BURINA

Book 1

by @oumfatima33

*BURINA*


        _Na_


  *Oum Fatima*

   

    _{Sahibar Hausa}_


  *_HAUSA WRITERS ASSOCIATION_*


   _(Take:- Don cigaban Adabin Hausa da al'ummar Hausa)_


*Da yaren Hausa ka ɗai muke rubutun mu, ba ma sirkawa da kowanne yare, kishin yarenmu ka ɗai muke yi, ba ma aron yaren wasu, kowanne yare kishin yarensa yake yi, Hausa/Fulani tushen mu.* ```Hausa writers association ta Hausawa ce```


 *GODIYA.*


_Yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kowa mai komai wanda ya bani ikon rubuta littafin BURINA, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad S A W da iyalan gidansa da sahabbansa da wad'anda suka yi imani da gaskiya._


_Bisimillahir raha'manin Rahim._


*Page 1*


Katsina State, Dutsimma Local Government. Y'an daka Primary School.


K'arfe 12:30am ya yi dai dai da kaɗa k'ararrawar tashin daliban da aka yi a makarantar, ko ina ka hanga daliban ne ke tururuwar fitowa daga ajujuwansu don tafiya gida. Ahankali take saukowa daga saman matattakalar ajinsu tana waige - waige da alama da abin da take nema, ahankali ta sauke ajiyar zuciyar jindaɗin ganin ta ba tare da ta sha wahalar nemanta ba kallonta ta yi tare da cewa "Yauwa Azima mu yi sauri mu tafi gida na baro Ummana bata jin daɗi yau sai na koma zan d'aura abinci."


"Subbahanallah mene ya sami Umman?"


Mubina taja ajiyar zuciya tare da bayyanar damuwa a kan fuskarta alamun ciwon mahaifiyar nata na damunta, cike da rauni ta amsa "Jikinnata ne ya motsa.


"Ya salam, Allah ya bata lafiya."


"Ameen."


Ta amsa tana shafa idanunta da hawaye ya kusa zubowa. Suka ci gaba da tafiya jikinsu a sanyaye, har suka k'araso in da zasu rabu, k'awarta Azima ta fara shigewa da yake unguwarsu ɗaya kuma a layi d'aya suke gida hudu ne a tsakanin su. 


A natse ta shiga zauren gidansu d'auke da sallama kafin ta karasa shigewa cikin madai-daicin tsakar gidan da yake a tsaftace an ajiye komai a muhallinsa babu alamar datti, daga cikin baranda ta hango mahaifiyarta kwance akan shimfiɗa ta yi matashin kai da filo tana barci sallamar da ta kara yi a karo na biyu ita ta farkar da mahaifiyarta ta ta amsa mata a hankali tare da cewa "Mubeena har kin dawo?"

"Eh na dawo Ummana."


Ta amsa a hankali tare da cewa "Ya jikin naki, kinji sauki?"


"Alhamdulillah, naji sauki Mubeena."


" Allah ya karamaki lafiya da nisan kwana."


" Ameen ."


"Yawwa Umma ina Abdulhalim."


"Kinga tun d'azu na aikeshi bakin kasuwa yayo cefane inkin dawo ki daura abinci ban samu na yi ba, amma tamkar an aiki bawa garinsu."


"Ok Umma bari in cire uniform sai in bishi na am...


Sallamar da aka yi ita ta hanata ƙarasa faɗar abin da ta yi niyya Abdulhalim ne ya shigo hannun sa d'auke da leda, karasowa ya yi ya aje ledar yana fadin "Wash Allah na."


 Mubeena ta kalleshi tana cewa "To uban shiririta aina katsaya tun ɗazun umma ta ce ta aikeka amma sai yanzu kake dawowa?."


" Kai Ya Mubeena nifa ba in da na tsaya kawai masu wasan biri na gani shi ne fa na tsaya na kalli kaɗan."


"Uhm Allah ya shiryeka."


Ta furta cikin doka masa harara sannan ta shige d'akin da yake mallakinta. d'akin madai - daici ne mai d'auke da karamin gado da sip mai biyu na ajiyar kayan sawarta sai mirror mai d'auke da kayan kwalliyar yar matashiyar budurwar , k'asan d'akin cafet ne malale, komai dai tsaf tsaf masha Allah.


Ta ajiye jakar makarantarta a saman table din da take home work ta karasa wurin sip d'in ta ta bude ta d'auko kayan da zata sauya doguwar rigar atamfa ce dinkin A shape, ta saka ta d'auko hula ta saka a kanta dan bata damu da daura kallabi ba, ta fito ta nufi madai - daicin kitchen ta duba gas taga ya kare ta dauko murhun gawayi ta zuba gawayi ta kunna wuta ta d'aura ruwa yana tafasa ta wanke shinkafa ta zuba sannan ta nufi gyaran kayan miya acikin abin da bai fi awa biyu ba ta kammala dafa shinkafa da miyarta ta yanka salad ta haɗa komai tsaf kamar ba karamar yarinya yar shekara sha biyu zuwa sha ukku ba dan yanzu ne take ajin karshe a makarantar primary school su ne zasu fita zuwa makarantar secondary wato J S S. 


Ba yi ta shiga ta d'aura arwalla ta shige d'akinta dan yin sallar azahar domin tuni Umman ta shige dakinta dan yin nata, Abdul kuma ya tafi masallaci, bayan sun idar suka yi zaman cin abinci gaba ɗayansu a kwano d'aya suke cin abincin, wannan itace aladarsu basa raba kwanon abinci sai dai in wani ne baya nan acikin su, bayan sun kammala sun sha ruwa Umma ta umarcesu su tashi su yi shirin tafiya islamiya har Abdul tunda ya ji sauki dayake shima ya tashi da dan zazzabi, shi ya hanashi zuwa makarantar Boko amma da yasha magani akamasa allura yanzu shi ke nan ya ware shi nefa har aka aikeshi yo cefane.


"To Umma ."


Suka amsa a ladafce, daga nan kowa ya shige d'akinsa itama Umman d'akinta ta shige a madai - daicin falonta ta dan kishingid'a a saman doguwar kujera wato 3 sitter dan ta huta domin har yanzu jikin nata ba kwari kawai tana daurewa ne sabo da damuwar da yaranta ke shiga da zarar sun ganta a kwance sannan da tasha magani taji sauki ba laifi amma har yanzu tana jin kirjinta na mata zafi da yake tana fama da (chronic ulcer) da hawan jini amma ulcer tafi matsa mata dan in ta tashi sai ta yi kamar ba zata rayu ba shi ya sa yaranta suke shiga matsananciyar damuwa saboda ita kaɗai garesu mahaifinsu Allah ya masa rasuwa da jimawa.


Mubeena ce ta fito daga d'akinta shirye cikin uniform arsh color, Riga da wando da kuma Hijab.

D'akin umma ta lek'a dan yi mata

Sallama tarussuna ta ce "Mun tafi Umma."


"Adawo lafiya, Allah ya bada sa a."


"Ameen Ummanmu."


Jerawa suka yi ita da Abdul suka wuce a hanya suka had'u da Azima da k'annen ta Umar da Maryam. Tafiya suke yi cikin natsuwa suna hira har suka k'arasa Makarantar DARUL QUR'AN da ke a bayan layin su. Suna isa kowa ya nufi ajinsa. Mubeena da Azima ajinsu d'aya . Abdul da Umar ajinsu d'aya sai Maryam ita ce ajinta daban.


Kowa na shiga malamin su ya shigo suka fara karatu cikin maida hankali.


*Oum Fatima ce.*

_(Sahibar Hausa)_




BURINA


   _Na_

*Oum Fatima*

_(Sahibar Hausa)_


 *_HAUSA WRITERS ASSOCIATION_*


   _(Take:- Don cigaban Adabin Hausa da al'ummar Hausa)_


*Da yaren Hausa ka ɗai muke rubutun mu, ba ma sirkawa da kowanne yare, kishin yarenmu ka ɗai muke yi, ba ma aron yaren wasu, kowanne yare kishin yarensa yake yi, Hausa/Fulani tushen mu.* ```Hausa writers association ta Hausawa ce```


Page 2


Bayan an tashi a makarantar, gida suka wuce. Suna zuwa, alwala suka nufi yi , Abdul ya wuce masallaci, su kuma ɗaki suka nufa dan gaba tar da sallar magrib.


Bayan sun idar , suka yi zaman cin abincin dare. 

Suna kammalawa, suka yi sallar isha'i. Zaman hira suka yi zuwa karfe 9:30pm Umman su ta umarce su da kowa yaje ya kwanta, akwai makaranta gobe."

To suka ce kowa yana kokarin shigewa dakinsa. Itama Umman ɗakinta ta shige ta yi shafa'i da wutur, ta yi addu'a, ta kwanta.


Bayan shigar Mubeena ɗakinta sai da ta duba littafinta na makaranta kasancewar, ta mai san karatu kuma tana ganewa sosai take maida hankali sabo da tana da Buri, a rayuwa da take san Allah Ya cika mata shi, bayan ta gama ta yi addu'a ta haye, gadonta. 


Washe gari bayan ta yi sallar asuba fitowa, ta yi ta nufi ɗakin Ummansu, da sallama ta shiga ta gaishe ta, tare da tambayar ta jikinta. Zaman yin karatun Qur'ani, suka yi. "Wannan ɗin koyarwar mahaifinsu ce, tun yana raye. Kullum bayan sallar Asuba kowa zai ɗauko qur'ninsa ya ƙara masa, in ya hadda ce na baya, Har yanzu ba su daina ba, Ummansu ce taci gaba da koya masu."


Bayan sun tashi karatu fitowa ta yi waje, ta yi duk wani aikin da ta saba. Bayan ta kammala, wanka ta yi, ta yi shirin makaranta bayan sun karya ta wuce tare da Abdul. 


A hanya suka hadu da su Azima suka wuce.


Kwanci ta shi ba wuya a wurin Allah, ahankali kwanaki suka riƙa shuɗe wa. Sai ga shi har su Mubeena sun gama, Primary ɗinsu, har sun shiga Secondary, a yanzu haka suna aji ukku, wato J S S 3. Masha Allah sun fara zama 'yammata dan sosai, makerin budurci ya fara kera su, mussaman Mubeena da ta kasance doguwa kuma kyakykyawar gaske ga nutsuwa da sanin ciwon kai. Dan kwata-kwata irin wannan rawar kan na 'yammata, farkon balaga bata yinsa kuma ba ruwanta da kowa, harkar gaban kawai take yi. Shi ya sa samarin anguwa dama wasu daga cikin yaran sa'anninta, suke mata kallon mai girman kai.


Note

*(Mutane da yawa, basa bam-bance, tsakanin girman kai, da kamun kai. Sai kaga da yarinya ta kama kanta bata irin ballagazancin nan a titi da kule-kule shi ke nan, sai akira ta mai girman kai. Ni dai a ra'ayina da akira ki ballagaza, gwara ace kina da girman kai. Dan duk mutum mai ilimi da sanin ciwon kansa, idan ya kalli mu'amalarki, ya san tsabar natsuwa ce da kamun kai)*.


Ashirye ta fito daga dakinta, cikin shigar Uniform ɗin ta Riga da Wando blue sai farin hijab kal-kal da shi, yasha guga, farar safa ce akafafunta, da baƙin takalmi, Tom's, sai bakar jakar goyo da ta goya, sai ƙamshi take.


Dakin Ummansu, ta nufa dan yi mata sallama. A natse ta shiga cikin ɗakin. Akan kujera one Seether, ta samu Umman tana kallon Tashar Arewa 24, suna shirin, gari ya waye.  


"Umma na fito, ta faɗa."


"To Allah ya kiyaye, cewar Umman tana miki mata kuɗin Makaranta. Tare da yi mata adawo lafiya. 


Fitowarta ya yi dai-dai, da shigowar Azima da ta biyo mata, “yauwa gwara da kika shirya da wuri dan yau ban shirya cin dukan latti ba”. Cewar Mubeena.

“ Ki bari ke dai, ai jiyannan, na daku Shi ya sa yau ko barci ban koma ba”. Cewar Azima tana kokarin shigewa, ɗakin Ummansu ta gaishe ta.


Tana fitowa suka wuce kai tsaye bakin titi suka nufa , adaidaita sahu suka tsayar suka hau, yaja suka wuce. Suna zuwa suka samu, an kaɗa assembly. Hamdala suka yi suka bi layi, bayan kammala aka sallame su kowa ya nufi hanyar ajin su. Suna tafiya suna hira da kawayen su har suka ƙara sa, bayan shigar su hira suka dasa, irin ta yammata masu tasowa, wadda bata wuce ta samari. Da yake sun kusa zana jarabawar J S C E ɗinsu shi ya sa ba sosai, ake masu karatu ba. 


Sai revision, har aka tashi, malami ɗaya ne ya shigo yai masu revision, aka tashi. Fitowa suka yi bakin gate dan samun abun hawa, amma shiru kamar an yi ruwa an ɗauke. Yau masu adaidaitan basa wuce wa. Ko da wani yazo wucewa, zaka samu acike yake. Kuma gashi sun bari duk boss sun cika sun tafi. Dayake basa san hawa boss, sunfi san adaidaita sahu wanda zai kai su har kofar gida. Gajiya suka yi da jiran suka fara takawa a natse sun kawo dai dai wata inuwar bishiya, Mubeena ta ce "gaskiya na gaji, mu tsaya inuwar nan, mu sami a bin hawa"  


"Ok! Mu tsaya ɗin, ni ma na gajicewar Azima”. Wuri suka samu suka tsuguna, suna magana kasa-kasa.


Tun daga nesa ya hango 'yan matan, sanye da uniform. Kuma nan take dayar ta dauke hankalinsa, yaji yana kokarin narkewa akan, kujerar motar da yake, tsabar shaukin da ya shiga. "Ganin yana kokarin sakin motar zai kaɗe su a banza ya sa shi faɗin kai “ wai me kake kallo? Sai ka zubar da mu?" Zabura ya yi ya rike sitiyarin motar yana sauke ajiyar zuciya. “Abokina gamo na yi.”

Gamo kuma ? Kamar ya?" 


Cewar abokinnasa. 


“Gamo da kyakykyawar halittar da ta sace zuciya ta alokaci ɗaya na ji ina ƙoƙarin zaucewa akanta.”


“A ina kenan?”


Kalli can! Ya faɗa yana nuna masa ƙasan bishiya. 'Yan mata ya gani, guda biyu sanye da uniform. Kuma nan take, ya ga ne wace ta zauta abokinsa, akallo ɗaya. Dan ba karamin haduwa ta yi ba, ta fita da ban.


Dukda kuwa karamar yarinya ce, dan bajin, tafi 15 ko 16. Amma Allah ya mata wani irin kwarjini!, Akallon fiskarta da ya yi, kawai yaji yana shakkar tararta. Jin yana kokarin, tsayar da motar ne ya sa shi dawowa daga tunanin da ya tafi.


"Me kake ƙoƙarin yi ne wai Mansoor?"


"Mu tafi mana."


Ina ba zan iya wucewa ba tare da na mata magana ba.

"Hmmm"


Ya fada yana kallon sa. Ƙoƙarin tashi suke su wuce suka ga wata haɗaɗdiyar mota ta tsaya a gabansu wucewa suka yi, ƙoƙari ya yi ya buɗe motar ya fito ya nufe su da sallam. 


Yana tsaya wa a gabanta, ya ji duk ya ruɗe ya ma rasa abin fada. Ganin zata tafi ne ya sa shi karfin halin fadin “ ƙanwata in ba damuwa kuzo mu sauke ku man”

“A'a mun gode” cewar Azima dan tasan Mubeena ba za ta, taɓa shiga ba. Ai kuwa dai tuni ta yi gaba, ba tare da ta ko kalli mutumin da ya masu tayin shiga motar ba. Da kallo ya bita kamar wani soko, sai da Habib ya masa magana tukun ya dawo hayyacinsa, “mu tafi Mansoor dama nasan baza ta saurareka ba”. Dan ni kallo ɗaya na mata naji kwarjininta ya sa mini shakkar tararta.


Suna yin gaba suka ci sa'ar samun abun hawa, suka wuce gida.


Na san masu karatu zasu so sanin asalin Mubeena. In sha Allah za ku sani ku dai kawai ku ci gaba da biyo ni.

Mu hadu a page na gaba.


*Oum Fatima ce*

_(Sahibar Hausa)_






BURINA


    _Na_

    *Oum Fatima*


_(Sahibar Hausa)_


 *_HAUSA WRITERS ASSOCIATION_*


   _(Take:- Don cigaban Adabin Hausa da al'ummar Hausa)_


*Da yaren Hausa ka ɗai muke rubutun mu, ba ma sirkawa da kowanne yare, kishin yarenmu ka ɗai muke yi, ba ma aron yaren wasu, kowanne yare kishin yarensa yake yi, Hausa/Fulani tushen mu.* ```Hausa writers association ta Hausawa ce```


* FREE BOOK *


_Page 3_


Wace ce Mubeena?


