GONAR SHARRI...

96

by @billysfari

GS 96.


Zain kuwa ko da yaje suka kai Irfaan gidansa bayan sun raka ango angama sayen baki tare da yi musu fatan alkhairi shi ya ɗauko Husnah da Khadija kawar Ayusher ya maida su gidan Kawu Ibrahim sannan ya juyo ya maido da motar Alhaji Sha'aban shi kuma ya tari abun hawa ya koma gida cike da gajiya.


Gaba ɗaya jinsa yake tamkar shi ya yi komai saboda yadda jikinsa yake ciwo ta ko'ina. Bai tabbatar da gajiyar ba sai da yai wanka ya shiga ɗaki ya kwanta, a lokacin jinsa yake tamkar ana saka muciya ana sassara masa duka jikinsa.

___________


A ɓangaren Kawu Ibrahim kuwa ko da ya koma gida ya tadda ƴan biki sun watse sai waɗanda ke nesa da zasu sake kwana dan wasu har sunyi shirin kwanciya kasancewar anyi hidima an gaji jiki yana buƙatar hutawa shi yasa suka kwanta da wuri. Kawu ya kira Umma ta waya yace ta samesa a ɗakin sa. Sai da ta fara haɗo masa abincinsa da tun rana bai samu ya zauna yaci ba sannan ta nufi ɗakin nasa. Sallama tayi ta tura ƙofar ta shiga Kawu Ibrahim na zaune ya rafka uhan tagumi, ta ajiye abincin agabansa tana kallonsa take cewa.


"Malam lafiya?".


"Janye min abincin nan Bilkisu bazan iya cinsa ba kwata-kwata, ni gaba ɗaya al'amurran duniyar nan mamaki suke bani, abubuwa ne gasu nan tamkar a shirin film suke faruwa akoda yaushe, wani idan ka ji sai ka kasa gasgata faruwarsa saboda tashin hankalin dake ciki." Jikin Umma a sanyaye ta nemi waje ta zauna tare da tattaro hankalinta gaba ɗaya akan mijin nata, yakan zo mata da labaran matsaltsalun da ake kawo masa ya warware da suka bashi mamaki a matsayinsa na malami ta kuma tsaya ta saurare sa ta bashi shawara ko kuma ta ɗauki darasin da yake son yi mata hannunka mai sanda aciki, shi yasa ranta bai bata komai ba yau ta shirya tsayawa ta sauraresa tana cewa.


"Haka rayuwa ke tafiya malam da abubuwan ban mamaki, wasu ƙaddarar Allah ke wanzar dasu cikin rayuwa wasu kuma son zuciya wasun su kuma kuskure ne, me yake faruwa ne Malam?" Kawu Ibrahim ya ja ajiyar zuciya ya sauke sannan yace.


"Matsalar iyalin gidan Alhaji Sha'aban ce. Kin san sai yau suka dawo shida Jauhar, to ita Maimuna yau taji labarin auren nasu ko nace idanuwanta suka gane mata.." Kafin yaƙarasa Umma da tasan dama hakan zata faru kobadaɗe duk daran dadewa tasan wannan ranar zata zo kafin ta taji wani babban tashin hankalin da yafi waɗanda takeji ta sauke ajiyar zuciya haɗe da cewa.


"Toh menene don ta ji ko ta gani Malam? Dama ai dole zata ji wannan auran indai da rai da lafiya. Kuma duk ba ita ta jawa kanta ba? Sannan namiji ai mijin macce hudu ne ko ba Jauhar ba tunda Allah ya yi zai ƙara aure ai dole sai ya ƙara, in dai dan ta wannan ne ku ƙyaleta za tayi haukanta ta gama ta karɓi ƙaddararta hannu biyu, don na tabbata ko me zatayi Alhaji bazai saki yarinyar nan ba tunda ba ƙaramin mutum ba n.."


"Ashha ai ki bari kiji karshen labarina Balkisu, ba a nan gizo ke saƙar ba. Kinsan wai ashe duk wannan abun da Maimuna kewa yarinyar nan ƴar ta ce ta cikinta?" Dariya Umma tayi haɗe da cewa.


