ba duk da yanada abun faɗe dayawa,bai san maiyasa Faisal yace abawa Halime Numbern shi ba amma duk da haka ya yi farin ciki ƙwarai, domin yasan zata samu taimako sosai.
MUBEENA
Har suka kai Gida kuka take yi har lokacin kuma Faisal bai tanka ma ta ba.
A hargitse ta nufi sashen shi saboda baƙin cikin halin ko In kula daya nuna mata har da hanzarin fitowa ya barta a mota. Cikin masifaffene kishin daya toshe ji da ganinta ta kutsa Bedroom ɗin da take kyautata zaton yana ciki....✍🏻