Malam Yusuf shi ne mahaifinta, haifaffen gari Dutsimma ne anan iyayensu suka haife su. Su uku iyayensu suka haifa.


Malam Ahmadu da Furera, su ne iyayensu da suka yi auren saurayi da budurwa.


Malam Ahmadu yana da rufun asirinsa dai-dai gwargwado. Domin kuwa manomi ne, yana noman amfanin gona, kama daga, Gero, Dawa, Masara, Shinkafa, Wake, Alkama, Waken suya, Ridi, Gyada. Da sauransu.


Kuma Alhamdulillah, yana samun amfani sosai Allah ya sa masa albarka acikin, noman sa . To a haka suke rayuwa da matar sa cikin rufin asiri. In lakacin damuna ya yi zai yi nomansa in amfani yazo gida zai kai kasuwa ya sayar da wasu daga ciki, wasu kuma ya ajiye a gidansa.


Cikin ikon Allah, a haka yafi karfin buƙatun gidansa, har ma yana taimakon mara sa ƙarfi.


Kasancewar sa, mutum mai matukar kyauta da taimakon wanda ba shi da shi. Shi ya sa mutane suke girmama shi, suke matukar ganin girman sa a anguwa. Dan kuwa yana taimaka masu sosai abinsa bai tsone mai idanu ba, shi ya sa yake da jama'a sosai.


Kuma Alhamdulillah yana zaman lafiya da kowa.


Ana haka, Allah ya ba matar sa Furera, karuwar samun ciki sun yi matukar farin ciki, sosai.


Lokacin da cikin ya isa haihuwa, ta haifi ɗanta na miji. Sun yi murna sosai, kuma mutane sun ta ya su murna sakamakon jinkirin, samun haihuwa da suka yi, dan sai da suka shekara goma da aure sannan Allah ya nufe su da samun haihuwa. Ranar suna yaro yaci suna, Muhammad Abubakar.


Haka sukaci gaba da rainon sa cikin kulawa shiru basu ƙara samun haihuwa ba, sai bayan shekara hudu, sannan Furera ta kara haihuwar 'ya mace, aka sa mata suna Aisha.


Rainon yaransu suka yi, cikin kulawa da tarbiyya. Sai bayan shekara shidda, har sun fidda rai Allah ya kara basu rabon haihuwar da na namiji, aka sa masa suna Yusuf.


Rainon yaransu uku, suka ci gaba da yi, alokacin Abubakar da Aisha duk suna zuwa makaranta.


**********


Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, ahankali kwanaki suka riƙa shuɗe wa, rayuwa na sauya wa." 

Abubuwa, sun faru masu daɗi da akasin sa. Malam Ahmadu na ƙara samun ci gaba a harkokin kasuwancin sa. Dan sosai yake samun ci gaba a harkokin arziki na karuwa, yaruwar su na ƙara sauyawa.


Sai gashi har Abubakar, ya kammala karatun Jami'arsa da taimakon Allah, da kulawar iyayensa. In da ya karanci medicine, yanzu haka cikakken likita ne, yana aiki a cikin garin Katsina.


Kuma a can yake zaune da iyalinsa, in da ya auri matarsa hajiya Maryam. Yar Katsina ce, iyayanta 'yan boko ne kuma wayayyu. Sai dai, kuma suna da ilimin addini, shi ya sa wayewar ta su ta kasance mai tsafta.


Anan yaci gaba da rayuwa, da iyalinsa sai dai yana zuwa Dutsimma wurin iyayensa da girma ya fara kama wa kuma yana kula da su sosai, don sai da ma yace zai ɗauke su, su koma Katsina amma suka ƙi yarda.


Yanzu haka Allah ya azurtasu, da haihuwar yara hudu.


Babban dansu mai suna Imrana, sai Marwan, sai Kalifa wanda yaci sunan kakan su wato malam Ahmadu suke kiran sa Kalifa, sai auta Abiha, sai Aisha, da yara suke kira, da Mamy. Ta yi karatu itama ta karanci Nursing(Aikin jinya). A yanzu haka ta yi aure a Kano. In da ta auri wani babban ɗan kasuwa. Sun haifi yara, biyu Hammad da Nusaiba, sai Yusuf, Shima ya yi karatun, amma shi fannin Education ya karanta, dan yana son koyarwa. A yanzu haka yana koyarwa, a makarantar Secondary ta Maza, a nan Dutsimma.


In da ya auri matarsa, 'yar ƙawar mahaifiyarsa, mai suna Sumayya.


Suna zamansu cikin so da ƙauna, da kuma tsantsar kulawa.


Haihuwar su ta farko, Allah ya azurtasu, da samun 'ya mace, kyakykyawar gaske, fara ƙal, mai kyawawan idanuwa, masu ɗaukar hankali tun tana jaririyar ta kuwa, wasu irin idanu ne Allah ya bata, masu tsananin kyau, da fisgar

 hankalin mai kallon su.


Farare ne ƙal kamar takarda, sannan kwayar cikin ta kasance lite blue, kalar sararin samaniya. In ta Buɗe su, har wani sheƙi suke yi, masha Allah!


Sannan duk wanda, ya gani sai ya tanka, damma bata fiya , buɗe su ba. Shi ya sa, mahaifiyarta, ta dage da yimata, azkar safe da yamma, sabo da bakin mutane.


Ranar suna aka sa mata, suna Mubina. Su Mamy Aisha duk sun zo, iyalan Daddy Abubakar ma sun zo shi ne dai bai samu zuwa ba sakamakon aiki da ya taso masa a asibiti amma ya bada kyautar baby an kawo kuma yace “zai zo daga baya yaga baby”, sabo da akwai matuƙar haɗin kai, da shakuwa, a tsakanin 'yan uwan, kuma duk ƙoƙarin iyayensu ne.


Tunda Imran ya ɗora idanu akan babyn, yaji ta shiga ransa yana mata so matuƙa, har yana cewa Momyn sa, shi dai da Baby zai tafi Katsina, ba zai barta ba. 


Mamaki ta yi sabo da kasancewarsa mara san magana. Dika-dika Shekarar, sa goma sha daya zuwa sha biyu. Amma miskilin, gaske ne, ba shi da yawan magana, yana da kamewa, da rashin hayaniya irin na yara. Amma fa akwai zuciya, dan in ya yi zuciya, har shiɗewa yake.


Bayan, haihuwar Mubeena da shekara biyu Allah yayi wa mahaifinsu malam Ahmadu rasuwa. Sakamakon ciwon cikin da ya yi fama da shi.


Sun shiga damuwa, sosai amma ba yadda zasu yi, sai hakuri.


"Allahn da ya halicce shi ya fisu son sa, kuma mutuwa rigar kowa, shi da ya tafi bai yi sauri ba, dan kowa lokacin sa yake jira, in ya yi dole ka amsa, kira ko, baka shirya ba. Kullu nafsin za'katul maut.(ko wanne mai rai, sai ya ɗan-ɗani mutuwa).

"Allah Ya sa mu cika da imani ya jiƙan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya ameen."


Bayan Furera ta gama, takaba, Dady yaso tafiya da ita Katsina amma ta kafe, in da malam ya mutu, itama a nan zata mutu. Dole ya hakura, amma yana kulawa da ita sosai, sannan ɗan uwansa ma yana bakin ƙoƙarin sa.


A kuma lokacin ne Umma Sumayya ta haifi Abdulhalim, tun daga shi kuma bata ƙara haihuwa ba.


Ba su ida ware wa daga mutuwar mahaifinsu ba, aka wayi gari da mutuwar, malam Yusuf sakamakon hatsarin da ya yi ahanyar dawowar sa daga makaranta, yana kan lifan ɗinsa mota ta bige shi. Shi ke nan, mutuwar kenan, mutuwar da ta girgiza gaba ɗaya ahalin. Suka shiga tashin hankali dan Sumayya kusan zaucewa ta yi, sai da ƙyar aka samu kanta. Amma tun daga nan, yawan damuwa, ta aure ta wanda, hakan ya haifar mata da hawan jini, da Ulcer, sabo da rashin cin abinci. Yaranta sun shiga damuwa sosai, dukda kuwa basu da wani isashshen hankali. Dan duka Mubeena Shekara takwas alokacin, Abdul nada shida.


Bayan abubuwa sun lafa, sukaci gaba da rayuwa, a ƙarƙashin kulawar dady. Dan shi yaci gaba da ɗaukar ɗawainiyar su baki ɗaya. Sannan dama Umman tana sana'ar haɗa kayan snacks, ana bata kwangilar haɗa na taruka, kamar biki, Birthday party, walima da dai sauransu. basu da wata, matsala sai ta kewar malam Yusuf.


Mubeena nada BURIN zama likita, tun tasowar ta. Sabo da rashin lafiyar maman ta da take fama. Dan in ta motsa mata ba ƙaramin wahala take sha ba, musamman Ulcer ɗin tafi takura mata.


Shi ya sa ta dage da karatu, ba wasa sabo da in suna hira da ummanta, tana faɗa mata BURINTA. Takance mata, sai ta dage ta yi karatu sosai, zama likita ba na ragwaye ba ne.


To shi ya sa, ta riƙe wannan a ranta.


Takance mata “Umma ina so in rinƙa kula da ke, in ciwanki ya tashi”.


Sai ta ce mata, “to Mubeena Allah ya nuna mini, lokacin da rai da lafiya.!!”


```Wannan shi ne asalin su, mu haɗu a page na gaba, dan jin yadda zata kaya.```


_Please comment and shere._


*Oum Fatima ce Sahibar Hausa*






BURINA


Na 


Oum Fatima


_(Sahibar Hausa)_


 *_HAUSA WRITERS ASSOCIATION_*


   _(Take:- Don cigaban Adabin Hausa da al'ummar Hausa)_


*Da yaren Hausa ka ɗai muke rubutun mu, ba ma sirkawa da kowanne yare, kishin yarenmu ka ɗai muke yi, ba ma aron yaren wasu, kowanne yare kishin yarensa yake yi, Hausa/Fulani tushen mu.* ```Hausa writers association ta Hausawa ce```


*FREE BOOK *


_Page 4_


*Dawo wa daga labari*


Sannu a hankali suka cigaba da karatunsu cikin kwanciyar hankali da tarin nasara don ayanzu haka Mubeena ta sauke Al-qur ani mai girma da wasu daga cikin littattafai. 


Abangaren boko kuwa suna ajin ƙarshe nan da wata uku masu zuwa za su zana jarabawar SSCE ɗinsu. 


Sai fatan ayita cikin nasara. 


Mubina ta zama cikakkiyar budurwa kuma 

Kyakykyawar gaske don kyawun nata har tsoro yake ba ummanta shi ya sa akullum take addu'ar Allah ya tsaremata ita daga sharrin mutum da aljan. 


Abangaren samari kuwa ba sauƙi don Allah ya bata farin jinin su tumma bata kai haka ba. Damma tana da matuƙar kamun kai ne shi ya sa take masu kwarjinin da ba kowa yake iya tarar ta da maganar so ba. Sai dai su dami kawar ta Azima da kamun kafa awurin ta. 


Saurayi daya ne yake damunta da naci ako da yaushe kuma yake iya mata magana kai tsaye. Dukda kuwa shima ya daɗe sosai yana bibiyarta kafin ya iya tunkararta. Kuma har yanzu ba wani kulashi take ba. Amma a haka yake naci, shi burinsa a ko da yaushe ta kulashi ta ba shi dama komai ƙanƙantar ta shikuma zai yi amfani da baiwar da Allah ya ba shi ta tsara kalamai ya yi wuf da zuciyar ta.


Amma har yanzu bai da ce ba, bai kuma fidda rai ba.


Mansoor kenan. Shi dai Allah ya jarabce shi da matsananciyar ƙaunar ta tun da ya ɗoura idanu akan ta ta gama da zuciyar sa. Yaji yana matuƙar ƙaunar ta kuma zai iya sadaukar da komai a kanta. 


Dan yadda take nuna wa bata san da shiba abin yana ƙoƙarin zarar da shi. 

 Ji yake kamar zaiyi hauka dan abin bai kama shi da sauƙi ba.


Kullum addu'a yake a kan Alla Ya mallaka masa ita yana kuma kamun ƙafa a wurin Azima da kuma Abdulhalim.


 


Duk sanda Azima ta mata magana akan rashin kula samari takan ce da ita. 


“Kinfi kowa sanin burina arayuwa Azima. Karatu nake so in yi karatu kuma mai san nutsuwa ta da kuma maida hankali sabo da karatun likata yana san nutsuwa ne da kuma maida hankali sabo da kula da rayukan al'umma ne.


Kinga kenan kule-kulen samari ba nawa ba ne matuƙar ina son cika BURINA. Sabo da haka na roƙe ki ki rabu da ni da maganar samarinnan please ta faɗa tana haɗe hannuwan ta alamar roko”.


Azima tace ”amma ai Mansoor yace zaki yi duk irin karatun da kike so a ɗakin sa shi zai tsaya maki kuma kin san zai cika alƙawari tun da yana matuƙar ƙaunar ki sannan kuma zai tsaya maki ya ɗauki nauyin karatun, tun da kinga dai ɗangata ne awurin iyayensa sannan kuma suna da kudi”.


Wani irin kallo take binta da shi mai dauke da jin haushi a hankali ta ja tsaki sannan. “To ni ban shirya ba, ban shirya yin aure ba sai na cika BURINA na zama cikakkiyar likita sanan, sabo da haka ki saurara mani da maganar mutuminnan please”.


Azima tace “to shi ke nan Allah ya zaɓa mana abin da yafi alkairi Ameen”.


Waye Mansoor.


Sunan mahaifinsa Alhaji Nafi'u maifiyarsa hajiya Salma.


Asalinsu yan dutsimma ne amma a Katsina suke da zama.


Mahaifinsa Alhaji Nafi'u ɗan siyasa ne a yanzu haka yana rike da mukamin sanata ne a nan Katsina. 


Mansoor shi ka ɗai Allah ya ba su, shi ya sa suke matuƙar son sa suka rai ne sa cikin gata.


A America ya yi karatun sa in da ya karanci lawyer, ayanzu haka cikakken lauya ne mai zaman kansa.


Yana da kyau ba laifi dan fari ne yana da tsayi ba can ba ɗan dai-dai wa daida dai bashi da laifi. Sannan dan gayu ne sosai ya iya ɗaukar wanka.


Yana da san rayuwar jin daɗi da facaka da kuɗi. Dan antara masa kuma shima yana ɗauka ba laifi.

Komai yake so yana samu. Abu ɗaya ne yake wahalar da shi a rayuwa itace soyayyar Mubina.


Ahalin yanzu ba shi da wani Buri da ya wuce mallakar ta.


Wanna kenanan.

 


ABUJA


************************* 


Zaune yake akan lafiyayyen gadonsa da ya sha shimfiɗar tsaftataccen farin zanin gado, ƙafafunsa amike suke da laptop ɗin sa a sama yana ta faman danne-danne. Ya yi nisa acikin abin da yake yi ɗin.


Da alama abu yake mai mahimmanci. Yafi awa ɗaya yana aikin kafin ya rufe laptop ɗin ya ajiye a saman bed side loca.


Saukowa ya yi daga saman gadon ya nufi wata ƙofar, banɗaki ne ya tura ya shige bakinsa dauke da addu ar shiga banɗaki, bai fi minti biyar ba ya fito ɗaure da arwala yanufi wurin da yake ibadar sa ya shimfiɗa darduma ya tada sallah.


Shafa'i da wutur ya yi, ya yi addu'o'insa ya tashi. Fitowa ya yi madaidaicin falon nasa da yake a tsaftace komai a muhallinsa babu alamar datti sai tashin sassanyar kamshin air freshener ke tashi sai kuma sanyin AC da ya sanyaya fallown.


Dining area ya nufa ya bude fridge ya dauko robar ruwa ya ɓalle marfin ya kafa kai.


Yasha yafi rabi sannan ya ajiye a saman dan madaidaicin dining table ɗin da ke awurin mai ɗauke da kujeru hudu. Fallown ya dawo ya kashe katuwar plasma da ke aiki a hanki ba wani sauti sosai, wutar ko ina ya kashe sannan ya nufi ɗakin sa.


Gadonsa ya haye ya yi addu'ar sa ya ja bargo.


IMRAN MUHAMMAD ABUBAKAR kenan wanda abokanen sa suke kira da IM.


Jaritaccen jami'in farin kaya ne da yake aiki da hukumar DSS anan ABUJA.


Ɗan kimanin shekara talatin da biyu aduniya.

Kyakykyawan gaske , mai natsuwa sanna ga aji ɗan gayu ne na bugawa a jarida, sannan miskilin gaske. 


Mutum ne mai matukar farin jinin al uma, mai tashen da 'yammata da yawa suke rubin sa. Amma shi ko a jikin sa 


Dan cewa ya ke “shi bai da lokacin wannan shirmen”. Dan aganinsa ɓatawa kai lokaci ne.


Aikinsa shi yafi ba mahimman ci sosai ayayuwar sa. Dan in yariƙe aiki to da ikon Allah sai ya kai karshen sa. Komai kulla kullar da ke cikin ta kuwa. Sabo da haka ake matuƙar alfahari da shi a hukumar su. 


Sannan kuma ya tara mahassada da basa san cigaban sa. Dan aganinsu duka-duka yaushe ya shigo aikin da har zai samu wannan ɗaukakar su suna nan. (Kun san akomai ɗan Adam dole zai samu masoya da makiya hassada ta yi yawa a zuciyar Al'umma da son zuciya kowa kansa kaɗai ya sani ba a san ci gaban wani arayuwa, muna manta cewa komai ka samu aduniyar nan shi ne rabonka, kai baka isa ka hana wani ya samu abin da Allah ya nufe shi da samu ba duk wanda ya nuna zai ja da ikon Allah shi ne a wahala Allah ka tsarkake mana zukatanmu).


Acikin yammatan da suka matso masa kuwa harda yar gwamnan Katsina da ta kasance 'yar aminiyar mahaifiyarsa hajiya Maryam wato Rufaida.


Tana matuƙar ƙaunar sa har kamar zata yi hauka take ji akansa. Dan tun da ta ɗaura ido a kansa taji duniyar nan ba wanda take so sai shi.ta kuma yi alwashin samun sa ko da tsiya ko da tsiya tsiya. Ta fara ganin sa ne wata rana da suka zo gidan ita da mahaifiyar ta anci sa'a yazo gidan dan baya zama a gida sabo da yanayin aikin sa a Abuja yake da zama. 


To alokacin yazo hutun karshen shekara ne ta haɗu da shi sun shigo shi kuma zai shige motar sa zai je su haɗu da abokinsa Samir. Shi ne fa ta tambayi mahaifiyarta hajiya zuwaira waye wannan saurayin da ya fita.


Take faɗa mata “ai babban yaron hajiya Maryam ne baya zama a gida a Abuja yake aiki Jami'in farin kaya ne shi ya sa baku taɓa haɗuwa ba”, ba kunya tace “ita fa taga miji dan tana san sa”. Uwar tace mata “kwantar da hankalin ki ai ba matsala zan yi magana da hajiya Maryam ɗin” shi ne fa bayan sun shiga sun gaisa da tambayar mai jiki da yake dama sun zo duba Abiha ne bata jin daɗi Asmar tace ta tashi. Shi ne take faɗa ma hajiya Maryam cewar Rufaida “ta ga ɗanta tana son sa sai ayi dakan ɗaka shiƙar ɗaka” ta karashe tana murmushi.


Hajiya Maryam ta yi murmushi tare da cewar “ai ba matsala in dai sun dai dai ta kansu sai ayi”


Amma a zuciyar ta tantamar amincewar take dan ta san halin kayan ta. 

To shi ne fa tun daga nan take bibiyar sa da naci da kissa da kwarkwasa amma a ban za shi ya daɗe ma baiyi noticing ɗin ta ba har ya koma bakin aikin sa.


Amma bata hakura ba dan har Abuja take binsa da yake baban ta yana da gida acan yana da wata matar, kuma ƙanwar Maman ta ma a can take aure. Shi ne teke zuwa can.


Duk in da ta san zata gan shi tana zuwa har dai ta tare shi take faɗa masa ita yar aminiyar mahaifiyar sa ce sannan yar tsohon gwamnan Katsina. Shi ne fa suke gaisawa sama-sama dan duk yanda ta yi ya bata wata damar da zata nuna masa san da ta yake yi masa ya hana ta damar dan bayan gaisuwa in ta gaishe sa ya amsa mata shi ke nan.


Ita kuma ta yi alkawarin jan hankalinsa tako wani hali shi ya sa ta kira babbar kawarta take faɗa mata halin da take ciki Nadiya tace “ta bari gobe zasu haɗu za su san abin yi”.


Wannan kenanan.


