NIKAAH (Marriage for rent)

NIKAAH 10

by @hanaady

NIKAAH* 

    *Marriage for Rent* )


           *By* 

       *HANAADY* 

   *Rahama Aminu Bala* 



 *WhatsApp ***


HE HAD THE COURAGE 

TO REMARRY.

WILL HE FIND THE COURAGE TO

LOVE AGAIN?


*Free book* 





*Page 10* 


_______________ Da matsanaicin ciwon kai Karime ta dawo part nasu ga wani zazzabi daya rufe ta kwance take saman sofa a living room rufe jikinta tayi duka da hijab d'inta sosai take kyarmar sanyi' hawaye take sosai yau take missing family nata Mamana ta furta tana mai jin yanda kanta ke mugun ciwo "tashi tayi zuwa bedroom ragowar kud'in daya bata ta d'auka direct k'ofar fita ta nufa gate man nasu baya inda ya saba zama sabida haka bud'e k'ofar tayi tareda ficewa tsakanin gidansu da babban gate d'in gidan akwai nesa sosai but haka ta d'aure tana tafiya isarta bakin gate d'in kenan gate man yayi saurin tashi domin bud'ewa gate d'in wuri ta samu ta tsaya tana mai jiran mai shugowa ya shugo ko itama ta fice "yau da kansa yake driving ra'be ya hankota jikin bango kasancewar motar tasa tinted ce that's why bata kula cewa Ramadan d'in ne ba


da mamaki yayi parking tabbas Karime ce ya furta tareda saurin fitowa daga motar juyawa tayi da zimmar tafiya kira sunan ta yayi jin muryar sane yasa ta tsaya but bata juyoba 'takawa yayi zuwa gareta cikin alamun mamaki yace ina zuwa Karima share hawayen fuskar ta tayi aaa lafiya ya kuma tambayar ta wani abu aka miki ne ?


Kai ta gyada alamun aaa then ina kuma zaki? Gida ta furta "gida ya maimaita eh ta bashi ansa why zaki tafi gida ? Ina son ganin Mamana tafin hannun sa ya d'aura saman forehead d'inta jikinta da zafi sosai "hannun ta ya kama zuwa bakin motarsa bud'e k'ofar motar yayi get in ya furta yana mai kallon ta kafad'a ta ma'ke ita bazata shiga ba cikin alamun rarrashi yace kin fasa zuwa gidanne ?

Gida zaka kaini ta furta da alamun excitement yes ya furta shiga motar tayi tana mai jin wani farinciki a ranta bayan ya zauna motar yayi wa key had'i da yin hon domin a bud'e masa get "tafiya suke babu wanda yayi wa d'an uwansa magana direct K Dara hospital yayi parking cikin rashin fahimta tace baka da lafiya ne ?


No ya bata ansa ataikaice ficewa yayi abunsa had'i da zagawo side d'in da take bayan ya bud'e k'ofar motar cewa yayi muje b'ata rai tayi nida akace za'a kaini gida me kuma zanyi a asibiti ok tunda ba zaki fito ba bari na mayarda ke gida ganin babu alamun wasa a tattareda shi yasa tayi saurin fitowa yana gaba tana binsa a baya waya yake ansawa 

      Koda suka isa jininta aka d'iba domin test bayan wasu y'an minutes results d'inta ya fito ba tada wani problem a yanda likitan ya fad'a masa sai da damuwa ce ta saka mata ciwon kai da kuma zazzabi an rubuta mata magunguna again Dr d'in yaja mata kunne akan ta cire damuwa domin zata iya haddasa mata wasu ciwuwwuka .


Daga hospital saida ya biya gidan wani friend d'insa ananne matar gidan ke d'aukar measurements nata acewar matar ta huta da bin Karime har gida domin d'aukar measurements nata tuni Ramadan ya bata kwangilar siyo ma Karime kayan lefe komai ya zama ready saidai ba'a mata d'inki ba kasancewar ita matar bata san measurements nata ba acewar matar da gobe take planning zuwa gidan Ramadan domin d'aukar measurements d'in Karime


"Karime baki ta saki ganin iyayen kayan da wai ake kira da nata bayan an saka dukkan trolley's d'in cikin boot d'in motar Ramadan bankwana suka yi da juna cikin aminci .