"Kai Malam wannan zancen ba gaskiya bane ba, wace uwa ce zata yiwa ƴarta haka fisabilillahi? kuyi tunani gaskiya. Wai ma ba wannan ba a ina kuka samu wannan labarin?" Umma ta faɗa tana sauke kallonta akan Kawu Ibrahim dashi kansa har yanzu bai gama yarda da zancen ba. Ya ɗaga kai ya kalleta cike da tabbatar mata kamar yadda ya ji aka kuma shaida masa yace.


"Ita Jauhar ɗin da bakinta ta tabbatar da hakan bayan uwarta ta furta zancen cewa..." Nan dai ya kwashe labarin a-z ya sanar da Umma wacce tuni zufa da tsananin tashin hankali suia ziyarce ta.


"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, Allahummah ajirni fi musibati wa ahlifni khairan minha ya hayyu ya qayyum, yanzu dama Maimuna ita ta haifi Jauhar shine bata taɓa sanar da kowa ba? wannan wace irin uwa ce haka? Toh me yasa zata ɓoye cewa Jauhar ƴarta ce kuma ta rinƙa azabtar da ita azabtarwa mai muni?"


"Shine bamu sani ba muma sai gobe idan Allah ya kai mana rai da lafiya mu tafi can wajen iyayen rikonta da suka bamu aurenta, idan ma takama har iyayenta su shigo a wannan magana don warware zare da abawa to sai a neme su.


"Tirƙashi! Amma inhar gaskiya ne Maimuna ta cuci Alhaji Sha'aban da yarinyar nan, kai har ita kanta ma ta cutar don ba wanda yasan yadda za'a warware matsalar nan tare da matsayin auren su duka ita da ƴar."


"Koma dai meye yanzu baza mu iya cewa komai ba sai mun samu tabbacin abunda suka faɗa ɗin." Daga haka Umma ta lallaɓa Kawu ibrahim suna hira har ta samu ya ci abincin sannan tabar ɗakin, lokacin ne tana fitowa Husnah da Khadija da Zain ya aje suka shigo, inda suma suka ɗora da abinda kunnuwan su suka jiyo musu acan gidan Irfaan ɗin wanda matar nan tafaɗa.

___________


Irfaan ango kuwa bayan abokansa sun tafi ya rufo gidansa ya koma ciki, zaunawa yai bakin gado kusa da Ayusher yasa hannu ya yaye mayafin dake rufe da fuskar ta yana sauke ajiyar zuciya, wacce ko ba'a faɗa ba kasan ta farin ciki ce da godiya ga Allah daya nuna musu wannan ranar, duk da dai ƴan abubuwan da suka faru sun rage kaifi da karsashin wannan farin ciki nasa. Ɗago idanuwa Ayusher tayi ta zubawa angon nata da ta ji ya kasa cewa komai sai kallonta da yakeyi fuskarsa na nuna ƴar damuwar dake ƙasan zuciyarta, ita kanta jikinta a sanyaye yake da labarin daya riske su ɗazu, da kyar ta iya buɗe baki ta ce.


"Noor Qalb da gaske ne Jauhar ƴar Aunty Maimoon ce?" 


Irfaan ya kasa cewa komai sai janyo Ayusher da yai kawai jikinsa ya rungume ko damuwar da yake ji zata ragu a zuciyarsa. Suka sauke ajiyar zuciya duk tare. Tsawon mintuna uku suna a haka Ayusher na shafa bayansa a hankali cike da son sama masa nutsuwa don ta fahimci yanayin da yake ciki ta cikin idanuwansa. 


"Ina jin matukar tsoro idan hakan ta tabbata, nasan dole ne cikin biyu tafaru da Yaya, ko dai ya rabu da Jauhar ko kuma ya rabu da Aunty Maimoon kuma hakan ba abu bane mai sauki awajensa duba da irin soyayyar da yake yiwa Aunty Maimoon ba kaɗan bace dan dukkanin mu mun san da haka. Jauhar kuma tausayinta da san ganinta cikin farin ciki ba zai barshi ya rabu da ita farat ɗaya ba." Ayusher ta ɗago daga jikin Irfaan idanuwanta cike da ƙwalla tace.


"Noor Qalb amma idan har Yaya ya rabu da Jauhar ba'a yi mata adalci ba, abun da ake guje mata faruwarsa shi zai faru don karshe za'a iya cewa.." Saurin ɗagowa Irfaan yai ya haɗe bakinsu waje ɗaya don baya son taƙarasa faɗar abunda ke bakinta, baya jin cewa a karo na biyu bazai iya yin abinda yayansa ya yi ba a farko in har ya rabu da Jauhar ɗin.


