NIKAAH (Marriage for rent)

12 NIKAAH

by @hanaady

NIKAAH* 

*Marriage for Rent* )


*By* 

*HANAADY* 

Rahama Aminu Bala 


*WhatsApp* 

***** 


*Follow me on Whatpad* 

*Rahama000* 


HE HAD THE COURAGE 

TO REMARRY.

WILL HE FIND THE COURAGE TO

LOVE AGAIN?




*Page 12* 


Cikin rashin fahimta Karime tace ban gane ba murmushi Zuby tayi sannan tace duk fad'in Islamiyyar nan babu macen dake gigin zuwa inda yake domin shi d'in nawa ne ni kad'ai sabida haka idan ma kin fara sonsa toh ina mai baki shawara tun wuri ki ajiye domin nawa ne ni kad'ai .


Kasa magana Karime tayi wata sabuwa ta furta cikin ranta a halin yanzu sam bata da kuzari ko wani k'arfin mayar da zance ,gaba tayi ba tareda ta furta koda kalma d'aya ba,saurin shan gabanta Zuby tayi magana fa nake miki dan kutumar uban ki, cikin b'acin rai Karime ta tsaya kafun Zuby ta kuma furta wata magana saukar mari taji saman kuncinta ,


cikin mamaki ta kalli Karime,tunda kika ga nayi shuru kamata yayi ace kin kama kanki domin wallahi ni Karime sam bana da sauki amma kika kasa hakan hada wani biyo ni had'i da zagin Baban Jummai ce miki akai bana son shi duk da shi d'in ba sona yake ba ina jinsa a raina domin da uba ake ado. 


Tana kai aya tayi gaba abunta direct gate ta nufa domin ji tayi komai ya fice mata a hanya take ta sababi fasa shiga flata nasu tayi zarcewa tayi sashen Dada ,acan kuwa sosai Dada tayi farincikin zuwan Karime ,kiran Sailuba Dada ta shiga wacce tana kitchen cikin sauri ta fito tared gaishe da Karime ansawa tayi ba yabo ba fallasa ,Sailuba maza had'a kayan lalle domin yau Karime bata barin sashen nan babu lallale ,saurin mi'ke tsaye tayi tareda kama hannun Little Dada gobe ayi mun yanzu kuwa Wallahi fama nake da ciwon fata


zaki zaune ko saina nuna miki b'acin rai na saida ta zun'buro baki kafun ta zauna , cire hijab d'in jikinta tayi tareda yayi gwon d'in Islamiyyar ta lallalen Sailuba ta fara saka mata Dada ce daga kefenta sai sababi take ina amfani hannun mace kaman na wani saurayi sam babu alamun lallale tareda fatar jikinki toh menene banbancin hannuwan ki dana shi Ramadan d'in ,Allah kuwa Dada akwai banbancin domin ne ai hannuwana duk wanda ya kalla yasan na mace ne sabida ai basu kai nasa girma ba haka zalika kafa ta sam bata Kai tasa ba


rufe mun baki shashasha Dada ta fad'a hada d'aga hannu kaman zata make Karime dariya Karime sannan tace wai Dada duk fushin nan akan lalle ne?


Eh mana tunda ana son miki gata kina 'ki last time ina sane dake guduwa kikayi danace ki tsaya ayi miki lalle yanzu tunda kinzo hannu ai shikenan, Dada a hannu kaidai za'a mun koh ? Sai yanda number ta bada Karime cewar Dada.

A bangaren Zuby kuwa mutuwar tsaye tayi domin sam ta kasa gane yanayin ta yau ita ce wata banza ta mara Kafiyar ki kuwa Mimi ta fad'a wacece fitowar ta kenan daga class nasu tuni har an tashi saurin wayencewa Zuby tayi bakomai kinga yarinyar ne? Dan murmushi tayi sannan tace lokacin da naje class nasu tuni ta gudu sai dai gone Allah ya kaimu Mimi ta bata ansa tareda fara tafiya ,bin bayan ta tayi tana mai sakawa da warwarewa .

A bangaren Ramadan kuwa bai dawo gida ba sai bayan sallar isa kiran sunanta ya fara shuru upstairs ya haye nanma bata nan fad'uwar gaba mai tsanani yaji tunowa da part d'in Dada ne yasa yaji ya d'an sami kwanciyar hankali,cikin sauri ya nufi sashen Dada,a hanya ya had'u da Khaleel gaisawa su kayi kwana 2 bana ganin ka Masjid Ramadan ya fad'a yana mai kallon Khaleel d'an murmushi Khaleel yayi sannan yace bananan ne naje Lagos oh Ramadan ya furta tareda cewa how's Dady? 


