34
💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔
( shi ya san gidan mai rowa)
```By```
```SASAAL```
```Page 34```
________kai tsaye Masallacin gidan ya wuce, saboda bazai iya da rigimar Mubeena ba, a irin wannan lokacin.
A ɗaki ta kulle kanta, tayi kukan da ya samata ciwon kai mai tsanani,har lokacin shaiɗan na ƙara zuzuta mata kyan Halima a zuciyar ta,har da yanda taga Faisal na narkar da idanuwanshi wajen kallonta da lallashinta.
"Bazan jure ba,wallahi bazan iya ba," ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka.
Haka ta wuni ko sallah batayi ba,sai kukan da ba shi da magani balle mafita.
Kiran sabuwar Aminiyarta Zainab tayi wanda halayyar su yazo ɗaya kamar Uwa ɗayace ta shayar da su,har ta fi Mubeena baƙin hali da kyashin talaka ya raɓe ta ya ci arziƙi,amma ita babu wani wanda yafi iyayenta arziƙi a dangin su da batasan gidanshi ba, kuma haka take zuwa tana lasar arziƙi ba.
Tsaki Zainab tayi bayan tagama sauraron bayanin Mubeena.
"Yanzu akan wannan kike kuka Mubee? duk kyanta ta kaiki? Gaskiya wallahi baki da wayo,shiyasa kuma Faisal yake miki haka,kicire duk wani damuwarki akanta,ki nuna kin karɓeta,kuma karki kuskura yagane akasin haka, ko akan ƴaƴanki ne, cikin ruwan sanyi zamu korata gida,ko mu sa ya aurawa munafikin drivern daya kawota, tunda ya nuna bayaso Iyayenku su sani, ki ɗaure karki bari su sani dan Ubanta da ƙafarta zata gudu, amma ki barta a sashen da ya kaita,karki kuskura ki bari ya dawo da ita sashenki kona yaranki,sannan 24 7 idan bayanan ki kirata ta gyara miki komai naki, kuma karki bari ya bata damar yin girki,kina jina?"
Da sauri Mubeena ta gyaÉ—a kai kamar Uwarta na bata umarni, tana faÉ—in"eh Zee,amma wajen daya kaita anan fa Maysarah yake sauka, kina ganin ba matsala? Kar yace zai dawo min da ita wajena bazan juri ganinta ba"
Dan jim Zee tayi, saboda ko ba komai zuwan Maysarah ya sauka a gidan shine burinta," a'a ki bari idan yace yanaso ta dawo sashenki saboda zuwan Maysarah, sai kice kin yarda ko dan saboda little sis É—inki da zata samu damar sakewa da shi,hakan ya yi ai, idan ya tafi basai ta koma ba, ko yaya kika gani?"
Zee ta tambayeta haushin Mubeena da mayyar ƙanwarta na mamaye zuciyar ta.
"Eh yayi Zee, thank you soo very much, I soo much love you, I'm so ecstatic da wannan shawara naki"
"Okay take care"
Zee ta yi hanzarin faÉ—a saboda haushin kanta daya kamata,na bawa Mubeena shawara
Da haka sukayi Sallama Mubeena na sauke ajiyar zuciya.
Ko da tayi wanka ta fito tsaf ta samu ko ina,su Sanam dama sun jima da tafiya gidan su,ganin kamar Mommyn su ba lafiya.
Babu fara'a ko É—igo a fuskar Faisal ya shigo sashen nata, idanuwanshi duk sunyi sha saboda bala'in dake shirin kunnawa cikin rayuwar shi.
Yayi mamakin yanda yaga fuskarta da fara'a da kuma yanda ta chaɓa ado so gorgeous.
Rungume shi tayi, haɗe da bashi haƙurin da ko shakka bayayi wani makircin aka koya mata,saboda yasan wacece Mubeena farin sani.
Kamar yanda Zee ta gayamata haka tayiwa Faisal batare da mistake ɗin ko kalma ɗaya,kuma har cikin ranshi ya gamsu da barin Diya a can, saboda hankalin shi,bazai kwanta da barinta a sashen Mubeena ba. Amma bai gam su da karɓar abincin a ɓangaren Mubeena ba,dole zai sama mata abubuwan ciye-ciyen da ko bataci abinci ba zasu gamsar da ita.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
A hankali Halima ta miƙe daga bakin ƙofa ta koma ciki.
Duk da shekarunta ba masu yawa bane sosai,ta gane rayuwa mataki-mataki ne,kuma duk soyayyar da wa su masu kuɗin za su nuna maka, su na ƙyanƙyanmin ka haɗa alaka na jini da su,ko tarayya da su awaje ɗaya,amma a haka dayawan talakawa suke zaɓar su wulaƙanta talaka ɗan uwansu don mai kuɗi yaji daɗi.
A haka Halima ta fassara abinda Faisal ya yi mata,maiyasa zai rabata da Ć´aĆ´anshi dama sashen Matarshi gaba É—aya? "Saboda ke Ć´ar Salmanu da Halime ce"
Zuciyarta ta bata amsa,kuka mai sanyi ta fashe da shi tana rufe fuskarta da tafukan hannayenta.
Juyi tayi ta yi barci yaƙi ɗaukarta.
A dai-dai wannan lokacin itama Inna ta kasa barci sai tunanin wani irin tarba Halimanta ta samu a hannun Mubeena?,yanzu a ina take kwance?.
Haka shima Faisal idanuwanshi soyewa sukayi barci ya ƙaurace mu su.
Mubeena kam tuni barci yayi gaba da ita saboda nutsuwar da ta samu da Mijinta.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
Fuskarshi a haÉ—e tsam,yake kallo da kuma sauraron bayanin Goggo ta video call É—in da sukeyi.
Jin yaki tanka mata yasa ta yi ƙaramin dariya da faɗin
"Maysarah kenan sai ka ga wata rana fa,ina zaune zakazo kana magiyar da warware wannan fuskar taka daka haÉ—e kamar zaka harbeni da faÉ—in "Goggo ki taimaka wallahi dagaske ina sonta har da É—an kukanka" ta faÉ—a tana sakin dariya tsokana.
Matsar da wayar yayi yana sakin ƙaramin murmushin dayake da matuƙar wahala yayi.
"Ja'iri ai daka tsayar da wayar naga murmushin naka,ko bayan ba raina Maysarah zaka tuna da kalamai na"
Katse wayar yayi da sauri,saboda ƙaramin dariya shi daya bayyana jerarrun haƙoran shi,kuma tsaf Goggo ta samu nasarar gani.
Dariya Goggo take kyakyatawa har da tafa hannuwa,babu kuma mai sata wannan nishaɗin sai Maysarah. Banda haka da tsananin fushin ƙin ɗaga kiran dayaƙiyi ta kira shi, amma gashi ta ɓige da dariya.
Shima sai da ya ƙara ɗan darawa bayan ya katse kiran kafin kuma yamayar da fuskarshi asalin yanda yake.
Abdulnaseer dake gefe shima dariya yake yi soyayyar ɗanshi dana Mahaifiyarshi na ƙara samun kyakkyawan matsuguni a cikin zuciyar shi.
Mom Fahima dake laɓe tana jiran taji yanda Inna da Maysarah zasu kwashe,tsaki tayi tana barin maɓoyarta.
"In sha Allahu haka zai mutu ba aure,tunda yaƙi auren Sumayya shegen yaro kawai, jinin Mayu"
Da ire-iren waɗannan surutan taƙarasa sashenta.....✍🏻