MAI KWAƊAYI

31

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 31```



 *Fort Hamilton Barrack*


_____A hankali ta buɗe ƙofar, tana sakin ƙayataccen murmushin masifar da zatasha idan ya ganta kai tsaye, sanye take cikin red gown haka jambakinta da takalmin ƙarfarta, duk jajayene, murɗewar da jikinta yayi ne zai tabbatar maka da aikinta, Marry Abokiyar aikin Maysarah kuma masoyiyarsa, farar fata ce,nacinta da yaƙi ƙarewa ne yasa dole yaɗan fara sake mata.


Ƙamshin Creed ɗin daya cika hancintane yabata tabbacin yana parlourn,sam ba haka taso ba,cikin sanɗa taƙarasa shigowa.


A kan lallausar Centre carpet yayi kwanciyar shi,irin kwanciyar da Goggo ta tsana,babu kaya a jikinshi,hakan yasa buɗaɗɗen jikin shi ke bayyane,da dogayen cinyoyinshi da ƙafafuwan shi da gashi ke kwance. Dagashi sai guntun wando.

Kallon ƙurilla Marry take mai, saboda samun shi a haka babbar sa'ar tane.

A hankali ta sunkuya tayiwa bayanshi shafar da tasan dole ya motsa,amma sai taji shiru tasan kuma Indai Maysarah ne may be tun tsayuwarta yasan tana wajen.

Zata ƙara kai hannunta,ya cafki hannun da iya ƙarfinshi,dole ta saki ƙara duk dauriyarta, ƙwalla na taruwa a idanuwanta.

Bai saki hannunba sai da ya tabbatar ta tara ƙwallar dazai hanata ganin shi da kyau,sannan ya miƙe fuskarshi kamar hadari. Da manyan takunshi ya wuce Bedroom ɗinshi yana banko ƙofar cikin ɓacin rai.


Duk da ƙwallar daya hana ganinta fita daƙyau sai da ganinshi a tsaye ya ƙara tafiya da imaninta, Maysarah ya daɗe yana shaida mata bazai iya auren ta ba,saboda baya ra'ayin auren Mace irinta, ko da zata Musulunta,ya kuma faɗa mata hakane gudun karta Musulunta da sunan zai aureta, daga baya ta ga ya yaudareta, amma duk da haka takasa rabuwa dashi, har dai ya haƙura ya ɗan fara kulata,ta saci ɗaya key ɗinshi ne, saboda surprise Birthday da suka shiryamai da ragowar Abokanan aikin shi.

Ƙwallarta ta share saboda itama tasan bata kyautaba yasha gayamata bayaso.


Ragowar ta kira,suka shirya parlourn,suna jiran fitowar shi.


Dama a ɗosane yake Marry ta zo taƙara kunnashi,janajin lokaci yayi dazai ajjiye iyali, don matsawar yacigaba da tafiya a haka akwai matsala.


Har bayan yayi wanka ya kasa jinshi dai-dai,ya ƙara kwanciya kusan two hours amma still bai daina jin abinda yake ji ba,dole ya yanke shawarar fita.


Idan yace abinda suka shiryamai bai burgeshi ba, yayi ƙarya,da wannan damar Marry tayi amfani ta riƙo hannunshi gudun karya kunyatata yasa yariƙe harda surbatar hannu,hotuna videos da tafi ne ya ƙaure,Marry bakinta kamar zai yage saɓanin Maysarah dake ɗan Murmushin da saika lura dakyau zakasan yanayi.


Bayan gama taron, Marry bata tsaya ba don tasan ba kulata zai yi ba.


Cikin rawar jiki tayi posting pictures ɗin,tuni ƙawayenta suka fara tayata murna.


Yusra na cikin mabiya shafukan Marry saboda yawan zuwa wajen Maysarah ita da Dad ɗinta suka santa,bin ƙwaƙwafi da son sanin menene asalin alaƙar su da Maysarah yasa take bibiyan shafukan ta.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


Kusan kullum tare ake musu gyaran jiki da Sumayya.


Yau ma duk suna tare,kowacce da latest Mobile ɗinta a hannunta suna latsawa.


Hannun Yusra har rawa yakeyi lokacin datayi playing videos ɗin da Marry ta ɗora harma da hotunan dukka.


Kasa riƙe kanta tayi,cikin fushi ta nufi ɓangaren Goggo dama a gidan ake musu gyaran jiki.

Ko kallon bayanta Maryam da Sumayya basuyi ba, dama muradi ne ya haɗa ƙawancen na su.


Cikin Sa'a ta samu dukka ƴaƴan Goggon na tare da ita, harda Mom Fahima da taƙi tashi saboda jin abinda zasu tattauna akai.


Jikin Mahaifinta ta faɗa tana sakin kukan ɓacin rai.


"Auta menene haka" Uncle Ghali yafaɗa da damuwa.

Bata yi magana ba sai wayar data miƙamai.

Salati yasa yana miƙawa Uncle Suraj,shima baƙaramin shock ya shiga ba, amma dayake mai wayone,sai ya basar da faɗin.

"Ashe Maysarah baturiya zai ɗauko mana" ya faɗa yana miƙawa Goggo wayar.

Salati tasa da tafa hannuwa. Mom Fahima zaraf ta ƙarɓi wayan,tana gama gani taja tsaki.

"Yanzu ke Yusra don baki da kunya saboda Namijin da bai san dake ba kike zuwa da kuka harda faɗawa jikin Mahaifin ki,sai kace kinga Mijinki na iskanci da wata,au ashe baki daina takurawa Maysarah da nacin ki ba,duk da kakarku ta hana" Mom Fahima ta faɗa cike da son ta gwara kan su.

Zancen Mom Fahima ya shigi kowa amma banda Goggo da tasa kukan acewa Maysarah yadawo gara ya auri baturiyar da dai yaje yana lalata acan.

Shi dai Abdulnaseer murmushi shi yake yi a zuci, domin yasan komai,kuma da alama garin zalamar su,zasu rasa Maysarah gaba ɗayanshi.

"Kiramin Faisal Sirajo maza"Goggo ta faɗa tana share hawayenta.


Dai-dai lokacin da Faisal yake shirin tafiya Kano taho da Halima kiran Uncle Suraj ya shigo wayarshi.

"Faisal maza kazo kuma duk yanda zakayi,karka bari Maysarah ya sauka awani waje idan ba gidan ka ba,kana jina" Uncle Suraj dake waya a harabar gidan a hankali ya faɗa.

"Okay In Sha Allah Dad zanƙoƙarta"daga haka baijira ƙarin kalma ɗaya daga bakin Faisal ba ya katse kiran.


Huci mai zafi Faisal ya fitar, kanshi na ɗaukar zafi.....✍🏻