Yana lafiya tare muka taho dashi but shi flight d'in Kaduna yabi domin akwai wani important meeting da yake son attending ok Ramadan ya furta tareda fara tafiya kasancewar da a tsaye suke magana.

Koda ya isa basa downstairs so direct upstairs suka nufa basa falo but ya jiyo hayaniyar Little a bedroom d'in Dada ,bakin k'ofa ya tsaya yana mai k'are mata kallo ,zaune take an gama saka mata lallen jingine take da sofa kusan rabin cinyoyinta a bud'e suke da gudu Little tayo kansa Dady sai a lokacin ne Karime ta san da zuwansa kallo d'aya tayi masa kaunda kanta tayi tareda cigaba da latsa wayarta, 


Khaleel dake bayan sa ya kosa ya bashi wuri koya shiga ciki su gaisa da Dada but mutunen naku ya babbake hanyar Karime ina Dada ya fad'a daga bak'in k'ofar ba tareda ta kalle shi ba tace Dada tana kitchen bin fuskar ta da kallo yayi babu hijab a jikinta rigar ta d'an matse ta daga sama wanda zaka iya hanko boost d'inta duk da ba wani sosai bane ,ajiyar zuciya yayi tareda juyawa ya kalli Khaleel muje ina son magana da kai 


da mamaki Khaleel yabi bayansa saman sofa suka zaune ,daga inda Ramadan yake tsaf yan kallonta sakin hannun Little yayi tareda cewa ki fad'a ma Dada gamu a gidanta da gudu Little tayi hanyar kitchen.

Gyaran murya yayi sannan yace ina zuwa give me two minutes nesa da Khaleel ya tsay kiran wayarta yayi ,a nata bangaren tana ganin kiran ta'ki dagawa sake kira yayi dagawa tayi tareda gyara murya sannan tace mai wayar bata kusa shout up Karime don't you dare try to act smart ki saka hijab d'inki and ki gyara wannan stupid zaman da kika yi ni wallahi ba zan saka hijab d'ina ya b'aci da lalle ,lallashin ta ya fara please my Best idan ya b'aci i promise zan siya miki wani , zun'buro baki tayi sannan tace toh wai menen dalilinka na saina saka hijab katse kiran yayi ganin Khaleel na k'okarin bin bayan Dada zuwa bedroom,


saurin shigewa bedroom d'in yayi tareda d'aukar hijab d'in saka mata yayi kafun tace wani abu yayi sama da ita Allah ka ajiye ne. Lafiya Dada ta fad'a cikin mamaki bai bata ansa ba illa ficewa da yayi murmushi Khaleel yayi domin tuni ya gane inda yayan nasa ya doso inde haka ne he is very happy for him , finally an fara samun cigaba tunda sosai yaga kishin Karime a idanuwan Ramadan .

Sauka yake saman stairs fuskar murtuke d'an kallon sa tayi sannan tace kaga kuwa wani abu a saman fuskar ka banza yayi da ita , ta'be baki tayi sannan ta kuma cewa kunnuwanka Allah d'aya yafi d'aya girma sosai furucin ta ya bashi dariya but mazewa yayi tareda k'ara shan kunu ,,kanada gira mai kyau yaji tana fad'a fitowarsu daga part d'in Dada kenan suka had'u da Fadeela matar Khaleel 

Bai mata magana ba haka zalika Karime saima kwantar da kanta da tayi saman jikinsa ,baki sake Fadeela tabi su da kallo, , saurin kiran Alia tayi sis dafatan kin taho dan wallahi yarinyar can gab Ramadan yake da fad'awa soyayyar ta a bangaren Alia kuwa sosai hankalin ta ya tashi .


Kiran Momy tayi akan wai Fadeela taga Ramadan d'auke da matar renting,zan masa magana Momy ta fad'a bayan sun gama wayar da Alia tsaki Momy tayi domin wani lokacin ji take duk abun ya fice mata .

A jiye ta saman sofa yayi , saida ya zauna yana fuskantar ta sannan yace , da izinin wa kika je part d'in Dada zun'buro baki tayi sannan tace yo da izinin kaina , d'an Kankance idanuwan sa yayi sannan yace i will punish you for fita ba tareda izinina ba, zun'buro baki tayi tana magana k'asa k'asa, me kika ce hannun ta ta nuna masa kaman mai shirin kuka tace wallahi wannan abun duk ya dameni ki cire mana ya fad'a yana kallonta kire mun hijab d'innan please,


cire mata hijab d'in yayi ganin tana k'okarin sauka daga saman kujerar ne yasa ya d'auke ta, ba bedroom zaka kaini ba waje zaka kaini acan zan cire shi domin bata mana toilet za yayi umarni ta yabi zuwa backyard bakin wani famfo ya ajiye ta zama tayi k'asa tareda fara cire lallen kasancewar jane sosai ya haska fatarta tsaye yayi yana kallon ikon Allah, bayan ta gama cire lallen wankewa tayi , muje tace tana kallon sa zuwa ina ya furta ka d'auke ni mu koma cikin gida baki da kafa ne ?


