23
Page 23
__________ A bakin ɗakin da Halime take ciki Nurse ta barta har tsaho rabin sa'a,batare da ta fito daga ɗakin ba.
Har Inna ta fara gyangyaɗi Nurse ɗin ta tashe ta da Baby a hannunta,cikin rawa jiki Inna tasa hannu ta ƙarbi Jaririyar, Ma sha Allah bata taɓa ɗaukar jaririya mai kyawun jaririya Halime ba,cikin karyewar zuciya ta ƙara tambayar Nurse ɗin ya ya jikin Halime? Bayan ta gama ƙarewa Jaririyar kallon cikin sekonni.
Kai tsaye ɗakin da Halime ta ke ta kaita.
Jinin da aka sawa Halime Inna ta bi da kallo, kafin ta dawo da fuskarta kan na Halime.
Ta yi tunani barci takeyi sai da ta kamo hannunta sannan ta saki murmushi ta na yi mata yaya jiki? Maiyake ma ta ciwo yanzu?
"Banajin komai Inna".
"Allah Yabaki lafiya kinji" Inna ta faɗa tana shafa gefen fuskarta.
A hankali ta tafara magana
"Inna ga Halima nan a hannunki,bazan hanaki riƙeta ba amma idan kinga ba hali ki tuntubi Yaya Faisal, lambar daya rubuta na cikin littafin Halima, Inna ki bata littafin da na bar mata ta karanta, zata ga labarina,sannan ki ce mata inasonta sosai, kuma idan Allah ya sa ta haɗu da Maysarah ta ce ina gaishe shi".
Kuka har da shesheƙa Inna ta sa"Halime yaushe zaki daina kirawa kanki mutuwa bana son ji dan Allah ki daina zaki rayu da ɗiyarki sama da yanda na rayu dake kinji"
"Naji Inna, Inna ki kira Baba Isiyaku da Aunty Indo na gan su" ta faɗa cikin dashashen Muryarta,a take fuskar Inna ya sauya zuwa ɓacin rai saboda ambaton Sunan Baba Isiyakun da ta yi,tasan ganin diddigin abinda Halime zata haifa ne ya kawo su, banda haka tasan ba zuwa zasuyi ba. A gefen Halime ta ajjiye Jaririyar.
Cikin ƴar fara'a Inna da Indo suka shigo haɗe da hirar su ƙasa-ƙasa, Baba Isiyaku na bayansu yana baza koɗaɗɗiyar Babbar Rigar shi. Kamar dai yanda Inna ta barta haka ta sameta a zahiri, amma a baɗini babu Halime ta jima da tafiya tun fitar Inna Allah Ya ɗauki ranta.
Ba Inna ba ko Baba Isiyaku mai ƙwaɗayin tsiya da burika kala-kala ji yayi duk sun rushe jikinshi har rawa yake yi.
Faɗar raɗaɗin rashin Halime a zuciyar Inna ɓata bakine saboda soyayyar Uwa da ɗa abune mai ƙarfi.
An kai Halime makwancinta,wanda yake tabbatar da ta tafi har abada.
Inna ta yi kuka mara iyaka, har bayan wasu kwanaki idan ta kalli jaririya da akayiwa huɗuba da HALIMA sai taji zuciyarta na karyewa tare da jin soyayyarta mai ƙarfi acikin zuciyarta. Wannan ne lokacin yaƙinta,wannan ne kuma damarta na ƙarshe na cikawa Halime burinta.bazata saurara ba kuma bazata gajiya ba har sai inda ƙarfinta ya ƙare.
Ranar Sadakar bakwai sai ga Faisal da Bala idanuwan kowannen su a kumbure, saboda faɗar Halime ya tabbata dagaske ashe mutuwa zatayi .
Ko da Faisal ya keɓe da Inna ko da wasa bata tambayeshi Mubeena ba, kuma tayi mishi alƙawarin matsawar ta kasa riƙe Halima, zata nemi shi ta layin waya amma yanzu bazata iya ba shi jaririya ba.
Ajiyar zuciya ya sauke yanajin hakanma ya fi sauƙi ya kuma ji daɗin da bata tambayeshi Mubeena ba, da haka sukayi Sallama bayan ya ajjiye mata manyan kudaɗe da sunan kuɗin hidimar jaririya Halima.