Da kansa yake d'aukar akwatunan zuwa cikin gida ganin boot d'in motar a bud'e ne yasa Hjy Karime dirowa daga mota katon cikinsu ta d'auka da tsiya k'ofar shiga ta nufa tana ja tana uban nishi "kici'bus su kayi da juna cikin mamaki yace me nake gani haka washe baki tayi sannan tace aaa taimaka maka nayi mana naga kaman kai baka iya d'auka ne ta yaya kika gane bana ina d'auka?


   D'an murmushi tayi had'i da d'aga gira sannan tace naga duk ka d'auke masu sau'kin shine tace maybe ya maka nauyine bari na d'aukar maka hannayen sa rungume a kirjinsa kallon ta yake ba kyaftawa sosai al'amarin Karime ya bashi mamaki wato ita mai karfi dama lokacin da suke saka kayan acan gidan Musa ya lura da yanayin ta ashe da ta samu dama cewa za tayi ita ma da ita za'a saka kayan


d'an murmushi yayi sannan yace wannan aikin na maza ne masu ji da k'arfi Karime zaro idanuwa waje tayi sannan tace aikuwa ni kam ina iyawa domin har baro nasha turata daga fanfo zuwa gidan Baban Jummai " nan gidan Ramadan ne sabida haka bani wuri ansa yayi tareda yin gaba bin bayan sa tayi tana mai cewa ai da ka bari na d'auka tunda kayana ne ga mamakin ta d'ayan d'akin ya kai mata kayan 


shiga tayi d'akin tana binsa da kallo gyara tsayuwa yayi sannan yace muje kici abinci ki sha magani" bana jin ciwon kan yanzu matsowa yayi daf da ita hannun sa ya d'aura saman forehead d'inta still da zafi shuru yayi na wasu y'an sec muje yace ta ita zuwa ina ta bashi ansa d'akin mu ya furta k'asa k'asa naga ka kawo kayana anan nayi tunanin daga yau nanne d'akina


hannun ta ya kama tareda cewa muje ganin babu alamun wasa a tattare dashi yasa tayi shuru "seat ya furta zama tayi tana mai zun'buro baki kitchen ya nufa takeaway daya siyo musu ne ya juye cikin plate zaune ya tarar da ita abincin ya ajiye tareda cewa eat bana jin yunwa ta fad'a kanta k'asa zaunawa yayi tareda d'ibar abinci da spoon bakinta ya nufo fuskar d'aure bud'e bakin nata tayi domin ta fahimci sam babu wasa tattare dashi 


saida ya tabbatar da koshi drugs d'in ya bata bada son ranta ba tasha drugs d'in domin Sam bata son shan maganai t Mi'kewa yayi zuwa bedroom wanka ya samu yayi ,lokacin daya fito living room d'in kwance ya tarar da ita 


  Dining table ya nufa zama yayi tareda fara cin abinci satar kallon sa take tana mai jin wani yanayi a tareda ita komai nasa burgeta yake a natse yake cin abincin yana yi yana d'an latsa wayarsa ajiyar zuciya Karime tayi tareda tuno labaran da Rumaisa ta fad'a mata akan Ramadan d'in Sa'ada da kuma Alia .


Kwance take saman couch sosai marar ta ke mata mugun ciwo ga wani zazzabi daya rufe ta "A nashi bangaren bacci yake hankali kwance , cikin dauriya ta tashi domin zuwa toilet bayan wasu y'an minutes fitowa tayi tareda komawa saman couch d'in "kuka take k'asa k'asa cikin baccin sa ya fara jiyo alamun kukan ta "daga kwancen daya ke tace are you ok Karima k'ara volume d'in kukanta tayi domin iya dauriya tayi ta sani a yanzu tana buk'atar d'auki .


  Wurinta ya nufa lafiya ya kuma fad'i ? Hawaye ne shabe shabe a fuskar tace cikina da kaina ciwo suke mun ,tada ta zaune yayi tareda cewa ko abinci da kika cine ya b'ata miki ciki ?