Babu takalma a kafana ta bashi ansa, d'aukar ta yayi zuwa bedroom d'inta yana ajiye ta ficewa yayi,harara ta banka masa sannan tace d'an rainin wayau nine d'an rainin wayau ta jiyo maganar sa aikuwa da gudu ta fad'a toilet ,na shiga ukku ni Karime mai na jawo ma kaina. Yarinyar nan ta fara ganin makwancina ya furta tareda samun wuri ya zauna saman bed, d'an le'kowa tayi zaune ta hango shi saurin komawa tayi ciki


banko k'ofar yayi cikin tsora tayi baya sannan tace wallahi bada kai nake ba dawa kike ya fad'a yana mai danganata da bangwon toilet d'in runtse idanuwan ta tayi sosai yaga tsoron sa cikin idanuwan ta d'an murmushi yayi sannan yace open your eyes , gyad'a kanta tayi alamun Aaa open your eyes ya kuma furtawa wannan karan a hasale yayi maganar saurin bud'e idanuwan nata tayi , maimaita abunda kika fad'a bazan iya ba ta furta d'an murmusawa yayi sannan yace kin fara rainani ko Karime dan Allah kayi hak'uri ba zan kuma ba ,


laifi nawa kika mun a yau d'innan biyu ta bashi ansa then dole na hukunta ki dan Allah kayi hak'uri buge bakin nata yayi da yatsan sa sannan yace koda wasa kada na kuma jin kina kiran sunan mahaliccinmu a cikin toilet ba zan kuma ba Mijin Sa'ada d'an ja da baya yayi sannan yace kiyi wanka zamu fita da haka ya ficewar sa .


Ajiyar zuciya tayi kafun ta fara cire gwon d'in jikinta, A bangaren sa kuwa bedroom dinsa ya koma acan ya shirya cikin dogayen kaya yadi ne white color sosai yayi masa kyau , na shirya ta bashi ansa koma kiyi sallama ya fad'a ba tareda da kalle ta ba kasancewar tsaye yake gaban mirror zaman hular kansa yake gyarawa , sallama tayi ciki ciki ansawa yayi tareda juyowa yana fuskantar ta fashewa yayi da wata irin dariya b'ata rai tayi ita fa bata son raini da wula'kanci cikin jin haushinsa ta nufi hanyar fita saurin ruk'o ta yayi, zaunar da ita yayi saman bed,


zama yayi sannan ya kama hannun ta k'ara murtuke fuska tayi cikin alamun rarrashi yace da wannan shigar zamu unguwar kallon kanta tayi sannan tace toh menene aibun shigata naga kayan jikina ranar bikinmu na fara saka su murmushi yayi sannan yace amma Best ina sabbin kayan ki b'ata rai tayi sannan tace wallahi na gaji da saka wasu kaya ba atamfa ba ko lace sabida haka ka shafa mun lafiya domin na kagara a kawo mun d'inkina kona fara sakawa ,


kice wad'annan kayan sabbi ne Ramadan ya fad'a yana mai k'okarin boye dariyar eh mana Mamana ta d'inka munsu sabida haka yau su nake ra'ayin sakawa ,na fasa zuwa dake tunda da wannan shigar zaki ga mamakin sa murmushi tayi sannan tace ta kwana gidan sau'ki .


Ficewa yayi daga bedroom d'insa zuwa nata duk abunda yasan zata buk'ata ya d'auka mata gaban mirror ya tarar da ita kallon kanta take tana d'an murmushi , ajiye kayan yayi tareda takawa zuwa gare ta rungume ta yayi ta baya murya k'asa k'asa yace me ake a gaban mirror?

K'okarin janye shi take daga jikinta , k'ara matse ta yayi sannan yace Umm fad'a mun Yana maganar yana mai d'aura bakinsa saman wuyanta kissing wuyan nata yayi ,ita fa bata son suna samun irin wannan kusanci domin a yanzu ta san matsayin ta zare hijab d'in jikinta yayi slowly ya zuge zip d'in rigar ta kankame jikinta ta fara a hankali ya cire zanin jikinta daga ita sai underwear rad'a mata yayi ya naga kinyi shuru Karime kasa magana tayi domin al'amarin Mijin Sa'ada abun mamaki ne


