Page 19 & 20
*SU MA 'YA'YA NE*
Da
Alkalamin Ummulkhair Abba Muhammad.
*Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai*
Page 19 & 20
Na daɗa fashewa da kuka na zube a ƙasa, ina cewa iyayena su yafe ni, mahaifiyata ta ɗago ni muka nufi ɗaki ta zaunar da ni, ta rarrashe ni har sai da na yi shiru. Gaskiya soyayyar iyaye ga ‘ya’yansu soyayya ce ta daban da babu irinta a duniya duk fushi da suka yi da kai kana shiga cikin mawuyacin hali su za su fara tallafa maka.
Ummata ta yi mini alƙawarin in sha Allah zan koma gidan mijina za ta samu mahaifina su tattauna.
Tana tunƙarar mahaifina ya ce ba damuwa Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri.
WASHEGARI
Suka ƙira ni bayan na zo na zauna a gabansu, suka faɗa mini hukuncin da suka yanke sun amince da na koma gidan mijina, na ji daɗin hakan sosai a raina. Kana suka gargaɗe ni da na san da wa zan ƙulla abota, sannan duk abin da zan yi kar na yi kai tsaye na shawarci iyayena ko mijina don duk duniya ba ni da tamkarsu da adashen da nake ko kuma sarkokina da na damƙawa ƙawata da na shawarci ɗaya daga cikinsu da ba zan tafka wannan asara ba, suka yi mini fatan Allah ya kiyaye gaba na amsa da amin na miƙe na bar wurin.
Online na hau na yi dace Abba ya hau take na yi masa sallama bai buɗe ba, da na ga haka kai tsaye na rubuta masa da iyayena sun amince da komawata ya zo da daddare ya ɗauke ni da ya buɗe ya karanta a tunanina zai yi mini reply na ya ji daɗin hakan mintuna ashirin na shafe yana online ina online bai ce komai ba.
Kawai na kashe datar na ajiye wayar. A zuciyata na ce, “Abba ya yi fushi da kalaman da mahaifina ya faɗa masa. Abba don Allah kar ka guje ni, kar ka rabu da ni idan ka yi mini haka tamkar ka salwanta rayuwata ce.”
Na ɗauki wayata na ƙira number shi 5 missed call bai ɗaga ba, na kuma hawa online da zumuɗin ganin amsar shi sai na ga har yanzu bai sauka ba kuma bai yi reply ba.
Ƙwalla na sauka a idanuna na duba contact na abokinsa Hashim sai na ga last seen nasa tun jiya da daddare bai kuma hawa ba, kawai sai na sauka a online, na ƙira number shi aka ce da ni switch off na yi jugum tare da rafka tagumi.
Na miƙe na fita don taya mahaifiyata aikin gida, bayan mun kammala na kuma hawa online Abba ya sauka amma ba saƙonsa da ya shigo, da na duba Hashim sai na ga yana online wani sanyi na ji a raina don saboda ko ba komai idan na faɗawa Hashim abin da ke tafiya zai samu Abba kuma zai saurare shi.
Voice note na yi na faɗa masa komai, da ya saurara ya ce da ni na kwantar da hankalina zai tafi wurinsa direct yanzu haka, kuma a daren yau in sha Allah za su zo su na koma gidana.
Tattausar murmushi na sake dalilin karanta saƙon, na yi wa Hashim godiya tare da addu’a na fatan alheri. Ya ce ba komai yi wa kai ne da haka muka yi sallama.
Hashim ya samu abokinsa ya yi masa faɗa sosai ya kuma ce da shi idan har bai canja halayyar da yake nunawa Ummi ba zai iya rabuwa da shi. Abba ya yi masa alƙawarin zai gyara in sha Allah.