```To ya kuke ganin tafiyar zata kasan ce kudai ku cigaba da biyo ni```.


*Sanan ayi shearing don Allah.*


_Free book ne_


*Sai kun jini Sahibar Hausa*







BURINA 

  

           _Na_


         *Oum Fatima*

_(Sahibar Hausa)_


 *_HAUSA WRITERS ASSOCIATION_*


   _(Take:- Don cigaban Adabin Hausa da al'ummar Hausa)_


*Da yaren Hausa ka ɗai muke rubutun mu, ba ma sirkawa da kowanne yare, kishin yarenmu ka ɗai muke yi, ba ma aron yaren wasu, kowanne yare kishin yarensa yake yi, Hausa/Fulani tushen mu.* ```Hausa writers association ta Hausawa ce```


* FREE BOOK*


 *Page* *5*


########


TALLAH! TALLAH! TALLAH! TALLAH! TALLAH! TALLAH!!!!


Assalamualaikum


Mutane na ina gabatar muku da ingantattun magungunanmu da sukayi fice wurin magan ce muku matsalolinku."


Gasu kamar haka


# Kalolin gumba #


# gumbar dan uban budurwa."


# gumbar dabino da ridi."


# gumbar Madara."


# gumbar saukar da ni'ma da motsa sha'awa."


# kalolin Zuma #


# zumar yar gata."


# zumar exclusive."


# zumar sabon budurci."


# zumar 3 in 1."


# lalata abin kishiya."


# hutar da malaminki."


# hatsabibiyar mallaka."


# set na saukar da ni'ma."


# set na sabon budurci."


# maganin sha da Lipton."


# turaren tsuguno."


# Jigidar mallaka."


# kalolin matsi."


Dama duk abinda kuke buka ta kuma akan farashi mai sauki.

Sannan muna aika wa a duk inda kuke. 


Ku dai kawai ku tuntube mu a wannan No.


***


Sayen na gari kudi a gida.


Sai kunzo.


*************************


Dutsimma


Ashirye ta fito daga ɗakinta cikin shirin tafiya makaranta. Fuskarta kaɗai zaka kalla ta shaida maka tana cikin matuƙar farin ciki.


Kasancewar a yau zasu zana final exam ɗinsu. Shi ya sa take farin cikin zata gama ta shiga babbar makaranta. Wadda ita ce tsani na farko da zata taka ya jata ga cikar burin ta, na zama kwararriyar likita.


Ada sanda tana yarinya, burinta kawai ita dai ta zama likita don ta kula da mahaifiyarta. A yanzu da ta girma ta ƙara hankali sai burinnata ya ƙara girma azuciyar ta fiye da da.


Sakamakon ƙarancin kwararrun likitoci mata da ake fama da shi a yanzu. Abin da bai kama ta na miji ya duba ajikin mace ba amma yake duba wa. Sabo da ba matan sosai ba matan sosai da suka karanci fannin. Dole sai mazan.


Shi ya sa ta yanke shawarar zama kwararriyar likitan mata da izinin Ubangiji. Sabo da tana a jerin mata masu matuƙar kishin 'yan uwansu mata. Sallama ta yi wa ummansu tana ta sauri ta wuce. Umman tace “zo nan, wai kin karya ma?”, “Aa sauri nake na kusa latti umma in mun fito zan je shop sai in saya lemo da biscuit”. “Ok! Allah ya bada sa'a” a cewar umman tana mika mata 1000, “na gode umma sai na dawo” ta faɗa tana wuce wa.


Tana fitowa ta biyama Azima suka wuce. Bakin titi suka nufa zasu tsayar da adaidaita ya faka motar sa a gaban su. Buɗewa ya yi ya fito. Da sallama ya ƙaraso gaban su kallo ɗaya ta yi masa ta ɗauke kai sai dai ta amsa sallamar acan cikin makoshin ta.


Mansoor ne yana kan hanyar sa ta zuwa Katsina zai koma gidan su ne da yake dama wurin kakanninsa yake zuwa nan dutsimman shi ne har ya haɗu da ita. Tun daga nan yake zarya. To yau zai koma ne yaci sa'ar ganinta a bakin titi. 

Ajikinta taji ana mata azababben kallon da ta tsana. Jin da ta yi bashi da niyar dainawa ya sa ta ɗago kai ta zabga masa harara da idanuwannan nata da suke ɗaukar hankalin sa, tace “malam lafiya ?”


 Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi ahankali yace “lafiya lau gimbiyar Mansoor”, wata hararar ta ƙara sakar masa tana ɗauke kai. “Fatan kin tashi cikin koshin lafiya?” Shiru ta masa, yaci gaba da cewa, “ina neman alfarma, abani izinin kai gimbiya makaranta”. Hannun Azima ta ja suna ƙoƙarin wucewa ya sha gaban su yana , haɗe hannayensa alamar roko yace, don alfarmar Annabi Muhammad (s.a.w.) ki ba ni wannan damar. 


Azima ta kalleta tana da cewa “don Allah Mubeena mu shiga ya sauke mu, mun daɗe bamu samu abin hawa ba , kuma ya kamata yaci alfarmar mai daraja da ya roƙa”. Ba Don tana so ba, sai don darajar wanda ya roƙa. Ahankali ta nufi motar , jiki na rawa ya buɗemata gaba." Nan ma sai da aka harare shi sannan aka shiga. Shi dai murmushi ya yi tare da faɗin “thanks”. Sannan ya rufe ya zagaya ɗayan side ɗin. Tuni su hajiya Azima an make a orners kwana tashin motar ya yi suka wuce.


Bayan ya sauke su , kuɗi ya ɗebo masu yawa, ya bawa Azima, yace “su yi break”. Karɓa ta yi tana masa godiya duk da taga hararar da mutuniyar tata ke ma ta. Ita dai tana sauka “thank you” kaɗai ta iya furta masa ta yi gaba amma shi hakan ma ya wadatar da shi. Sai da ya ga shigewar su cikin gate ɗin makarantar sannan ya sauke ajiyar zuciya ya juya ya shige motarsa ya tafi cike da farin cikin kasancewar sa da ita na ɗan lokacin da suka samu a motar duk da ba wata hira suka yi ba.


Suna shiga ta kalli Azima tace, me ya sa kike mani haka? Don me zaki anshi kuɗin sa?” Azima tace “to ya kike so in yi ne Mubeena?” Wulaƙanci dai ba kyau wallahi. Ban za ta ma ta, ta yi gaba zuwa ɗakin da zasu yi jarabawa ɗin. “Oho ke kika sani” cewar Azima kawai anbamu kuɗi sai inƙi karɓa don mugun abin tsiya.


Bayan sun kammala da farin ciki suka fito suna ta sallama da kawayen su da Malaman su. Ana ta ɗaukar hotuna ana bankwana. Dan wata ƙila wani ganin karshe ka yi masa ba lallai ku sake haɗuwa ba. Wasu sai dai kaji mutuwar su wasu bama zaka ji labarin mutuwar ta su ba. 


Da farin cikinta ta dawo gida bayan ta yi wanka da sallah ta ci abinci , ta zauna kusa da ummansu acikin baranda suna ɗan taba hira umman ke ce mata “Mubeena ya kama ta ki shirya kije gidan hajiya ki ɗan yi kwana biyu tun da kin gama jarabawar, don jiya da muka yi waya take tambayar ki, tace ta daɗe bata ganki ba”. “Haka ne umma zanje in sha Allah hajiya Annah tsohuwa mai ran ƙarfe taci zamanin ta , tana cin namu yanzu”. “Ungo nan Mubeena” cewar umma ta ma ta daƙuwa tare da cewa “kema naki iyayen ai za su tsufan in dai ba mutuwa ba”. Mubeena ta canza fuska tana cewa “in sha Allah umma zaku yi tsawon rai tare da mu”.

“Hmmm!”  Cewar ummah. 

Hajiya Furera kakarsu ce ta wurin Uba suna kiran ta da Annah. (Ina fatan kun gane).


“In sha Allah ranar Litinin sai in ta fi ko ummah?”. “Allah ya kaimu", “wai ina Abdulhalim ne?” “Bai dawo ba daga makaranta” “ok ta faɗa”. 

“Yauwa kuma baban ku Abubakar ya kira ɗazu yace in kin huta daga gajiyar jarabawar zai aiko driver ya ɗauke ki kije can Katsinar ki yi kwana biyu”. Ok dama mun daɗe bamu haɗu da Abiha ba.


*************************


Abuja


Karfe 8:00am ya fito cikin shirin tafiya office. Sanye yake cikin wani haɗaɗɗen suit ash colour sai ta cikin fara ce sai baƙin neck tied a wuyansa da baƙin takalmi ƙafa ciki sai ɗaukar idanu suke agogon hannunsa ma baƙi ne na fata ƙirar Italy. Wani irin sihirtaccen kamshi yake fitarwa. Ya yi kyau sosai Masha Allah. Dole 'yammata su hauka ce masa don ya isa ya kai.


Sauri-sauri ya yi break fast don ya kusa latti kuma jiran sa ake a office za su yi wani meeting ne , kuma a yau yake san wuce wa Katsina.....✍🏻