Baba Isiyaku ya susuce ya ruɗe gabaɗayan shi, sai sabbatu da koke-koke, saboda mutuwar Salmanu da ya dawo mai sabo, ba irin asirin da bai tonawa kanshi ba,amma duk da haka yakasa samun sukuni azuciyarshi.
*Maiyafaru Mubeena bata biyo Faisal ba*
Tun ƙawayenta na wajen aiki ba su lura da damuwar da take ciki ba, har suka fara ankarewa, Aminiyarta Labiba ce ta biyo ta har gida don jin maiyake faruwa.
Kasa riƙe kanta ta yi, cikin kuka take bata labarin duk abinda ya faru tun farko.
"Labiba tsakanina da Halime taimako ne kawai, banda haka ko abinci bazan iyaci a kwanon da ta ci ba, Salmanu shi kanshi kawai So ne ya jani da kuma kyawunshi,sannan don rashin adalci Faisal ya ce zai kawomin yarinyarta gidan nan tayi rayuwa da ƴaƴana bazan jure ba Labiba" ta ƙarasa faɗa cikin kuka har cikinta na motsi
" Mubee duk laifin kine, Ni gaskiya shi yasa ko taimakon su bana son yi, saboda ƙyanƙyamin su ke bani,yanzu Mubee har akwai abin so a kyawun talaka, Ni dai shawarar da zan baki tun da su ƙwaɗayayyune da har zasu iya bawa wanda ba su sani ba ƴar su, to sai ki wofintar da ita, nasan bazatafi ƴaƴanki komai ba, ƙarshe ki haɗata da talaka ɗan uwanta suyi aure ko cikin ma su yimiki hidima ne,dama kin san basa wuce 15-16 suke aure,yanzu ki nuna mishi kin amince ki dawo da soyayyar ku, ko ya ya kika gani?"
"Labiba ki na ganin Faisal zai amince na aurar da ita kamar yanda kika ce?"
"Eh mana, kuma banga amfanin zamanki anan ba Mubee,ki bishi Abuja ku zauna tare Ni dai shine shawarata"
Sosai ran Mubeena ya yi fari tas. Bayan tafiyar Labiba ta shirya cikin kwalliya mai kyauwun da ta kwana biyu batayi ba.
Murmushi Faisal ya yi, ya kuma karanci makircin da aka ɗora Mubeena akai,tsaf yagama sauraron magiyarta, na ya yafe mata ta amince ya kawo ƴar Halime, amma tanaso idan ta haihu ta koma Abuja saboda kar wani a gidan su ya ankaro da zaman ƴar Halime a gidan.
A karo na biyu ya ƙara sakin murmushi, tabbas Mubeena ta Manta Suraj Abdallah Bari ne Mahaifinshi, idan banda haka bazata soma wannan wasan kwaikwayon da shi ba, da mamaki ya bi bayanta da kallo, idan tarin dukiya ne yake sawa ka ɗora tsanar duniya akan talaka dan zai raɓeka, ai shine ya kamata yaji wannan tsanar ba Mubeena da Ubanta ya ke yaron ɗan ƙaninshi ba(Maysarah) ya ƙi ya nemi asalin gumin shi sai raɓe-raɓe ajikin ƙaninshi da ɗan ƙaninshi. Cikin makirci sai da yasan yanda ya yi Maysarah ya bashi wani yanki na Business ɗin shi yake kula da shi, shi yasa ya ɗora buri kan sai Maysarah ya auri ƙaramar ƙanwar su Mubeena, amma take wannan abun tabbas zai bata mamaki da sai ta yi kuka da kanta.
Sarai taji sanda Bala ya zo ya sanar da shi Mutuwar Halime, amma saboda kawai kalmar rakaɓa ƴarta da Halime ta roƙa a cikin rayuwar su, duk da Mijinta ne ya buƙaci haka, sai tayi biris ta nuna kamar bata gane abinda Bala ya sanar da Faisal ba.
Faisal da ya fita iyawa shima sai ya basar yaciga da harkokinshi, kafin Bala ya dawo su fita tare, batare da ya nuna mata ina zasuje ba,kuka tasanya mai ƙarfi bayan fitar su, ta tabbata kenan ƴar Halime sai tayi rayuwa da su?...✍🏻