black color abaya ya saka mata ribbon d'in kanta ya zare tareda saka mata kalar fari ,y'ar kallo Karime ta zama domin she is out of words mayafin ya d'aura saman kanta ganin ana ganin gashin kanta ne yasa ya zare ribbon d'in tareda nannad'e gashin sannan ya d'aure shi da ribbon ,Saida ya tabbatar da ya shirya ta kafun ya sagala mata jakka white color dukawa yayi cikin natsuwa ya saka mata takalmi shima white color ,mutuwar tsaye yayi domin ba k'aramin kyau Karimen sa tayi ba janta yayi zuwa mirror kallon kanta tayi wani irin murmushi tayi sannan tace wai ashe haka nake da kyau


sosai maganar ta ta bashi dariya . Ganin yana dariya yasa fara'ar fuskar ta ta fara gushewa d'an kama kansa yayi sannan yace kinyi kyau sosai Karime fari tayi da ido cikin wani salo tace dagaske Mijin Sa'ada,kasa bata ansa yayi domin sosai ta tafi da imanin sa shafa fuskar ta tayi cikin wani yanayi yace kinyi kyau sosai Karima , kissing hannuwan ta yayi wanda suka sha jan lalle, janta yayi zuwa jikinsa sosai bugun zuciyar sa ya k'ara sun dad'e haka daga bisani itace ta fara k'okarin zare jikinta, d'an kyaran murya yayi sannan yace muje koh kai ta gyad'a domin bata iya magana ,gaba yayi ita kuwa ganin fita za suyi ne yasa ta bud'e wata locker ragowar kud'in daya bata ne ta fiddo cikin jaka ta saka da niyyar siyen wani abu a hanya domin sosai take ji kwadayi .


A mota fito da kud'in ta tayi tana lissafawa bayan ta gama lissafi ri'ke kayan ta tayi tana mai kallon gari driving yake hankali kwance he don't know why yau d'innan wani farinciki yake ji , lokaci zuwa lokaci yakan kalle ta , tsintar maganar ta yayi nace hada shago zamu koh? Kina buk'atar wani abu ya fad'a ba tareda ya kalle ta ba washe baki tayi sannan tace aaa kasan ni idan ina period akwaini da kwadayi Allah ya fad'a yana mai kallon jefenta sosaima tace toh yanzu me kike so fara da zan samu ,fara ya maimaita eh bai kuma cewa komai ba haka suka cigaba da tafiya ,, sunyi tafiya mai d'an nesa kafun ya tsaya wani shopping mall fita yayi , zagayawa yayi tareda bud'e mata k'ofar motan ,cikin fara'a tace aida baka wahalar da kanka ba bai bata ansa ba gaba yayi abunsa,bin bayan sa tayi tana y'an maganganun akan tsaruwar wurin gaf da zasu shiga ya juyo yana fuskantar ta please Karime banda magana zun'buro baki tayi akan me za'a hanani magana nida bakina, 


Kankance idanuwa yayi sannan yace bakin ki bakina ne Karime so please don't talk okay ya idasa okay d'in cikin alamun lallashi ok ta bashi ansa tana mai zun'buro baki, toh tunda kace bakina naka ne kaima naka bakin nawa ne da wani irin kallo ya bita kasa jure hakan tayi sabida haka saddar da kanta ta hannu yasa tareda d'ago ha'bar ta cikin wani yanayi yace Karima komai nawa naki ne bawai bakina kadai ba kasa bashi ansa tayi domin yanayin kallon da yake mata ya girme tunanin ta , d'an gyaran murya yayi sannan yace please banda magana koh kina so mutane suce daga kauye kike kai ta gyad'a masa alamun aaa


Hannunta ya kama da mamaki yace wad'annan kud'in fa? Nawane ta bashi ansa menene amfanin jakar ki, kud'in ya ansa tareda saka mata su cikin jaka b'ata rai tayi domin ita tafi son ri'ke kayanta a hannu .

Bayan sun gama shopping d'in mota suka shiga tunda taga sun d'au hanyar kauyen su ta fara b'ata rai sam bai lura da yanayin taba domin hankalin sa yana kan driving d'insa , chocolate take ci but ji tayi ta fita ranta cikin fushi da b'acin rai tace ka sauke nina taka da kafa ta bana buk'atar ka kaini da motar ka , kallon ta yayi ganin yanda ta b'ata rai yasa ya nufi gefen titi parking yayi tareda cewa lafiya Karima ? Fashewa da kuka tayi sannan tace aiba saika mayar dani gida ba zan taka da kafata dama tunda na sanda dawowar budurwar taka ai dole na koma kauyen mu amma shine zaka mayar dani gida ba tareda na d'auko komai ba cikin kayan lefena tunda ta fara magana yake binta da kallo sosai lamarin Karime ke bashi mamaki wato ita a tunanin ta gida zaya mayarda ita sabida Alia .