*Please comment ande shere*


```Sahibar Hausa ce```





*BURINA* 


     *NA* 


  *_Oum_* *_Fatima_* 


       { _Sahibar _Hausa_ }


  

 *HAUSA* *WRITERS* *ASSOCIA* 


 { *_Take_* :- *Don* *ci* *gaban* *adabin* *Hausa* *da* *al'ummar* *Hausawa* }


 *FREE* *BOOK* 


 *Page* *6* 


TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!! .


Assalamualaikum, mutane na. Maman Abeel mai kayan gyara, ta shirya tsaf wurin kawo maku duk wasu nau'in kayan gyaran jiki da ma duk maganin matsalolinku. Kuma akan fara shi mai sauki sannan kuma suna aika kayan su a duk inda kuke. Kudai kawai ku tuntube ta a wannan No

 


***


Sayen na gari maida kudi gida.


_________________________


A yau yake san wuce wa Katsina in ya taso office. Don jiya Dady ya kira shi a waya, yake faɗa masa jikin Abiha ya motsa, kuma dama yana son zuwa gidan ya gan su, sannan yana son zuwa Dutsimma ya gano tsohuwa hajiya Annah.


Karfe 1:00 na rana ya fito daga office. Gida ya wuce kaitsaye yayi shirin tafiya KT. A shirye tsaf ya fito acikin shigar wani lallausan farin yadi ɗinkin zamani, daya yi matukar karɓar sa.


 Kansa ba hula sai tattausar baƙar sumar sa da tasha gyara sai sheki take, ƙafafun sa sanye cikin haɗeɗen bakin takalmi, sai agogon hannun sa ma ya kasan ce baki, sassanyan ƙamshin turaren sa mai sa nutsuwa yake fitar wa.


Agogon da ke hannunsa ya kallah ƙarfe 2:30 ya nuna. Iskar bakinsa ya furzar anatse ya fara takawa cikin irin takun ƙaƙƙarfan jami'in da ya karɓi horo.


Lafiyayyar bakar motar sa ya nufa kirar Reng Rover, buɗe wa ya yi ya shiga da bissmillah ya tashi motar Mai gadi ya buɗe ma sa ƙofa yana masa asauka lafiya, leƙo wa ya yi ya ce "Malam Salihu ni na wuce ka kula da gidan." Ya fada yana zaro kudi ya bashi, karɓa ya yi ya na kwara ro addu'a, kai kawai ya gyada masa ya fice a gidan ya na mai ɗauko wayar sa ya danna wa SAMEER kira. Ringing buyu ya daga ya ce "on mah way." 


"Ok" kawai ya faɗa yana ajiye wayar, ya nufi inda zai ɗauki SAMEER su wuce air phot kasancewar jirgin karfe 3:00 zasu bi.


"Sai muce a sauka lafiya."


Sai dare suka sauka sakamakon basu taso da wuri ba. Suna Isa ya sauka ya shige gida shikuma Sameer ya wuce nasu gidan. Ɓangaren sa ya wuce a matukar gajiye, Tsaf tsaf ya tarar da ɓangaren na sa a gyare kasancewar ko ba ya nan ana gyara wa ko da yaushe. Wanka yayi da sallolin sa ya kwanta ko abin ci bai nema ba madara kawai ya dauka a fright ya sha ya kwanta.


Washe gari misalin ƙarfe 9:00 na safiya ya tashi Bayan yayi wanka ya shirya a cikin wata hadadiyar shadda.


 Anatse ya fito daga ɓangaren nasa, kai tsaye ɓangaren iyayensa ya nufa.Ɗakin Dady ya fara zuwa da sallama ya shigo ƙawataccen fallown nasa da ya tsaru da kayan more rayuwa, agyare yake tsaf-tsaf sai tashin kamshin turaren wuta, da na ruwa ya ke yi.  


A saman kafet ya samu Dadyn yana karyawa, wuri ya samu ya zauna yana tan ƙwashe ƙafafun sa.


 "Dady Ina kwana na sameku lafiya?" 


Ya fada a natse kansa a kasa 


"lafiya lau alhamdulillah IMRAN ya hanya? Ammah shigowar dare kayi ko?"


"Eh Dady da yake bamu taso da wuri bane."


Dagowa yayi ya kalli Dadyn "Yaya jikin Abiha?" Ya tambaya fuskar sa na bayya nar da alamun damuwa!.


"Da sauki sosai, Ina ga ta shaki ƙura ne ko kuma hayaki shiyasa ta samu attack." 


Dadyn ya bashi ansa.


 "Allah ya bata lafiya"


 Ya fada, shiru ya ɗan ratsa kafin Dady ya dube shi yace "dama Ina san maga na da kai ne shiyasa na kira ka."


"Kansa a ƙasa ya ce to Dady Ina sauraronka" ya fada da girmama wa.


 "Ba wani Abu ba ne maganar aure ce, ya nisa kafin ya ci gaba da cewa da farko dai Allah ya maka komai a rayuwa. Ya baka Rai, ya baka lafiya, ya kuma rufa maka asiri. To ya kama ta ka kai rauwarka matakin gaba, ma'ana ajiye iyali. Don shine cikar kamalar duk wani mutum da ya kai lokacin yin, sabo da haka Kane mi mata kayi aure, wannan shine dalilin kiran." 


Ƙara sadda kansa yayi kasa ya e "insha Allah Dady."


"To Allah ya maku albarka baki dayan ku"


"Ameen"


Ya faɗa "yaushe zaka je Dutsimman ne?" 


"Gobe nake san wuce wa in Allah ya kaimu."


"Ok Allah ya kaimu" 


"Ameen"


"Bismillah ko kaci abinci"


 Dady ya fada. Zaman sa ya gyara yana jawo food plaks din gaban sa ya bude, kyakykyawar wainar shinkafa ce da tayi kyan suya sai kamshi take. Guda hudu yasa a plate ya bude karamin plaks din shi kuma far fesun kan rago ne da ya dahu sosai yaji kayan hadi, shima zuba wa ya yi sai shayi da ya haɗa yayi Bismillah ya fara karyawa.


Bayan ya kammala sallama yayi wa Dady ya wuce ɓangaren mahaifiyar sa. Da sallama ya shigo makeken fallown da ya cinye tsala-tsalan set din royal chair guda ukku, sai katuwar plasma data kusa rabin bango. lallausan Capet ne ya malale tsakiyar fallown Wanda yake iri daya da la bulayen da aka ƙawata fallown da su kalar dark green.


Komai da ka sani na jin daɗin rayuwa da wadata akwai shi a fallown. Abiha ya samu kwance saman kujera tana danna waya, sai Marwan da Kalifa dake wurin cin abinci suna karya wa. 


Suna haɗa ido ta nufo shi da sauri tana dariya


 "Lah ya IM yaushe kazo? Kazo lafiya?" Ta faɗa a jere.


Murmushi yayi ya na faɗin "towacce kike san in ansamaki Auta?"


"Duka Yaya" ta faɗa tana kama hannunsa.


"To jiya na shigo da dare, kuma lafiya lau na zo."


 Ya faɗa yana kaiwa zaune saman kujerar da ta tashi.


 "Yaya jikin ki?" 


Ya fada yana kamo hannun ta ya zaunar kusa da shi.


"Naji sauki sosai Yaya"


 ta ansa masa, da kulawa sosai ya kalleta


 "kin tabbata?" 


"Eh"


Ta ansa tana jin-jina kai alamar tabba tar wa,


 "Ok Allah ya kara lafiya"


 ya faɗa yana dago kansa, Marwan da Kalifa suka haɗa baki wurin gai she sa, ya amsa musu da kulawa dukda kasancewar sa miskili, kuma mara san magana amma yana sake wa da Yan uwansa sabo da yana matukar Son su, sai dai baya daukar raini kuma kanayin ba dai-dai ba zai hukuntaka.


Suma a bangaren su suna matukar son yayan nasu, kuma suna girmama shi.


 "Momy fa?" 


Ya tambayi Abiha.


 "Tana sama"


 Ta ansa masa.


"Ok" 


Ya fada yana hayewa stape ɗin da zai kai shi saman, yana zuwa ƙofar ɗakin ta ya ƙwan ƙwasa sannan ya jira aka bashi

 izinin shiga. Da sallama ya shigo ya samu tana ninke Dardumar da tayi sallar walha. Bayan ta ajiye Dardumar akan lokar dake gefen gadon, zama ta yi bakin gadon.


 Kallon sa tayi ta ce "ka zauna mana".


A saman doguwar kujerar dake ɗakin ya zauna yana fuskantar ta.


"Ina kwana Momy na same ku lafiya?" 


"Lafiya lau alhamdulillah."


Ta ansa masa "ya hanya?" Ta tambaye shi.


"Alhamdulillah" ya ansa mata.


"Ya aikin?"


Takuma tambaya 


"Alhamdulillah!"


"Allah ya taimaka yaci gaba da tsare ku, ya kuma dora ku akan makiya."


"Ameen!" ya ansa yana mai jin daɗin addu'ar ta domin kuwa ita ce take tafe da shi a duk inda ya sa ƙafa.


Shiya sa yake matuƙar son mahaifiyar sa, bai haɗa sonta da komai ba a duniya.


Idanu ta ƙura masa tana karantar yana yin sa da ta hango damuwa kara-ra.


"Lafiya kuwa yayan su? Mai ke damun ka?".


Ajiyar zuciya ya sauke yace "Momy Dady ne ya ce wai in fitar da matar aure."


Murmushi tayi tare da cewa "Masha Allah ashe na kusa samun sirika."


A sanyaye yace "Momy ban shirya ba hasali ma ni bani da wata budurwar da zan ce gata zan iya aurar ta ba. Gashi Ina kan wani aiki ne mai matukar mahimmanci yanzu haka a office".


Momy tace "To Yayan su ai aiki bazai hana aure ba, kuma maganar wadda zaka aura ai ga Rufaida nan tana son ka sosai kuma ko jiya mahaifiyar ta ta kira ni akan magar." 


Imran yace "Momy ni bana son yarinyar nan bata da kunya, kuma ta cika rawar kan tsiya"


Momy tace"zata dai na insha Allah tunda tana sonka duk abin da ka ɗora ta akai shi zata yi, amma kaje kayi tuna ni"


"Ok Momy ya faɗa ba wai don yanajin zai amince ba".


IMRAN yace "Momy gobe in Allah ya kaimu zan wuce Dutsimma"


"Ok Allah ya kaimu ta faɗa"


Momy tace "zan baka sko ka kai mata da na Ummanku ma" 


(Umma Sumayya)


"Ok "


Ya faɗa yana miƙe wa


 "Momy bari in wuce zan je mu hadu da Sameer ne"


Momy tace "Ok ka gaishe shi"


"Zaiji insha Allah ya bata ansa....


 _Sahibar_ _Hausa_ _ce_







*BURINA* 


     ```NA``` 


 *Oum* *Fatima* 


 *_HAUSA_* *_WRITER'S_ _ASSOCIATION_* 


 *FREE BOOK* 


 *Page* *8* 


 _Bismillah hirrahmanir_ _rahim_ 

________________________


Fitowa ta yi ɗauke da plate da robar ruwa a hannunta Ƙara wuce sa ta yi bata ko kalle sa ba.


 Da kallo ya ƙara binta yana mamakin ƙarfin halin yarinyar.


"To duka ma guda nawa take, yaushe ma aka haifeta" ya fad'a a ransa,


Wani miskilin murmushi yayi ya gyaɗa kai. 


Annah ce ta fito daga ɗakinta hannun ta riƙe da casbaha, wuri ta samu ta zauna tana cewa


 "IMRANA ashe ka dawo, ya na ganka hannu biyu yo Ina kilishin da na ce ka sayoman".


Kallonta yayi yana faɗin


"kefa daɗina da ke kin fiya kwaɗayi" 


"eh ɗin wa ya ki daɗi ni miƙo min In ka sayo ka tsaya ja min rai"


Ta faɗa tana miƙa ma sa hannu. Kai kawai ya girgiza ya ɗauko laidar daga gefen kujera ya miƙa ma ta. 


Karba tayi tana washe baki tana faɗin 


"yauwa ko kai fa, Allah ya maka albarka ya kare ka daga saharrin maƙiya ya baka mace ta gari mai kirki kamar ka ba marowaciya ba".


"Ameen"


Ya ansa yana 

fad'in


"yadda zakiji daɗin zuwar ma ta kwaɗayi ba"


"Eh daɗin abin nima ɗa na yana kawo min komai ba, kuma sai na je kwaɗayin dole dai amin abinda nake so ba" 


ta faɗa tana kai lomar kilishin ta.


 "me zai hana ayi miki" 

ya faɗa yana murmushi.


Hira sukaci gaba dayi kaɗan-kaɗan tana bashi labarin kakan su Malam Ahmadu ya na ma ta tambayoyi tana amsa masa. 


Karfe 9:00pm ya miƙe ya yi ma ta sallama ya na nuna ma ta wata laidar da ke aje daga gefen kujera tare da cewa


"ki kira waccan yarinyar ta dauka" 


Annah ta washe baki tana faɗin yauwa ɗan albarka ashe itama ka sayo mata ka ga har na rage mata to bari in aje abina da safe na Ƙarasa"


Shiru yayi yana ƙoƙarin wucewa ya ji ta tana faɗin 


"Ina ita waccan koɗaɗɗiyar uwar miskilancin tsiya ace mutum ba zai zauna ayi hira da shi ba kullum yana ƙule a ɗaki sai shegen danne-dannen waya ko da yaushe, ko da yake ai jirgi ɗaya ne ya ɗaauko su ita da shi ɗin"


Ta faɗa tana raka bayan sa da harara, kai ya gyaɗa yana cewa 


"ke kuma sai surutun tsiya ba, da ma Bakin ki ko ciwo baya yi".


Harara ta raka bayan sa da ita dan sarai ta ji abinda ya faɗa.


Shidai wucewa ya yi abin sa. Yana fita kai tsaye ɗakin da yake sauka ya nufa a natse ya gabatar da duk wani abin da yake yi kafin kwanciya bacci ya haye gadon ya kwanta yana duba wayar sa da ya ga miss call da yawa kuma duk na Rufaida ne, sai na Momy ƙwara ɗaya sai na Sameer Shima ɗaya. 


Momy ya fara kira suka gaisa ta tambaye shi ya su hajiyar, yace suna lafiya magana suka yi kaɗan ya kashe wayar yana ƙoƙarin kiran Sameer kiran Rufaida ya shigo a karo na biyu dan ta kira da suna waya da Momy.


Saida ta kira sau huɗu yaɗaga bata da niyar dainawa Sannan ya ɗauka, shiru yayi bayan ya ɗauka ita ce ta gaishe shi ya ansa ƙasa-ƙasa,


Shiru tayi ta rasa abin faɗa sai shine yace ina da aikin da zanyi fa, da sauri tace 


"dama na kira ne inji kana lafiya?" 


"Ina lafiya"


"Sai da safe" ya faɗa yana kashe wayar,


 Sameer ya kira suka dan yi magana sannan ya ajiye wayar ya kwanta.


Washe gari da misalin ƙarfe 9:00am ya shigo parlour, azaune ya same ta tana karyawa, kallo ɗaya tayi ma sa ta ɗauke kai 


"Ina kwana" 


ta faɗa ba tare da ta kalli inda yake ba.


 Haushi ya kamasa har bai San sanda ya daka ma ta wata razananniyar tsawa ba yana cewa "ke wai ni sa'anki ne?".


Afirgice ta ɗago tana zuba ma sa idanun ta da suka cika da hawaye duk ta ruɗe ta firgice. 


Tsaki ya ja yana mamakinta to hawayen na miye kuma? Lalle yarinyar nan da sauran ta ya faɗa a ransa yana zuba mata idanun sa da suka Ƙara ruɗata ta.


Baki na rawa tace "to ni me nayi kuma?, Allah ya baka haƙuri".


Kansa ya ɗauke daga barin kallonta yace "je ki kawoman break fast".


Da sari ta tashi ta nufi kiching tana tunzura baki gaba tana ƙun-ƙuni aranta, 'mutum sai masifar tsiya ni Allah da na san zaka zo da ban zo ba, wannan duk wadda ta aureshi ta shiga ukku da baƙin halin sa don har tausaya ma ta nake baiwar Allah'. 


Fitowa tayi hannun ta ɗauke da kayan breakfast ɗin da ta haɗo ma sa, a saman center table ta ajiye ta tura gabansa ta tsuguna ta haɗa ma sa komai.


Tashi tayi ta ɗauki nata ta shige ɗakin Annah ta ƙarasa ta haye gadonta, tana jinta tana mitar mutum bai da aiki sai hawa gadon mutane, ke dai gadonki ya bani wallahi. 


Tana jinta tayi ma ta shiru tana ɗaukar wayar ta da ake kira har sau uku. Wani kiranne ya ƙara shigowa, ta ɗauka ta Kara akunenta. Shiru ta yi bayan ta ɗauka tana sauraren ajiyar zuciyar da ya ke saukewa kamar Wanda yayi tsere,


 "Amincin Allah ya tabbata ga ma abociyar kyawu da kwarjini, da fatan kina lfiya" 


Mansoor ya faɗa cikin kwantar da murya da salon da yake amfani da shi na iya tsara kalamai wurin sace zuciyar ƴammata.


"Alhamdulillah"


Ta ansa masa, yaci gaba da cewa 


"nayi matuƙar farin ciki da kika ɗauki waya ta danna san yau ranar sa'a ta ce". 


Ya ci gaba da cewa


 "don haka ba zan taɓa mantawa da ita ba, don har sadaka zanyi don nuna farin ciki da nake ciki" 


Har ga Allah bata san sanda murmushi ya yalwatu a saman kyakykyawar fuskar ta ba har labban ta na motsa wa ba, mamaki ya kama ta kawai dan ta ɗauki wayarsa shine yake wannan jin daɗin harda wai zaiyi sadaka, ita sai ya bata tausayi ma wallahi, 


'Ɗorawa kai wahala' ta ayyana a ranta.


 "Ina da abinyi in baka da abin faɗa" 


ta ce tana ƙoƙarin kashe wayar.


Dasauri gudun karta kashe masa wayar yace 


"dama na kira ne naji muryarki ko zan samu nutsuwa"


"To ai kaji ko!"


Ta bashi ansa, "kwarai kuwa kuma na yi matuƙar farin ciki da wannan damar da kika bani".


 Shiru ya ratsa kafin ya ce "Azima tace kin je kadan garu"


"Eh"


