28
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
```By```
```SASAAL```
```Page 28```
________Bala bai motsa idanuwanshi ba,har motocin Maysarah su ka ɓacewa ganin shi. Ajiyar zuciya ya sauke tunowa da kalaman Halime yasa ya ji ƙwalla na cika idanuwanshi,"Allah Ya jiƙanki Halima"ya faɗa a hankali yana komawa bakin aikin shi.
Iska mai zafi Uncle Suraj ya fesar,kanshi na ƙara ɗaukar zafi, ba shawara yake so suyi da Abdulnaseer ba wannan karon akan auren Maysarah da Maryam, umarni zai ba shi,a matsayin shi na Yaya a gareshi. gudun kar ya huce a kanshi yasa Faisal ya yi mishi sallama na shi ran shima ba daɗi saboda tsananin burikan da suka ci akan auren.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Ayyukan da suka yiwa Inna yawa ne yasa tace Halima ta É—auko hijjabi taje gidan su Sama'ila(gidan Yusha'u)siyo mata bushashen tattasai.
Kusan satin shi guda kullum da wuri yake dawowa ko Allah zai sa Halima ta zo siyan bushashen kayan miya, a ɗakin dayake ajjiye hatsi na soron gidan yake zama,amma shiru har tsahon kwanaki, kwatsam yana cikin ɗakin Matarshi yaji sallamarta,da hanzari ya sauko daga kan gadon, ya ma manta Harira Matarshi na gefen shi a zaune,bata tanka mai ba sai ƙwafar da tayi a ɓoye,tunda ta jima da jin labari a bakin Matar Abokin Yusha'un cewar son Halima yake yi.
Cikin ɗan borin kunya ya miƙe ya zura rigarshi da sunan zai tafi ɗakin soro ya huta, nan ba bata tanka mai ba,dama tagaji da zama da shi.
Shu'umin kallo mai cike da ma'anoni ya bi fatar Halima da shi,ya na ayyana yanda zata kasance tsakanin shi da ita, batare da la'akari da ƙarancin shekarun ta da basu wuce takwas ba saɓanin shi dayake kusan shekarun arba'in da ɗoriya. Duk Harira na kallon shi daga bakin ƙofar da take tsaye.
Cikin sanyi muryarta mai daɗin dake cike da ƙuruciya ta gaishe da Harira,tare da miƙa mata kuɗin bushashen tattasan da zata siya,duk da ran Harira a ɓace yake bai hanata sakarwa Halima murmushi ba,haɗe da tambayarta Inna da Babangida,harga Allah kyawun yarinya da nutsuwarta suna burgeta,lokuta da dama sai taji ina ma da ƴarta ce.
Bayan ta sallami Halima sai ta laɓe a hanyar da zai sada ka da soron gidan saboda ta ganewa idanuwanta mai Yusha'un ya ƙulla.
Yana maƙale harda cire dogon wandon shi yabar iya guntun na ciki, yana jiran ya ji tahowarta ya fizgota ciki.
Kanta na ƙasa bata lura da hannun da ya ziro ba tunda yamma tayi kuma soron ba wani faɗine da shi ba,don haka wajen ya yi duhu. Da iya ƙarfin shi ya fizgota yana toshe mata baki, ya fara ƙoƙarin rufo ɗan ƙofar langa-langar da aka ɗan ɗosanawa ɗakin,cikin azama ya cire guntun wando shi, ya yaga ɗan hijjabin kanta. Ihu! mai ƙarfi Harira ta sa wanda ya ja dukka hankalin mutanen gidan ciki harda Inna"ga Yusha'u zai ƙeta haddin Halima mugu azzalumi wallahi sai ka sakeni" Harira ta faɗa da iya ƙarfinta, maganganun tane sukasa Inna zabura talgen da take ƙoƙarin tuƙawa ya zubo kan dukka biyun ƙafafuwanta amma azabar kalaman Harira sunfi na talgen da ya zubo kan ƙafafuwanta, da iya gudun ta tayi sashen.
Yana jin surutan Harira amma hankalinshi baya jikinshi burinshi kawai muradin shi ya cika,tura ƙofar Harira tayi dai-dai lokacin daya samu damar cirewa Halima riga, kokawa shida Harira suke yi amma duk da haka bai saki Halima ba shi dai ya samu damar cimma muradinshi. A haka iyayen Yusha'u da Inna dama sauran jama'ar gidan suka same su.
Kukan kura Inna tayi ta fizgo Halima dake kuka a hannunshi, fuskarta yayi jajir saboda matsar da fuskarta yasha a hannun Yusha'u,Inna batabi ta kan hayaniyar su ba,ta nufi na su sashen,kai tsaye wayan da Faisal ya siya mata da É—auko ta kira Bala,cikin kuka ta koramai bayanin abinda ke faruwa.
Dama Bala yana kusa cikin abinda bai haura minti talatin ba sai gashi da Ć´an sanda,har lokacin gidan Yusha'u cike yake da jama'a kowa na mishi tofin Allah ya tsine mai.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Wannan karon Uncle Ghali da kanshi shida Yusra(autar su Mubeena) ne suka je tarbar shi.
Dariyar shi ta rainin hankali yake ta yiwa Maysarah. Cikin wayewar da ya huda ta da kuma ɗan fuskar dayake sakar mata, Yusra ta rungume shi da sunan tayi farin cikin ganin shi,Uncle Ghali dake gefe su murmushi yake saki ranshi fari fes samun Maysarah a matsayin Siriki babban nasara ne a gareshi,ɗan zameta Maysarah ya yi fuskar shi babu fara'a kamar kullum,yana ƙoƙarin barin wajen,ba yau ta fara fuskarta irin wannan wulaƙancin daga gareshi ba, dan haka yanzuma bazai zama abin haushi a wajan taba. Yusra kyakkyawace domin babu mai kyanta tsakanin Sumayya da Maryam, tana kuma tsananin ji da wannan kyawun nata, ta kuma tsani taga wanda ya fita ko wanda ya kamota, kowa yasan haka ko acikin ƙawayen.matsalar ta ɗaya gajeriya ce sosai saɓanin Sumayya da Maryam da suke da ɗan tsaho ba laifi.
Kai tsaye gidan su Maysarah suka wuce.
Mom Fahima kamar zata goyashi sai dai ko gaisuwar Yusra bata amsa ba, Uncle Ghali ma daƙyar ta amsa nashi,duk Abdulnaseer na kallon su ya kuma shiryawa kowannen su.
Itama Yusra daƙyar ta danne yanda taga Sumayya ta iya kame kanta daga yiwa Maysarah shishshigi kamar yanda suke mai itada Maryam. Abinda bata sani ba Sumayya wani Black takeso shima ɗan Nigeria ne amma mazaunin Birtaniya, sai dai shima neman kuɗi yake yi a can ba ɗan kowa bane, shiyasa Mom Fahima ta nuna ƙin amincewarta.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Jifa Uncle Suraj ya yi da wayarshi bayan gama sanar da shi ganin Uncle Ghali da Yusra a Airport har Yusra ta samu damar rungumar Maysarah, yanzu haka suna gidan Abdulnaseer gaba É—ayan su.
Tunawa da Ghali zai iya shigar da buƙatar auren Yusra da Maysarah ya sa ya kuma rarumo wayar hannu shi har rawa yake yi wajen neman layin Abdulnaseer.....✍🏻
Follow my Arewabooks account @sasaal74