Bud'e k'ofar motar tayi tareda ficewa , ajiyar zuciya yayi tareda bin bayan ta ganin ya biyota yasa ta zunkud'a da gudu dakyal ya samu ya kamota tutture shi take ita wallahi ya barta ta taka da kafata d'aukar ta yayi zuwa cikin motar lock ya saka kafun ya d'aura kansa saman staring motar ya kasa gane matsalar Karime , jikinta sanyi yayi sam bata son ganin Mijin Sa'ada cikin wani damuwa , hular kansa ta cire d'ago kai yayi yana kallon ta d'an matsowa tayi kusa dashi shafa fuskar sa tayi tareda k'ara matsar da fuskar ta gaf da tashi hancin ta ta goga saman nasa lumshe idanuwan sa yayi yana mai jin wani sabon yanayi matsar da bakin ta tayi dai dai kunnen sa ta toh kayi hak'uri idan na b'ata maka rai ta furta cikin alamun jan hankali wanda ita a ganinta ba bani abu tayi ba


,bud'e idanuwan sa yayi tareda binta da kallo, so Karime you knew how to seduce me idasa maganar yayi yana binta da wani irin kallo ,kayi hak'uri please ta furta janyota saman cinyar sa yayi ,zame mayafin kanta yayi had'i da ribbon d'in kanta ,akan me zan mayarda ke gida shagwabe fuska tayi sannan tace yo tunda first love taka zata dawo bayan haka ai dama data dawo ne zan koma gida baice da ita komai illa rungume ta da yayi lamo tayi tana jin heartbeat d'in sa d'agowa tayi daga jikinsa da kallo ya bita kafun yace naso Alia ada but a yanzu bana tunanin ina sonta , murmushi Karime tayi sannan tace zuciyar ka ta Sa'ada ce koh cikin wani yanayi tayi maganar saurin had'e bakinsu yayi sosai yake kissing nata, rikice mata yayi ganin abun na mijin Sa'ada ya wuce tunaninta yasa ta saka masa kuka 


d'agowa yayi daga jikinta saurin zuge zip d'in rigar ta tayi tareda saurin komawa wajen zaman ta sai faman goge hawaye take da tafin hannun ta d'an murmushi ya saki tareda cewa Karima kice kika yi seducing nawa ,and here you are crying ,rufe fuskar tayi da gashin kanta murmushi yayi sannan yace duk lokacin da kika kuma seducing d'ina zan kuma baki mamaki ragguwa wallahi niba ragguwa bace ta fad'a tana mai d'ago kanta dagaske ya fad'a yana mai sakin murmushi,eh mana a kauyenmu tsorona ake sabida haka niba ragguwa bace idasa maganar tayi tana shirin kuka, kukan ya isa matata, bana son kina wahalar mun da kanki domin all of you are mine , zun'buro baki tayi sannan tace ai d'azu cewa kayi bakina ne naka .

Shafa fuskar ta yayi sannan yace ked'in matata ce mallakina nace komai naki Karima nawane ,sake jawota jikinsa yayi kissing forehead d'inta yayi murya k'asa k'asa yace forehead d'inki nawane , kissing kumatun ta yayi cikin wani salo yace suma nawa ne slowly ya gangaro zuwa lips d'inta kissing nasu yayi suma nawane , slowly ya matsar da hannun sa inda ba tayi tunani ba shafa boost d'inta yayi cikin wani salo yace they are mine ,Karima not just your lips komai naki nawane , you belong to Ramadan Karime kasa magana tayi domin mijin Sa'ada ya kashe mata baki murmushi ne ya su'buce masa domin ya fahimci matar tasa babu bakin magana,gyara mata zama yayi tareda fara driving hankali kwance. Da taimakon ta suka isa layinsu,d'an nesa da gidansu yayi parking saurin ficewa ,sai faman washe baki take ,bayan ya fito daga ne yace wannan murnar ta mecece ?


Ina murna ne yau zanga Mamana bayan haka dole nabi sako da lungu na kauyenmu domin na nuna masu wayewar ta shafa fuskar ta yayi sannan yace kina washe baki, kanki na rawa a haka zaki nuna musu wayewar , zun'buro baki tayi sannan tace to ya zanyi d'an murmushi yayi sannan yace mata wasu aji basa magana cikin hayayaga and suna magana ne cikin sanyin murya da tattausa lafazin su , jikinta sanyi yayi domin tasan duk abubuwan daya lissafo bata yin su ,


zanyi k'okarin koya domin ina son mutan kauyen nan suga canji a tare dani,bama kaman Baban Jummai da Maman Jummai da fara'a tayi maganar murmushi yayi tareda cewa ki shiga kinga dare ya soma kai ba zaka shiga ba ? D'an murmushi yayi sannan yace Karima ai bana fad'a gidan mutane ba tareda izinin suba ki shiga idan sun buk'aci shugowa ta zan shugo , gyara mata zaman mayafinta yayi ,saina jiki zan jira a mota and please ki kawo mun Sa'ada toh ta ansa masa tareda fara tafiya,d'aurewa yayi baiyi dariya ba domin sosai taso bashi dariya yadda take tafiya ita a dole ta zama y'ar birni.