Ta amsa masa, "please gimbiya zan zo in ganki kinsan bazan iya jiran har sati biyu ba ba tare da na ganki ba, dan kema kin san sabo da ke nake zaune a garinnan".


"Kai ka so hakan".


Ta bashi ansa "haka ne kuma zan ci gaba da zama har san da zan ɗauke ki gaba ɗaya ba". 


"Hmm" kawai tace 


"Shikenan bari in barki ki huta sai na zo" 


Ya faɗa ya na murmushi,


 "ni dai ban gayyaceka ba" 


ta faɗa tana kashe wayar. 


WhatsApp ta buɗe group ɗin su na G G S S Dutsimma ta shiga suka ɗan taɓa hira da kawayensu har akayi kiran sallar azahar, Sannan ta tashi ta shige toilet, arwala ta yi ta tada sallah.


______________


A bangaren IM kuwa bayan ya gama breakfast ɗin Annah ta fito suka gaisa.


Ƴandaka ya wuce gidan Umma Sumayya don ya gaisheta ya kuma kai mata saƙon Momy.


Yana isa unguwar a ƙofar gida ya haɗu da Abdulhalim da fara'a sosai ya tare shi, don sun saba ko da baya nan suna waya dashi kuma in yazo hutu suna haɗuwa.


 A natse suka shiga cikin gidan da sallama, Abdul ne ya shiga ɗakin Ummansu ya sanar ma ta da zuwan yayan su,


 "kace ya shigo mana ya zaka baro shi a waje".


"To umma"


 Abdul yace yana fita ya ce ma sa ya shigo inji Umman. 


A natse ya ƙaraso ɗakin bakin sa ɗauke da sallama, da fara'a sosai Umma ta ansa ma sa tana yi masa maraba.


 Ƙoƙarin zama yake a saman Capet, da sauri Umma tace,


 "A'a ya zaka zauna a ƙasa? Maza tashi ka hau kujera"


To Ummah ya faɗa yana tashi ya hau kujerar kansa a ƙasa ya ce 


"Ina kwana mun same ku lafiya". 


"Lafiya lau alhamdulillah"


 Ta amsa tana tambayar sa mutanen gidan 


"duk suna lafiya sunce a gaishe ku" ya faɗa.


"To mu na ansawa"


"Ina auta mutuniyata"


Umma ta tambaya.


" Tana Lafiya ta ce a gaishe ki".


"Aiko Ina ansawa" 


Kansa ya ƙara saddawa yana tambayar Umma jikinnata ita ma tace 


"jiki alhamdulillah".


Tashi tayi ta ɗauko mishi ruwa da lemo ta ajjiye ma sa, sannan ta nufi kiching ta ɗauko ma sa abinci,


 Sosai ya ci tuwon shinka far da miyar taushe ya sha ruwa, cikin hirar da suke ne ya ce ya kamata ta ga babban likita, insha Allah za ta je ko Egypt ne taga k'wararren likita,


 Umma tace 


"A'a yayan su ai nanma suna bakin ƙoƙarin su Allah ya saka da alkairi". 


"Ai can ɗin zaki fi samun kulawa Ummah In sha Allah zaki je" 


Godiya ta yi sosai da sa masa Albarka, Sosai ya ke burge ta saboda ya na da tarbiyya da girmama na ga ba da shi dukda ana ganin miskilancin sa da rashin magana amma yana da kirki sosai kuma yana da sauƙin hali, dan sosai yake sakewa suyi hira da ita, ya ɗauke ta tamkar mahaifiyar sa.


Tashi yayi ya na faɗin


 "Umma ni zan wuce ga wannan inji Momy" 


Ya faɗa yana ajjiye ma ta laidar , sannan ya zaro kuɗi ma su yawa ya ajiye ma ta ya tashi,


Albarka sosai ta sa mashi tana godiya take tambayarshi yaushe zai koma, yace 


"gobe insha Allah"


 tace 


"to shikenan zan ba Abdul saƙon auta da na Momy ya kawo".


"Ok"


Kawai ya ce ya fito Abdul ya yi masa rakiya har ƙofar gida, shima kuɗi ya bashi ya ce ya sai abinda ya ke so bai yi ma sa tsara ba ba,


 Godiya yayi Shima ya koma gida cike da murna.


Tun daga nesa ya hango ta a ƙofar gida tsaye da wani saurayi a jikin mota suna hira, shi gani yayi ma kamar ta na ma sa murmushi, abinda bai taɓa gani ba a fuskarta tun da ta fara girma.


Nan take yaji ranshi yayi bala'in ɓaci, wato har ta fa ra hira da samari du ka ma yarinyar nawa take da har zata fa ra kula samari?


 Ya tambayi kanshi "shine har da jerawa da wani ƙaton gardi har ta na wani washe mai haƙora wai ita ga Mai saurayi"


 Wani dogon tsaki ya ja tare da ɗauke kansa yana Ƙarasawa wurin suka haɗa idanu wani mugun kallo ya ma ta da yasa gabanta faɗuwa.......


Oum Fatima


{ _Sahibar_ __Hausa_ }







*BURINA* 


    *NA* 


       *OUM* *FATIMA*


 *FREE* *BOOK* 


 *HAUSA* *WRITERS* *ASSOCIATION* 


 *Page* *9* 


Ba shiri tayi ma Mansoor sallama ta shige gida. Cikin fara'a Mansoor ya mika masa hannu yana gaishe sa. Don yana ganin sa ya san suna da alakar jini, sabo da kamannin da ya ga sunayi ya sa shi yanke hukuncin cewa yayanta ne.


Shima hannun ya mika masa fuskarsa ba wal-wala suka yi musabiha. Wucewa ya yi ba tare da ya tsaya amsa sauran gaisuwar da yake ta faman yi masa ba 


Yana shigowa fallown ta kara sauri zata shige dakinta. "Zo nan" ya faɗa ba alamar wasa ya na zama saman kujera. A ɗarare ta zo ta tsuguna kusa da ƙafafun sa, shiru yayi ya na kallon ta na tsawon sakanni, kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce "wato dama abin da kikeyi kenan ko?" Shiru ta yi, ya ci gaba da cewa "keda zaki tafi makaranta shine kika fara kula samari ko?".


Namma shirun tayi masa , abinda ya kara kular da shi kenan ya ja tsaki yana cewa "Ok tunda auren kike so za'ayimiki, zan fada ma Dady kar ma yayi asarar kuɗin sa wurin nema maku makaranta dan ba karatun zaku yi ba, tunda kuka fara kula samari za su hure maku kunne ne kawai, gwara kawai a aurar da ku ku je ku ƙarata."


Tunda ya fara maganar sa, sai yanzu ne ta ɗago da sauri jin mai yace. Ganin babu alamar wasa a maganar sa ya sa gaban ta yayi wani irin tsinke wa ya faɗi, kenan yana nufin zai ce wa Dady ayi masu aure? To karatun fa? Yana nufin baza ta cika BURINTA ba kenan, BURINTA tun na yarinta ya tashi a banza kenan? Kai ina ba zaiyiwu ba.


A karon farko da ta saka kwayar idonta a cikin nasa idanun, da sauri ya dauke kansa sakamakon wata irin faduwar gaba da ta ziyarce sa. Tunda yake ba macen da ya taba kallon idonta gaban sa ya fadi, sai wannan yar yarinyar da aka haifa a gaban sa.


A sanyaye tace dan Allah  Yayanmu kayi hakuri kar ka fada ma Dady, Wallahi ban ce ya zo ba, kuma ai Annah ce tace sai na fita.


"Ok".


"Kawai dan ta ce ki fita shine ke kuma kika fitar ko?".


Yaci gaba da cewa "ai kawai magana ta ƙare zanyi wa Dady magana, ace ya turo magabatansa kawai". Dan da nan hawaye ya cika idanunta suna ƙoƙarin zubowa, kansa ya dauke daga barin kallon ta yaci gaba da danna wayar sa.


A sanyaye tace "Dan Allah Yayammu kayi haƙuri na roƙeka kar ka shiga tsakanina da cikar BURINA, zama kwararriyar likitan mata shine BURINA", kuma ba zai cika har sai nayi karatu!.


"Please yayammu!" ta fada tana fashe wa da kuka har da shesh-sheka. Kallonta yayi na wani lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya, ahankali yace "tashi kije", 


"ka hakura?"


Ta fada tana kallon sa.


 "kije nace ko"


A sanyaye ta wuce tana share hawaye, bayan ta yabi da kallo yana juyowa suka yi ido huɗu da hajiya Annah tayi kicin-kicin da fuska tana kallon sa. Shima tashi fuskar ya haɗe yana dauke kai.


"To almasifatu uban me kayi wa marainiyar Allah take kuka".


Harara ya zabga mata sannan yace "kece kika bata izinin fita wurin wani ƙaton banza ko?". Baki da hanci ta bude tana kallon sa, kafin tace. "Habubakar ka harara ba ni ba, kuma ni na ce ta fita" taci gaba da cewa "in bata fita wurin samari ba yo kwaɗa ta zamuyi mu ci?" Ta Ƙara sa tana kafe shi da idanu alamar dai ansa take jira daga gare shi.


Jin ya mata shiru bai kula ta ba ya sata cigaba da faɗin "yarinya zankaɗeɗiya san kowa ƙin ɗan baƙin ciki, ace baza ta yi samari ba".


Imran yace "duka yarinyar nan nawa take da kike wannan zancen akan ta"


"A'a ka manta yau aka haifeta!, kaga Imrana ka fita idanuna in rufe na dai gaya maka to Allah na tuba bokon banza bokon wofi mu da bamuyi bokon ba mi ya rage mu kuma ma ai zatayi a gidan mijin ta tunda ana yi".


Tashi yayi ya fice yana gyaɗa kai kawai dan bai ma san mai zai ce mata ba kuma. Dakin sa ya shiga yana ansa wayar Sameer da ya kira shi.


A ɓangaren Mubeena ta na shiga ɗakin ta fada saman gado tana fashewa da kuka, wannan wane irin lukutin tashin hankali ne, shikenan Mansoor ya ja mata, tana zaman ta lafiya lau ya zo ya ja mata masifa a wurin Yayansu. Sai da tace kar yazo amma dan naci shine ya kwaso kafa ya zo, ko uban me zata masa.


Ƙaran da wayar ta ɗauka ne ya sa ta dakata daga kukan da take yi ta kalli wayar, Azima ce mai kiran harara ta zabga ma wayar kamar ita ce tayi mata laifin, Sannan ta ɗaga. Tana ɗaga kiran ta balbale ta da masifar wa yace ta fada wa Mansoor inda take, ai gashinan abinda ya zo ya ja mata.


"iKon Allah"


Azima tace "ko sallama babu daga ɗaga waya za ki kama masifa mai ya ja maki haka Mansoor din?" Ta tambaya tana ƙunshe dariya don dama ta san za'ayi haka tun da taba Mansoor address din inda take ta san zata sha masifa.


Gaba ɗaya ta fada mata abinda ya faru, murmushi Azima ta yi tana cewa "ai ta kwana gidan sauki kice zamu sha biki?" Ta cigaba da cewa to yanzu kin fada wa Mansoor ɗin? Ko ni in fada masa dan na san zan samu babban goron albishir".


"Allah ya isa tsakanin na da ke Azima" 


Mubeena ta fada tana fashe wa da kuka, sannan ta kashe wayar.


Dariya Azima ta ƙyal-ƙyale da ita tana aje wayar ita ma. Sosai tayi dariya tana mamakin halin ƙawar ta ta.


_____________


Washe gari


Ashiye ya fito tsaf cikin shirin tafiya gida. Sanye yake da wani  lallausan tsadadden yadi maroon colour dinkin zamani daya matukar zama a jikin sa sosai kayan suka yi ma farar fatar sa kyau, ya saka hula da takalmi da agogo wanda suka da ce da shigar sa. Shar ya fito kamar wani ango sai zabga ƙamshi yake 


A natse ya shigo cikin fallown. Mubeena ya samu kwance saman doguwar kujera ta yi zurfi a cikin tuna ni bata ma ji sallamar da yayi, sai Baba Lami ce ta ansa masa daga kiching, dan tun jiya da abinnan ya faru take cikin damuwa, kuma wal-walar ta ta ragu dukda dama ba Mai yawan maga bace. Kana kallonta zaka fahimci tana cikin damuwa, kuma tun ranar bata ƙara daga kiran Mansoor da Azima ba dan fushin har ita ya shafa tun da tana goyon bayan sa.


Sun kira har sun gaji amma taki daga wa. Jiya Mansoor da ya kasa jure wa har zuwa yayi, taƙi fita Annah ta yi faɗan har ta gaji amma ta mata shiru. Dan ita duk abinda zai shiga tsakanina da cikar BURINTA to suna raba hanya ne shi yasa daman can bata taɓa ba wani saurayi dama ba. Amma gashi yanzu rana daya Mansoor ya rusa komai.


Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama maganar zucin da take, suka hada idanu. Zaune ta tashi kanta a kasa tace "Ina kwana Yayanmu?".


"Kina lafiya?" ya faɗa yana kallon yanayin ta".


"Eh"


Ta ansa masa, kllonta ya ƙara yi yana karantar ta, tana cikin damuwa sosai ya san akan maganar jiya ne. Shikuma har ga Allah ba da gaske yake mata ba yayi mata haka ne dan ya tsorata ta. Dan shi a gaskiya ba zai lamun ci kule-kulen samarinnan ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa "je ki dauko kayan ki ki same ni a mota zamu wuce KT.


Kallon sa tayi tana cewa "Yayammu ai ba yau zan tafi ba, sai na koma gida na shirya Sanna, kuma ma har Abdul zamu je ai" 


"Ni kuma nace yau zki tafi, ki tashi kar ki ɓatamun lokaci malama" ya faɗa yana duba agogon hannun sa.


Tashi tayi a sanyaye ta shiga ɗakin dan yin abinda ya umar ce ta. Fitowa tayi cikin shigar Abaya Maroon colour da ta amshi farar fatar ta Tana jaye da jakar kayan ta. Tayi kyau sosai sai dai fuskar ta ba bu wal-wala ko k'aɗan.


Annah ce ta fito daga dakinta tana cewa "har ka fito Imrana zaka..." 


Ta kasa ƙarasa abinda tayi niyyar faɗin sakamakon ganin Mubeena ita ma cikin shirin tafiya........ 


Oum Fatima







*BURINA* 


   *NA* 


      *OUM* *FATIMA* 


 *FREE* *BOOK* 


 *HAUSA* *WRITERS* *ASSOCIATION* 


 *Page* *10* 


"A'a ya na ganki da shirin tafiya ina zaki je ke kuma?"


Mubeena ta ce "Yayammu ne ya ce in fito mu tafi wai". Kallonta ta maida kansa tana tambayar sa "kamar ya ta fito ku tafi? Ban gane ba" ta ƙarasa faɗa tana kaiwa zaune saman kujerar da ke kusa da ita.


Kansa ya ɗauke yana mayar wa kan wayar sa da yake dannawa ya ce "Dady ne ya ce in tafi da ita". "Shi Habubakar ɗin?"


"Eh"


Kawai ya ce ya ci gaba da abin da yake yi, "to shikenan Allah ya kiyaye ku gaishe da mutanen gidan". "Zasuji " ya faɗa yana ajiye mata kuɗi mai yawa a gabanta, yace "ni na wuce".


Fita yayi ya nufi motar sa ya tsaya yana amsa waya ta fito.

Jakar hannun ta ya ansa ya sa a bayan mota sannan ya buɗe mata gaba ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ɗayan side ɗin ya shiga ya tashi motar suka wuce Malam Habu yana daga masu hannu da addu'ar sauka lafiya, kudi ya Ciro ya bashi, yana ta godiya suka fice a gidan.


Ganin ya nufi unguwarsu ya sata sauke ajiyar zuciya, dama tunanin da take kenan basuyi sallama da Ummanta da kuma Abdul ba.


Yana tsaya wa ta buɗe motar ta fice da sauri ta shiga gidan bakinta ɗauke da sallama, fitowa yayi shima ya nufi cikin gidan. Da sallama ya shigo cikin gidan, a baranda ya same su suna zaune saman tabarma, "Yayan su Kaine maraba, ƙaraso man?" Umma ta fada da fara'a sosai a kan fuskarta.


A natse ya ƙara so ya zauna saman Capet ɗin da Mubeena ta shimfiɗa masa. Da girmamawa sosai ya gaida Umman, ta ansa masa da kulawa sosai itama.


"Ko tafiyar ce ?" Umma ta tambaye shi.


"Eh Umma dama zamu wuce da Mubeena ne Dady ya ce in tafi da ita".


"To ba matsala Allah ya kiyaye".


"Ameen" ya fada.


"Matsa mun ni intashi" Umma ta ce wa Mubeena da taje ta lafe a jikinta kamar wata mage. Ɓata fuska tayi tana matsawa, suka hada idanu, da sauri ta ɗauke kai ganin irin hararar da ya mata.


Umma ce ta dawo hannunta dauke da laidar da ta hada wa Momy tsarabar su kuka, kubewa , daddawa da sauransu. Sai tsarabar Abiha su Alawar Madara, Gullisuwa, Iloka, ta mikawa Mubeena ta ce "gashi wannan ki kaiwa Momyn taku wannan kuma na Auta ne, kice Ina gaishe su"


Ansa tayi tana cewa "aiko Blood zataji daɗin tsarabar nan Umma kin san ta da kwaɗayin tsiya kamar hajiya Annah" ta karasa maganar tana dariya.


"Kinci gidanku Mubeena uwar tawa ce mai kwaɗayi? Kana jinta ko Yayansu".


Murmushi yayi ya na cewa "ai Umma tsohuwar ce akwai san daɗi"


"To ku tashi ku ban wuri tunda kaima biye mata za kayi " Umma ta faɗa fuskarta cike da murmushi. Yana murmushi ya tashi yana cewa "to mu zamu wuce Umma". 


