MAI KWAƊAYI

30

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 30```


________Ɗan autan su Baba Shehu ne Khalid mai tsananin jin ƙai ba ko sisi, sai zaman majalisa,girman kan da kowa yasan shi da shine da ganin jikinshi ba kaya yasa matan guduwa.

"Khalid! Kai ko maiya kaika wannan tunani? duk manyan ƴan matan dake garinnan ku rasa abun haikewa da biyaya sai Halima, ni kam na shiga uku na" Mahaifiyar Khalid da shi kaɗai Allah yabata ta faɗa haɗe da sakin kuka, haƙuri da ban baki Mazan suka yita bawa Inna, bayan Halima ta farfaɗo an kaita ɗaki,bayarda Inna ta iya tunda wannan ne karon farko da suka yarda anyi mata ba dai-dai ba, kuma tanada ƙarfin ramawa sai ta haƙura,bayan sun tabbatar ta haƙura harta shige ɗaki,sai suka rufarwa Khalid dama dayawan su haushin shi sukeji,ko gaishe su baya sonyi sai faɗin ran tsiya,dukan tsiya sukamai kamar zasu rabashi da ranshi kafin su ƙyaleshi.


Inna kwanan zaune tayi,itama Halima ko ta fara barci sai ta zabura tana surutai da koke-koke.


Tana ganin lokaci yayi dazata saduda tabawa Faisal Halima, batare da yin shawara da kowa ba,duk wahalar da Mubeena zata ba ta,ba ta isa ta canza ƙaddarar Ubangiji akanta ba,yafi ta cigaba da zaman gidan su ana bibiyarta, domin duk ƙarfin Shari'a bazai dawowa da Halima mutuncinta da suke ƙoƙarin ƙetawa ba.


★washe gari Inna ta buƙaci Halima ta ɗauko mata littafin late Halime data ɓoye domin ainihin Number Faisal na ciki.

Da Halima ta ɓukaci jin mai Inna zatayi da Number Uncle Faisal bata ɓoye mata ba,kuka da magiya ta hau yimata kan bataso ta rabu da ita,kawai su koma ƙauye suyi zaman su.

"Halima zaman ƙauye bazai yiwuba gareki inaso kiyi ilimi mai zurfi ki cikamin burin marigayiya Halime amma idan kina tare dani wannan burin bazai cika ba, Allah shine gatan bawa idan da rabon ɗaukaka a tare dake zaki ɗaukaka kuma wata rana zakiji daɗi,barinki wajena abune naɗan lokaci a wajen Allah kinji" Inna ta faɗa kuka na ƙwace mata.ita da Halima sai aka rasa mai lallashin wani.

Tana gama saka Number Faisal ta danna kira,kuka mai ƙarfi ya ƙwacewa Halima,kife kanta tayi tana toshe bakinta.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Rigimar su Uncle Suraj har gaban Mahaifiyar su,a take kuma ta takawa kowannen su birki,kuma tayi rantsuwar ko bayan ranta wani a cikin su yayiwa Maysarah maganar auren ƴarshi matsawar ba shi ya gani da kanshi yace yanaso ba to bata yafe musu ba,meye amfanin takuramai akan aure tunda ba Mata sukaga yana bi ba, haka ita da marigayi suka matsawa Abdulnaseer yaje ya kwaso musu Fahima,yanzu gashi tazame mu su alaƙaƙai.

Goggo Bata magana su musamata saboda itace ƙarfin komai na Abdulnaseer, sai tace yayi yake yi,su kuma Abdulnaseer shi ƙarfin su,don haka kowa yaja bakinshi ya tsuke.


Zafin furucin Goggo yasa Mom Fahima yin zuciyar bawa Sumayya damar fito da Mijin da takeso,amma tayi rantsuwar tunda ta rasa, to wallahi suma sai su rasa.


Maimakon Maryam da Yusra suma su fitar da Miji, sai iyayen su suka ƙara hure musu kunnen su koma karatu,kuma su kwantar da hankalin su kamar anyi auren su da Maysarah an gama.


Ƙaruwar shekaru da kuma son ya dawo kusa da Mahaifiyarshi, yasa Abdulnaseer tattarawa suka dawo Abuja,cikin danƙareran gidan daya zuba manyan kuɗaɗe ya siya.da naci da Magiyar Abdulnaseer tsohuwa Goggo A'isha ta baro Bari zuwa Abuja.


Shirye-shiryen gagarumin bikin Sumayya ne ya kankama da Mijinta da shima maikuɗi ne amma ba irin wanda Mom Fahima take buri ba, jin labarin Maysarah zai halarci bikin ne yasa Uncle Ghali yanke shawarar dawowa, gaba ɗaya dama kuma dalili yake nema, gudun kar ayi zargin yanabin Abdulnaseer duk inda ya koma,shima gida ya siya maikyau,tun bikin na saura wata uku yayi hikimar dawowa gudun zargi.


Satin shi biyu da dawowa, sai ga Uncle Suraj shima ya siyi nashi gidan bayan layin su Abdulnaseer,Uncle Ghali kamar zai ari hauka tsabar takaici.

Goggo da Abdulnaseer duk kallon ikon Allah suke yi,suna kuma mamakin kwaɗayi irin na su,to kodai Maysarah ya tara wani dukiya ne da shi da Goggo basu san da shi ba🤔.


Gaba ɗaya kowannen su sai shirye-shiryen biki sukeyi kamar sune Amaryar,ita dai Sumayya dama bani good time take dasu ba,gata da girman kan tsiya,shiyasa bata shiga sabgar su,amma duk don Maysarah zai zo suka tattara gabar dake tsakanin su da Sumayya suka watsar.

Akan dole suka fara shiri da Yusra da Maryam.


Ana cikin wannan takun saƙar Faisal ya samu kiran Inna,yaji daɗin hakan saboda nutsuwar Mubeena baya tare da ita balle suyi tashin hankali,sai dai kawai ta dawo gida ta tarar da Halima.

★Washe garin ranar ya nufi Kano tahowa da Halima....✍🏻