Kai ta gyada alamun aaa then meke damun ki ,kasa bashi ansa tayi cigaba da kukan ta tayi d'an siririn tsaki yaja tareda duba time 9:40 daren is still young ki shirya mu koma Hospital bai jira ansar taba yayi gaba abunsa domin yau d'innan a gajiye yake that's why ya kwanta da wuri sosai yasha aiki akan wani project akan gida wani Hostel da company d'insa keyi so yayi participating sosai ,Ramadan irin mutanen nanne masu participating a aiyukansu basa zuba ma ma'ikatan su ido suyi san ransa akan aikin company that's why company d'insa ya sami karbuwa .


Tunda suka d'au hanya take kuka k'asa k'asa , driving d'insa yake but yana jin ba dadi'domin ya fahimci ciwon yana takura ta sosai "Bayan isarsu tambayoyi Likitar tayi mata dan d'an murmushi akan fuskar Likitar tace shekarar ki nawa ne?

24 Karime ta b'ata ansa murmushi ta kuma yi sannan tace how comes baki san lokacin da kike period ba ,cikin jin kunya Karime tace bana maida hankali akan sanin lokacin Hmm gaskiya cewar Likitar but ki riga calculating lokacin period d'inki is very important domin akwai lokacin da unexpected zaya iya zo miki baki shirya ba cikin kunya ta ansa da in sha Allah zan ki yaye.


bayan wasu y'an minutes Likitar cewa tayi kina da pad a gida pad Karime maimaita ,No Ramadan ya bama matar ansa ok Dr ta furta tareda fara wasu y'an rubuce rubuce paper ta mi'ka masa asiya mata wad'annan magungaunan and ga  sanitary pad nan a siyo mata 


tare suka tafi bayan ya gama siyo komai hanya suka d'auka zuwa gida driving yake hankali kwance,saukar maganar sa taji cikin kunnen ta you have to be serious akan irin wad'annan stuffs d'in naku na mata 


shuru tayi domin still marar ta tana mata ciwo imagine baki San time d'in da kike period ba banza tayi dashi domin abunda take ji ya wuce tunain mai tunani "parking motar yayi tareda zagayowa ya bud'e mata k'ofar cikin dauriya ta fito taimaka mata yayi zuwa cikin gida "zaunawa tayi saman sofa tana zubar hawaye cikin yanayin tausayi yace kije toilet ki saka pad d'in mana idanuwan ta a rufe ta mi'ke tareda nufar hanyar bedroom d'in su


bin bayan ta yayi da pad a hannunsa , time d'in daya isa tana toilet tsayawa yayi kusa da toilet d'in yana jiranta 


Kayan jikinta ta cire tareda watsa ruwa tabbas period nata yazo but bai wani zuba ba ,wanke pants d'inta tayi tareda d'auko kayan data cire domin baza ta iya wanke su yanzu ba,tsaye ta tarar dashi kayan hannun ta yasa ansa tareda mi'ka mata pad d'in ansa tayi tana mai bin pad d'in da ido ficewa yayi zuwa d'aya d'akin da kayan ta suke pant ya d'auko mata tareda saka kayan da ta cire cikin laundry basket , 


pant d'in ya mi'ka mata tareda nufar toilet wanka ya kuma watsawa yanda ya barta haka ya tarar da ita da mamaki yace ki saka pad d'in mana kada towel d'in jikinki yayi stain ,kunya take ji ta rasa ta inda zata saka pad d'inne bata ta'ba amfani da ita bane that's why .


Ansa yayi tareda cewa saka pad d'in ne bakya iyawa ,saka mata ita yayi perfectly mi'ka mata yayi fuskar ba yabo ba fallasa yace Karime na fahimci sosai na fara shagwaba ki satar kallon sa tayi ta lura yau baya cikin walwala ,juya masa baya tayi d'an murmusawa yayi tareda d'aukar wa an baccin toilet ya koma domin shiryawa da ido ta bishi cikin zuciya take magana wato shi ta fahimci baya son taga jikinsa amma ya iya kallon nata harma dasu tattaba ta. 


