MAI KWAƊAYI

35

by @nafisatusasaal01

💔💔```MAI KWAƊAYI```💔💔

 ( shi ya san gidan mai rowa)




  ```By```

```SASAAL```



 ```Page 35```


________★ daƙyar Faisal yakai kanshi masallaci sallar asubahi,saboda kanshi dake yimishi ciwon rashin barcin da bai samuba,da kuma damuwar dayake ciki.


Bayan ya dawo daga Sallah yaƙara tashin Mubeena,cikin faɗan da bai saba yimata ba," kina kiran kanki uwa amma kullum saina tashe ki sallar asubahi, are you n't feeling ashame of your self?,wannan babban abun kunyane wallahi" yana gama faɗa ya kwashe mobile's ɗinshi yabarta da sakakken baki.


Yaushe Faisal ɗinta ya koma mafaɗaci haka,this is not the first time da take makara sallar Asubahi ita da yara but bai taɓa magana ba,"maiyasa yanzu to yayi?"


Ta tambayi kanta,"ohh may be saboda misunderstanding ɗin da suka samu jiya ne. taɓe bakinta tayi tana ƙoƙarin tashi badon ranta yaso ba.


Akan abin sallah tasamu dukka ƴaƴanta, banda Mujaheed dayake nashi ɗakin saboda tare sukaje da Daddynshi.



Sai wajen 11:00am suka fito yin Breakfast saboda ranar weekend ne,babu wanda ya tuna da Halima acikin yaran balle suyi zancenta,amma Mubeena tana sane, murmushin mugunta ta saki aranta tana ayyana irin yunwar dazai gasa Halima.


Kiran sallar ƙarfe ɗaya ne ya tashi Faisal. Kai tsaye wanka yafarayi kafin ya fito yin Breakfast, lokacin Mubeena da yaran dukka sun koma barci.


Saida yaci ya ƙoshi sannan yafito parlourn ya zauna yana ƙoƙarin kiran wayar Maysarah.

A kuma lokacin ne ya tuna Halima ta karya kuwa?

Gabanshi ne ya faɗi saboda yasan balallai Mubeena tasa masu aiki su kai mata abinci ba.


Da hanzari ya katse wayar da dama ba'aɗaga ba ya nufi part ɗin.



Tunda asuba ta tashi bayan tayi sallah ta jera duk siyayyan kayan sawa da mayukan shafawan da Uncle Faisal yayi mata a mazaunin su sannan ta ƙara gyara ɗakin ta wanke Bathroom ɗin ta jera tsadaddun liquid soap ɗin daya siyomata dasu toothpaste dukka.


Parlourn da har lokacin bata daina santin kyanshi aranta ba tafito shima ta gyarashi tsaf.


Tun tana jiran Breakfast har ta cire rai,ta saba awajen Inna ƙarfe bakwai da rabi ta karya ko ƙarfe takwas.


Littafin Mahaifiyarta da Inna batasan ta ɗauko ba ne,ta ciro daga inda ta ɓoyeshi.


Tun bataje ko ina ba tafara kukan tausayinta da jin tsananin tsanar Baban su Sama'ila( Yusha'u) a ranta.


Tsananin tausayin Mahaifiyarta da yunwar dayake neman kashe tane yasa idanuwanta suka ƙarayin ja sukayi ciki-ciki,jikinta ma ya ɗauki zafi.


Dole ta rufe littafin ta ajjiye,saboda sallar azahar da aka kira,a zaune tayi saboda bata da kuzarin miƙewa.


A yanayin data lura sam batasamu karɓuwa a wajen Matar gidan ba, idan har zarginta gaskiya ne,to yakamata ta sawa ranta fuskantar wulaƙanci sama da haka.


A haka Faisal ya fara ƙoƙarin buɗe ƙofar,bata motsaba don koba shi bane,bazata gudu ba gara su kasheta itama ta huta.


Dasauri yaƙaraso ɗakin,sai da yayi sallama,jin shiru bata amsa ba yasa ya murɗa ƙofan ɗakin ya shiga.


Ganinta nannaɗe a kan abun Sallah kamar bata motsi yasa ya birkitota,fuskarshi da damuwa sosai,bai cemata komai ba yakama hannunta ya miƙar da ita har cikin Motarshi mai kyau da tsadan gaske ya kaita. Sannan ya koma ya kulle part ɗin, restaurant mai kyau da tsada ya kaita,yayi mata order abinci kala-kala.