Da sallama ta shiga gidan nasu ,babu kowa tsakar gidan, d'aga labulan d'akin Mama tayi ,zaune ta hango ta ,tana ta fama d'aura kuka a leda , fad'awa d'akin tayi tareda rungume Mama ,cikin sakin fuska had'i da mamaki Mama tace daga ina Karima bata sami damar bama Mama ansa ba Maman Jummai ta fad'o d'akin salati tasa tareda kama baki badai guduwa kika yiba , saurin tashi tsaye tayi tareda gaishe da Maman Jummai ,ri'ke gaisuwar badai guduwa ki kayi ba bata jira ansar Karime ba tayi waje kuka Maman Jummai ta saka tareda fad'awa d'akin Baban Jummai zaune yake saman tabarma kud'i a gabansa sai faman lissafi yaki ,lafiya ya fad'a cikin nuna damuwa wallahi Baban Jummai zuwa gidan kaso ya kama ka domin ga y'ar banzanr yarinyar can ta gudo ,cikin tashin hankali ya fara tattara kud'in sa .

A can cikin d'akin Mama kuwa kallon tuhuma Mama tayiwa Karime ,Mama ba gudowa nayi ba hasalima tare muke dashi zaro idanuwa waje Mama tayi sannan tace mijin naki ?

Eh Mama yana waje , fad'owa Baban Jummai yayi cikin d'akin ,ba tareda yace komai ba ya kama kunnen Karime muje waje dan ubanki naji dalilin dayasa kika kasa tsare mutunci ubanki ,shegiya mai farar k'afa ,waje ta jata sosai kunnenta ke mata wani irin zugi wato bak'in ciki kike mana kada muci arziki daga sama , d'an Allah Baban Jumma ka ri'ka bincike akan abunda aka fad'a maka cewar Mama ,rufe mun baki munafuka yanzu haka da saninki ta gudo d'aga kai Karime tayi tana kallon Mama ,Mama Jummai kuwa shewa ta saka sannan tace eh mana bakinciki ne taga ko baka mata sisi ba ,kuka Karime ta fara ganin yanda Mama ke hawaye ,maza Maman Jummai ban dorina domin yau sainaga ubanda ya tsaya mata badai hassada kike da kwanciyar hankalina ba , kina son ganina gidan kaso koh toh yau d'innan naga mai kwatarki .


A kan idanonsa ta shige gida ajiyar zuciya yayi tareda sakin murmushi ,kiran Sadiq ne ya shugo,na kira na fad'a maka Abba ya iso and he asked of you kayi k'okarin dawowa gida da wuri kasan dai dokarsa ok man ba zan manta ba a hasale Ramadan yayi maganar sosai Sadiq yayi dariya,tunda old Man na gari ai dole bya 9:00 mu bayyana gida ,ni wallahi a yau d'innan ma ina da wurin zuwa ,akwai wata Beb da zamu had'a tsaki Ramadan yayi tareda katse kiran domin Sam baya son jin wasu labarai akan y'an matan sa,


jinta shuru ne yasa ya kira wayar ta, tsaye take tana kuka gefen ta Mama ita ma kukan take domin ba karamar biyayya takewa Baban Jummai ba duk da ba gani yake ba duk yanda taso ya bata dama tayi magana yak'i k'arshe cewa yayi idan ta sake tace wani abu yau d'innan saita bar masa gidansa ,cikin mugunta Maman Jummai ta mi'ko masa dorina , ringing d'in wayarta tane ya mayar da hankalin su kanta , zaki daga kiran ko saina shemeki cewar Baban Jummai ,yanzu haka mutan gidanne ke kiranta sun gane ta gudu , 


d'aga kiran tayi Karima na jiki shuru kasa magana tayi ,jan majina kad'ai ta iya saurin fitowa daga motar yayi domin jikinsa ya bashi akwai wani abu , takawa yayi zuwa bakin d'an k'aramin gidan su , hello kina jina Karima bashewa tayi da kuka domin Maman Jummai tsula mata dorinar tayi saurin shiga zauren su yayi daga cikin zauren ya hankota tsaye ta juya masa baya , yarinya dan kin samu an taimaka miki da har yanzu kinan babu ubanda zai aure ki duk da auren naki na dan lokaci ne shine zaki gudo sabida bak'in ciki , a duk akuyen nan babu budurwar mai shekarun ki sosai Maman Jummai ke binta da bakaken maganganu kuka take sosai dorinar Maman Jummai ta tsula mata 


