25
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 25```
________Wannan karon ko muhimmanci Baba Shehu bai bawa zugar ta su ba,balle har ya tuntuɓi Inna akai.
Tun suna ƙunƙuni, har kowa ya gaji ya zubawa sarautar Allah ido,ga shi ba daman samun koda ƙwaɗe Halima ne, saboda kullum tana ɗaki.
Cikin ƙaddarar da Ubangiji yake zartarwa bayinsa, Halima na ta ƙara girma, tsananin kyawun da ta gado Uwa da Uba,na ƙara bayyana.
Lokacin data kai shekaru bakwai sai Inna ta ƙara tsaurara ɗaukota daga Makaranta domin tun kafin lokacin ta shi ya yi,take zuwa ta jirata,saɓanin da, da sai bayan antashi take zuwa, bakomai kuma yaja hakan ba sai raɗe-raɗin da takeji abakin yara sa'annin Halima na cewa wane yace yana son Halima wane shima yace yana sonta,tasan kuma dama kaɗan zasu samu suyi amfani da shi.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Mubeena ta haifi kyakkyawar ƴar ta Mace, Sunan Mahaifiyar Faisal aka sa mata, sunayi mata kara da Sanam,kafin zagayowar shekara sai ga Mubeena taƙara haihuwa,abin mamaki kafin wani shekara ɗayan ta ƙara haifar wani,ba kuma komai ya sa Mubeena take haka ba, sai don cirewa Faisal tunanin kawo mata Halima cikin gidanta. Tsaf Faisal ya karanci ina ta dosa, amma bazai hanata ba tunda jikinta ne,sai dai bayajin akwai abinda zai sa ya karya alƙawarin daya ɗauka.
Haihuwar Mubeena akai-akai bai kawo komai aran Uncle Suraj ba sai son ta dabaibaye mi shi ɗa ita da ƙwadayayyen Ubanta.
Cikin ɓacin rai ya nemi Faisal awaya bayan ya samu labarin ƙarin haihuwar Mubeena a karo na uku, har yagama faɗan da zai yi Faisal baisamu zarra cemishi komai ba,sai haƙuri da ya yi ta ba shi,saboda har ga Allah bashida abin cewa, kowa yaga Mace wayayyiya kamar Mubeena na haihuwa haka akai-akai dole yasan akwai wata manufa aƙasa.
Ta farko da ta ukun duk Mata ne na biyun kuma Namiji ne. Ta hora su akan alfahari da wulaƙanta duk wani na ƙasa da su kamar yanda iyayenta suka tarbiyantar da ita,ba don komai ba, sai don ko da Halima ta zo su kaɗai sun isheta,a wannan ɓangaren Faisal bai karanci ina Mubeena ta dosa ba tunda dama alfahari da jin kai tambarin su ne.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
A tsarin shiga, da siɗewar da fatar ta tayi da mayukan sa haske, kai tsaye bazaka iya tantance asalin ƴar wacce ƙasa bace, hatta gashin kanta ba asalin na ta bane, hular gashi ne mai tsadar gasken daya ɓoye na ta aciki tamkar babu shi.
A haka ta shigo parlourn ko sallama ba bu,hararar da ke fidda bacin rai Mom Fahima ta sakar mata da gefen ido tana yimata alama da Abdulnaseer dake zaune yana aiki a system,domin tasan baƙaramin aikinta bane ta wuce batare da tagaishe da kowannen su ba.
Fuskar da batason gani saboda idanuwanshi dake tuno mata da Maysarah ne ya juyo da su, yana amsa gaisuwarta,ba shi da fara'a sam a fuska kamar yanda fuskar ɗanshi Maysarah yake, amma zuciyar su mai kyau ce ga waɗanda suke ƙarƙashin su da duk wani mai mu'amalantar su, amma Banda Sumayya da Uwar riƙonta Mom Fahima.
Bai tambayeta daga ina take ba, saboda ya dade da share duk wani lamarin Sumayya acikin kanshi da kuma cireta amatsayin wacce yake burin Maysarah ya aura.
Bayan Sumayya ta wuce, Mom Fahima ta ƙara matsowa kusa da shi,tana gyaran murya.
Hakan yasa ya jinkirta aikin dayake yi, ya zuba mata idanuwanshi masu hanata rawar gaban hantsi kamar dai na Maysarah.
"Na ce ba,baka ƙara tuntuɓar Maysarah da zancen auren su da Sumayya ba,bai kamata ace har yanzu Maysarah ba shi da Iyali ba,sannan dole yakamata kayi mishi ya auri Sumayya saboda ita ce ta dace da shi, itace kuma zata juri waɗannan bauɗaɗɗun halayyar na shi, ko yaya kake gani?."
Ta faɗa tana sakin ajiyar zuciya samun daman amayar da maganar da ya maƙale mata kwana da kwanaki,da kuma fatan Allah yasa ya amshi zancenta....✍🏻
Me kuke gani shin ya Sumayya da ce da Maysarah kuwa??