Kamar yadda Hashim ya alƙawarta wa Ummi da daddare za su zo cikin yardar Allah sun je, aka taɓa hira kaɗan Abban Ummi ya yi musu nasiha gabaɗayansu, ya juya kan Ummi ya yi mata faɗa sosai ya kuma dinga ba wa Abba haƙuri yana cewa, “Gaskiya yaro ka yi haƙuri ashe haka yarinyar ta dinga yi maka? Yau da bakinta ta dinga faɗa mana abubuwan rashin ɗa’a da take maka kake shanyewa, da ta kai ka maƙura tura ta kai bango tukun ka sake ta. Ina fatan hakan da ya faru da ita ya zamar mata aya ta gyara ƙura-ƙuranta. Na ja mata kunne ko yatsa kar ta kuma ɗaga maka, idan ta maka laifi ka yi mata faɗa ta ƙi ka same ni, ku guji dukan juna a zamantakewar aure yana ɗauke albarka. Allah ya yi muku albarka.”
Shi dai Abba kasancewar bai san abin da Ummi ta faɗawa iyayenta kawai sunkuyar da kai ya yi ƙasa ya ce, “Ba komai Abba, Allah ya ƙara mana fahimtar juna. Mun gode sosai Allah ya ƙara girma.”
Hashim ya yi sayayya ma iyayen Ummi mai yawa yayin da suka miƙe ya ajiye a gaban iyayen Ummi.
Suka yi gaba Ummi na bin su a baya, suna zuwa daidai mota Hashim ya bude mata seat na gaba, “Allah ya ja zamanin Maman twins Bismillah.”
Murmushi na yi kawai na shiga na zauna, Hashim shi ma ya zauna a seat na baya Abba ya ja mota.
Abba yana tuki a zuciyarsa ya furta, “Irin maganganun da mahaifin Ummi ke yi kuma yana danganta ta da laifin da ba ta da shi, ni mai laifin kuma yana ba ni haƙuri, anya Ummi ba wanke ni ta yi a gaban iyayenta ba, ta kuma jingina laifin ma kanta? Idan har hasashen da na yi ya tabbata haka ya kamata na ajiye maƙaman yaƙina mu zauna lafiya da Ummi. Duk da dare ne kallo da na yi wa Ummi juna biyu da take ɗauke da shi na nan daram ai furucin da Hashim ma ya yi ya isa na gaskanta.”
Suka ajiye Hashim a gidansa, sai suka nufi nasu gidan.
Bayan mun watsa ruwa, muna zaune a bedroom Abba ya tambaye ni da don Allah na faɗa masa abin da na faɗawa iyayena dangane da saɓanin da muka samu don maganganun da mahaifina ya yi masa bai fahimce su ba. A yadda na tsara ba ni da niyyar faɗawa Abba hanyar da na bi don samun sulhu a tsakaninmu, amma da ya buƙaci ji sai na faɗa masa.
Na durƙusa a gabansa cikin nuna kaskantar da kai na ce, “Abba don Allah ka janye ƙudirinka dangane da juna biyun da nake da shi ba mu san alherin da ke ɗauke da wannan haihuwar ba.”
Ya sauke ajiyar zuciya, “My dear na saduda na bar wa Allah lamarinsa, Allah ya raba lafiya. Allah ya sa ki haifa mini soja.” Murmushi na yi kawai ban ce kanzil ba.
Daren wannan ranar Abba ya nuna mini tsantsar so da ƙauna, ya jiyar da ni daɗi mun kashewa juna ƙishirwar sha’awar da muka daɗe da ita tana addabar mu.
Abba dai mutum ne mai juyayyen ƙwaƙwalwa, ba mu shafe wata ba muka koma zaman doya da manja, ya kuma dawo da halayyarsa sai dai zan iya cewa ba kamar na baya ba, watarana zai dadaɗa, watarana kuma ya sauya, a duk lokacin da ya sauya fita a harkarsa nake ba na biye masa ya gama hauragiyarsa ba zan ce da shi kanzil ba. Don na fuskanci idan na ce zan dinga sa’insa da shi to zai iya haifar da matsala. Da na haifu na samu ɗiya mace ko ɗaukar ɗiyar bai yi ba ballantana ya nuna murnarsa, saura kwana uku suna ya tsallaka ya bar garin ba tare da ya bar mini ko sisi ba, na shiga tashin hankali dalilin haka, Allah mabuwayin sarki Hashim ya tura mini dubu ɗari ya Nabil dubu talatin wannan kuɗaɗen na haɗa da ma na sayar da wani zoben gwalna 70k sai na miƙa mata 200k na ce da ita Abba tafiyar gaggawa ta kama shi ga abin da ya bayar a yi hidimar suna. Da ma Abban Hashim tun da ya samu labarin haihuwar ya aika mana da rago da buhun shinkafa.