,kasa d'aurewa yayi kiran sunan ta yayi tareda shigewa gidan ,da kallo suka bishi direct wajen ta ya nufa babu kunya ya rungumo ta jikinsa baki sake suka bishi da kallo Karime yaushe kika fara bin maza Maman Jummai ta fad'a hannu saman ha'ba k'ara volume d'in kukan tayi jinta a jikinsa sosai ta saki baki tana kuka shafa bayan ta ya shiga yi alamun rarrashi , kai daga ina zaka fad'o gidan mutane cikin hayagaga Baban Jummai ke magana tana rungume jikinsa yace nine mijinta zaro idanuwa Baban Jummai yayi tareda saurin mi'ko masa hannu suyi musabaha a bangaren Maman Jummai kuwa kasa cewa komai tayi sai uban zara na mujiya take ,Mama kuwa tunda Ramadan ya shugo tayi saurin komawa d'akinta domin Karime ta fad'a mata tare suke .

zareta daga jikinsa yayi d'aga kai yayi yana bin gidan da kallo su Baban Jummai kuwa bin sa da ido suke wurin da zata zauna yake nema bayan Maman Jummai ya hango wani katon icci kama hannun ta yayi zuwa wurin zaunar da ita yayi saman iccin slowly ya duka kissing forehead d'inta yayi tareda share mata hawayen fuskar ta ,wato Maman Jummai baki ta saki tana mai kallon ikon Allah , Baban Jummai kuwa dadi'yaji domin inde wannan ne mijim tabbas yasan kud'i kaman akwai su kaman m suyi magana kenan yanzu aka fara wasan saurin boye murmushin sa yayi domin baya so Maman Jummai ta gane .

Wurin Baban Jummai Ramadan ya nufa do'kawa yayi har k'asa ya gaishe da Baban Jummai ,Baban Jummai kuwa kasa boye fara'ar sa yayi dan shifa a yanzu ya manta da wata Maman Jummai cikin saki fuska yace ashe tare kuke Eh tare muke Ramadan ya fad'a cikin girmamawa , tashi hakanan yaron kirki cikin kunya Ramadan yace ina Maman Karima ? Tana cikin d'aki Baban Jummai ya bashi ansa mi'kewa yayi yana bin bayan Baban Jummai da sallama ya shiga d'akin zaune take har ta saka hijab a jikinta , cikin kunya suka gaisa da ita ,a bangaren Maman Jummai kuwa baki sake ta bisu da kallo , mi'kewa Karime tayi tareda bin bayan su kusada Mama ta zauna saman tabar ma Ramadan kuwa daga bakin k'ofa ya d'an tsugunna mutunen naku kuwa Baban Jummai gado ya haye yana mai fuskantar Ramadan , bayan sun gaisa fad'a musu dalilin zuwan su akan makarantar Karime ne suna buk'atar takardun tana gama secondary School ,Baban Jummai murmushi ya saki sannan yace ai matarka kace kana da damar da akanta bata ta'ba jin furuci mai dadi'ba a kanta awajen Baban Jummai sai yau ke maza ki d'auko takardun Baban Jummai ya fad'a yana mai binta da ido tashi yayi tareda nufar wata tsohuwar wardrobe ana ta d'auko duka takardun ta saka su tayi cikin jakarta ina su Sa'ada Ramadan ya fad'a da murmushi akan fuskar sa , suna gidan Jummai Mama ta bashi ansa fad'owa Maman Jummai tayi cikin d'akin cikin masifa tace uban me Jummai tayi ake kiran sunan ta aaa dama tambaya ake akan ina su Sa'adatu shine nace suna gidan Jummai Mama ta idasa maganar cikin shakku kallon Karime Maman Jummai tayi sannan ta saki shewa ashe baki san Jummai ta haihu ba kina nan kina auren haya kanwar ki har tayi haihuwa ta biyu, shekaru dai ja suke Karime tuni tsararra kin ki sun yi aure wasu ma yara hudu hudu gare su.

Shewa ta kuma sakawa sannan tace Karime sarkin bak'in jini ki sami lokaci kije barka gidan kanwar ki tunda Maman Jummai ta fara magana hankalin sana kan Karime kuka take k'asa k'asa, Mama kuwa d'ukar da kanta tayi Baban Jummai kasa magana yayi domin dama tsoron Maman Jummai yake mi'kewa Ramadan yayi tareda kallon Maman Jummai cikin sakin fuska yace in sha Allah zan kaita tayi barka , wurin Karime yayi , tada ta tsaye yayi tareda cewa please ki daina kuka ok sake fashewa da kuka tayi kama hannun ta yayi zuwa waje marfin mota ya bud'e mata tareda cewa please get in.