Lokacin da ya fito bata d'akin , d'aya bedroom d'in ta shiga cikin sabbin kayan daya siyo mata ta d'auki wata rigar bacci mai kyau ta saka murmushi ne ya su'buce mata domin rigar ta matuk'ar burge ta ,bata da tsaraici ko kad'an iya kwaiwa ce sabida haka cewa tayi bari nayi kwanciya ta sabon d'akina kashe hasken d'akin tayi tareda kwantawa saman gado da murna ta kwanta domin gobe Saturday zata fara zuwa islamiyya .


Ana shi bangaren yayi mamaki daya jita shuru , d'akin ya nufa bayan ya kunna hasken d'akin kwance ya tarar da ita sai sharbar bacci take hankali kwance ,takawa yayi zuwa gareta gefen ta ya zauna , hannun sa ya d'aura saman kashin kanta slowly ya fara shafa shi kissing gashin nata yayi bud'e idanuwan ta tayi cikin muryar bacci tace mijin Sa'ada


ya rasa gane wani magic ke d'auke da wannan murya ta Karime, tana saka shi cikin wani hali matuk'a kasancewar cikin yanayin bacci take wani irin murmushi tayi masa sosai tayi wani irin kyau idanuwan ta ya kalla wani irnin yanayi yake ji mi'kewa tsaye yayi tareda nufar k'ofa zuciyar sace ki umartar sa daya bar mata d'akin if not ba za'a kwashe lafiya ba 


, gaf da zai fita ya kuma kallon ta still murmushin fuskar ta bai d'auke ba haka zalika yanayin kallon ta bai canza ba please ka kashe mun hasken kafun ka fita ,kaman yanda ta buk'ata hakan take domin ya kashe hasken d'akin


" tsaye yayi yana kallon saitin ta duk da ba wai ganin ta yake ba , zuciyar sa ta kasa controlling jikinsa , takawa yayi zuwa gareta gadon ya hawo tareda matsawa very close to her fuskarta ya laluba jin ana shafa mata fuska ne yasa ta bud'e idanuwan ta mijin Sa'ada ta kuma furtawa bai ansa ba illa jawota jikinsa da yayi anan zaka kwana ne ?


Shhhhh Karima ba komai akema magana ba ,jin furuncin sa kama bakin ta tayi shafa gashin kanta yake yi cikin wani salo kissing eyes d'inta yayi zuwa kuncinta lumshe idanuwan ta tayi tana mai jin wani sabon yanayi, bakinta ya laluba kissing nata yake cikin natsuwa irin tasa sosai al'amarin nasa ya firgitata domin sunan Sa'ada yake ambata romancing nata yake ita kuma ana ta bangaren kukan zuci take yi .


Bayan wasu y'an minutes zare jikinsa yayi tareda nufar bedroom d'insa , haushin kansa yake ji why yake biyewa gangagar jikinsa da kuma zuciyar sa akan yarinyar can lumshe idanuwan sa yayi yana mai tuno yanda moments nasu ya kasance, anata bangaren kuwa kuka take shabe shabe yau dai taga ta kanta she is not Lucky akan komai na rayuwa ganin ba sarki sai Allah ne yasa ta share hawayen ta,bayan wasu y'an minutes bacci ne yayi gaba da ita.


Kasancewar yau Saturday ba aiki, a gida ya wuni but basu wani had'u da ita ba ya fahimci kaman bata son had'uwa dashi .

Wanka ta fito pad take son sakawa a jikin pant nata but bata san ya za tayi ba domin ajiya bata mayarda hankalin ta kalli yanda yayi ba , ficewa tayi zuwa bedroom d'insa zaune yake yana wani aiki a system d'in sa ,tsaye tayi masa banza yayi da ita aikin sa yake hankali kwance


" mijin Sa'ada ta kira sunan sa cikin yanayin murya irin ta Abdulkarim yes ya furta still hankalin sa na kan screen d'in system d'in d'an gare murya tayi domin she clearly remember Rumaisa ta mata fad'a akan ta ri'ka tausasa lafazin ta a gabansa ,saka mun za kayi kallon ta yayi tareda cewa Karima sakatar ki ta soma yawa zun'buro baki tayi sannan tace kada ka mun dariya akan me kenan had'e kafafuwanta tayi kallon ta yayi towel ne jikinta satar kallon gashin kanta yayi boyayyar ajiyar zuciya ya saki tareda cewa ina jinki .