Tun da na sauƙa lafiya nake bin shi wanne suna za a sa wa jaririya ya ƙi ba ni amsar daga ƙarshe ya ce duk sunan da ya yi mini sai na zaɓi suna Sumayya.
Kamar yadda al’ada take a haihuwar fari mata kan tafi gidansu wankan jego haka ni ma Inna ta matsa da sai na je ba ta ga amfanin zamana ba miji ba ya gari ban so hakan ba na fi so na zauna a ɗakina ba don komai sai don halin Abba kar ya ƙi zuwa kuma kar ya ƙi aika saƙo iyayena su fahimci zamantakewarmu, amma idan a gidana ne babu wanda zai fahimci hali da nake ciki.
Abin da nake tsoro shi ya faru na shafe sati biyu babu aike babu aikarwa daidai da waya ba ya ƙira idan na yi masa magana a online ba ya kula ni, kuma abokinsa Hashim ya faɗa mini ya dawo daga tafiyar da ya yi.
Tun Inna ba ta ƙorafi, ta fara tana cewa mutum ko dabba ya ɗaure ya kamata ya waiwaya ballantana matarsa da ‘yarsa.
Ban ɓoye damuwata ba na faɗawa Hashim halin da nake ciki ya ce kuwa in sha Allah a daren yau za su zo.
Da kaya niƙi-niƙi suka zo kuma ina da yaƙinin Hashim ne ya yi wannan sayayyar, ba su tarar da mahaifina ba saboda ya fita, da Inna kawai suka gaisa, suna gaisawa ta miƙe ta ba mu wuri.
Da fara’ata na gaishe shi ciki-ciki ya amsa. Na juya na gaishe da Hashim ya amsa da fara’a har da tsokana, “Ni ina ta cewa Maman twins ashe ke dai ɗaya za ki haifa mana, to Allah ya sa next year ki haifo mana twins ɗin kuma mata don ni a rayuwata ina son ‘ya’ya mata.”
Abba saurin ɗago kansa ya yi jin furucin abokinsa yana masa fatan abin da ya tsana a rayuwa.
Hashim yana matuƙar son ‘ya’ya mata sai dai Allah bai arzurta shi da su ba har yanzu ‘ya’yansa huɗu ne duk maza.
Sumayya na kwance tana bacci, Abba ko ganin inda take bai yi ba, ni ma ban yi karambanin miƙa masa ita ba don zai iya yarfa ni.
Hashim ne ya sa hannu ya ɗauke ta yana yi mata wasa tare da faɗin ya yi wa ɗansa na fari Abdallah kamu. Jin haka na tuntsire da dariya.
Da Hashim muka dinga hira, shi kuwa Abba bai cewa komai daga ƙarshe ma ya miƙe da su tashi su tafi.
Hashim ya sa hannu a aljihu ya ciro kuɗi ya miƙa mini, shi kuwa Abba ya yi gaba abin shi.
“Ki ci gaba da haƙuri Ummi, mahaƙurci mawadaci. Watarana sai labari.” Furucin Hashim kenan yayin da ya damƙa mini kuɗi.
Na ce da shi, “Babu komai. Ina godiya da hidima Allah ya jiɓanci lamuranka duniya da lahira. A gaishe da Mummy Abdallah.”
Na rako shi ya yi wa Inna sallama ta ce, “To ina shi angon karnin yake.”
Na yi saurin cewa, “Sun tashi kenan aka ƙira wayarsa ya fice don amsa waya.”
Na nunawa Inna abubuwan da suka kawo bayan tafiyarsu.
Abba zuwa ɗayan nan da ya yi bai kuma zuwa ba, Hashim ƙafarsa biyu kuma duk zuwa da zai yi da abin ihsani.
