JUYIN KWAƊO 12
🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad
Page-12
ADVENTURERS.
Tafiyarsu ta miƙa a cikin dajika da tsaunika, sun yi tafiya irin wadda ba su taɓa yi ba a rayuwarsu, hatta shi kansa Uwais bai taɓa yin doguwar tafiya irin wannan ba, dan ko shi kansa ba sanin hanyoyin ya yi ba, ta hanyar wannan taswirar da suke ɗauke da ita ne kaɗai suke iya gane hanyoyi. Batun abinci kuwa tun kafin su ji yunwa Uwais yake kawo musu abin da za su ci, tun abincin ba ya musu daɗi har ya zamto sun fara sabawa da abincin.
Ranar da suka cika kwanaki biyar da barin ƙauyen Askar cif, suka shiga wani daji me yawan dogayen duwatsu. Su huɗun cif suna tafe a tare, Arman da Adam na kan gaba, yayin da camera ɗin Adam ke rataye a wuyansa, dan ba ya rabo da ita, daga zarar ya ga abin ɗauka zai ɗauke shi a hoto. Ivana da Uwais kuma na daga baya suna hirar da suka saba yi a lokuta irin wannan.
“Me yasa kake yawan kallona?”
Ivana ta jefa masa tambayar, dan za ta iya cewa daga zarar tana wuri Uwais ba shi da abin kallon da ya wuce ita.
“Saboda irin shigar da kike, da farko na ɗauka cewa ke ba musulma ba ce, sai da na ga yanda kike suturta jikinki lokacin da za ki yi sallah, amma kuma bayan kin idar sai ki yaye ki koma shigarki mai nuna tsaraici!... Sai na cewa kaina, idan har za'a suturta jiki yayin yin ibadar Allah, me zai hana a ci gaba da suturta jiki ko ba lokacin da za'a bauta masa ba, domin zamanki da irin wannan shigar na cikin saɓa masa!”
Hatta Adam da Arman sai da suka tsaya suna dubansa, saboda ya yi magana ta hankali. Ganin suna kallonsa yasa yace.
“Ku yi haƙuri fa, na fuskanci kamar hakan ba komai ha ne a zamaninku... Amma ni gani na yi ya kamata ace na faɗa mata gaskiya”
Ivana ta dubi shigar dake jikinta ta slacks trouser peach color, da farar blouse, wandon sam bai kai idon sawunta ba, har gwanda ma rigar na da ɗan tsayi, kuma duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, domin ita kanta ta san cewa abin da suka yarda da shi a matsayin wayewa kauce hanya ne...
“Ki yi haƙuri idan maganata ta sa kin ji ba daɗi!”
Uwais ya sake faɗa yayin da suka ci gaba da tafiya, ta girgiza masa kai tana murmushi, alamun ba komai, sannan ta gyara zaman jakar guitar ɗinta dake goye a bayanta, dan yanzu Arman ne yake ɗauka mata kaya.
“Mi ye sunan abin da yake cikin jakar nan, na ga kina yawan kulawa da shi”
Uwais ya tambaya. Ivana ta kalle shi, amma kamar yanda wancan Uwais ɗin yake mata magaba ba tare da ya kalleta ba shi ma wannan haka.
“Guitar sunanta, kuma ana yin kiɗa da ita, kamar dai sarewarka!”
Ya jinjina kansa.
“Ina son kiɗa sosai”
Ya faɗa, kamar yanda wancan Uwais ɗin ya taɓa faɗa mata cewar yana son kiɗan guitar.
“Ka iya busa sarewa?”
“Sosai, ko kina so ki ji?”
Ta gyaɗa kai, sai ya saka hannunsa ya zaro sarewar tasa dake saƙale a ƙugunsa, sannan ya kafata a bakinsa, ya soma busa sarewar cikin sauti me daɗin saurare, wanda ya cakuɗe da yanayin sanyin dajin da suke ciki. Hatta su Adam kansa busar sarewar tasa na musu daɗi.
Hakan yasa tafiyar tasu ta ƙara armashi, suna tafe yana musu busa me kwantar da hankali, a lokacin kuma suka yi kiciɓis da tawagar wasu mutane, sanye cikin shigar jajayen kaya. Hakan ya sa suka tsaya suna kallon yawan jama'ar, kafin su yi wani yinƙuri har mutanen sun musu ƙawanya... Kuma sam ba su da kataɓus, dan sarkin yawa, ya fi sarkin ƙarfi.
ASRA.
Tsaye take a cikin dakarun da take da alhakin koyar da su salon yaƙi na masarautar Jiyad, yayin da suke a wani babban fili da aka tanada domin koyar da faɗa a cikin masarautar, wani lallausan yashi ne zube a ƙasan wurin, yayin da muggan makamai na koyon salon yaƙi ke aje a ko wace kusurwa na wurin. Ta harɗe hannayenta, yayin da take kallon yanda ɗaliban nata ke nuna mata abin da ta koyar da su.
