MAI KWAƊAYI

32

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 32```


________Takaici kamar ya yi kuka, da tuni ya daɗe da isa Kano, uzurin Mubeena ne yadawo da shi.

Bala ya kira ya mishi bayanin gobe da sassafe ya je ya taho da Halima.


A gaban Goggo Faisal yayita kiran Maysarah, amma bai ɗagaba.Ƙwafa tayi,tana faɗin dole Maysarah ya fitar da Matar aure tunda ya iya sumbatar Baturiya.


🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂 


Zazzaɓi mai zafi ne ya rufe Halima saboda fargabar rabuwa Inna,itama Inna ranta sam ba daɗi,tun suna sa rai da zuwan Faisal har suka cire, sai yamma liƙis Bala ya kira Inna yayi mata bayanin da sassafe zai zo ya tafi da Halima.


★ Ko karyawa Halima batayi ba,Bala yazo tafiya da ita. Da kuka da majina shaɓe-shaɓe Halima ta rabu da Inna,itama Inna tasha kuka kamar ƙaramar yarinya.



*ABJ*


11:14am


Mubeena da ƴaƴantane suke Breakfast a sashenta,Faisal kuma na aiki a system. A dai-dai lokacin kiran Bala ya shigo wayarshi,ba tare da shakkar komai ba, Faisal yaɗaga ya basu umarnin shigowa.


Cikin few minutes sai ga Bala da Halima dake sanye cikin brow Abaya daya ƙara fidda kyawunta, tana maƙale a bayan Bala idanuwanta jajir saboda kukan data sha.

Murmushin da Bala bai saba ganin Faisal da shi bane akan laɓɓan shi.


"Oyoyo daughter" ya faɗa yana buɗe mata hannun shi,cikin sanyinta ta nufeshi,kafin a hankali ta faɗa jikinshi tana sakin kuka.


"Ohh no! Diya(Sadiya)"ya faɗa yana bubbuga bayanta. Baki Bala yasaki yana kallon su, yana kuma jinjina soyayyar da Faisal yake yiwa Halima.


Abincin da Mubeena take cine ya sarƙeta,a take kuma tafara tari ba ƙaƙƙautawa, dasauri Sanam ta miƙa mata ruwa tanayi mata sannu.gurin Daddyn su data kafe da idanuwa su Sanam suka bi da kallo, a tare dukkan su,suka miƙe, cikin iyayin dayafi ƙarfin shekarunta,take faɗin" Daddy who is she" dai-dai lokacin da suka isa kusa da shi


Sakin Halima yayi yana kamo hannun Sanam da ragowar ƙannenta Mujaheed da Bibi.


"Sister ku ce ƴar gidan Auntyna"

"Daddy anan zata zauna, inasonta tanada kyau ko Aunty"

Bibi ta faɗa tana kallon Sanam dake ƙarewa Halima kallo,bata cika son ganin mutanen da suka fita kyau na raɓar taba, musamman irin su Halima dogaye, wannan dalilin yasa ganin farko datayiwa Halima,taji sam bata sonta.

Batacewa Bibi komai ba sai kawar da Fuskarta da tayi.

"Nima inason ta menene sunanta Daddy"Mujaheed ya faɗa yana kamo hannun Halima.


"Diya" Faisal ya faɗa yana murmushi.

"Wow nice name"Suka haɗa baki wajen faɗa.


Ganin yadda Mubeena ta nufo su yasa Faisal cewa yaran suje suyi wasa,dama Bala tuni ya fice,sai Halima dake zaune kanta aƙasa.


"Meye wannan ka kawomin?" ta faɗa tana pointing ɗin Halima,ganin bai tanka mata ba sai ƙoƙarin tashi dayake keyi.yasa ta cigaba da faɗin


"Faisal dakai nake, budurwarka ka kawo min ko ƴar Halime?,tayaya wannan zagamemiyar yarinyar zata zama ƴar Halime da take nakashashiya da Salmanun dayake baƙyauyen usul, ni zaka mayar illiterate,ta ya ya yariyar da batafi 11years ba zata zama haka,?bayan rayuwar talauci da wahalan da sukeyi, ka fitarmin da ita kafin Iyayen mu suji kanmu"

Ta faɗa kuka na ƙwace mata.


"Wallahi! Wallahi! Wallahi! Duk ranar da su Daddy sukaji labarin zaman Diya agidannan, to aure na dake ya ƙare,dole ƴar Halime sai ta zama yanda kike son ganinta, ko dole itama sai ta zama nakasasshiya irin Mahaifiyarta?,Mubeena kiji tsoron Allah kinsan Salmanu sama da yanda na san shi, kuma sak yanayin jikinshi ƴar shi tayi,to mai kike son sani bayan wannan?"


"Diya?har da sauya mata suna, wallahi Faisal bazan iya zama da wannan acikin gidana ba,ai kamar ka kawomin kishiya ne,har da rungumeta a gabana"da kuka taƙarasa faɗa tanajin kamar duniyar na juya mata bai-bai.


Itama Halima kukan takeyi,cikin sanyinta mai tafiya da imanin mai kallonta tace"Uncle kamayar dani wajen Inna kaji" fararen hannayenta masu laushi Faisal ya riƙo da sunan lallashinta.

Mubeena dake kallonta da tsananin mamakin ashe nakasasshiya kamar Halime zata iya haifar zuƙeƙeyar budurwa irin wannan,kukan kura tayi ta afkawa Halima da iya ƙarfinta....✍🏻