FreeArewaPen original
SU MA 'YA'YA NE
- 1views
- 29chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Am very simple with simplistic mind you will know that if you come closer to me
Sample · Chapter 1&2
*SU MA'YA'YA NE* Da Alkalamin Ummulkhair Abba Muhammad.Burinsa idan ya yi aure su shafe shekaru biyar da matarsa suna soyayya kafin su haihu. Sai dai kash! Ita kuma ta ƙi aminta da wannan tsarin.....Burinsa ko da zai haihu 'ya'ya maza zalla yake so, sai dai kash! 'Ya'ya mata ya dinga haifa bai san su ma 'ya'ya ba ne ya wulankanta su ya wofintar da su da mahaifiyarsu. Daga ƙarshe su suka share masa hawayen da 'ya'ya mazan ba su share ba. *GODIYA* Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata’ala, wanda ya sanar da bayinsa abin da ba su sani ba. Ya Allah ka tsarkake mini alkalamina ka sa na isar da saƙon da zai kasance shiriya ga bayinka, ka toshe mini ƙwaƙwalwata ga duk abin da idan na rubuta zai kasance fitina ga al’ummar Musulmi. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Fiyayyen halitta masoyinmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama da alayensa da Sahabbansa.*SADAUKARWA*Wannan littafin sadaukarwa ne ga ‘yan’uwana mata waɗanda ke fuskantar tsangwama wurin wasu dalilin haihuwar ’ya’ya mata zalla da suke. Labarin ya kunshi irin tarin kalubalen da ke addabar iyaye mata da suke da 'yaya mata, inda a wasu wuraren maza ke wofintar da su. *'Ya'ya mata su ma 'ya'ya ne* suna taka matsayin da duk wani ɗa namiji zai taka.*Ba lalle ba ne da ka fara karanta labarin ka ji daɗinsa, sai ka yi nutso a kogin sosai.*Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.*Page 1&2*MAIDUGURI BIRNIN SHEHU Asibitin koyarwa (teaching hospital) misalin ƙarfe 9: 00am A jikin kofar ofishin cikin harshen Ingilishi aka rubuta (Consultant cardiologist.) Kana shiga cikin ofishin a jikin bangon idon ka ne zai yi tozali da wannan rubutun da aka rubuta a jikin ƙarfe da ruwan gold (zinari) ‘YA’YA MATA (su ma ‘ya’ya ne) A bangon ofishin hotunan dakta Sumayya Habib Umar ce a manne wadda ta ɗauke su ana ba ta lambar girmamawa, akwai hotonta da Gidauniyar kula da lafiyar zuciya ta Burtaniya, sai a ƙasar Saudiyya tare da Yarima Mohammed Bin Salman, da kuma wani hotonta a ƙasar Amurika tare da hukumar lafiya, sai kuma a Mumbai da ke ƙasar Indiya da wata ƙwararriyar likitar zuciya, sai kuma a nan ƙasarta Nijeriya tare da Ministan lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate. Daga wani ɓangaren kuma hoton shugaban ƙasa ne sai kuma na gwamnan jaha da sarki, wanda yawanci jazaman ne a same su a ma’aikatu da ofishoshi. Dakta Sumayya zaune take kan ƙayataccen kujera mai juyawa baya zuwa hagu cikin rantsatssen ofishinta ta ba wa kofar baya, sanye take da doguwar shadda gezna black blue da aka yi masa aiki zubin zamani da ratsin ruwan zaiba. A jikin ɗan ƙarfen da ke teburin sunanta ne da a ka rubuta da ruwan gold, (zinari) DR. SUMAYYA HABIB UMAR.&nbs...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.