MAI KWAƊAYI

29

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 29```


________Har wayan ya gama ringing ba'a ɗaga ba, still ya ƙara kira ba ayi response ba dole ya haƙura zuciyarshi na tiririn haushi su dukkan su.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Suna cikin hayaniya motar ƴan sanda ya iso layin. Yusha'u najin jiniya yasan dole shi akazo kamawa,da iya ƙarfin shi ya fizge ya bi ta ragowar ƙofofin gidan ya gudu.

Salati mutanen wajen suka ƙara ɗauka Iyayen shi nata kukan baƙin cikin abun kunyar dayaja mu su.


Jikin Inna da Halima babu inda baya rawa, musamman Halima dake kuka kamar ranta zai fita.

Jin Yusha'u ya gudu yasa hankalin Inna ya ƙara tashi,sai take ganin kamar zai biyosu cikin dare. A daren Bala ya kai Inna Asibiti aka ƙara duba ƙafarta da duk ya tashi sannan suka dawo gida.

Ɓarawon barci ne ya sace Halima banda Inna data kasa runtsawa tunani kala-kala na zuwa kanta, banda tana tsoron Mubeena da ta haƙura ta bawa Faisal Halima amma tasan wata sabuwar uƙubar zata fuskanta, domin alamu ya nuna ƙarara Mubeena bata ƙaunar zuwan Halima gidan su.



Daƙyar Faisal yake jure amsar wayar Bala saboda zafin da kanshi ya ɗauka,ita dai Mubeena ko ta kanshi batabi ba,saboda ta lura Faisal yanzu yafison farin cikin wa su akan nata.


★da sassafe Bala ya ƙara zuba duba Inna da Halima,bayan sun gaisa Bala yayi gyaran murya cikin ƙarfin hali da kuma jin nauyin abunda zai faɗa yace"amma Inna bakya ganin mayar da Halima wajen Maigida zai fi kwanciyar hankali,tunda shi Yusha'un ba mu san ta ina ya ɓuya ba, kar yazo ya ƙara biyo baya wata rana,ko yaya kika gani?" Bala ya faɗa da addu'ar Allah Yasa ta amince

"Bala Ina jin tausayin maraicin Halima nasan kuma daƙyar idan ba matsalar dayasa Mubeena ta gujemu ba kenan,to kaga kai mata Halima zai zama kamar takura ne a wajen su"

Ta faɗa muryarta na rawa. Cikin son kwantar mata da hankali ya yi tayi mata bayani da nuna mata Mubeena daban Faisal daban.

Daƙyar Bala ya shawo kan Inna ta yarda da hasashen shi, amma tace ya bari zatayi shawara.


Bata da Abokiyar shawarar da ta wuce Indo,kuma samun layin Indo abune mai wahala,don haka ta tsara sati mai zuwa dole taje ƙauye. Sai dai itama Indo bata goyi bayan kai Halima gidan Faisal ba.


Idan Inna takai Halima makaranta sai ta yi zaryar hanyar yafi sau uku wasu lokutan acan take wuni tun safe sai dai taje gida ta girka abinci ta dawo har sai an tashe su daga Islamiyya, tun masu Makarantar basa tausayi ta har suka fara,wannan dalilin yasa suka bawa Inna damar fara siyar da kayan yara idan sun fito break.

A haka Inna ta shashantar da Maganar zuwan Halime gidan Faisal,ga kuma cinikin da take samu, sosai yake rufa musu asiri. Kishi kamar ya kashe Inna Huwaila.


Cikin dumbin nasara da cikar muradin ƙwarewa a karatun harshen Hausa Halima ta kammala primary school ɗinta,ta ƙara kyau da zama ƴar budurwa saboda tsayin ƙafar da ta biyo na Salmanu.

Bayan shagalin kammala primary school ɗinta da kwana biyu,Babangida yasamu nasarar cafke Namijin dayake yawan gani na salallaɓowa ɗakin Inna duk dare batare dasu su Inna sun sani ba, kuma bai taɓa gayamusu ba gudun shigar su damuwa, dambe su ka tafka bana wasa ba, amma duk da haka Babangida bai sake shi ba,kokawar su ce ta tashi dukka mutanen gidan, ganin mutum tsirara ba kaya yasa Halima yanke jiki ta zube awajen Inna da Inna Huwaila ihu suka sa daya tashi dukka mutanen gida,dama da ƴar shara yake zuwa kullum baya saka wando gudun kar ya samu tangarɗa.


Dukka Mazan gidan da makami suka fito matan ma kowacce da abun duka.


Sai dai ana haska kwarton kowa yasaki ihu Matan suka hau guduwa... To fa ko dai aljanine.....


Pls kuyi manage🙏🏻