"To Allah ya tsare ya kaiku lafiya" umma ta fada. Itama kuɗi ya ajiye mata sannan ya fita tana ta sa masa Albarka.


Har zaure Umma ta a rako su, suka shiga mota sai da suka tafi sannan ta dawo gida tana musu fatan alkairi.


Tunda suka ɗauki hanya shiru ya ratsa motar baka jin komai sai sautin Karaun Al-qur'ani mai girma, kira'ar Shek Ahmad Sulaiman a cikin Suratul Maryam. Ahankali ta lumshe idanun ta tana bin Karatun a hankali bakinta kadai yake motsawa, kallon ta yake ta kasan idanu lokaci zuwa lokaci yake sauke ajiyar zuciya.


Wata irin nutsuwa yaji tana saukar masa, hakanan yake jin daɗin yanayin. Cikin awa ɗaya da mintina suka shigo garin Katsina, suna zuwa kofar gidan yayi horn mai gadi ya buɗe masa yana yi masa barka da zuwa. Hannu kawai ya ɗaga masa yana Kara sawa parking space ya tsaida motar, a hankali ta buɗe idanunta tana kallon harabar gidan. 


A kasalance ta buɗe motar ta fito, wucewa tayi cikin gidan bata ko tsaya ɗaukar kayan ta ba. Bayan ta yabi kallo yana magar zuci, 'to wa tabari da zai daukar mata kayan'. 


Zagaya wa yayi ya buɗe bayan ya ɗauko jakar tata da laidodin tsarabar, ya nufi cikin gidan. Da sllama ya ƙara so fallown. Duk anan ya samu mutanen gidan, da sauri Abiha da ta ruƙun ƙume Mubeena, tana murnar ganinta ta nufe sa da fara'a tana masa sannu da zuwa. Marwan da Kalifa ma gaishe sa kukayi ya amsa da kulawa sannan ya nufi Momy da ke zaune saman kujera tana ta faman murmushi.


Tsuguna wa yayi a kusa da kafafun ta ya gaishe ta cike da girmama wa, da kulawa sosai ta ansa tana dafa kansa. Tambayar sa ta yi ya ya baro su, yace duk suna lafiya sunce a gaishe ku.


"Madalla muna ansawa".


Laidojin da ya ajiye a kasa ya nuna mata yana cewa "gashinan inji Umma ta ce akawo maki"


"Madallah an gode Allah y saka da alkairi".


Abiha ta kalle sa tana cewa "Yaya to ni Ina nawa?".


Hararar ta yayi yana yin gaba. Ɓangarensa ya a nufa dan yayi wanka ya huta. Da sauri Abiha ta Kara so gurin Mubeena tana cewa "Blood wai Umma bata baki tsaraba ta ba".


Murmushi tayi tana cewa "ta bayar yana wuri na", "yauwa ai dama nasan Ummata ba zata manta da sakona ba".


Momy ce ta kalleta tana cewa"Allah ya shirye ki kwadayayya kawai", duk dariya suka sa mata, fuka ta ɓata tana cewa, "ni muje ɗaki Blood ki bani kuma Allah ba wanda zan ba tunda suka yi mun dariya". Ta faɗa tana hararar Kalifa da yake dama shine abokin faɗan nata shi take bi, basa jituwa dan kamar suna ganin hanjin juna duka shekar biyu ne a tsakanin su, shi kuma da san girma. Tashi tayi tana daukar jakar Mubeena ta nufi ɗakin ta , itama bayan ta tabi suka shige.


_______________


A ɓangaren Rufaida ta ɗagawa mahaifiyarta hankali akan Imran dan ta yi iya yinta dan ganin ta janyo ra'ayinsa amma abu ya gagara. Ita kuma ba zata iya hakura da shi ba don kamar Kara mata sonsa ake, kullum tana posting pictures din sa a social media da kalaman soyayya. Duk wadda ta nuna itama ta kyasa kuwa sai sun kwashi bala'i da ita dan tace ko inuwarsa wata macen tayi gigin raba to sai ta mata rashin muruncin da kare ma ba zai ciba, dan ita kaɗai aka halicci IMRAN MUHAMMAD ABUBAKAR.


Da taga duk wani ƙoƙarin ta yana tashi abanza, shine fa ta ɗagawa mahaifiyarta hankali akan tayi wa Momyn sa maga ai tasan duk abinda ta sa shi to zaiyi ko miye in dai bai saɓa shari'a ba, sabo da yana matuƙar ƙaunar mahaifiyar sa kuma yana mata biyayya.


Wannan kenan


Bayan ya ɗan huta yayi wanka ya shirya cikin kananan kaya da suka matukar yi masa kyau. Fitowa yayi kai tsaye part din Dady ya nufa a zaune ya samu Dady a saman kujera yana duba jarida. Wuri ya samu ya zauna a saman Capet yace "Barka da huta wa Dady, na same ku lafiya".


"Lafiya lau alhamdulillah, Imran ka dawo lafiya?"


"Alhamdulillah Dady"


"Masha Allah ya ka baro su hajiyar?", Dady ya tambaya 


"Duk suna lafiya sunce a gaishe ku".


"Madalla muna ansawa", Dady ya fada. Shiru ya dan ratsa sannan Dady yaci gaba da cewa "to Imran Ina muka kwana a magar auren ka?, So nake kafin ka koma agama magana asa rana".


Sadda kansa ƙasa yayi yana cewa " to Dady insha Allah zanyi kokarin".


"Ok to Allah ya zaba maka ta gari Ina jiran ji daga gare ka". 


"To Dady a huta lafiya" ya faɗa yana mikewa ya wuce. Bayansa Dady ya bi da kallo yana matukar San Dan nasa sabo da yaron kirki ne yana yi musu biyayya,sosai yake masa addu'a Allah ya kare shi daga shrrin maƙiya ya kuma bashi mace ta gari, da yawa daga cikin abokan sa sun masa tayin yaran su mata ko zasu hada su aure yaƙi karba don baya san yayi wa ɗansa dole. Shi yasa ya bashi zabi ya fitar da kansa.


Oum Fatima







*BURINA* 


   *NA* 


      *OUM* *FATIMA* 


  

 *FREE* *BOOK* 


 *HAUSA* *WRITERS* *ASSOCIATION* 


 *Page* *11* 


Da dare bayan ya shiga ɗakin Momy yake faɗamata yanda sukayi da Dady. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce "Yayansu kawai haƙuri zakayi ka amshi Rufaida, tunda baka da wani zaɓin bayan ita, kuma kaga yarinyar nan tana matuƙar ƙaunar ka duk abinda take yi da baka so a hankali zata daina in ka nuna baka so, maganar so kuma zaka sota a hankali, amma idan kana da wata wadda kake so zaka iya gabatar da ita".


Jin yayi shiru ya sa ta ci gaba da cewa "ko jiya mahaifiyar ta ta yi mun maganar tace duk tabi ta damu akan ka, kuma kaga masoyi ai yafi maƙiyi ko? Ta Ƙara sa faɗa tana kallon sa. Shiru yayi kan sa na cushewa gaba ɗaya ya rasa mafita ahalin yanzu. Har ga Allah shi dai baya san Rufaida, soyayyar sa dama zuciyar sa duka akwai mamallakiyar su, sai dai baya ganin lokacin bayyanuwar ta ya zo, dan haka bashi da wani zaɓin da ya wuce karɓar Rufaida ko dan Albarkacin mahaifiyar sa ce ta yi masa tayin karɓar tata. Sabo da tana da matuƙar girma da daraja a wurin sa da zai iya yin komai domin farin cikin ta.


Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce to shikenan Momy na amince Allah ya sa alkairi ne, sai ki faɗawa Dad. Daɗi sosai Momy taji dan bata yi tunanin amincewar sa cikin sauki ba duk da ta San shi din Mai tsananin biyayya ne a gare ta Dan tun farko da umar ni ta bashi kai tsaye to tabbas zai amince ne kai tsayen. Da fara'a sosai a saman fuskarta ta ce "Allah ya yi maka albarka ya sa alkairi acikin auren".


"Ameen" 


Ya faɗa kasa-kasa, sannan yayi mata sallama ya fice. Yana fita ita ma ta tashi ta yi shirin tafiya ɗakin Dady, da sallama ta shiga hannun ta ɗauke da tea plaks mai kyau da ta ɗora akan wani kyakykyawan tiren silver sai kofuna da ta jero, wuri ta samu ta dora akan center table din da ke gaban kujerar, da fara'a ya ansa mata yana cewa "yauwa Momyn yara, kamar kin san jiran shayinnan nake kuwa na jiki shiru".


"To ai gashi, ɗanka ne ya tsaida ni dama". Ta karasa faɗa tana miƙa masa shayin da ta zuba masa cup. Karɓa yayi ya fara kurɓa a hankali sannan yace "inajinki". Kallon sa tayi tana cewa "Sako ya bani in faɗa maka ya fitar da matar".


Da fara'a sosai ya kalleta yana cewa "Masha Allah wacece, su waye mahaifanta?". "Eh yar wajen aminiya tace hajiya Salma matar tsohon gwamna".


"Ok kina nufin Alhaji Idris"


"Eh shifa"


"Masha Allah Allah ya tabbatar da alkairi, insha Allah zan yi wa Alhaji sani magana, (mahaifin Sameer) sai musa ranar zuwa". "Ok Allah ya kaimu" cewar Momy.


Washe gari Momy ta kira hajiya Salma ta faɗa mata ai ya amince har Dadyn sa ya ce za su zo insha Allah. "Alhamdulillah" ta faɗa tana washe baki. Kai tsaye ɗakin Rufaida ta tafi ta sanar mata, ihun murna ta saki tana rungume ta take faɗin thankyou so much Momy, BURINA ya kusa cika na mallakar IM amatsayin miji!. Ta ƙara she da sakin wata dariyar farin cikin.


Hajiya Salma na fita ta ɗauki wayar ta ta kira Nadiya tana ɗaga kiran ba ko sallama ta saka ihu tana faɗa mata ai takusa zama Mrs IMRAN MUHAMMAD ABUBAKAR . Take fada mata ya amince har ma iyayen sa zasu zo neman auren, ai bama sai anje ga plan B ɗin ba abar maganar zuwa wurin Malaman nan. Dama ita fa dan ta rasa mafita ne shiya sa.


Nadiya tace "ya dai kamata muje a ƙara riƙe maki shi sosai don kin san ba wani sonki yake ba sabo da mahaifiyar sa ya amince to kinga kuwa kina da aiki a gaban ki. Rufy tace to koma dai menene ki bari in mun hadu mayi maganar, yanzu ki barni inyi celebration ɗina kar ki ɓata min mood da wani zan cen baya sona. Ko baya sona ni Ina sonshi kuma shima zai so ni ne!".


"Ok saimun haɗu, ayi celebration lafiya amarya". 


"Ok by" ta faɗa tana kashe wayar.


Acikin satin aka gama komai aka tsaida rana watanni ukku masu zuwa , abinka da harkar manya , akuma satin ya tattara ya koma bakin aikin sa.


_________ /__


Ɓangaren Mubeena kuwa dama kiran da Dady ya yi mata ashe registration ne za ayi musu ita da Abiha an nema musu admission zasu wuce makaranta. Alokacin da taji daga bakin Dady, ba ƙaramin farin ciki ta yi ba. Ganin tana gab da fara karatu kuma shine tsanin cikar BURINTA. Dan haka farin cikin ta ba ɗan kaɗan bane dan har azumi tayi na godiya ga Allah. Ba ɓata lokaci aka sama masu admission a Federal University Of Abuja. Inda Mubeena ta dauki Medicine, ita kuma Abiha Mass communication. Dan haka ba department ɗin su ɗaya ba amma makaranta ɗaya ne, nan da sati hudu zasu fara attending Lecture insha Allah.


Shi yasa zata koma Dutsimma kafin lokacin tayi sallama da mahaifiyarta da ɗan uwanta da kuma aminiyar ta. Da kuma abokan arziki, dan duk wani shirye-shirye Dady ya sa Yayansu yayi musu shi, dan admission ɗin ma shi ya sama musu yayi musu komai har gidan da zasu zauna shi ya sama musu ɗan madai-daicin gida mai kyau sannan ya ɗaukar musu mai gadi ya saya musu sabuwar mota ya ɗaukar musu direba dan har yanzu Abiha bata driving amma ta koya ba sosai ba dai take yi. Momy kuma ta basu Baba attine amin tacciyar mai aikin ta ce, dan ta kula da su kuma ta rika yi musu wasu ayyukan.


A cikin satin ta wuce Dutsimma cike da farin ciki, Dady yasa driver ya kaita. Bayan taje ta yiwa Umma bayani ta taya ta murna sosai. Washe gari bayan ta huta ta fita taje gidan su Azima take faɗa mata sun sami admission a Abuja, itama ta taya ta murna har take fada mata itama ta samu anan FUDMA (Federal University Dutsimma). Mubeena ta ce "Ina tayaki murna Besty amma na so ace makaranta daya zamuyi".


"Haka Allah ya so Besty amma ai zamuna waya kuma zaki rika zuwa hutu ko?" 


"Eh hakane Allah dai ya bamu sa'a acikin kararunmu ya cika mana BURIKANMU". 


"Ameen Besty".


"Jiya Mansoor ya zo yake tambaya ta address dinku a Katsina, wai zaije ya ganki ya kasa jure wa bakya daukar wayar sa. Nace masa nima ban sani ba".


"Gara da baki fada masa ba, zan kuma fada masa yayi hakuri ni karatu zanyi. In Allah ya kadarto ni matarsa ce to dole zan aureshi, in kuma ni ba matarsa bace to duk abinda zaiyi bazan auresa ba. Sabo da haka yanzu dai yayi hakuri ya ƙyale ni inyi karatu na a natse, mu jira lokaci mu barwa Allah zabi".


"Hakane Allah ya zaba abinda yafi alkairi".


"Ameen" 


Tashi tayi tana faɗin "kinga yamma tayi bari in wuce sai munyi waya"


"Ok muje in taka maki"


Fitowa sukayi daga ɗakin Azima suka shiga ɗakin Ummansu ta yi mata sallama sannan ta rakota har ƙofar gida ta wuce sannan ta koma gida.


Bayan ta koma gida kayayyakin da zata tafimusu dashi ta ida sa harhaɗawa dan Umma ta haɗa musu kayayyaki irin Wanda ƴammakranta suke so sannan ta haɗa musu kayan kwaɗayi irin wanda Abiha take so tayi musu dambun naman kaza da na kifi ta yi musu Snack's, sosai dai ta hada musu kayayyaki.


Ana ya gobe Mubeena zata wuce Katsina daga can kuma su wuce Abuja, da dare bayan sunyi sallar isha'i Ummansu ta zaunar da ita tayi mata nasiha sosai, akan rike muruncinta na ƴa mace. Tace "gurinnan da zakije sabon guri ne da baki saba da shi ba zakiyi rayuwa ne ba a gaban idona ba kamar yadda kikayi da, to abinda nake so da ke shine, ki sani karatu kika je, to kiyi karatu ki maida hankali kiyi abinda ya kaiki ko dan cikar BURINKI, Mubeena sannan kiji tsoran Allah ki rike muruncinki, ki cigaba da amfani da tarbiyar da muka baki, banda shashanci duk abinda kika san bazakiyi anan ba to a canma kar ganin ba idona yasa kiyi abinda da kika ga dama. Domin kuwa inni bana ganinki to Allahn da ya halicce ki yana ganinki, na roƙeki ki kama mutuncinki ki tina da maricinki kiyi abinda ya kaiki ki dawo, ba ruwanki da abokan banza kiyi mu'amala da mutanen kirki sannan ki kula da ibadarki banda wasa da sallah ki yawaita addu'a insha Allah Allah zai kare ki, daga dukkanin sharri kiyi mun alkawain zakiyi amfani da abinda na fada miki!".


"Insha Allah Umma zan kasance mai biyayya ga abinda kika umarce ni matukar bai saba wa umarnin Allah ba!".


"Allah ya miki Albarka ya baki sa'ar abinda kika je nema".


"Ameen Umm na gode Allah ya ƙaramaki lafiya da nisan kwana mai albarka!"


"Ammen kije ki kwanta kinga gobe zaki wuce".


"To Ummah sai da safe"


"Allah ya tashe mu lafiya"


"Ameen" ta faɗa tana wuce wa ɗakinta. 


Washe gari ta shirya tsaf drivern Dady ya zo ya ɗauke ta da kaya niki-niki. Mubeena hada ɗan kukanta da zasuyi sallama da Umma da Abdul kamar wadda ta tafi kenan kasancewar, tunda ta tshi a gidansu bata taɓa yin nisa da gida ba irin haka, sai wannan karon. Iyakar inda take zuwa ta ɗan kwana biyu bai wuce gidan hajiya Annah ba, sai kuma Katsina gidan Dady.


Sai magriba suka isa, suna zuwa ta shige ciki, mai gadi ne ya shigar mata da kayan ta. Da fara'a mutanen gidan suka tarbeta suna tambayar ta mutanen gidan. Tace duk suna lafiya kuma suna gaishesu. Bayan sunyi sallah sun ci abinci, kayan da ta zo da su suka baje suna duba wa ita da Blood ɗinta, Kalifa yana ta tsokanar su da wai ba sabanba sai wani zumudi suke........


(Gashinan ba yawa dai ban samu lokaci ba ne)


Oum Fatima










*BURINA* 


   

   *NA* 


      *OUM* *FATIMA* 


 *FREE* *BOOK* 


 *HAUSA* *WRITERS* *ASSOCIATION* 

 


 *Page* *12* 