Zuwan Hashim na farko da ya zo shi kaɗai na tambaye shi abokinsa ya ce ya yi masa maganar zuwan amma ya ce shi ba zai zo ba ya ma kashe wayar don kar a same shi, amma Hashim ya ce da Inna Abba na fama da zazzaɓi shi ya ce da shi ya zo ya duba lafiyar matarsa da ‘yarsa.
A zuwa na biyu kuwa ya ƙirƙiri ƙaryar abokin nasa ba ya gari.
Kwanana Hamsin a gida Abba bai yi maganar komawa ta gidansa ba hankalina ya tashi sosai.
Da na tuntuɓi abokinsa ya ce da ni ba ya ma gari yana Legas.
Na tsarawa Hashim ina son komawa ɗakina ya sanar da iyayena Abba ba ya gari amma ya ba shi umurnin da ya dawo masa da matarsa kafin ya dawo tun da ta kammala zaman wanka. Na shirya haka ne kar Abba ya ce zai sawwaƙe mini amma idan ya gan ni a gidansa daram ba yadda ya iya.
Kamar yadda na tsara haka Hashim ya sanar da iyayena ya zo ya ɗauke ni ya mai da ni gidana tare da sayayyar kayan abincin da zan iya kai wa wata guda ina ci ko fiye da haka.
Hashim ya faɗa mini ya sanar da mijina komawa ta ɗakina amma a kwana a tashi yau satina uku Abba bai dawo ba.
Nakan yi masa magana jifa-jifa ta WhatsApp bai taɓa yi mini reply wannan hali nasa idan da sabo na sabo na saba, hatta idan na ƙira ba zai yi picking ba haka kuma ya gindaya mini kar na taɓa kuskuren ƙiransa da wani layi da ba nawa ba ko da lambar iyayena ne ko na Fadila, su dai a muradin kansu su ƙira, amma muddin ni na yi haka to na yi kuka da kaina sai isa ko gwada ƙiransa da wani layi ban yi, akwai time da ban sani ba Fadila ta sa number ta a private number na ƙira ya yi picking ya ji muryata da ya dawo sai da na sha mari wai don munafurci ne nasa lambar a private number na rantse da ba ni na nasa ba na ce amma ina tunanin Fadila ce da ta zo mini tasa a take ya ƙira ta ya tambaye ta ta ce tabbas ita tasa kuma ta manta ba ta fitar ba dallin haka na tsira ba don haka ba a wannan ranar Allah ne kaɗai zai fitar da ni a hannun wannan bawan nasa don yadda yake muzurai.
Sumayya tun ranar da muka dawo gida na kasa gane kanta, rigimar da ba ta yi shi ba lokacin da nake gida yanzu take yin shi kwana nake ba na runtsawa saboda kukanta da rana ma idan har ta yi bacci ba ta wuce 2hrs, kukan da take yawan yi sai nake tunanin ko ciwon ciki ke damunta ta WhatsApp na nemi izinin Abban Sumayya ina son kai ta asibiti saboda Hashim ya ɗan ba ni kuɗi bai ba ni amsa ba, sai na lazimci karanta Suratul Fatiha a man zaitun ina tawassali da shi ina ba ta da fatan idan har tana fama da ciwon ciki Allah ya yaye mata.
Domin ni ba na iya taka ƙafata na fita ko’ina ba tare da izinin mijina ba duk mawuyacin halin da zan tsinci kaina, da na gama wanka ma da ma al'ada mai jego kan yi ziyara ba inda na je, abu masu muhimmanci ma Abba bai bari na zuwa ballantana yawon arba’in ban ma fara tambayar zuwa ba.
Zagaye ɗakin nake da Sumayya a kafaɗata kaina na sarawa saboda rashin isasshen barci don daren jiya ko second ban runtsa ba don kukanta ga shi wayewar garin yau ma mun doshi 11:00 na rana tana rusa kuka.
Ji na yi an bankaɗa labule Abba ya shigo ba sallama, na ɗan rutsuna kaɗan na yi masa sannu da zuwa ya banzartar da ni.
Yana ajiye jakarsa ya shiga toilet ya yi wanka, bayan ya fito Sumayya na hannuna tana kuka na je gabansa na durƙusa.
“Sannu da zuwa Abban Sumayya, ga shi ka yi mana zuwan bazata ban shirya maka komai ba.”