Tun daga nesa suka fara jin takun sawun masu gadin Malik Cangaz, hakan yasa ta dakatar da ɗaliban nata tun kafin ƙarasowar sarki wurin. A kan idonsu aka buɗe ƙofar filin, Malik Cangaz tare da masu tsaronsa suka shigo cikin filin. Hakan yasa Asra da ɗalibanta duka suka durƙusa domin kwasar gaisuwa.
Sai da sarki ya amshi gaisuwar tasu, sannan kowa ya miƙe kan ƙafafunsa, hakan ya bawa Asra damar matsawa kusa da Malik, domin jin abin da ke tafe da shi. Yau ma kammaninsa sak na matasa, ba za ka ce shi ne mahaifin gimbiyoyin uku ba, kai kace wani yayansu ne.
“Horarwa na tafiya yanda ake so Asra!”
Cewar Malik cike da izza, Asra ta yi murmushi tana duban mahaifinta, sannan ta jinjina kanta a ladabce.
“Sosai ma kuwa Darvesh (Holy man)”
“Ko za mu iya ganawa na wasu daƙiƙu?”
Faɗin Malik Cangaz, Asra ta gyaɗa kai, a tare suka taka zuwa wata kusurwa dake cikin filin, wadda ta fitar da su (balcony) dake can saman fadar, daga wurin ma za ka iya hango gine-ginen gidaje masallatai da kuma kasuwar masarautar kaf.
“Zuwa yanzu kwanaki uku kacal suka rage a ɗaura auren Iqrah da yariman Azad... Duk wasu shirye-shirye mun kammalasu, ɓangaren tsaro ne ba mu yi komai ba, dan haka ina so a tabbatar da tsaro a masarautar nan, domin akwai tarin baƙin da za su zo daga baƙin masarautun da suke maƙotantaka da mu... Ba na son a samu wani kuskure!”
Asra ta jinjina kai tana saƙala gashin kanta a bayan kunnenta.
“Zan tabbatar da hakan Darvesh...”
“Zuwa gobe zan je kaiwa abokina sarkin Mamlakatul Dahi goron gayyata, domin ba na so na aika Manzo! Na fi so na je da kaina domin isar da saƙon... Dan haka ki shirya, ina so ki min rakiya!”
Asra ta risina cikin girmamawa.
“An gama Darvesh...”
“Na sallameki”
Da haka ta juya ta barshi tsaye a wurin yana kallon girman masarautarsa. Kafin kuma amintaccen hadiminsa ya shigo wurin a hanzarce.
“An kamo matasan da ake zargi da cin amanar ƙasarmu ta hanyar fitar da bayanan kasuwancinmu na sirri ya shugabana!”
Cewar hadimin, bayan ya kwashi gaisuwa. Malik ya dube shi cike da isa, sannan ya furta.
“A kai min su kurkukun cikin ƙasa, a gana musu azaba ta mako guda, kafin na kai ga zartar da hukuncin da ya dace a kansu, kafin su mutu ina so su ɗanɗana azabar da za ta bawa duk wani me sha'awar aikata laifi irin nasu tsoro!”
Hadimin ya risina cikin alamar dake nuna ya karɓi saƙon shugaban nasa.
“An gama ya kai wannan adalin sarki!”
Daga haka shi ma ya fita daga wurin ya barshi, tsaye cikin sallalamin jiran ranar da boka Jalis zai sake naimansa. Domin tun bayan ranar da suka haɗu a kan maganar gano matasan nan uku bai sake naimansa ba, kuma hakan na nuna cewa har yanzu boka bai gano inda suke ba. A tsarinsa shi kuma ba ya zuwa wurin bokan ba tare da bokan ya naime shi ba... Amma a wannan karon dole ya karya ƙa'idar, dole ya je ya ji yanda aka yi aka haihu a ragaya.
MAMLAKATUL AFSAH.
Cike da zaƙuwa Malik Safraz ya ɗaga kai ga tawagar ɓoyen da yakan aika domin bincike, ya ƙagu su sanar da shi inda takobin mulkinsa yake.
“Ya shuganmu, haƙiƙa takobinka ya bayyana a ban ƙasa, sai dai samunsa shi ne abu mai matuƙar wuya a gareka!”
Muryar ɗaya daga cikinsu ta furta, ba tare da ya bayyana ba, domin ko shi kansa ba ya iya ganinsu sai idan sun so hakan. Ya ɗaga kansa ya kalli saitin inda maganar ke tashi, sannan ya furta.
“Shin har akwai wani abu da zai gagareni samu a faɗin wannan duniyar?”
“Ƙwarai kuwa ya shugabanmu, kuma wannan takobi na ɗaya daga ciki!”
“Me nene dalilinku na faɗin hakan?”
“Wanda yake tare da takobin shi ne abin ji, domin ko da yankar naman jikinsa za'ayi a kan takobin nan sai dai a yi, amma ba zai taɓa bari a raba shi da wannan takobi ba...”
