MAI KWAƊAYI

33

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 33```


________Ta samu nasarar zuba mata marin da ya ɗauke ji da ganin Halima na wasu daƙiƙu,kafin ta rufeta da duka ta ko ina,daƙyar Faisal ya ƙwaceta.

Barin Parlourn yayi ya kullo Mubeena ta ciki.

Ƙaramin sashen daya raba ɓangarenshi dana mubeena ya kaita, two Bedroom flat ne babu abinda babu a ciki, amma basayin amfani da shi,saboda anan Maysarah yake sauka duk lokacin da ya yi ra'ayin sauka a gidan Faisal, amma lokuta da dama yafi sauka a Hotel.


A hankali ya zauna kan ɗaya daga cikin lafiyayyun cushions ɗin da aka ƙawata parlourn da shi,duk don Maysarah yaji daɗi.

A gefenshi ta zauna,kafin a hankali ya janyota jikinshi,yana lallashinta haɗe da shafa lallausan gashinta da bai taɓa ganin relaxer ba,laushin shi sai ya babbanta dana Mubeena. Lumshe idanuwanshi yafarayi saboda nutsuwar dayake ji yana shigarshi. Sai yakejinta kamar ƴar baby a jikinshi.

Bugawar da zuciyarshi ya farayi dasauri-dasauri ne yasa ya zameta idanuwanshi na sauyawa.

Bai shirya canza matsayin Diya a zuciyarshi ba,tayaya ma hakan zaiyu?abune da bazai taɓa faruwa ba har abada.dole ya fara ƙoƙarin yakice abinda yake ji,ya zaunar da ita a gefenshi yana ƙara share mata hawayenta.

"Ya isa mana!"

Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa ya ɗauko mata kayanta.


A hankali ta share hawayenta ta bin bayanshi da kallo kafin da maido hankalinta kan parlourn, ƙamshin Maysarah dake manne a parlourn ne yake shiga hancinta. Lumshe idanuwanta tayi tana tunanin yanda rayuwarta zai kasance tare da Mubeena da ƴaƴanta,a haka Faisal yadawo ya sameta a inda ya barta.


Ɗayan ɗakin ya kaita wanda shima set na komai ne a ciki, amma Maysarah bai taɓa sauka a ciki ba.


Waro idanuwanta masu haske tayi kan Faisal "Uncle ni kaɗai zan zauna anan"

Ƙarfin halin jinjina mata kai yayi.yana ɗauke idanuwanshi daga kallonta.

Haɗiye ƙwallarta tayi tsoron na shigarta.

 Ƙara fita Faisal yayi batare da yaƙara ce mata komai ba,gudun kar ta mishi kuka saboda wannan ne kaɗai solution ɗin shi a yanzu.

Yana fita ta fashe da kuka tana kwanciya kan lafiyayyen gadon,a haka barci mai nauyi ya ɗauketa.


Sai yamma liƙis Faisal ya dawo da uban siyayyan kayan sawa dana amfani dayayi mata har da abinci.


Kanta haɗe da gwiwa ya sameta tana kuka ƙasa-ƙasa, saboda yunwar dake neman illatata,rabonta da abinci tun safe.


Da ɗan saurinshi ya ƙaraso ya tsugunna a gefenta. A ɗan zabure ta ɗago saboda bataji shigowar shi ba.

Tsayawa yayi kallonta na few minutes.

"Bakya gajiya da kuka Diya?"

Ya faɗa yana ƙure kallonshi a Fuskarta ko zai hango muninta.


"Uncle yunwa nake ji"

Ta faɗa tana sakin siririn kukan shagwaɓar data saba yiwa Inna.


Dariya yayi ƙasa-ƙasa wanda yafi kama dana yaƙe dakuma son ƙaryata zuciyarshi.

Bashida kuzarin ce mata komai don haka yajawo ledan abincin ya bata ya miƙe da faɗin "good night"

Dasauri ta miƙe tana ƙoƙarin bin bayanshi da kuka haɗe da faɗin

"Please Uncle I'm scared,I can't live here alone" bai kulata ba ya rufo ƙofar. Kasa tafiya yayi sai bayanshi daya jinginar da ƙofar sashen yana runtse idanuwanshi saboda kukanta dake shiga kunnen shi.

Ya fi minti goma kafin ya bar wajen yana tafiya kamar wanda akayiwa dukan tsiya....


Dan Allah afuwa nasan page yayi kaɗan dayawa In sha Allah akwai update zuwa dare,uzurine yamin yawa.

Nagode da bibiya🙏🏻