Fuskar nan babu annuri kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa a faɗace ya ce, “Ke dalla can tashi ki ba ni wuri, kuma ki yi nisa da ni don kukan yarinyaki ɗin nan juya mini ƙwaƙwalwa yake. Abinci ko da kin girka mini ba cin shi zan yi ba, don na ci a restaurant.”
Jiki a sanyaye na miƙe na yi nisa da shi kamar yadda ya buƙata da na samu wuri na zauna na shiga rera kuka ‘yata na yi ni ma na yi.
Abba ya yi mini kashedin ko da ya shigo gida ni da ɗiyata kar mu zo inda yake.
Sai na kauracewa sashen da yake gabaɗaya ma don a zauna lafiya.
BAYAN WASU KWANAKI
Cikin hukuncin Allah Sumayya ta rage rigima da kuka da take sosai kaɗan ake ɗan taɓawa.
Duk da kashedin da Abba ya yi mini sai na ga bai kamata mu yi ta zama haka ba, na ƙudira a raina yau kam sai na je wurinsa kuma na nemi iznin zuwa gidan Hashim da gidan iyayensa don Hashim ba ƙashin yadawa ba ne.
Abba tsaye yake a gaban mirrow yana gyara kasumbarsa na same shi ina ɗar-ɗar dai na daure na ce, “Abban Sumayya don Allah so nake ka amince mini na je na gaishe da iyayen Hashim da kuma matarsa.”
“Ki je ki shirya sai ki zo ki same ni akwai sharaɗin da zan gindaya miki a tafiyar.”
Cikin jindaɗi na tafi don shiryawa a gaggauce na shirya don kar na daɗe ya ce ya ma fasa ba inda za ni.
Da na shirya na je kitchen na ɗan tsinci wani abu daga abin da Hashim ya saya mini na san shi da iyayensa sun fi ƙarfin abin da zan kai musu amma ina jin nauyin zuwa ba tare da na ba da komai ba, kyautatawa mai kyautata maka. Kuma Abba tafiyar da ya yi hannu rabbana ya shigo mini gida.
Na zo gabansa na tsaya, “Gani Abban Sumayya na gama shiri.”
Ya dube ni a wulakance, “Awa ɗaya na ba ki za ki yi ki dawo gidanki.”
Ya duba agogon da ke hannunsa, “ Yanzu ƙarfe shabiyu 12:00pm ki tabbatar ƙarfe ɗaya na rana kina gidanki. Ki tura mini hotonki shaida kina komawa gida.”
Ya yi gaba ina bin shi a baya, zai buɗe motarsa ya gan ni.
“Mene ne kuma kika biyo ni?”
“Abban Sumayya na za ta kai za ka kai ni.”
“Saboda na zama direbanki ko?”
Muryata na rawa, “A’a saboda dai kana a matsayinka na mijina.”
“To ba zan tafi da ke ba ki je can ki hau adaidaita, kuma ki ji wannan tsayuwar da kike kina asarar lokacin da na ƙayyade miki ne.”
Ya shiga motarsa ya yi gaba, ni kuwa sisi ban da shi da ma dubu biyu ya rage mini a akawun ɗina da na hau facebook sai na ga wata shahararriyar 'yar kasuwa wadda gidauniyarta ta shahara wurin taimakawa gajiyayyu da marayu ta yi posting na wata baiwar Allah da take cikin matsanancin jinya kuma babu kuɗin kai ta asibiti ana buƙatar taimako al’umma kowa ya tura abin da ya yi niyya. Yadda na ji tausayi dattijuwar matar na ce ina ni mashahuriyar mai kuɗi ce na ɗauki nauyin jinya saboda halin da na ga take ciki, kawai sai na tura abin da nake da shi.
Ga shi yau na yi niyyar fita an bar ni idan har ban je ba da wuya Abba ya kuma bari na, na ɗaura ɗamararar zuwa da ƙafa kuma tsakanimu akwai tazara mai nisa.
