24
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 24```
________ Kai tsaye Faisal gidan su ya wuce,ranshi a dagule da abubuwan da suke shirin tunkaroshi.
Daga yanayin tsari da hadiman dake jeka ka dawo a tsakankanin sashen kasan sashen mutanen da suka fi kowa matsayi ne a cikin gidan.
Mom Zuwaira( Mahaifiyar Faisal) da Dad É—in shi a zaune suna hira jefi-jefi cikin izzar da suka É—orawa rayuwar su.
Cikin girmawawa, ladabin da tsananin tsoron Mahaifinshi da aka horar da su akai ya gaishe su, Mommynshi ce kawai ta amsa, amma Dad ɗin bai kalli ko da gefen dayake ba, sai tambayar daya jefo mai" mai kake zuwa yi ƙauye Faisal?"
Bai bashi damar magana ba, ya ɗora da faɗin"kar ka bari naji wani labarin da zai saɓa abinda nake tunani" Ya faɗa cikin izzar daya riga ya ƙama jikin shi.
Jikin Faisal har rawa yake yi gumi naɗan tsatsafo mai ta goshi, cikin kamewa da ƙoƙarin ɓoye ainihin halin dayake ciki yace
"In sha Allah Daddy ba matsala"
Kai kawai ya jinjina mai, kafin ya sako mishi hirar Maysarah da ya tsole idanuwan dukkan su.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Baba Isiyaku da kanshi ya kawowa Inna kuÉ—i ma su yawa na kula da Halima, har lokacin bai gama dawowa hankalinshi dakyau ba, saboda wasu lokutan haka zaiyi ta surutu shi kaÉ—ai.
Bayan kwana arba'in É—in Halime, Inna ta tattara kayanta dana Halima suka nufo Birni.
Babu wanda baya tanka kyawun Halima,haka Jama'ar gidan da maƙota sukayi ta shigowa da sunan ƙara ganin Jaririya da kuma gaisuwar Halime, alhali tsabar gulma ne yake shigo da su.
A daren ranar da Inna ta sauka ƴan uwan Baba Shehu suka ƙara haɗa baki kan Inna ta mayar da Jaririyar da ta ɗauko kada hidimar yayiwa Baba Shehu yawa,wannan karon Mahaifin su dake kwance ba lafiya ne ya tsawatar mu su, maimakon su bar zancen sai Matan su,suka ƙara zugo su.
Shi kan shi Baba Shehun kunyar tunkarar Inna da wannan maganar yake yi,amma saboda son ya farantawa Ć´an uwanshi rai, ya tukareta da zancen.
Ba iya Baba Shehu kaÉ—ai ba, har Ć´an Uwanshi sai da Inna ta wanke su tsaf a tsakar gidan babban gidan, ta kuma yi rantsuwar matsawar zatabar gidan Shehu to sai dai ya sake ta,idan ta tafi, ta tafi kenan.
Sakin Saude abune da bazai yiwuba awajen Baba Shehu,shima kuma yana ganin rashin adalci ne raba Inna da Jaririyar jikarta.
Bai ƙarabi takan zugar ƴan uwanshi ba,saboda duk hidimar Halima babu ko kwabon shi aciki, don haka makwanci bazai sa ya saki Matarshi ba.
Sana'a kala-kala Inna ta kama,kaya ma su kyau man shafawa maikyau,makwancinta shi kanshi sai da Faisal yasa aka gyara É—akin Inna duk ta hannun Bala.
Halima na ta wayo tana ƙara girma,bazakace ƴar Halime bace saboda Banbancin komai na su.
Yawan tanka kyawunta da mutane suke yi,yasa ko fita tayi wasa da Yara Inna bata bari.
Daga baya ta lura Haliman ita kanta ba maison wasa cikin mutane ba ce,ga rashin son hayaniya.
Tana shekara uku Inna ta sanyata a Makarantar kuÉ—i,tare suke zuwa,da zarar lokacin tashi ya yi Inna zataje ta É—aukota, tunda Babangida baya zama kullum yana Kasuwa.
Hakan da Inna take yi da Makarantar ƙuɗin da Halima take zuwa baƙaramin sosa ran su yake yi ba,uwa uba kyawun Halima wanda idan baka sani ba sai ka ɗauka ruwa biyu ce,kuma bakomai ya jawo hakan ba, kyau ne ya haɗe da tsananin tsaftar da Inna bata gajiya wajen yi.
Zuga Mazajen su suka fara yi, wai Inna bata kare mutuncin aurenta dana gidan su, kullum tana titi kai yarinya Makaranta da kuma ɗauko ta,sai kace ƴar gwal, banda haka ma, a ina Inna take samun kuɗin dukka hidimomin da take yi har da gyaran ɗaki?,a wannan karon harda zugar Inna Huwaila aciki,domin ko ishashen barci ta daina samu tsabar Haddasar daya hanata sukuni ...✍🏻
Kuyi manage bayawa
Nafisa
***