Su dai basu kula shi ba suka yi wucewar su. Washe gari bayan sun karya, shirya wa sukayi suka tafi saloon aka wanke musu kai, akayi wa Abiha kitso Mubeena kuwa cewa tayi bata so dan dama can ba son kitso take ba kuma gashi Allah ya bata gashin, haka Umman ta take fama da ita. Da ƙyar ta bari aka yi mata manyan kalba wadda ta sauko har gadon bayanta, sanna aka yi musu wankin kafa da gyaran farce akayi musu Jan lalle. Sosai suka yi kyau Masha Allah kamar wasu amare.


Sai kallon hannunta take tana sakin murmushi, dan tana son lalle sosai kitsone dai basa haɗa hanya.


Suna zuwa gida Momy ta kalle su ta ce "inye ƴammatan Momy kunyi kyau sosai, Masha Allah". Kalifa ne ya kalle su ya ce "sai wani rawar kai suke wai su yan jami'a, adai bi a hankali don baku wuce kwailaye ba in kuka jera da yammatan Abuja".


B'ata fuska sukayi suna kallon Momy Abiha ta ce "Momy kin ganshi ko? Wai mune kwailaye?".


"Ku rabu da shi kunji ko, haushi ya ke ji zaku wuce birnin tarayya ku bar shi anan". Gwalo Abiha ta yi masa hada kar-kaɗa harshe kamar wata yarinya, da gudu ya bita suka fara zagaye falon sai da Momy tace kar ya sake ya dakar mata ƴa sannan ya kyale ta.


Washe gari Dady ya basu kudi mai yawa ya ce Marwan ya kaisu su yo shopping. Wani babban Mall ya kaisu inda suka ɗebo kaya sosai. Ita Mubeena ta fi son shigar Abaya da Lafaya dan haka duk su ta debo, English wears kaɗan ta ɗebo irin su street sketch, Tomy sketch, palazzo trousers sai Shet Shet ɗin su. Sai su Shoes and bags, sai kayan kwalliya da turaruka. Ita kuma Abiha gwanar kananun kaya duk su ta ɗebo masu kyau da tsada. Haka dai suka dawo da kaya niƙi-niƙi.


Washe gari ta kama ranar Monday ranar da zasu tafi. Dady da kanshi ya kai su har can ya danƙasu a hannun Yayan su. Yayi musu nasiha sosai Sannan ya sa musu kuɗi a account ɗin su yayi musu sallama ya wuce sabgogin sa. Sai gobe in sun huta Yayan su zai raka su makaranta r,su Karasa abinda ya yi saura. 


Shima sallama ya yi musu akan su shirya gobe da ƙarfe 10:00 na safe zai zo ya kaisu, suka ce to. Bayan ya tafi kowa ta zabi ɗakin da take so kasancewar ɗakunan ukku ne a cikin fallown guda biyu daga ciki in ka ɗan bi ta wani corridor zaka same su, sai guda ɗaya daga gefen kiching shi Baba attine ta ɗauka. Su ma Kowa na ta ɗakin ta nufa dan shirya kayanta.


Bayan ta gama kiching ta shiga ta samu Baba attine tana Dan gyare -gyare. Itama kayan ciye-ciyen da suka zo da shi ta fara kintsawa na sawa a fright ta saka. Zuwa magarib sun gama gyara komai yayi yadda suke so, Baba attine ta dafa mausu abu mai sauki suka ci. Bayan sunyi sallar isha'i suka ɗan taba hira kaɗan kowa ya shige ɗakin sa dan ba'a haɗa kayan kallo ba sai zuwa gobe za'a haɗa musu.


Mubeena bayan ta shiga ɗaki wayar ta ta ɗauka ta kira Umman ta suka gaisa, ta faɗa mata sun sauka lfy ta tambaye ta Abiha ta ce tana ɗakinta, tace to ta gaishe ta Abdul ma ya karɓa suka gaisa, sannan ta kira Azima ma sukayi hira kaɗan ta kashe dama su Momy tunda suka sauka suka yi waya a wayar Abiha. Addu'a tayi ta kwanta don gobe ta shirya da wuri kamar yadda Yayansu ya ce.


Washe gari da asuba ta tashi tayi sallah ta leƙa dakin Abiha ta tashe ta, ta leka dakin Baba attine ma ta samu ta tashi. 


Bayan ta gama karatun Qur'ani tayi azkar ɗinta kamar yadda ta saba kullum tayi addu'a. Tashi tayi ta shiga kiching ta haɗa masu break fast sabo da ta saba ko a gida ita ke yi , shiyasa ta kware sosai a fannin sarrafa abinci. Ta karɓi horo sosai a wurin ummanta dan gwana ce a wannan fannin. Kuma ita ma tana da shauƙi akan girki shiya sa bata jin wahalarsa.


Danda nan ta kammala soya doya da ƙwai sannan tayi mata miya dan tun kafin suzo Yayansu ya zuba masu kayan abinci a store, so akwai komai dama. Ta dafa shayi mai daɗi sai tashin kamshi yake. Zuwa karfe 8:00am ta kammala ta jere a dining ta shiga ta yi wa Abiha magana akan ta tashi ta shirya, ta wuce itama dan ta shirya dan Baba attine ta gyara gidan tsaf ta sa turaren wuta da na ruwa ko ina sai kamshi yake.


Ashiye ta fito tsaf cikin shigar Lafaya lace Mai matukar kyau da tsada. Sosai shigar ta karbe ta kasancewar ta doguwa kuma Sanna tana da kyakykyawan jiki, sai lafayar ta zauna sosai ajikin ta kuma ta haska farar fatar ta, kasancewar lafayar dark blue ce. Jaka da takalmin da ta saka baka ke ne haka ma agogo ga wani bakin glass da ta saka afuskarta sai daddaɗan kamshi take fitarwa.


"Wow Masha Allah kai Blood kin ganki kuwa irin wannan wankan na jan magana kar fa ki haɗa Malaman da ɗaliban gwara kawuna ba tare da sun sani ba!". Abiha ce mai maganar itama tayi kyau a cikin shigar Riga da Wando da ta saka sai kimono haɗaɗɗiya data ɗora akai, tayi kyau sosai itama kasancewar ta daman kyakykyawar.


"Murmushi tayi tana cewa kai Blood banda sharri dai ke baki ga yanda kika yi kyau ba"


"Eh amma ai ban kai kiba ". " Muje muyi break fast lokaci na wucewa kinsan Yayammu dai ba jiran mu zaiyi ba" 


"Ok" muje to cewar Mubeena.


Karasa wa suka yi dining area a natse suka karya. Suna gama wa sai gashi ya zo knowking yayi, Baba attine ta je ta bude masa da sallama ya shigo yana gaisheta ta amsa da fara'a tana cewa "ai kuwa sun shirya dama kai suke jira". 


"Ok" kawai yace yana karasa wa cikin fallown. Tunda ya shigo ya sauke idanunsa akan ta ya kasa ɗauke wa. Tayi masa kyau sosai wanda har yake jin kamar kar ta fita a haka wasu kartin banza suyi ta kallon ta, tinawa da hakan kadai yaji ransa na neman ɓaci. 


Fuska ya haɗe ya ƙarasa shiga ya samu wuri akan kujera ya zauna. Abiha ce ta karaso kusa da shi ta zauna tana cewa "Yayammu Ina kwana antashi lafiya". "Lafiya lau alhamdulillah" ya ansa mata yana kai kallon sa kanta tasowa tayi itama daga dining din tazo ta zauna. "Ina kwana ta fada" ciki-ciki ya ansa yana hararar ta kasa-kasa. Kai ta langwabar tana masa kallon "me nayi kuma?. Kansa ya dauke yana mikewa ya ce "muje".


Harya nufi kofa ya jiyo muryarta mai daɗi tana rasta kunnuwan sa. "Yayammu ko zaka tsaya kayi break fast?"


Ji yayi bazai iya mata musu ba kallonta yayi "yace muje ki bani".


"Ok" ta faɗa tana yin gaba yabi bayanta. Abiha kuwa wuri ta samu ta zauna tana kiran Momy a wayar ta. Bayan ta ɗauka suka gaisa take faɗa mata yanzu za su wuce makarantar ga ma Yayansun har yazo. Fatan alkairi tayi musu tace ta gaishe da Mubeena.


Suna zuwa ta haɗa masa tea ta bashi ya fara sha ahankali sannan ta zuba masa doya da miyar. A natse yake ci yana kallon ta kasa-kasa ita bata ma san yana yi ba wayar ta take faman dannawa.


Ji yake kamar kar ta fita a haka yadda tayi kyannan wasu banzayen su kalle ta, gashi dai jikinta duka rufe yake da lafayar sannan fuskarkarta ba wata kwalliya tayiba bayan kwalli da lipstick da ta saka. Amma a haka tayi kyau sosai, ga glasses din da ta saka ya kara fitar da wankan ta fito a wata Classic lady.


Kadan ya ci doyar ya tashi ya goge bakinsa yace su tafi. Sallama sukayi wa Baba attine sannan suka bi bayan sa, suna zuwa Abiha ta Bude baya ta shige itama tana kokarin shiga bayan yayi mata kallon direban ku ne ni. Ba shiri ta rufe ta nufi gaban da ya buɗe mata ta shiga ya tashi motar suka wuce.


A natse yake tuka motar suna hira shi da Abiha, ita kuma tana ta kallon garin. Garin ya mata kyau sosai dan bata taba zuwa ba, wanna shine zuwanta na farko dan haka ta buɗe Ido ta sha kallo abinta har suka karasa. Abiha ta fara fita tana kokarin fita ne ta ji muryarsa yana cewa "Dan Allah Mubeena kuyi abinda ya kaiku banda kula samari kinji in kuma kuka yi zan sani ne" ya fada yana kafeta da Ido 


Kanta ta sadda kasa tana cewa "insha Allah".

Daɗi sosai yaji a ransa jin tace baza ta kula kowa ba. Itafa ya fara bata mamaki, to wai ma Ina ruwansa in sun kula samari ai sun Isa ko.


Fitowa sukayi suka jera gwanin sha'awa, kallon su Abiha ta yi tace Masha Allah kunyi kyau sosai Yaya kamar wasu couples. Da sauri Mubeena ta kalle ta jin abinda ta faɗa, shikuma gogan dauke kai yayi kamar bai ji abinda ta ce ba suka ci gaba da tafiya.


Bayan ya gama musu komai kowa ya nufi inda zai yi lecture sannan ya wuce wurin aikin sa in sun tashi driver zai zo ya ɗauke su.


A cikin farin ciki suka gama ranar su ta farko a makaranta sun ga abubuwa da ya wa, sannan sunga mutane da ban da ban. 


Abiha ita ta far gama lecture ta jira Mubeena ta gama suka wuce gida. Agajiye tuɓus suka dawo, suna zuwa suka tarar Baba attine ta yi musu abinci mai dadi. Wanka suka farayi sukayi sallah sannan suka yi zaman cin abinci.


____________/____


A ɓangaren amarya Rufy kai ya dau zafi ana ta shirye-shiryen biki don bikin yana ta matsowa dukda har yanzu ta kasa samun kan angon duk ydda ta so ya saki jiki da ita hakan ya gaga ra ko kiran ta baya yi sai dai ita ta kira shi damma yanzu in ta kirashi yana ɗagawa su gai sa, ita zata yi ta masa hira Yan ansa mata da eh da A'a amma bata damuba tunda dai ya amince da auren, za azo lokacin da ko kara ta aje ta ce kar ya tsallaka ba zai tsallaka ba.


A haka kwanakin suka yi ta matso wa ɓangarorin guda biyu ko Ina shirye-shirye ya kan kama. Ban garen ango su Momy sun hada lefe na gani na fada har ansa ranar kaiwa.......


Oum Fatima






*BURINA* 


   *NA* 


       _OUM_ _FATIMA_ 


 *FREE* *BOOK* 


 _HAUSA_ _WRITERS_ _ASSOCIATION_ 


 *Page* *13* 


An kai lefe gidan su amarya lefe na gani na faɗa, dan kuwa sosai Dady ya saki kuɗi aka haɗa kaya masu kyau da tsada. Shirye-shirye ya kan kama ta ko wani ɓangare, dan dika-dika saura sati ɗaya ɗaurin aure kuma har yanzu angon bai dawo ba,

dukda yace acikin satin zai dawo. Amarya duk tabi ta damu, dan kuwa sosai ta shirya ma bikin sun shirya event kusan kala hudu amma ango ya ce ba da shi ba. Da ƙyar ta samu ya amince zai halarci dinner kawai shima sai da ta faɗawa Momy tasa baki sannan.


Gaba ɗaya ji yake baya wani zumuɗin auren ko dan ba wani Sonta yake ba.ji yake jikinsa na sanyi in ya tuna da wata daban zai fara aure ba ƙaunar sa ba. Yana jin kamar bai kyauta mata ba, kamar ya ci amanar ta dukkuwa da bama ta san yana yi ba kuma yana da tabbacin ba ma ya gaban ta shiyasa in ya tuna jikinsa yake yin sanyi.


Amma babu komai lokaci yana zuwa da zata sani, kuma ta so shi dan yana ji a zuciyar sa shi aka haifawa ita. Shi kaɗai yake da ikon mallakarta, da wannan tunanin yake karfafawa kansa gwiwa duk da kuwa yana shiga far gabar kar wani ya kusanci zuciyar ta ya samu nasarar ɗauke masa ita.


"Ina ba wanda zaiyi wanna gan-gancin ma" ya faɗa ba tare da yasan maganar ta fitoba. "Kai da waye Man?" Sameer ya faɗa yana ɗago kai daga duba katinan bikin da ke zube a gabansa yana ware waɗanda zai rabawa mutanen su na nan abokan aikin su. Dukda ma wuri ya so ya ƙure musu amma ahakan zai raba, dan tin tini yake fama da angon kan shirye-shiryen bikin amma yaga kamar baya wani ɗokin bikin, don haka shine tsaye akan komai.


"Ba komai manta kawai ". IMRAN ya faɗa yana dafa kansa da yake masa ciwo kaɗan-kaɗan.


"Are you Ok?"


Sameer ya tambayeshi.


"Kaina yake dan mun ciwo bari in shiga in ɗan kwanta".


"Ok Allah ya sauwake, kasha magani sannan, gashi gobe zamu wuce KT".


"I know" ya faɗa yana shigewa bedroom ɗinsa. Shima Sameer ɗin har-haɗa katinan yayi ya dauki wanda zai ɗauka ya aje sauran ya fita daga gidan. Dama ya zo gidan IMRAN din ya nuna masa katinan da ya bugo za su raba wa abokan su Sanna kuma su gashi gobe za su wuce Katsina, saura kwana huɗu darin aure kenan shiyasa yake sin duk ya gama yau.



Ɓangaren Mubeena kuwa Alhamdulillah suna karatun su cikin kwanciyar hankali, ta tattara duka nutsuwarta ta ɗora akan karatunta ba ruwanta da kowa inta shiga maranta iyakarta da mutane in sun haɗu su gaisa tayi wucewar ta in an tashi driver ya zo ya maida su gida.


Dukda kuwa mutane da yawa suna san mu'amala da ita kasancewar ta kyakykyawa kuma mai farin jinin muta ne ba mazan ba ba matan ba amma sai dai wannan kwarjinin nata yake sa musu shakkar ta. 


Hatta kuwa irin tsagerun ɗalibannan suna shakkar ta sabo da ta kame kanta bata banzatar da kanta ba balle wani ya rainata kuma bata shiga sabgar kowa ba. Kullum in basa lectures zaka same ta ita da Blood dinta a masallaci ko dai wani wurin da aka tanada dan hutawar dalibai suna hirarsu.


Bata da Kawa a dependent ɗin su sai wata yarinya Mai suna RUMAISA da suke gaisuwa, ahankali yarinyar ta shiga jikinta har suke ɗan mu'amala zaka gansu tare suna karatu wani lokacin. Kasancewar itama Rumaisa tana da hankali kuma tana da Maida hankali akan kararu shi yasa Mubeena ta ke kula ta dukda bata saki jiki da ita sosai ba.


Yanzu haka sun kusa fara exam nan da da sati biyu zasu fara shiyasa ta yi busy sosai take karatu. Kuma gashi gobe zasu wuce KT bikin Yayansu tare ma zasu tafi ana gamawa zasu dawo suyi jarabawar su sai hutun first semester.


Hakanan kawai taji bata farin cikin zuwa bikin kuma bata bakin ciki kadaran kadahan dai, sai Abiha ce kawai ke ɗoki, da zumudin bikin dan hatta dinkunan su anyi musu anko da komai kawai zuwa za suyi asha shagali. Kallon ta kawai take sadda take nuna mata kayan fitar bikin nasu a waya da ta sa Momy ta turo mata ta zaba masu. Jin tayi shiru yasa Abiha tambayar ta"Blood are you Ok".


"Yes am okay" Mai kika gani" 


"Gani nayi kamar bakya jin dadi"


"No kawai hakanan nake jin zuciyata ba dadi"

"Ayya sorry kiyi addu'a kairan insha Allah"


"Thanks dear" ta fada tana duba wayar ta jin kira na shigowa. Har ya katse bata ɗauka ba, saida aka kira sau ukku Abiha ta ce "Blood ki ɗauka man".


Number ta tsirawa ido, kamar ta so ta gane ta. Wani kiranne ya ƙara shigowa a karo na hudu, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗaga kiran da yake dab da yankewa. Da sllama ta ɗaga, sannan tayi shiru tana sauraren ajiyar zuciyar da ya ke ta saki.