 Abincin ta kalla sannan ta kallashe da idanuwanta da sukayi ja.

Alamar ta ci yayi mata.


Kamar jira take yi,ashe yunwa masifa ne bata taɓa ɗanɗanar azabarshi ba sai ranar.


Ko na minti ɗaya Faisal bai ɗauke idanuwanshi akanta ba,ko zuciyarshi zata sadadu ta gane banbancin dake tsakanin su.


Hamdala tayi ta ɗago fuskarta da sunan ta saci kallonshi,ko yaga yanda taci abinci,tsaf idanuwanta suka faɗa cikin na shi,dasauri ta rufe fuskarta tana sakin dariya, shima dariya ta ba shi, tsokanarta yafarayi suna ta dariya dukkan su.


Maimakon yakaita gida sai wuce da ita gidan Abokinshi,director ne na makaranta dayake son sata,

Ba su samu matsalar komai ba,suka gama magana,sai yamma Faisal ya kira drivern shi yazo da wani motar yamayar da Halima gida,shi kuma ya wuce gidan su.



Bayan Mubeena sun farka sunyi lunch ita da ƴaƴanta,sai ta haɗa kan su, suka fice suma suka bar gidan batareda ta nemi Faisal ba,saboda gudun mitarshi har lokacin kuma tana sane da rashin bawa Halima abinci.


Sai bayan sun zo gida ta tuna Uncle Faisal bai bata key ba, drivern da zata iya yiwa magana kuma yana ajjiyeta ya juya,dole haka ta zauna har bayan magriba sauro duk sun cinje mata ƙafafuwa,


A kan idonta Mubeena da ƴaƴanta suka dawo,sai dai babu wanda ya lura da ita acikin su.


Ganin har ƙarfe tara basu gama tsara yanda tafiyarshi da zai yi jibi zai kasance ba,yasa ya keɓe ya kira Mubeena ya roƙeta ta bayarda abinci akaiwa Halima,a daƙile ta amsa mai,tana katse kiran.


Son taƙara zuwa taci mutuncinta yasa ta ɗebi abincin da kanta na tafi kai mata.


Ba ƙaramin daɗi tajiba na kulle Halima awaje da Faisal yayi, kuma duk a tunaninta yana sane yayi hakan,"banda mugun asirin ku ina Faisal mai tsananin ƙyaƙyamin talaka zai so taimaka muku,ai ga irin tanan kwaɗayayyu kawai" ta faɗa tana dangwarar mata da abincin haɗe da barin wajen,dama daga Faisal sai Maysarah ne,suke da key ɗin sashen.


Tayi kuka irin wanda bata taɓayiba,abincin ma kasa ci tayi tsabar baƙin ciki.


Sai goma Faisal ya dawo,kai tsaye sashen shi ya nufa,saboda hutu yake ɓukata, takalmin ƙafarshi kawai ya cire barci mai nauyi ya ɗaukeshi.


Hijjabin jikinta ta lulluɓe ƙafafuwanta da shi, lokacin da gari yayi tsit sai kukan tsuntsaye, ga shi securities ɗin gidan basa hango ta balle suji dalilin zamanta a wajen.


A hankali ta ɗaga hannu ta sama taroƙi sassauci a wajen Ubangiji kuma ya amsa mata,barci mai nauyi ya ɗauketa fuskarta yayi jajir da cizon sauraye.



★duk da alarm ɗin dake tashin shi kullum sai da ya makara sallar Asubahi sosai,don sai wajen bakwai ya tashi,da hanzari ya ɗoro alola yana mamakin irin wannan barcin dayayi batare da yayi wanka ya cire kayan jikinshi ba.


Yana zaune akan abin sallah har wajen ƙarfe takwas,sannan ya miƙe yana ƙoƙarin cire kayan shi domin watsa ruwa gudun karya ƙara makara yasa ya haƙura da wankan ya farayin sallah,zuciyarshi ce tayi wani irin bugun dayasa kanshi ɗan sara mai, jin mukullin sashen da Halima take a aljihun shi.


A haukace ya faɗa sashen mubeena,sai dai bai ga wani abu dayayi kama dana Halima ba balle ita kanta.


A karon farko yaji ƙwallar tausayinta na cikowa idanuwanshi yana faɗin "ohhh nooo!" saboda zuciyarshi dake bashi tabbacin a waje kenan ta kwana.


A haukace ya nufo sashen takunshi kamar zai huda ƙasa.....✍🏻