Da haka Irfaan ya faɗa wata duniya data shagaltar dashi da barin tunanin da yakeyi yana jinsa cikin wata duniyar daya ji wata irin nutsuwa na saukar masa a hankali. Daƙyar ya jurewa cire bakinsa daga nata yana sauke wani irin numfashi mai karfi kafin ya kalli Ayusher ɗin yace ta tashi tayo alwala su yiwa Allah godiya daya cika musu burin su tare da tabbatar musu da mafarkin su. Ayusher ta miƙe a kunya ce ta nufi toilet yana binta da kallo sannan shima ya miƙe ya wuce ɗakinsa ya ɗauro alwalar tare da sauyo kayan jikinsa zuwa jallabiya ya dawo ɗakin.


Zaune ya tadda ita a bakin gado ya ɗauki abun sallah daya gani saman chest of drawer ya shimfiɗa musu, Ayusher ta miƙe da yake lafaya ce ajikinta da ta rufe mata ko'ina sai kawai tabi bayansa ta kabbarta sallah. Raka'a biyu ya jasu suka sallame ya sake tashi ya yi wasu raka'a biyun suka sallame sannan ya ɗaga hannu sama ya yi musu addu'a sosai, ya juyo ya dafa goshinta ya yi mata addu'a kamar yadda Annabi ya umurta. Bai da matsala da ita ta fannin ilimin addini sanin ko wacece ita kafin ya mike ya ɗakko ledar dake gefe ajiye.


Ciyar dasu ya yi har suka koshi sannan ya kwashe sauran ya je kitchen ya saka acikin fridge ɗinta da yaga har an jona yafara sanyi.


Koda ya dawo ya tarar da ita tsaye tana ninke abun da suka yi sallah, ya buɗe wadrobe ɗin kayanta ya ɗauki hijab da wasu kuyan bacci, tsaye Ayusher ta jishi ta bayanta ya sakalo kansa ta tsakanin wuyanta yana sumbatar fatar jikinta, runtse idanuwa ta yi tana jin wani irin yanayi na shigarta daya haifar da subucewar abun sallar dake hannunta data gama ninke wa.


"Zo muje ki raka ni ɗakina mu kwanta". Ya faɗa cikin wata irin fitinanniyar murya dake tabbatar da a bukace yake da matarsa. Ba tare daya bata damar cewa uffan ba ya ja ta suka nufi ɗakinsa har lokacin kansa na tsakankanin wuyanta yana sumbata haɗe da shaƙar ƙamshin dake tasowa daga cikin fatar jikinta ita kuma sai faduwa gabanta keyi. Suna shiga ciki ya shiga warware mata lafaya ɗin yana cewa.


"Wannan abun dai na gano akwai takurawa atare dashi, duk anbi an nan naɗe min jikin mata dashi sai kace an samu dami." Ayusher ta saki murmushi tana sadda kanta ƙasa dai-dai lokacin daya gama warware lafayar ya cillar gefe, bai tsayawa cewa komai ba ya sake janta suka shiga bedroom kai tsaye ya wuce dasu toilet suka wanko bakinsu da sabbin toothbrush ɗin dake ciki sannan suka fito. Irfaan bai tsaya komai ba ya kashe musu fitila sannan ya cire jalabiyar dake jikinsa, Ayusher na ganin haka gabanta ya sake tsananta buguwa bata ankare ba taji ya janyota jikinsa suka faɗa kan gado.


(Muna ganin haka muka janyo kafafuwan mu tare da rufo misu ƙofar muna faɗin asuba ta gari amarya da ango.)


MUNA SAKE BADA HAKURI BISA KUSKUREN DAYA FARU JIYA NA SAKA MAKU PAGES BIYU IRI DAYA, YANZU GA WANNAN PAGE ƊIN A UNLOCKE SAI YA YI REPLACING KUDIN WANCAN PAGE DIN,DUK DANA TABBATA WASU BASU BUDE DAYAN BA MUKAYI CLEARING ISSUE ƊIN, MUN GODE SOSAI👏


#A heart touching story

#Gonar Sharri

#Alhaji Sha'aban

#Hajja Maimoon

#Jauhar

#Billy s Fari

#Hajja ce

#Ƴan Tagwaye