Sallamar ya ansa mata sannan ya ɗora da cewa"bakya tausaya mun wai dan Allah, shikenan tun da kika tafi kika yi blocking ɗina inyi ta kiranki bana samu. Ina cikin damuwa sweet heart Ina cikin damuwa sosai na rashin kula nin da ba kya yi, kinga bani da lfy ma, please sweet heart dan Allah ki bani dama ko mun ƙan-ƙantara ta insha Allah nasan zaki so ni ko da kaɗan ne". Ya karasa maganar kamar zaiyi kuka.


Sosai tausayinsa ya kama zuciyar Mubeena, ta sani Mansoor yana matuƙar son ta tunda tsawon shekara hudu kenan yana ƙoƙarin ganin ya shawo kanta tumma bata ida cika budurwa ba yake son ta kuma bai taɓa zuciya ya rabu da ita ba duk sharesan da take. Kullum ƙoƙarin kyautata mata yake, dan haka ta gamsu da shi ɗin masoyinta ne na gaske dan duk acikin samarin da ke haukan son ta ba wanda yayi juriyar da yayi. Dan haka zata bashi dama amma da sharaɗi.


Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama wannan tunanin tace "I'm sorry Mansoor ba wai wulaƙanta ka nake ba, kawai dai ban shirya ma soyayya ba ne yanzu karatu nake son yi a natse dan cika BURINA shiyasa ka ga na ajiye harkar soyayya a gefe dan ba abinda ya kaita sa mutum shagala ya manta da duk wasu BURIKAN sa da yake son cimmawa a rayuwa. Babu abinda ya kai soyayya rufe idanun mutum ga barin ganin komai sai abinda yake so ɗin.


Ni kuma Ina da BURI a rayuwa da nake son cikwa. Ina son na zama kwararriyar likitan mata, kuma hakan ba zai samu ba har sai nayi karatu, karatun kuma ba zaiyiwu ba sai na natsu na maida hankali na wuri ɗaya sannan. Dan TAURA BYU  bata taɓa haɗuwa a baki." 


Numfashi ta sauke Sanna taci gaba da cewa "Na amince zan baka dama amma da sharaɗi".


Da sauri cikin zumuɗi yace "na amince da ko wane irin sharaɗi ne indai har zaki amince ki karɓi soyayya ta".


"Na amince zan karɓi soyayyarka amma zaka bani lokaci har in gama karatu na nayi maka alkawain zan gabatar da kai a matsayin wanda zan aura in lokacin yayi, amma a yanzu bazaka riƙa zuwa inda nake ba da sunna hira, Sanna bazaka riƙa takura ni da kiran waya ba lokacin karatu ba in ka amince da wannan shikenan".


Ajiyar zuciya ya sauke jin abinda ta ce bashi da wani zabin bayan amince wa da abinda ta ce ɗin dukda ba haka ya so ba. Amma ba komai hakanma ya gode dan wannama nasara ce ba ba a gare shi, ahankali wata rana da kanta zata bashi izinin neman auren ta.


"Shikenan na amince na gode da hakanma".


"Shikenan sai anijima"


"To amma dan Allah zan riƙa kiran ki muna gaisawa ko sau ɗaya ne a rana".


"Ok" ta faɗa tana kashe wayar ta sauke ajiyar zuciya, suka haɗa ido da Abiha, tana ƙoƙarin ɗauke kai Abiha ta ta "wane shi?".


Numfashi ta sauke ahankali sannan ta bata labarin tun farkon haɗuwar su da shi har zuwa yanzu. Ajiyar zuciya Abiha ta sauke sannan ta ce "taɓ gaskiya yayi ƙoƙari, sannan ya cancanci ki bashi dama gaskiya sabo da soyayyar gaskiya ya ke maki tunda har ya jure duk abinda kika masa. Allah ya zaɓa abinda ya fi alkairi"


"Ameen" ta faɗa tana mikewa ta shige ɗakin ta tana shiga tayi duk abinda zatayi ta kwanta.


Washe gari suka wuce KT tare da Yayansu da Sameer, jirgin safe suka bi dan haka da wuri suka Isa, inda suka samu Marwan ya zo daukarsu suka rankaya gida yana ta tsokanar su Abiha da ya makaranta, Yaya makarantar da dadi ko kuwa.


"Sai dai ace Alhamdulillah Yaya amma karatu fa ba sauki sai mutum ya dage". Cewar Abiha, "haka ne Allah y taimaka sai ku dage ɗin ai". Ya fada yana kallon Mubeena da ta lumshe idanun ta, tun da ta gaishe sa bata ƙara magana ba "ya'ya ƴammatan Umma lafiyarki kuwa?".


"Ba komai Ina dan jin ciwon kai ne kaɗan" 


"Subuhanallah, Allah ya sauwake, bari muje kisha magani ki huta zai daina insha Allah".


"Ok" ta faɗa tana maida idanunta ta rufe. Tunda suka taho yake kallon ta ƙasa-ƙasa yadda ba mai ganewa, tun zuwan su ɗauko su ya fahimci bata cikin wal-wala aransa yake tunanin ko mai ke damunta. Duk bayan lokaci yake kallon ta ta madubi, hakanan shima yake jinsa wani iri.


Suna ƙarasa wa gida suka fito cike da murna aka tarbesu, da gudu Abiha ta shige tana kwala kiran Momy itama da fara'a ta tarbeta tana "oyoyo ƴammakranta an dawo".

Mubeena ce ta shigo ita da Baba attine dake ɗauke da wasu kayan sauran kuma mai aikin su ce ta ɗakko. Shigowa sukayi shida Marwan sun tadda gidan ya fara karɓa baki na kusa da suka fara zuwa dangin Momyn sa, hajiya Anna ma an hallaro tuni tana sashenta da aka ware mata. Sama-sama ya gaisa da mutane baiko kula tsokanar da suke masa ba ya shige wurin Momyn sa suka gaisa ya tashi zai wuce sashen sa dan yayi wanka ya huta Shima kannasa ciwo yake masa. Momy tace "kaje ka gaishe da hajiya ta zo tana sashenta".


"Ok" ya ce yana wucewa part ɗinsa dan Sameer tun a airport suka rabu Shima drivern gidan su ya je ya dauke sa.


Yana shiga wanka ya fara yi yayi salla sanna ya ɗan ci abincin da Momy ta aiko masa sanna ya fito ya nufi sashen Annah. Da sallama ya shigo, afallow ya same ta tana lazimi zama yayi suka gaisa tana tsokanar sa da ango, ana ɗaurawa da ita zai tare a Abuja da ita za a ci kayan dadin amarcin. Cewa yayi "ai dama nan kika fi kauri kwaɗayi ba to ba inda zani da ke to" "zamu gani ai ta faɗa" tambayar sa ya ta ganshi haka mai ya sameshi, ya ce ba komai.


Yana fitowa daga nan part ɗin Dady ya nufa, a fallow ya same shi yana kallon labarai. Guri ya samu ya zauna a natse ya gaishe shi, ya amsa masa da kulawa yana tambayar sa hanya sannan ya tambaye shi shirye-shirye yace "alhamdulillah", nasiha sosai yayi masa sanna ya tashi ya nufi part ɗinsa yana daga kiran Rufy da take ta Kiransa tun yana wurin Dady........


Please comment and shere fisabillah


 _Oum_ _Fatima_ 


Oum Fatima









*BURINA* 


       *OUM* *FATIMA*


    

   *FREE* *BOOK*


 


 *HAUSA* *WRITERS* *ASSOCIATION*


 *Page* *14* 


*** Saida ya ƙarasa ya samu wuri ya zauna sanna ya amsa wayar ta ta. Tana jin ya ɗauka ta fara masa ƙorafi, "haba dan Allah Honey me yasa kake mun haka, kar ka manta fa yau saura kwana huɗu aurenmu amma inyi ta kiranka baza ka ɗauka ba. Dama kai baka kirana, nice mai kiran ka amma ahakan ma baza ka bani lokacinka ba me yasa?. Ta karasa fada kamar zata yi kuka.


Iskan da ya zuƙa abakinsa ya fitar sannan ya ce "I'm sorry Rufaida Ina tare da Dady ne kike kira". Numfashi ya sauke sannan yaci gaba da cewa.


"Ke kuma bakisan in kin kira mutum baiyi picking ba kiyi masa uzuri ba".


"Shikenan mubar wanna maganar, yanzu yaushe zaku zo ku hadu da kawaye na kaga mu tuni har mun fara bikin mu".


"Ai na fada maki dinner kawai zan halarta".


"Shikenan to"


"Send me your account number. Zan sa maki kudi kuyi duk abinda zakuyi ba sai mun haɗu da wasu kawaye ba".


"Ok" 


tace sannan ya katse kiran. Wayar ta bi da kallo haushi kamar ya kashe ta, sannan ta yi ƙwaffa tana cewa "it's your time, nima nawa time din yana zuwa" 


ta fada tana kallon kawarta Nadiya.


"Ba zaizo ba ko?" 


kai ta daga mata kawai.


"Hm aiko me ya maki ke kika ja, kin bi kin nace masa kamar ba Rufyn da nasani ba babbar yarinya Mai aji, haba da Allah".


"Hm baza ki gane ba Nadiya, ya kai a nace masa ne".


"To ai shikenan Allah ya bada sa'a" 


ta fada tana cewa bari in kira Wanda za su shirya mana wurin da zamuyi bridal shower ɗin gobe, wai ankawo kayan da zakiyi amfani da su din?".


"Eh Momy tace tayi order daga Dubai so Ina tunanin sun iso".


"Ok ba matsala" 


cewar Nadiya tana duba wayar da ke hannun ta.


_______ /_


Ɓangaren Mubeena kuwa bayan ta gama gaishe da mutane ɗakin su ta wuce tayi wanka Abiha ta shigo musu da abinci, kadan taci ta sha magani ta kwanta dan da nan barci ya ɗauketa sabo da dama tana bukatar hutawar.


Sai la'asar ta tashi ciwon kan ya mata sauki, sallah tayi ta wuce sashen Annah suka gaisa take tambayar ta Umman su sai yaushe zata zo, Annah ta ce


 "sai gobe in Allah ya kaimu, driver zai je ya dakko su, ai da tare zamu taho to ta tsaya ƙarasa soye-soyen kayan bikin ne".


"Ok Allah ya kaimu, bari in kira ta inji" ta fada tana daukar wayar ta ta kira Umman bayan sun gaisa take faɗa mata Besty zata biyo ta su taho tare.


 "Ok ba matsala sai ki ce ta shirya da wuri" 


"To Umma sai kun karaso", "Ina Abdul?"


" Baku hadu ba? Ai tare suka taho da hajiya".


"Ok bamu hadu ba kila suna tare da Kalifa Dan shima ban gan shi ba".


"To sai anjima Umma" 


ta fada tana kashe wayar. Azima ta kira bayan ta ɗauka tace "Besty ki shirya gobe da wuri zaku taho keda umma".


"Ok Allah ya kaimu"


 cewar Azima, hira suka taba kadan anan take fada mata yadda sukayi da Mansoor, sosai ta ji daɗi sabo da Allah ya sani tana san taren su da Mansoor, sabo da mutumin kirki ne bashi da wata makusa sannan yana mata so mai tsana ni.


Sallama sukayi akan sai sun haɗu goben, sai dare ta koma part ɗin su bayan ta gama shirin baccinta ta kwanta suna taba hira ita da Blood ɗinta kiran Mansoor ya shigo wayarta. Sai da ya kira sau ukku sannan ta ɗauka suka gaisa ya tambaye ta ya karatu take faɗa masa ai suna gida sunzo bikin Yayansu.


Yace "Aikau nima Ina Katsinan daman kinsan ke kike kaini Dutsimma, yanzu da ba kya nan ba sosai nake zuwa ba. Insha Allah zan zo ɗaurin auren dan an gayyaci Dady na ma".


Bata ce kar yazo ba sukayi sallama ta yi addu'a ta gyara Kwanciyar ta.


___________ 


Washe gari ta kama ranar da amare zasuyi bridal shower, wani babban whole suka kama, anshirya wuri sosai ya tsaru daga gani an san bikin na manya ne.


Da kyar Abiha ta shawo kanta ta amince da zuwan su bridal shower ɗin. Bayan la'asar suka shirya da wasu ƴammatan daga cikin ƴaƴan dangin Momyn da suka zo zasu tafi tare.


Dukda kuwa wasu daga cikin ƴammatan suna jin haushin auren dan akwai masu san IMRAN din aciki.


Tayi kyau sosai acikin shigar lace ɗin da sukayi anko ita da Blood ɗinta, ɗinkin doguwar riga da ya zauna sosai ajikin ta yayi mata kyau. Lace ɗin milk colour ne sai Golding da akayi masa kwalliya dashi, sai tayi amfani da Golding ɗin mayafi takalmi da jaka kuma tasa milk lite make up ce a fustarta wadda ta fitar da sihirtaccen kyanta mai sawa a shagala a kallonta. 


Sosai tayi kyau, sai yaba kyan da tayi Abiha ta ke tana ta kashe musu selfie, wasu daga cikin yammatan kuwa sai taɓe baki suke yi irinna hassada.


Fitowa sukayi daga cikin gidan su biyar ita da Blood, sai Besty sai biyun sun kasance ƴaƴan yayun Momy ne Samha da Hasina. Tunda suka fito farfajiyar gidan ya ganta ya kuma kasa ɗauke idanu akan ta, kamr yadda duk abokansa suka zuba mata idanu.


Ji tayi idanu sun mata yawa duk taji ta tsargu, ahankali ta ɗaya idanunta basu faɗa ko Ina ba sai tsakiyar nasa idanun da yake mata wani irin kallo Wanda ba kowa zai fahimta ba.


Da sauri tayi kasa da kanta tana jin faɗuwar gaba. Shima kansa ya maida ga abokan shi da gaba ɗaya hankalinsu yana kan yaran musamman ma ita. Nan take yaji ransa yayi masifar ɓaci, ya ja tsaki yana fadin "kai da Allah ku dawo hankalinku kuka wani tsirawa yara ido salon kuja wa mutane raini kawai" 


ya faɗa yana maka musu harara.


"To uban san girma ka sani ko mun gani mun yaba ne, ni Allah tun da na fara ganin ƙanwar nan taka da muka je ɗauko su da zamu taho, naji ta sace zuciya ta please man kashige man gaba mana".


 ya faɗa yana kallon IMRAN da yake masa wani shegen kallo mai ɗauke da jin haushi, ya ɗauke kai kawai ba tare da ya bashi amsaba.


Murmushi kawai Sameer yayi ya dauke kan Shima. Yana sane yayi maganar sabo da ya fi kowa sanin abokinsa, ya ga kuma take-taken sa yana so ya tabbatar da abinda yake zargi ne.


Suna ƙara so wa kusa da su suka gaishe su, suka amsa da fara'a su Samha sai iyayi ake anga manyan guys masu aji da naira.


"Ina zaku je"?" 


Ya tambaya yana kallonta. Ahankali cikin natsuwar ta da ake ma kallon Jan aji ne tace


 "zamuje bridal shower ɗin amaryarka ne".


 ta faɗa tana kallon sa itama.


"Ok" ya faɗa yana mikewa "muje" 


ya faɗa ya nufi motar sa ba tare da ya kula kowa ba. Tsaye sukayi suna tuna nin suje Ina? Jin bata biyo shi ba ya sa shi juyowa ya kalleta.


 ba shiri tabi bayan shi suma sauran suka rufa mata baya suna mamakin lallai wannan yarinyar ta samu matsayi a wurin Yayansu. 


Suna zuwa ya bude mata gaba ta shiga ya rufe, Abiha da Azima suka shiga baya. Ganin motar baza ta ishe su ba ya sa Sameer tasowa ya ɗauko wata motar ya ɗauki su Hasina ya cewa abokan su yana zuwa Sanna suka tafi.


Inda ake bikin ya kaisu ya ce kar su daɗe, sannan  suka koma gida wurin abokan su da ke jiransu.


Anyi bridal shower lafiya amarya ta tarbesu da murna ta karrama su dukda, da Abiha kaɗai ta sani a matsayin ƙanwar sa. Amma hakanan taji wannan yarinyar Mai kama da mijin da zata aura bata mata ba kwata-kwata, amma dai ta danne bata nuna ba ta karrama su da kayan biki iri-iri.


Ana kiran magriba suka kira driver ya Maida su gida da kayan biki niki-niki.....


(Domin tallata maku hajar ku zaku iya magana da ni kai tsaye a number ta kamar haka ***)


 _Oum_ _Fatima_










*BURINA* 



      *OUM* *FATIMA*



         *FREE* *BOOK*





 *HAUSA* *WRITERS* *ASSOCIATION*



 




 *Page* *15* 




*** Washe gari su Mamy Aisha suka iso ita da yaran ta, Nusaiba ta haɗe da ƴan uwanta suka cigaba da hidimomi su, Hammad ma ya haɗe da su Kalifa da Abdul.


Bangaren amarya kuwa sunci gaba da gudanar da bikin su, duk abinda suka tsara sunyi shi cikin wadata da facaka da kuɗi. Dan kuwa bikin ƴar tsohon gwamna ake sannan ƴa ɗaya da mahaifiyarta ta mallaka a duniya, babbar ƴar kasuwa da take shigo da kayayyaki daga kasahen duniya, zata aurar da tilon yarta kuɗi kam sai dai ace Allah ya basu hakuri.




Yau ta kama ranar Assabar ranar ɗaurin aure kenan. Ranar farin ciki ga ahalin guda biyu, ranar da ta kasance ta musamman ce awurin amarya RUFY ranar da BURINTA zai cika na mallakar gwarzon da yammata ke rubibi. Sai gashi ta samu nasarar ɗauke tsoka ɗaya a miya, dan haka dole ranar ta zama ta daban a cikin da ban.


Amma a bangaren ango ya kasance sabanin yanayin da amarya take cikine. Dan kuwa ya tashi da maban-banta yanayi ne. Kamar yanajin far gaba, kamar wani irin ɗaci da rashin daɗ…