Dan Allah ka saka mun kada ya b'ata mun towel d'an kallon ta yayi yanda ta had'e kafafuwanta ji yayi abun ya matuk'ar burgeshi , hannun ya mi'ka mata alamun ta bashi cikin sauri ta mi'ka masa .


Sosai ta Kura masa ido domin tana son koyon yanda ake sakawa ,bayan ya kammala mi'ka mata yayi godiya tayi masa tareda saurin shigewa toilet.


Ajiyar zuciya yayi tareda cigaba da aikinsa , lokacin data fito zama tayi d'an nesa dashi ,batareda tunanin komai ba ya ajiye system d'in sa tareda cewa come here , d'an matsawa tayi jawota yayi zaune yake jingine da bed ita kuwa kusan a zaune take saman jikinsa , samun kanta tayi da son shafa fuskar sa , tafin hannunta ta d'aura saman fuskar sa lumshe idanuwan sa yayi so that tayi abunda take so peacefully .


Shafa fuskar sa tayi zuwa karan hancinsa , slowly ta d'aura lip's d'inta saman forehead d'insa he is lost with this simple kiss , d'ago fuskar sa tayi da hannun ta ,mijin Sa'ada ta furta cikin irin wannan muryar dake rikita masa lissafi kallon juna suke ,he was wondering why even something small like this felt so good to him , I don't know how to use pad ne that's why nazo ka sakamun d'an murmushi yayi sannan yace farkon zuwan ki gidannan i thought ko karatu bakya iyawa d'an murmushi tayi sannan tace dole za kayi tunanin haka duba da daga kauye nake and babu wayewa tareda ni .


Ta yaya kike fahimtar yaren turanci haka murmushi ta kuma yi sannan tace Hassan Usman Katsina Polytechnic kusada kauyen mu take so staff school nasu nayi , kallon juna suke bako kyaftawa itace ta fara yanje eyes d'inta tareda k'okarin sauka daga jikinsa bai hata ba sabida yasan yanda zuciyar sa take reacting akan Karime .


Yauma takeaway ya siyo musu Hjy Karime tune ta gama cinye nata .


Shugowa Momy tayi cikin falon nasu saurin tashi Karime tayi tareda gaishe da ita cikin kyarmar jiki bata ansa ba illa kallonta data kai inda yake abinci ne bakinsa that's why bai samu damar magana ba

tafiya Karime ta fara domin basu wuri tabbas ta san menene ya kawo momy sashensu ina kuma zaki cewar Momy ?


Saurin dawowa tayi tareda sadda kanta k'asa cikin nuna kular sa yace welcome Momyna washe baki Momy tayi my son kana lafiya?

Yes Momyna zama Momy tayi tareda cewa magana nazo muyi kona ce alfarma nake nema wajenka cikin mamaki yace you should have called me part naki No my son kada ka damu besides bana iya tuna when last na shugo part naka 

zama yayi kujerar da Momy take kitchen Karime ta shiga tareda d'auko lemun kwali da ruwan roba ajiyewa tayi saman center table hanyar d'akin su ta nufa ke zonan cewar Momy jikina kyarma ta dawo tareda sadda kanta k'asa shuru yayi yana mai kallon ikon Allah zuba mun lemun a cup Momy ta buk'ata jikina kyarma Karime ta tsiyaya mata lemun cikin cup ansa Momy tayi tareda cewa samu wuri ki zauna ba musu Karime ta samu daya daga kujerun falon ta zauna .


Alfarma nake nema wajenka my son akan me ya bugata yana mai kallon Momy it's about Alia gaban sa saida yayi matsanaicin fad'uwa what about her ?


I want to you to call her akan me Momyna, she was the one that left me and now you want me to call her for what reasons?


*


Please

Comments and follow the Author.