MAI KWAĆŠAYI

26

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 26```


________Ya ɗauki wasu daƙiƙu yana ƙare mata kallon, yarasa yaushe Fahima zatasan ta girma, ta daina hange da kwaɗayin dukiyar da ba na ta ba, yanda ta san adadin abinda Maysarah ya mallaka ko shi kan shi dayake Mahaifinshi bai sani ba.

gyaran murya ya yi,yana ƙoƙarin danne fushin shi kafin ya fara magana.

"Bani da ra'ayin Maysarah ya yi irin rayuwar danakeyi,kuma yanada damar zaɓar Matar dayake so,no need mu takuramai,duk wacce ya kawo yanaso da kanshi i have no choice,so please banason muƙara maganar nan dake". Ya faɗa yana cigaba da aikin shi.


Kamar ya É—aure ta haka ta kasa motsi,maiyake nufi?tasan indai don Maysarah yace yanason Sumayya ne, to har abada Sumayya bazatayi aure ba.


Tsaki ta yi ƙasa-ƙasa yanda bazai jiyo ta ba, ta tashi ta bar parlourn ranta na suya.

Bai damu da halin da zata shiga ba, saboda farin cikin su bazai kashe rayuwar ĆŠa guda É—ayan da Allah ya bashi ba.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Kullum idan Inna zata je kai Halima Makaranta sai sun haÉ—u da Yusha'u a hanya, tun Inna bata tunanin maiyake kawo shi hanyar har ta fara,a iya saninta Yusha'u kasuwa yake zuwa neman kuÉ—i,kuma tasan ba shi da kuÉ—in saka É—anshi a Makarantar da Halima take zuwa.

Tunanin fakon Halima ne yake kai Yusha'u hanyar Makarantar su yasa Inna shiga cikin zullumi,bazata yarda Yusha'u yaƙara kassara mata rayuwar jininta a karo na biyu ba.


Kai tsaye shugaban Makarantar su Halima tayiwa maganar abinda ya ke tsakaninta da Yusha'u,kuma yanzu tana ganin shi a layin Makarantar,ita tanaso idan da hali zata cire Halima, gudun mugun abinda Yusha'un yake shiryawa. Kwantar mata da hankali ya yi,ya kuma yi mata alƙawarin daga ranar bazata ƙara ganin Yusha'u a hanyar Makarantar su ba tunda ba sana'a yakeyi awajen ba.



Duk yanda Inna taso Halima ta zama wajen ƙauracewa wasa da yaran gidan sai taga Haliman ma har ta fita son hakan,ƙawayenta na Makaranta kawai take wasa da su,idan ta dawo gida always tana cikin ɗaki sai idan uzurin toilet ya fito da ita. Duk iya kushe-kushen Inna Huwaila takasa samun abun tankawa kai tsaye ajikin Halima,wannan dalilin yasa tsanar Halima ya samu babban matsuguni a zuciyar Inna Huwaila sama da wanda tayiwa Mahaifiyarta (Halime).


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


BARI KADUNA STATE 


11:30am


Duk girman gidan babu wani hayaniya kamar kwana É—aya baya daya wuce,ko ina na gidan tsit sai tsofaffi ma su gadi da sojojin dake É—an zirga-zirga,duk wanda yasan gidan da mutanen da suke ciki yasan akwai dalilin Ć™auracewar shige da ficen su dama hayaniyar su da baya Ć™arewa, haka sababbi kuma Ć™osassun motocin da akayi parking a parking lot É—in gidan.



Sanyi Ac da ƙamshin shi ne suka cika ɗakin duk da kwanan shi ɗaya adakin,

Kwanciyar rub da ciki ya yi, duk da ya kwanta a karkace gadon bai ƙarasa cinye dukka tsahon shi ba, sanye yake cikin Mr Porter Pyjama,a zahiri kamar mai barci amma staf yakejin kiran da tsohuwar Kakarshi take ƙwala mai.


"Maysarah! Maysarah!"a haka ta ƙaraso har ɗakin dayake asalin mallakinta,bai sawa ɗakin key ba, don haka kai tsaye ta buɗe ƙofan.

"Wani irin kwanciya ne wannan Maysarah, kwanciyar ƴan wuta?" Ta faɗa tana riƙe haɓa."au kace gadon ma kaɗan ya yi maka, to ai sai nasa aƙeramaka naka na daban,maza tashi ba'ayimin irin wannan barci isar acikin gidana" ta faɗa tana tana kai mai duka.

A hankali ya juyo da Lion face ɗin shi.....✍🏻