Ga shi yau ana kwaɗa rana sauri da nake har tuntuɓe na dinga yi saboda mintunan da aka ba ni, mintuna talatin na shafe sai gani a gidan mahaifiyar Hashim ƙafafuna sun yi kura da su saboda ban sanya safa ba, ina shiga ina haƙi kamar wacce ta yi gasar tsere, ina ganin buta na ɗauka na wanke fuskata da ƙafata.
Mahaifiyar Hashim ta shimfiɗa mini darduma, da na zauna na ta yi mini sannu da zuwa na amsa, cikin girmamawa na gaishe da ita, ina kuma mai jin nauyinta don tamkar surkuwa na ɗauke ta.
Wannan shi ne karo na biyu zuwana gidanta, kafin mu yi aure da Abba ya kawo ni bayan aurenmu mu kuwa ya ce babu inda zan fita sai na shekara biyu a ɗakina. Amma sai ga shi na yi sa'a ina tambaya aka bar ni, kuma da wuya a kuma bar ni zuwa wani wurin. Abba Hashim da iyayensa su ne kawai yake ganin ƙimarsu da darajarsu.
Na samu tarba wurin Umman Hashim duk da ba ta san da zuwana ba ta shiga jero mini abubuwa kamar za ka yi tunanin ta san da zuwan. Yadda Hashim ke hidimtawa iyayensa nake fatan mu ma Allah ya ba mu 'ya'yan da za su ji kanmu.
Ta karɓi Sumayya tana ta tsokanarta, “Wannan kishiyar ai gwamma da maigidan ba ya nan kuka zo, don na san yana ganinta na zama sorry a wurinsa kwace mijin za ta yi.”
Dariya na yi, “To ai yanzu ma ba ta ɓaci ba za mu biya ta kasuwa kawai ya gan ta da an daidaita sai mu nema miki gida ko da mai ɗakina ɗaya ne, wannan katafareren gida na sabbin jini ne.”
Na ƙarashe maganar da miƙewa da niyyar tafiya, “Ya haka ko ruwa ba ku sha ba na ga kin miƙe?”
Murmushi na yi, “Za mu ƙara zuwa yini har dare yanzun abin a gaggauce ne.”
“To ai shike nan ga shi ba abin da kika taɓa wanda na kawo.”
Ta miƙa mini Sumayya ina goyata na ce, “Umma alhamdulillah.”
Ɗaki ta shiga ta fito da leda duk ta juye abubuwan da ta zuba mini ta ce, “Idan ma ba za a ci ba, a ba wa almajiri.” A ƙunya ce nasa hannu na karɓa tare da godiya, abin da na zo da shi da ma na ajiye a gefe nata ɗin, na so saya mata goro kasancewarta ma'abociyar son goro rashin kuɗi ya hana. Ta jefa mini kuɗi cikin ledar wai kishiyarta ta ba wa, na ji daɗin kuɗin don ko ba komai na samu na komawa gida.
Haka muka yi sallama, gidanta da gidan Hashim gida biyu ne tsakanin ina fita na zarce gidan.
Zaƙiyya na ganina ta tashi ta rungume ni, bayan ta sake ni ta ce, “Shi ne za ki zo ba sanarwa kuma tsakar rana warhaka, kyawunsa 9:00am kina gidan nan 10:00pm ki koma gida kin ga mun yi hira sosai.”
Murmushi kawai na yi, don da ta san ƙa’idar da aka shimfiɗa mini ba za ta furta hakan ba.
A 3 seater na zauna, sai ga ta ta iso da tire da abubuwa a maƙare, duba agogon bango na yi mintuna shabiyar suka rage a abin da aka ba ni.
Sai na miƙe ina gyara goyo. “Mene ne haka?” Ta ce da ni, “Tafiya zan yi, zan zo zuwa na musamman yau ɗin kawai Allah ne ya diro da ni.”
“Ba ki isa ba kuwa.” Ta janye mayafina ta riƙe, “Ko gaisawa ba mu yi ba, Daddyn Abdallah ma na bedroom yau bai fita aiki ba saboda ya tashi da zazzaɓi ba ku gaisa da shi ba ki ce tafiya. Ni da na je gidanki na shantake har dare to yau ke ma idan har na ba ki gyalenki sai ƙarfe tara ko kuma angon naki idan ya zo.”
