27
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 27```
_________Girar shi ɗaya ya ɗage yana kallonta,kafin ya miƙe gaba ɗayanshi, zara-zaran yatsun shi yasa ya na ɗan dafe kanshi,har lokacin bai ce mata komai ba.
Sexy eyes ɗin shi da barci yasa suka ƙara zama wani iri ya ƙara zuba mata,"Menene matsalan" ya faɗa da husky voice ɗin shi.
"Abinci na girka maka mai daɗi,na gaji da jiran wannan lalataccen barcin naka,shine na zo na tashe ka" ta faɗa tana Murmushi a fuskarta, murmushin gefen baki yayi,tsohuwar tana matuƙar burgeshi, amma rigimarta ya yi yawa banda haka tana gani jiya bai samu barci da wuri ba, amma still bazata barshi ya huta ba.
"Okay ina zuwa"
Daga Bai ƙara tanka mata ba ya wuce Bathroom. Itama fita tayi tana Murmushi soyayyar Maysarah aranta, Maysarah daban yake da sauran jikokinta.
A nutse yake komai na shi. Har wunin ranar babu wanda ya leƙo sashenta da sunan hira kamar yanda suka saba saboda tsoron Maysarah.
★washe gari da sassafe yabar gidan zuwa Kano.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Yaren Hausa tafi mayar da hankali wajen koya a rubuce, saboda karanta kundin Mahaifiyarta.
Daga wannan ranar Inna bata ƙara ganin Yusha'u ba,ma su Makarantar sun tattauna da shi,jin za'asa akamashi idan bai daina bibiyar su ba, yasa ya haƙura ya daina bibiyar layin tare da zurfafa tunani wajen samun wata mafitar, har ga Allah ya na tsananin son Halima, sai dai yasan ko duk duniya za su taru Inna bazata taɓa bashi aurenta ba, kuma ko afuska ba sa'an auren ta bane tunda ko Mahaifiyarta ya girme mata nesa ba kusa ba,ga talauci daya kanannaɗe rayuwarsa. To amma idan ya samu yayi lalata da ita fa?iya wannan abun kunyar kaɗai ya isa yasa Inna ta bashi auren Halima,a na shi gurɓataccen tunanin da hasashen.
Tunawa Halima na zuwa siyan bushashen kayan miya wajen Matarshi yasa ya saki ajiyar zuciya haɗe da mugun murmushin da shi kaɗai yasan munafar kayan shi.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Da speed motocin suke shigowa layin wanda hakan yasa Maigadi buɗe mu su hanyar shiga da hanzari.
Ta window sashen su take kallon komai,har motocin suka gama shigowa bayan wa su daƙiƙu sai ga Maysarah a bayyane akan idonta gaba ɗayashi, babu kowa age da gefenshi gaba ɗaya suna bayanshi. Saitin zuciyarta ta dafe ƙwallar soyayyar shi na cika idanuwanta.Maryam kenan ƙanwar Faisal Uwa ɗaya Uba ɗaya. Da gudu ta nufi madubi tana ƙara gyara sumar kanta na fulanin usul.
Kamar Uncle Suraj zai goyashi haka ya saki Fuskarshi da fara'ar da sam kana gani bata dace da fuskar ba, saɓanin na Maysarah dake tsamke ba don raini ko don wata manufa ba,a'a haka halittar su yake,amma kwaɗayi da son nuna soyayyar da babu shi a zuciya, yasa Uncle Suraj ƙaƙabawa na shi fuskar dariyar dole.
A haka Faisal ya same su Daddyn shi na ta surutun dake neman sawa Maysarah ciwon kai da shi kanshi daya aro halayyar da ba nashi ba.
Batare da jiran Maysarah ya mishi magana ba ya miƙamai hannu da fara'ar shi ,kamar mai ciwon hannun haka ya miƙawa Faisal na shi hannu,yawu mai ɗaci Faisal da Mahaifinshi suka haɗiya,ran kowannen su sai da ya so su da abinda Maysarah ya yi.
Daga gaisuwa sai ya ja bakin shi ya tsuke yana jiran Matar gidan ta fito su gaisa ya tafi saboda jirgin rana zai bi.
A haka Maryam ta fito cikin shiga mai tsari da kyau, tana yauƙi da yin ƙasa da murya wajen gaishe shi.
A hankali Faisal da Uncle suraj su ka zame, akabar Maryam ita kaɗai saboda taja ra'ayin shi har yasake su yi hira.
Ganin duk sun fita yasa taji wani farin ciki ya lulluɓe ta,Ƙara gaishe shi tayi cikin lanƙwasa da murmushinta mai birgewa.
Maimakon ya amsa mata, sai ya bar danna wayar dayake yi, ya zubo mata idanuwanshi mai tarwatsa zuciyar dubban ƴan mata irinta,girar shi ya ɗage mata alamun lafiya.
Ruɗewa ta yi ta hau kame-kame har lokacin bai janye idanuwanshi ba daga kanta ba.
Ƙarshe da ta kasa jurewa miƙewa ta yi zuwa kiran Mahaifiyarta, a hanyar ta na zuwa tasaki ƙaramin kuka tana naushin iska.
Ko minti ɗaya Maysarah bai ƙara ba bayan ya gaisa da Mommyn Faisal ya tashi domin tafiya.
Yana daf da isa wajen Motar shi, Bala ya nufo shi cikin hanzari,yana daf da samun damar ƙarasawa sojojin bayan Maysarah suka tare shi, tsoron su ya hana shi magana ƙarshe yana ji yana gani Maysarah da tawagarshi suka bar gida....✍🏻
Kuyi following ɗina A Arewabooks @sasaal74 Ni kuma nayi alƙawarin posting 2pages kullum.
Nagode da soyayyar ku