“Waye shi?”
Malik Safraz ya tambaya ransa na ɓaci.
“UWAIS!”
Muryoyi uku suka ba shi amsa take, a nan ne fa hantar cikinsa ta fara motsi, domin in har Uwais ko Feroza na raye a ban ƙasa mulkinsa na cikin haɗari!... Ke nan me ya kamata ya yi a wannan gaɓar!?... Tambayar ta tuno masa da wata hatsabibiya ɗaya da zai iya sawa wannan aikin hankali kwance. Lokaci guda ya yi murmushi, sai kuma ya haɗa da dariya yana jinjina kai, sannan laɓɓansa suka furta sunanta.
“NATILA!”
GARIN QUDWA, YANKIN GABASHIN SAHARAR SUBAH.
Hayaniyar jama'ar dake kaikawo a cikin 'yar ƙaramar kasuwar garin ce ta cika ko ina. Komai na kayan siye da siyarwa daga ƙasashen duniya akan kawosu kasuwar wannan gari na Qudwa. Domin garin ya kasance cibiyar kasuwanci, duk da garin bai cika girma ba.
Ko wani mutum dake cikin kasuwar za ka same shi sanye da shiga irin ta garinsu ko yankinsu, ko kuma masarautarsu. Yayin da ake hada-hadar cinnikayya a cikin kasuwar. Wata iska me ƙarfi ta taso daga cikin sahararar dake gabas da kasuwar, hakan yasa ƙura ta shiga bule mutanen cikin kasuwar. Kafin wata guguwa ta shigo cikin kasuwar, sannan ba ta sauƙa a ko ina ba sai kan rufin wani shago.
Kaɗan-kaɗan iskar ta fara raguwa, har ta ɗauke gaba ɗaya. Yayin da wannan guguwar ta rikiɗa zuwa wata doguwar budurwa. Sanye cikin baƙaƙen kaya, ta yi kitso guda biyu a kanta, tsayin jelar kitson har cinyoyinta. Fuskanta kuma a rufe yake, a hankali ta yi tsugunnon mage a kan rufin shagon, sannan ta shiga baza idonta a kan mutanen dake kai kawo...
Dan iskar da ta taso ba ta sa kasuwancin da ake gudanarwa ya dakata ba, sautin murmushin da ta yi ya fito tare da motswar ƙyallen da ta rufe fuskarta da shi, domin ta hango abin harinta, ci gaba ta yi da bin sawunsa, har ta ga sanda ya shiga wani loko da take da tabbacin babu kowa ciki.
Take ta ɓace daga saman shagon, kuma ba ta bayyana a ko ina ba sai a cikin lokon, sannan a gaban mutumin da take bibiya. Shi kansa mutumin da ya ganta sai da ya razana, hakan ya sa kayan dake hannunsa suka zube a ƙasa, ya ɗaga hannayensa sama kamar me laifi.
A wannan karon budurwar dariya ta yi, sannan ta buɗe fuskarta, kyakkyawar fuskarta ta bayyana gare shi, haƙika tana da kyau, amma kyawun ɗan maciji. Lokacin da ya ganeta bai san sanda ya saki fitsari a wando ba, jikinsa ya soma kyarma, domin ganin NATILA na dai-dai da ganin mutuwar mutum.
“Sannunmu da sake haɗuwa, Malam Ayyaz!”
Jikin Ayyaz na rawa ya shiga ja da baya yana son bata haƙuri, cikin wani irin sauri da ya ɗararma hankali ta isa gabansa, sannan ta saka hannayenta ta riƙe wuyansa.
“Dole na kasheka, sannan na ciro zuciyarka na kaiwa shugabana, na masa alƙawarin sadaukar masa da zuciyarka a daren yau!...”
Ta ƙarashe maganar wasu zaƙa-zaƙan fiƙoƙi na fitowa daga haƙwaranta na sama. Sannan ta kafasu a wuyansa, nan take Ayyaz ya fara shure-shure, amma Natila ba ta saki wuyansa ba sai da ta zuƙe fiye da rabin jinin jikinsa. Duk da haka ba ta ƙyale shi ba, da ta saki wuyan nasa ta ɗaga hannunta me yalwar dogayen farata, ta caka a ƙirjinsa, sannan ta ciro zuciyarsa, kana ta saki gangar jikinsa ta faɗi ƙasa.
Zuciyar dake riƙe a hannunta ta kalla, bakinta duk ya ɓaci da jinin jikinsa, ta sa bayan hannunta goge bakin nata, sannan ta sake rufe fuskarta, ta tsallake gawarsa ta ɓace a iska.
Salma Ahmad Isah ✍️
___________
_😳 Akwai matsala!_
_Ko su waye suka kama ADVENTURERS ɗinmu?. Shin ya za a yi su kuɓuta?_
_Batun wannan Natilar! Ya kuke ganin haɗuwarta da ADVENTURERS ɗinmu za ta kasance?._