Tashin hankali mai zan faɗawa Zaƙiyya ta fahimce ni, na duba agogon da ke bango yadda sakanni ke motsawa kamar na dakatar da tafiyar da yake sai na koma gidana ya ci gaba.
Juyawa ta yi ta shiga bedroom, wallahi da gyalena na hannuna sai dai ta fito ta ga babu ni, cikin falon idanuna suka dinga yawo ko zan ga gyalenta ko hijabi na sanya na fice amma babu.
Idona kyar akan agogon bangon yayin da zuciyata ke ta bugawa na taraddadin jinkirina abin da zai haifar.
Tare suka fito da mijinta a bedroom, Hashim a kafaɗarsa ɗansa Suhail mai kimanin watanni takwas, ya kuma riƙe hannun Sudais shi kuma mai shekaru uku, abin ya ba ni sha’awa an ce da ni bai da lafiya amma ka ga ‘ya’yansa na tare da shi, Allah ka nuna mini irin wannan rana da Abba zai ɗauki Sumayya ko da hannunta ya riƙe.
Bayan sun iso inda nake, sai ta ce, “Daddy Abdallah, ko kai idan ka ce da ita ta zauna za ta yarda ta zauna, ni ba za ta ji nawa ba, ta yaya mutum ya zo gidan babban aminin mijinsa ko gaisawa ba a yi ba ya ce zai tafi.”
Tana gama faɗin haka ta yi kitchen, na dubi Hashim kana ganina ka san babu nutsuwa a tattare da ni, “Don Allah Daddyn Abdallah ku yi haƙuri kai da Madam, zan kuma zuwa na wuni har dare.” Ina maganar ina ganin agogon da ke bango mintuna biyar kacal ya rage a lokacin da aka ba ni.
“Mene ne za ki yi a gidan kika matsu haka?”
Shiru na yi saboda ba ni da amsa. “Na fahimta Abba ne matsalar zan ƙira shi na ce ni na riƙe ki. Koma ki zauna.”
Ya ƙira shi a gabana ya ce da shi bayan ya ɗaga wayar “Na riƙe Madam naka sai dare za ta dawo ya ce da shi, “Babu damuwa.”
“Ya dube ni, “To sai hankalinki ya kwanta mijinki ya ce ba damuwa.”
A nan na samu kuzari muka gaisa na yi masa ya jiki ya amsa da sauki, ya zauna muna ta hira yara na yi masa taɓara amma ko a jikinsa.
Sai 5:00pm Abubakar da Abdallah suka dawo a makaranta da shi ke makarantar irin mai haɗe da tahfiz ne. Har ƙasa suka durƙusa suka gaishe ni suka kuma gaishe da iyayensu tarbiyyarsu ya burge ni matuƙa.
Rayuwar Hashim da iyalansa ya burge ni yadda suke nunawa juna soyayya da sanin darajar junansu na yi wa kaina addu’ar Allah ya wanzar da irin haka tsakanina da mijina.
Bayan sallar isha'i Hashim ya mayar da ni gida matarsa ma ta haɗa mini tara ta arziƙi.
Hira kaɗan suka taɓa shi da abokinsa ya koma gidansa.
Ya dube ni, “Sai warhaka za ki dawo gida ko? To bari ki ji ni a tsarina matata ba za ta yi tambele a layi ba, sai isa ki shirya zaman kulle, idan har na bar mace ta fita a ta daɗe la’asar ya same ta a gidanta. Zan yi maganinki ki yau gobe ko an ce da ke ki zauna ba za ki zauna ba.”
A firgice na kalle shi ganin ya cire belt, muryata a raunane na ɗaga kai, “Abban Sumayya da izininka fa na kai wannan lokaci.”
“Ina jin nauyin Hashim sai isa na ce na amince, ke ga yadda muka yi da ke me ya sa ba za ki bijire ki ce sai kin taho ba, ni nake aurenki ko Hashim ke aurenki, ki take dokar da na gindaya miki kin bi nasa.”
“Ka yi haƙ….” Tagwayen mari da na ji saukar su ya sa ban ƙarashe maganar da ya fito daga bakina ba.
Mu haɗu a next page.
Taku ce Ummulkhair.