MAI KWAƊAYI

22

by @nafisatusasaal01

```Page 22```


________Yana zaune ko takalmin ƙafarshi bai cire ba ta banko ƙofar ɗakin, batare da la'akari da yanayin Fuskarshi ba ta fara magana cikin kuka"ta yaya zaka amincewa karɓan abinda Halime zata haifa batareda izinina ba".

"Saboda kece kike aure na?, bance ki kula da shi ba, inada kuɗin da ko nanny nawa ne zan ɗauko suyimin abinda nake so, bansan haka zuciyarki ta ke ba Mubeena,menene amfanin irin taimakon da kike yi mu su?" ya ƙarasa faɗa cikin huci ya na kallon ta.

"Iyakacina da ita taimako ne amma ba ta raɓeni ba,kuma matsawar ka karɓo abinda Halime ta haifa cikin gidannan to kowa zaiji kanmu" ta faɗa tana ƙoƙarin barin ɗakin.

"Ba sai kowa yaji kan mu ba Mubeena! wallahi har rabuwa zan iyayi dake saboda mai fuska biyu munafiki ne,wani irin zuciyace dake haka? ace ko gaisuwa ki kasa yiwa Halima,sannan yarinya na hasasowa kanta mutuwa saboda yanke yaƙinin zata cigaba da rayuwa,kuma duk Mijinki ne sila amma baki russuna ba kishi na neman sakaki ɓarar da ladanki, bana buƙatar shawararki kan abinda zanyiwa Halima, don haka ki daina wahalar da kanki".tana ƙoƙarin juyowa ta yi magana ya daka mata tsawa"get out of sight Mubeena!"

Da gudu ta fita daga ɗakin cikin kukan da ta shigo da shi.


Babu wanda ya nemi ɗan uwanshi har wayewar gari.


★da sassafe ta fita Office ɗin da ta jima batajeba saboda yanayin jikinta, ko breakfast bata tsaya yi ba.

 Shima Faisal ko ƙofar sashenta bai kallaba ya bar gidan ya nufi gidan su.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Satin su Halime ɗaya a Asibiti aka sallamo su,mafi akasarin danginta na ɓangaren Uba basu zo dubata ba saboda alhakin mutuwar Salmanu da su ka ɗora mata ita da Innarta, ciki har da Baba Isiyaku acewarshi, su suka hana Salmanu nutsuwa waje ɗaya banda mugunta menene Halimen bazata iya yiwa kanta ba, har da zata bar gidan Mijinta ai tanada sandar dogarawa.


A dangin Inna babu wanda ya kula su sai tsirarun da suka kasa jurewa.


Rubuce-rubuce shine yazama abokin hirar Halime, ta rame ta ƙara koɗewa ta dawo fara fat,kullum sai ta yi tunanin maiyasa Aunty Mubeena ta daina neman ta? ko dai Bala ya gaya musu wani mugun abune akanta? wannan dalilin yasa ta tutunɓeshi ta wayar hannu.

Bai yi mata gamsasshen bayani ba amma yace ta bari ranar sati zaiyi ƙoƙari yazo.



Har ta cire rai da zuwan Bala sai gashi washegarin ranar da ya yi mata alƙawari.

Iyakacin abinda ya sani ya gayamata alaƙar Faisal da MAYSARAH da ita kanta Mubeena kuma duk kuɗin da yake kashe mata MAYSARAH ne ya sa drivern kakar su Goggo A'isha ya bashi tun ranar da lamarin ya faru kuma duk ranar da ta tambayeshi kuɗi wannan drivern yake tuntuɓa kamar yanda ya bashi umarnin kome takeso ya afaɗamai ya gayawa kakar su ita kuma ta gayawa Maysarah( kenan Maysarah yasan abinda Faisal ya aikata?) sannan shi bai taɓa hirarta da su ba saboda babu wannan ma sakin fuskar a tsakanin su.


Ƙwalla ne ya cika idon Halime cikin sanyi da son sanin waye Maysarah ta tambayi Bala ina zata samu Number Maysarah ta yi mishi godiya kafin Allah ya ɗauki ranta.

"Haba Halima ki daina irin waɗannan maganganun In sha Allahu idan kika haihu lafiya zan kaiki har Inda Kakarshi ta ke ita kuma nasan zata sadaki da shi, amma samun Number shi ba abu bane maiyiwuwa ba a gareni.

Bala ya faɗa cikin son kwantar mata da hankali.

"Idan ban samu zuwaba ka yi min alƙawarin zaka kai ƴata ko ɗana suyi mishi godiya idan suma basu samu zuwaba, duk ranar da Allah ya sa ka ganshi kayi mishi godiya kace mishi Halime tana gaishe shi kuma ta tafi da burin son ta ganshi tayi mishi godiya" ta faɗa cikin kukanta mai sanyi,

Daga haka ta juya cikin gida daƙyar, ta bar Bala a tsaye cikin karyewar zuciya.


Labarin MAYSARAH da taimakon da ya yi mata shine rubutun ƙarshe a littafin HALIME.


★Washe gari ta tashi da matsanancin nakuɗa haɗe da ɓallewar jini, cikin gaggawa Inna da ƴan uwanta suka nufi Asibiti da HALIME.





CIGABAN LABARI


fuskar nurse ɗin ne ya sauya sai dai batacewa Inna komai ba sai alamu da tayiwa Inna da hannu kan ta biyo ta suje.....✍🏻