Shiga tayi tana mai k'ara volume d'in kukanta, kayan da suka siyo ya kira wasu matasa taimaka masa su kayi zuwa cikin gida ganin Ramadan ya doso hanya da kaya ni'ke ni'ke yasa Baban Jummai saurin komawa gida domin bayan fitowar su Karime biyo bayan su yayi , ba k'ara mar siyayya Ramadan yayi musu ba bayan sun gama shigar da kayan kud'i ya bama su Baban Jummai addu'a kuwa yasha ta wajen Baban Jummai cikin kunya ya bama Mama nata kason Allah sarki Mama sosai tayi masa godiya .


Yanda ya barta haka ya tarra da ita kuka take kaman ranta zai fita,zama yayi tareda rungumo ta jikinsa , zuciya ta ciwo take mun Mijin Sa'ada, na kasance mujiya mutane basa son ra'ba ta , maza basa sona duk fad'in kauyen nan babu namijin dake Sona ,kasa cewa komai yayi sosai take jin kukan ta cikin ransa sun dad'e cikin motar daga bisani ne ya fara driving ganin bacci ya d'auke ta , around 10:55 ya isa gida direct part nasu ya nufa , d'aukar ta yayi zuwa cikin gida kwantar da ita yayi baya son ta tashi , cikin rashin sa'a kuwa bud'e idanuwan ta tayi mijin Sa'ada ta furta tareda dafe kanta ,zama yayi tareda cewa matata please ki manta abunda ya faru k'asa tayi da kanta lafiya Karima ?

Wanka nake son yi ta fad'a tana k'okarin sauka ,taimaka mata yayi zuwa toilet ,bayan fitar sa kuka ta saka ,a kitchen ya shiga domin saman masu abunda za suci .

Lokacin daya shugo bedroom d'in bata fito ba , bedroom d'inta ya shiga tareda d'auko pant da pad ,bayan ya saka pad d'in a jikin pant nata ajiye mata yayi saman bed yanda zata gani, fita yayi zuwa part d'in Abba..


Lokacin da ta fito murmushi tayi ganin sa'kon mijin Sa'ada, shiryawa tayi cikin night gwon mai d'an tsayi da kauri batada tsaraici ko kad'an iya kwaiwar ta ta tsaya. 


Kwanciya tayi tareda tunano bakabken maganganun Maman Jummai ,da sallama ya shugo d'akin hannun sa d'auke da abinci ajiye abincin yayi , tunani kike again murmushi tayi sannan tace mijin Sa'ada na'am Karima nagode da hidimar ka akan iyayena ,kina jin yunwa kai ta gyad'a alamun eh ,da kansa yake bata abincin a baki sosai taci kun san Karime bata wasa da cikinta kasancewar dare ya soma indomie biyu ce ya dafa masu amma saida ta take ta tas ruwa ya bata bayan ta shane murmushi yayi sannan yace aje ayi brush koh zun'buro baki tayi kafun ta tashi zuwa toilet .

A bangaren Ramadan kuwa wanka ya samu yayi sosai yake jin gajiya , kwanciya yayi kusa da ita saurin share hawayen fuskar ta tayi tareda k'okarin sauka daga saman bed d'in ri'ko hannun ta yayi tareda cewa ina zaki?


Zan koma d'akina acan zani kwana ,bakya son kwana wuri d'aya da nine Umm? Share hawayen fuskar ta tayi sannan tace akwai tunane tunanen da nake son yine , tashi yayi zaune tareda jawota jikinsa rad'a mata yayi please can you share your pain with me meke damun ki please cikin yanayin kuka tace wai meyasa banida Sa'a a rayuwata nid'in kaman mujiya haka neke , k'ara matse ta jikinsa yayi sannan yace you are special Karime duk wanda yace bak'in jinine dake bai sanki bane d'ago kai tayi tana kallon sa , murmushin takaici tayi sannan tace babu wanda ya ta'ba cewa yana sona a rayuwa ta ,age mate nawa tun muna age of 15 suka yi aure,yanzu haka kusan yaransu 4 , Jummai kanwata ce sosai domin na bata wajen shekara 5 amma har tayi haihuwa biyu, gyara masu kwanciya yayi sosai ya rungumo ta jikinsa cikin wani salo yace had it been you are not on your red days da mun sami baby a yau d'innan bata gane turancin nasa ba sabida haka cewa tayi nice baby murmushi yayi sannan yace kina son baby sosai ?

Aaa ni gaskiya ba zaka kirani da suna baby ba d'an murmushi yayi sannan yace ina nufin kanwa ko kanin Sa'ada sai yanzu ta gane me yake nufi saurin runtse idanuwan ta tayi domin wannan al'amari ya girma tunanin ta .


Toh readers mu had'u next page.


Please

Comments

Vote

And follow the Author.


More comments more typing 

More voting more typing.